Kishiyar Uwa Complete Book Hausa Novels by Nussad.txt

Author :  Nussad Category :  GNOVELS

Chapter   3 / 14

6K to 9K   out of 39.3K words

ta ke yaji kanshi yana juyawa , wanka ta jashi yayi, a hakan dai ta bashi wannan abinci ya ci , kana ya fada mata kanshi na yin ciwo zai kwanta rakashi tayi har sai da ta tabbatar da ya kwanta sannan ta fito daga ɗakin ta, fita tayi daga gidan domin sanar da k'awarta halin da ake ciki.


Har bayan magariba bai tashi ba har Asabe ta dawo daga gidan Baraka , sannan ya tashi daga baccin , zuciyarsa yaji ta b'aci gaba ɗaya yaji auren da ake shirin yi masa ya fita a ransa , yaji ya tsani yarinyar gabaki ɗayanta, haka ya kwanta ransa na b'aci, ko da gari ya waye mahaifinsa ya kirashi bai je ba , har aka kwana uku bai je ba , kai auren ya taho dangin sa nata harkokin biki amma shi banda shi, dan haka mahaifinsa ranshi ya b'aci yayi niyyar zuwa har gida ya same shi.


Da wata ranar talata lokacin saura kwana biyu a ɗaura auren mahaifin nasa yayi dirar mikiya a gidan, faɗa ya rufe shi dashi, sosai shi kuwa ko a jikin shi ,sai ma duban mahaifin na sa da yayi yace masa shi ya fasa auren daskarewa mahaifin nasa yayi abinda bai taba ji ba , juyawa yayi ba tare da yace komai ba ya tafi gida cike da damuwa, ko da ya sanar da matan nashi sosai su ka ɗauki zafi akan haka, amma da yayi musu bayanin yadda zasu fi ganewa su san ba laifin sa ba ne ba, sai su ka daina hargagin da su ke yi , a haka aka bawa iyayen yarinya hakuri abin ka ga k'auye gari fa ya ɗauka aka yi ta ƙananan maganganu, daga baya komai ya lafa, ita kuwa data ga haka sai ta saki jikinta tayi ta iya shegen ta abin ta , ta kuma mai da zuwa wajen boka sha yanzu kamar masallaci, mahaifinsa ya nema masa ak'alla yara sunyi biyar tana wargaza auren daga baya mahaifinsa ya hakura ya zubawa sarautar Allah idanu, yayin da tsanar Asabe ta dawo sabuwa a zuk'atan matan gida da yaransu .



Yanzu shekarar malam Iliya goma da aure , batun gwagwarmayar da ya sha , a harkar sana'arsa da rayuwar auren sa da Asabe Alhamdulillah, komai ya kankama ya samu rufin asiri sosai , babban abinda ke damunsa shi ne rashin haihuwa domin a wannan cikin shekarun aminyar Asabe Baraka ta haihu namiji aka sanyawa d'an nata sunan mahaifinta wato Adamu, a wannan shekarun mahaifin malam Iliya ya sanya ana tayiwa d'ansa addu'ah akan Allah ya dawo masa da d'ansa daga Sharrin matarsa Asabe, Allah kuwa ya amsa addu'arsa da ya dade yanayi.



A garin yawon fatauci, wata rana malam Iliya fatauci ya kaishi zariya , bayan ya gama komai yana shirin dawowa gida a nan Allah ya haɗa shi da mahaifiyar Fatima wadda ake kira da maimunatu ta kasance haifaffiyar garin zariya ce , sosai ya yaba da hankalinta , bai yi mata magana ya bita gidansu ya tambayi izinin neman aure mahaifinta ya amince , amma ya faɗa masa shi fataucine ya kawo shi zariya , shi haifaffen garin kano ne, ya kuma tambaya akan in ya tashi dawowa, magabatan sa zasu zo nema masa aurenta , a haka suka rabu badan junansu sun so ba , ko da ya fad'awa mahaifinsa yayi murna sosai ya faɗawa matansa amma yayi gargadi mai kyau akan kar wanda ya fitar da zancen, haka kuwa aka yi aka ɓoye maganar har sai da biki ya rage y'an kwanaki, amma Asabe bata da labari.


Alhamdulillah lallai rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya , domin kuwa a ranar jumaah ne aka daura auren malam Iliya da maimunatu mahaifiyar Fatima , mace mai hakuri da kawaici , mahaifin malam Iliya shi yayi komai na auren. Sai ranar da aka daura auren sannan Asabe taji , ranar ansha bala'i domin kuwa gidansu malam Iliya ta tafi ta dinga yi musu hauka amma ba wanda ya kulata ta k'arashe rashin mutuncin ta tayi gida kamar mahaukaciya, ta koma a ranar , ko da ta koma gidan bai kulata ba ta ƙarasq wulakancinta ta hakura .

Dare nayi 'yan kawo amarya suka kawota aka a jiye ta a ɗakinta suka mata fad'a sosai , aka ce a kirawo Asabe domin a musu fada amma ta aika musu sak'onnin zagi ba arziki su ka tattara yanasu yanasu su ka yi waje cike da Allah wadai akan halin Asabe , aka bar amarya a cikin gidan mijinta .

Sai muce Allah ya bada zaman lafiya , ya kauda fitinar Asabe amin.



Godiya mai tarin yawa a gareku yayata y'ar uwata wato Usaina musa saleh bisa ga gudummawarki gareni Allah ya taimakeki a aikinki ya bada sa'a amin.



Godiya a gareku yan moonlight writer's association Allah ya k'ara had'a kawunan mu amin ya taimakemu amin , ina godiya sosai.


Please🙏🏻
Share
&comments

To be continue........



🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿

🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸
(True life story)

🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/


*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Ina k'ara godiya ga Allah subahanahu wata'ala da ya kara bani damar ci gaba da littafina na kishiyar uwa, kuma ina godewa mahaifana da y'an uwana da suka jajirce wajen ganin na ci gaba da rubutu na , haka ma fan's nawa ina kara godiya.

🥰😍 ina ganin comments kuma inajin dadi sosai wallahi.

Sadaukarwa ga duk makaranta littafin nan tare da y'an moonlight writer's association, Allah ya k'ara hada kawunanmu amin y Allah .

Shafi na 6️⃣
Aka bar amarya gidan mijinta , da dare yayi sosai abokanan ango suka rakoshi , amma fafur Asabe ta k'ek'asa k'asa ta hanasu shiga gidan, ban yadda suka iya haka suka koma , suka yiwa malam Iliya fatan alkhairi shi ma yayi musu sallama sannan suka tafi , shi kuma ya shiga cikin gida aikuwa yana shiga ta ce da wa Allah ya had'ani in ba dakai ba ta shiga yi masa ruwan bala'i amma yayi mata banza wannan ya k'ara kular da ita sosai , ya juya zai tafi tayi sauri ta rik'e masa wuyan rigarsa ta baya , a fusace ya juyo ya sauke mata wani wawan mari a kuncinta wanda saboda tsabar razana da mamaki sai da ta zube k'asa , ni kuma da nake tsaye ina kallon abinda ke faruwa dariya nayi a hankali saboda kar masifar ta dawo kaina, amma ke ma Asabe in banda tsaurin ido ta yaya zaki rikewa sabon ango wuyan riga ki hanashi shiga d'akin amaryarsa abinda yafi haka ma zaki gani🥴 , saboda duk rashin mutuncinta bata tab'a rik'e masa riga ba da sunan rashin kunya sai yau , tana a zaune kafin ta dawo hayyacinta har ya shige d'akin amaryarsa Maimunatu sai rufe k'ofarsa taji garam aikuwa da sauri ta zabura kafin ta k'arasa har ya sanya sakata , sai dai muce asha amarci lafiya malam Iliya😍. Asabe kuwa kwana tayi tana hauka a tsakar gidan in ta gaji ta zauna in suka motsa mata tayi ta buga musu k'ofa haka ta kwana bata runtsa ba tsabar masifa.

Washe gari da safe kuwa suna fitowa suka ganta a zaune a tsakar gidan rana d'aya duk ta lalace , saboda masifar kishi , aikuwa tana ganin sun fito haka ta nufi maimunatu da itace sauri yayi ya kareta tare da watsawa Asabe mari ni kuma abin nema ya samu matar direba ta haifi mota ina kallon ta ina mata gwalo amma bata ganni ba ta juyo kenan b'arina ni kuma na fece🚴🏻‍♀️ a miliyan, a ranar haka ta hanasu sakat a gidan ya zamana ko ina maimunatu zata shiga sai dai malam ya rakata , a haka ta dinga rayuwa har malam ya koma da sana'arsa wato fatauci , aikuwa gida ya zamar mata kamar birsin dam ma iyayen malam da k'annensa suna sonta shi ne abin ya zame mata da sauk'i .


A lokacin da suka cika wata biyar da aure Allah ya azurta maimunatu da samun ciki zo kuga murna gurin malam Iliya , rana samun kulawa sosai , tunda Asabe taji maimunatu na da ciki shikenan fa hankalinta ya tashi abinda take ta gudu gashi ya faru , da sauri ta garzaya gidan aminiyarta baraka , a tsakar gida ta zube had'e da dafe kai " na shiga uku ni Asabe Baraka tawa ta k'are a gidan malam " ta fad'a cike da tashin hankali " nutsu kiyimin bayani" cewar Baraka wadda ke yiwa Ado wanka a lokacin yana da shekaru takwas da haihuwa," wai wachchan matsiyaciyarce keda ciki " a razane Baraka ta dubeta da gaske kikeyi mun shiga uku , to yanzu menene abin yi "? Ta tambayeta " to ai nima shi nake nema shiyasa na zo gurinki " bara na gama shirya Ado " ta ce tana kokarin tashi" to kawai Baraka tace domin kuwa hankalinta ba'a jikinta yake ba , rana gama shirya shi ta barshi a gida suka dauki hanyar wajen boka , sunyi masa bayani a cikin bayanin kuwa har da son haihuwar da Asabe ta ke son tayi yace musu zai fara ba ta haihuwar kafin nan , aikuwa a take ya sanya aljani ya shiga jikinta a take a wajen ta samu ciki sannan yayi mata alk'awarin sawa malam kiyayyar maimunatu da abinda ta haifa godiya sukayi masa sosai suka tafi gida .

Bayan kamar wata biyu da samun cikin Asabe ya bayyana malam yayi murna sosai na tunanin Allah ya dubeshi lokaci guda ya bawa matan sa ciki , a koda yaushe ya kanyi addu'ar Allah ya saukesu lafiya , a b'angaren Asabe kuwa burinta ta haifi namiji kullum burinta kenan, ana cikin wannan yanayin mainmunatu ta fara fuskantar matsala wajen malam gashi cikinta ya farayin nauyi , tsangwama sosai take sha wannan alamu ne na Cesar boka ya cika aikinsa, ana cikin wannan rintsin Allah yayiwa malam mahaifin malam Iliya rasuwa bayan gajeriyar jinyar da yayi Allahu Akbar giwa ta fad'i aikuwa anayi rashi ba Kad'an ba , gashi a wannan lokacin sosai aikin boka ke ci saboda tun iyayensa basu gane ba da 'y'an uwansa har suka gane sosai iyayensa sukayi masa fad'a amma abu kamar tiri , sai ma gaba abin yakeyi ,.


Bayan wasu 'yan watanni da rasuwar malam lokacin cikin maimunatu ya tsufa sosai gashi ba kwanciyar hankali , wannan ya sanya ta rame ta lalace , tayi bak'i , abin tausayi ga ba kulawa daga wajen miji sun rigada sun maidashi rak'umi da akala bayajin maganar kowa sai ta Asabe, Allah ya taimaki maimunatu kannensa na zuwa ta tayasu hira dan haka sai damuwarta ta ragu sosai, ana wannan yanayin ciwon nakuda na kamata ga malam baya nan , ciwo takeyi sosai tun dare har safiya amma Asabe na jinta bata koda lek'a ba , ita a burinta ma kawai maimunatun ta mutu kowa ma ya ana cikin haka Allah ya jefo da hadiza k'anwar malam din aikuwa tana ganinta cikin wannan halin ta juya ta sanarda mahaifanta aikuwa basu dade da zuwa ba Allah ya sauketa lafiya ta samu d'iyarta mace masha Allahu yarinya son kowa kyakykyawar sosai, kowa in ya ganta sai ya kara kallonta saboda tsabar kyau, a lokacin da Asabe taji anyi haihuwar an samu mace murna tayi sosai da sosai a ganinta ita zata haifo namijin , haka akayi suna malam bai dawo ba k'anin malam din shi ya sanyawa jaririya sunan mahaifiyar maimunatu yarinya taci suna Fatima, komai y'an uwan malam sukayi saboda yana chan harkar fataucinsa, ko da ya dawo bai wani nuna murna sosai ba duk kuwa da abinda yake nema shiya samu , haka dai rayuwa tayi ta yin juyi da rayuwar Maimunatu da yarinyarta Fatima cikin rashin kulawa da k'unci , bayan watanni hud'u Asabe ma ta haifi d'iyarta mace bataso hakn ba amma kuma ba yadda ta iya lokacin malam yana nan dan haka zo kaga murna da farin ciki ba kama hannun yaro , ranar suka aka sanyawa yarinya zainabu , anyi shagali sosai , a haka rayuwa tayi ta tafiya har Fatima tayi shekara d'aya ko tsakar gida basa iya fitowa, a sannan ne Asabe it a da k'awarta sukayi mata asiri akan in ta tafi karta dawo gidan a lokacin ne aka aika mata da zancen mahaifinta bashida lafiya , da kyar aka barta ta tafi da sharad'in bazata tafi da Fatima ba haka ta barwa mahaifiya malam iliya ta tafi, cike da kewar yarinyarta, Allahu Akbar a hanyarsu ta tafiya Allah ya aiko da wani gagarumin hatsarin motar da maimunatu take ciki tayi hatsari mutane da yawa sun rasu Allahu Akbar Allah ka jik'an musulmi amin, a lokacin da labarin hatsarinsu ya Shiva cikin k'auyen ba k'aramin tadawa mutane hankali yayi ba da kuma aka sanar musu da cewa ba Wanda yayi rai a cikin matafiyan lallai mutanen k'auyen sunji rasuwar tata musamman ma y'an uwan malam dashi malam din , amma Asabe a lokacin ne ma duniyarta ta koma sabuwa ba ta da wata damuwa a haka har aka karaci alhinin rasuwar akabar masu rashi da rashinsu.

Bayan kamar data biyar a lokacin Fatima tayi wayo sosai dan haka Asabe ta takura da sai an kawo mata ita ai itama mahaifiyarta ce da kyar iyayen malam suka bada ita, to fa tun lokaci ta fara zan wahala har kawo yanzu ba wanka ga aikin da yafi karfinta shi ake bata tunda ta tashi bata san mecece kulawa ba duk kuwa da 'yan uwan malam na k'ok'ari amma wani lokacin basu ma San anayi ba , babu irin rayuwar da Fatima bata gani ba a gurin KISHIYAR MAHAIFIYARTA data baya da abin ya fara sakinsa sai ya bar harkar fatauci ya koma gona don ya dinga kulawa da yarinyarsa haka kuma suka rufe masa baki ta yadda bazai tab'a fad'awa Fatima labarin mahaifiyarta ba. Wannan kenan


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
(ASALIN LABARI)
Kwata kwata malam bayajin dadin rayuwar da d'iyarsa ke ciki , gashi yanzu yana halin rashin lafiya mai tsanani ga tsufa ya kamashi, gashi a yanzu ne yarinyarsa take buk'atar kulawa a gareshi .

Ranar wata Asabar da safe baraka ta je wajen Asabe , da zancen auren Fatima da Ado tunda ya matsa mata , da sauri Asabe ta amince ga bisa la'akari da tayi na ganin y'an birni in dai sun shigo garin suka d'ora idanunsu akanta su ce suna San ta , iya kuma ba kowa tayiwa burin auren irin wadannan ba sai Abu , ta sanar da ita babu damuwa , amma sai da su ka sanya aka kulle musu bakin malam din , aikuwa tana fada masa ya amince duk da zuciyarsa bataso amma haka ya yadda, lokacin da ya sanarda Fatima bata mu da masa ba duk kuwa da babu Wanda ta tsana a duniyar nan sama dashi,sosai ake tayin shirye shiryen biki , a wannan lokacin ciwon malam yayi tsanani.



Ranar wata Asabar bayan Fatima ta dawo daga tallah, sallama tayi a d'akin mahaifinta ya amsa mata muryarsa na karkarwa saboda ita kadai ke kulawa dashi , "Fatima ki yafemin na miki laifi na hadaki da wanda bakya so nasan ban kyauta ba amma ina ganin gwara haka fiyeda ki zauna cikin bak'in ciki , sai maganarsa ta katse numfashinsa yana kai kawo chan kuma sai taji shiru , aikuwa da gudu ta fita tana k'walawa inna Asabe kira ," Inna! Inna! Inna kizo wallahi baba ya rasu mun Shiva uku" da gudu Asabe ta fito ta nufi d'akin malam din abirkice dan ganewa idonta meya faru........

Godiya ta musamman gareku masoyana ina fatan kuna cikin k'oshin lafiya kuma zakuji dad'in karatu , ayi karatu lafiya.


Luv u all my dear fan's😍😍


Please🙏🏻
Share
&Comments

To be continue...........




🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿

🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸(True Life Story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸



GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DAYA BANI DAMAR CI GABA DA RUBUTUN LITTAFINA , MAI SUNA KISHIYAR UWA .


GODIYA TA MUSAMMAN GA Y'AN MOONLIGHT WRITERS ASSOCIATION, ALLAH YA K'ARA HAD'A KAWUNANMU AMIN

GODIYA TA MUSAMMAN GA Y'AN UWA NA DA ABOKAN ARZIKI.

GODIYA TA MUSAMMAN GA FANS DINA , DAMA FANS DIN LITTAFIN KISHIYAR UWA, INA GODIYA SOSAI, INA FATAN ALLAH YA BANI DAMAR KARASA ISAR DA SAK'ON DA NAKESO NA ISAR , KUMA BANA FATAN NA BAKU KUNYA .


MASU TURO DA COMMENTS INAJIN DADIN HAKA.

INSHA ALLAHU YANZU MUKA NUFA CIKIN LITTAFIN GADAN GADAN , INA FATAN ZAKU BIYONI DOMIN JIN MAI YAKE SHIRIN FARUWA.


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
SHAFI NA7️⃣-8️⃣

Koda inna Asabe ta k'arasa cikin d'akin , ganin halin da malam yake ciki ya sanya ta zunduma ihu tana kururuwa , Abu ce ta fito daga d'akinta cikin yatsina fuska tana duban Asabe cikin gadara " wai ke inna ki damu mutane da sanyin safiyar nan baki ganin mutane suna yin bacci", galala Asabe ta tsaya tana kallon Abu cikin ido kana ta dubeta " yo ke dan k'aniyarki kina ganin mahaifinki cikin wani hali amma kuma kika tsaya kina yiwa mutane zancen banza" "ni dai gaskiya ana takuramin wallahi " ta fad'a ta komawa cikin d'aki ta banko k'ofar d'akin, maganar Fatima ce ta dawo da ita cikin hayyacinta " inna bari na duba in baba muhammadu yana nan "( kanin malam iliya ) , bata jira me zatace ba ta fallah da gudu ta bar Asabe na sallallami had'e da tafa hannaye.

Ba'afi mintuna biyar ba sai gasu sun shigo cikin azama , kanin nasa ya shiga cikin d'akin da sauri dan ganin me yake faruwa, da Sauri ya dawo ya dubi Asabe "maza shiryashi asibiti zamu kaishi har yanzu da sauran ransa " wata ajiyar zuciya Fatima ta saki kana ita kuma Asabe ta shiga domin shirya shi .

Baba muhammadu ne ya shigo shi da samari biyu suka taimaka masa suka Sanya malam a cikin mota , domin tafiya da shi asibitin , Fatima ta k'ekasa k'asa akan tanason zuwa amma Asabe ta hana ta haka tanaji tana gani aka tafi da malam asibitin.


Ko da suka k'arasa basu samu wata matsala ba aka shigar da shi d'akin da za'a dubashi , an dubashi anan aka gane yawan tunanin da yakeyi da kuma wani abu da ya ajieshi a ransa ya haifar masa da ciwon zuciya mai tsanani, sosai wannan maganar ta razana k'anin nasa, haka ma Asabe ta girgiza da wannan maganar , ita bama wannan

3 / 14