Kishiyar Uwa Complete Book Hausa Novels by Nussad.txt

Author :  Nussad Category :  GNOVELS

Chapter   8 / 14

21K to 24K   out of 39.3K words

da ya k'arasa gidan ko takan LAILA bai bi ba ya kwanta . amma ne fafur bacci yak'i zuwa, ransa ya kai mak'urar b'aci , minti bayan minti sai ya juya yayi tsaki , to shi menene ma zai dameshi dan ta fita, ni kuwa nace muje zuwa malam yallab'ai Alhaji Ahmad, hhhhhhh. sai da tsakar dare sannan ya samu bacci ya d'aukeshi, bayan ya gama tunane2sa ko na menene oho🥴

A b'angaren LAILA ma gajiya tayi da jiranshi , ganin bai dawo ba sai kawai ta kwanta ita ma , kasancewar ita ba ta damu da damuwar wani ba ta ta kawai ta sa ni.........



DANALLAH A DINGA YIMIN SHARING NA BOOK DIN NAN PLZ👏🏻

Please
Share
&
Comments



To be continue........


🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿

🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸

(True life story)

🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸



CHAB ANA WATA GA WATA GASKIYA BAZAMU LAMINTA BA ACE KHAF BABU MASOYAN LAILA INA, AI MU GASKIYA MUNA BAYAN LAILA 100%.


HMMM SISTER BABU RUWA NA IN KIKA HAD'U DA FANS D'IN FATIMA , ZAKIYI BAYANI🥴😝

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/


*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

SHAFI NA 25_26

Washe gari da safe ko fitowa baiyi ba, saboda rashin baccin da ya samu jiya, LAILA kam koda ta fito ta tarar bayanan a zatonta ya fita hakan ya bata damar ficewa daga gidan bayan ta barwa Aisha mai girka musu abinci sallahu, akan abinda zata girka musu.

A chan b'angaren Fatima ma bata fito ba sai wajen k'arfe goma na safe , Mummy bata taso ta ba kasancewar tayi tunanin ko unguwar da taje ne ya sanya bata tashi da wuri ba, batasan al ' amarin da ya faru ba , tsakanin yaran nata guda biyu, bayan Fatima ta tashi sai da tayi wanka duk da fuskarta a d'an kunbure take hakan bazai hana mutum ya gane taci kuka ta k'oshi ba, da sallama ta shiga d'akin mummy , " yauwa haba daughter, ina ta tunanin ko lafiya yanzu nake shirin in tashi inje in duba ki , mummy ta fad'a tana k'ok'arin juyawa saboda dama ta bata baya tana kallo cikin d'akin ", juyawa tayi jin Fatiman tayi shiru , " innalillahi lafiya ke kuwa naga fuskarki duk ta tashi , meye ya sameki , cikin kad'uwa Mummy ke fad'ar haka",sai a sannan Fatima tayi k'ok'arin bud'e bakinta sannan ta ce " Mummy kaina yakeyi min ciwo tun jiya da daddare, ta fad'a tana k'ok'arin kawar da k'wallar da ta taru a idanunta", janyota jikinta tayi sannan ta tambaye ta taci abinci girgiza mata kai tayi alamar a'a , umartarta tayi da taci abinci sannan ta sha magani da to ta amsa , sannan ta juya ta fita, ta nufi dinning area.

A chan b'angaren kuwa sai sha d'aya na safe ya farka , a lokacin baccin da yayi ya saukar masa da ciwon kan da ya dawo gida yanayi, toilet ya shiga yayi brush , yayi wanka , kasancewar yayi sallar asubah, ya sanya yana gama feshe jikinshi da turare ya nufi d'akin LAILA kasancewar duk a up stairs d'in yake, da sallama a bakinsa ya tura , amma ne yana shiga yaji shiru tsammaninsa tana toilet dan yaji zubar ruwa, amma kusan 20 minutes, babu wanda ya fita a toilet, dan haka ya k'arasa bakin toilet d'in ya k'wank'wasa , shirun da yaji ne ya tabbatar masa da bata ciki , aikuwa rufe band'akin yayi , baya ya kashe ruwan , sannan ya nufi down stairs, a k'asan ma dai bata nan , Aisha mai girka musu abinci ce , ta fito daga kitchen, da alamar ta gama aikinta zata koma masaukinsu na masu aiki, " am ina matar gidan , ya fad'a kamar ba shi yayi maganar ba", da sauri ta rusuna har k'asa ta gaidashi sannan ta shaida masa ta fita, gyad'a kai kawai yayi kasancewar ransa yakai k'ololuwar b'aci, ya rasa mai ya sanya LAILA har yau bazata chanza ba , nuni yayi mata da hannu alamar taje, dan haka ta tashi ta fita abinda , shi ma hanyar falon ya nufa, yana fita ko abinci bai nema ba, ya shiga motarsa , gateman ya bud'e masa , ya cilla hancin motarsa ya nufi gidan Mummynshi.

Fatima tana zaune tana cin abinci , duk da ranta bayaso kasancewar har yanzu bakinta ba appetite, da sallama ya shigo cikin falon , ba kowa a cikinshi , Fatima dake zaune tana ganinshi gabanta ya fad'i dan yanzu wani mugun tsoronsa takeji, shi kuwa bai ma kula da ita ba , gadan gadan ya nufi dinning area'n kasancewar yunwar da yakeji ga b'acin rai na fita LAILA bata tambaye shi ba, zama yayi k'ansa a k'asa, kamar daga sama ya tsinkayo muryarta na gaida shi, amsawa yayi sannan ya yi mata nuni da alamar ta zuba mishi abincin , aikuwa cikin rawar jiki shiga zuba mishi abincin , kunun tsamiya ne da kosai sai k'amshi tarugu yake yi , sannan farfesun hanta, sai kuma shayi Wanda tasan dole zai buk'ata, shi kuwa duk wani motsinta idonshi na kai , amma sai ya nuna kamar ma ba kallonta takeyi ba , hakan ne ya bata damar fecewa bayan ta gama zuba mishi abincin, da ido ya bita, kasancewar yanason yaga mai ya sanyata rawar jiki haka, da ya tuna kuma da abinda ya faru jiya murmushi kawai yayi, sannan ya fara cin abinci.
Bayan ya kammala a lokacin Mummy ta fito da shirin fita unguwa gaisawa suka yi sannan ya mata a dawo lafiya , har ta kai k'ofar falon ta juyo had'i da cewar " yauwa ka sanya k'anwar taka ta sha magani , batajin dad'i ", da kanshi kawai ya amsa sannan ta juya ta fita shi kuma ya kishin gid'a, ya fuskantar TV saboda anayin labarai.

Lokacin da aka kirawo sallah , hakan ya sanya ya nufi toilet d'in Mummy alwala yayi , sannan ya nufi masallaci, ko da ya dawo tana falo a zaune, sannu da zuwa ta mishi , ya amsa yana satar kallonta, " ki kawomin abinci nan, abinda ya fad'a kenan yana gyara zaman shi a jikin kujerar", cikin sauri ta nufi kicin d'in , da kallo ya bita kawai , ko da ta gama zuba mishi abincin, kallonta yayi had'i da cewar " ke kinci ne" kai ta girgiza alamar a'a , " kurma kika koma, ya k'ara jefa mata wata tambayar, " a'a kawai tace je ki d'auko chokali", bakinta ta motsa alamar tana son yin magana ganin ya had'e fuskarsa ya sanya ba musu ta d'auko, nuni yayi da ta sanya ciki , ta sanya sannan suka fara cin abinci, cikin nutsuwa take ci , shi kuwa gogan duk lomar da zata kai bakinta sai ya kalla, kwata kwata bata wani ci da yawa ba ta tashi alamar ta k'oshi , wani mugun kallo da ya zuba mata shi ya sanya dole ta koma ta zauna suka ci gaba da ci, bayan sun gama ya sanya ta d'auka magani , cikin ya mutsa fuska , ta zuba a baki ta kora da ruwa, sannan ta nufi d'akin ta .

A b'angaren LAILA kuwa, sai k'arfe biyar ta koma gida , ko da ta shiga , ganin Aisha a kicin tana girkin dare , hakan ya sanya ta tambaye ta ko ya dawo, anan ta shaida mata ai dama bai fita ba, sai bayan ta fita sannan ya fita, kasancewar LAILA y'ar duniya ce hakan bai sanya ta damu ba tayi shigewar ta d'akinta.

Sai bayan sallar isha'i sannan ya koma gida , bayan ya yi musu sallama , ya nufi hanyar gidanshi, ko da ya koma bai nunawa LAILA yasan ta fita ba, har tayi zaton ko Aisha k'arya ta mata , shi kuwa yana sane , amma ya share ta , saboda ya gane bazata shiryu ba, sai wani ikon ubangijin.

Ana cikin haka , aka koma makarantar su Fatima , sosai tayi murna da komawar ta su kasancewar ba wani Hutu ne sosai ba, ko da ta koma yallabai shi ya ci gaba da kai ta makaranta kafin a samu mai kaita , na musamman a cewarsa😝🥴😳.

Ranar Friday misalin k'arfe biyu a lokacin an yi sallah, ya nufi gidan na su, a falo ya samu Fatima ita kad'ai kasancewar Mummy ta fita tun safe, bayan ta gabatar masa da abinci ta juya zata nufi d'akinta , cikin d'aga murya ya kirawo sunanta , chak ta tsaya , " gurinki na zo ba gurin Mummy ba ina son , ki fad'amin gaskiyar ke wacece, saboda ina miki kallon wadda na sani amma kin k'aryata ni, ina jinki bismillah fara ", a sanyaye ta zauna , sannan ta fara bashi labarinta daga farko har k'arshe sannan ta d'ora da cewar ina son nayi karatu mai zurfi, duk da a baya jajirtaccen malamina yaso nayi, amma Allah bai nufa ba", " sannan kuwa wanene , har haka mai muhimmacin da bazaki manta dashi ba , ya fad'a ya na kallonta da son ta ba shi amsa ", nan ta zayyane mishi komai daga bisa tace" har yau har gobe ina mishi fatan alkhairi a rayuwarsa , saboda ya so rayuwa ta da ci gaba, ta fad'a a yayin da hawaye ya sulmiyowa fuskarta", " ko zan iya sanin sunan malamin ", abinda ya ce kenan,"" sunansa malam Ahmad " dam gabansa ya fad'i shikenan hasashen da yake yi ya zama GASKIYA , yau ga Fatima yarinyar da ya tafi ya barota a k'auye cikin wahalar rayuwa , Allah ya k'ara had'a su , yarinyar da tun lokacin da yaje bautar k'asa ya d'aura idonsa akanta yake k'aunar yarinyar tun tana y'ar k'aramar yarinyarta, cikin dashewar da rawar murya ya furta " da.. da....dama kece dama kece Fatima , Allah na gode maka..............

MASOYA YALLAB'AI AHMAD GAREKU🥰

Dan Allah a dinga yimin sharing na book d'in nan plz.👏🏻👏🏻


Please
Share
&
Comments


To be continue.....................

🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸

(True life story)

🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/


*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

INA GODIYA DA IRIN RUWAN COMMENTS DA KUKE TA ZUBA WA , INA JIN DAD'I SOSAI.

INA GANIN ADDU'O'INKU , MASOYA NA DA MA MASOYAN BOOK D'IN KISHIYAR UWA, ALLAH YA K'ARA DANK'ON ZUMUNCI AMIN.

SHAFI NA 27_28

Ita kuwa Fatima, kallonsa kawai ta tsaya tana yi , ta gaza fuskantar kalma d'aya daga cikin zantuttukan da yake yi, komawa tayi kamar wata sokuwa , idanu da hanci ta zuba mishi kawai tana kallon , shi kuwa zuba mata idanu kawai yayi kallon ikon Allah, " Fatima dama kece, dama , daman ni nasan , ina yawan ganin nasan fuskarki, ashe dama kece, Allah na gode maka, ya fad'a yana k'ara kallonta", " kingane ni, ni ne fa malaminki mai k'aunarki , malam Ahmad", da sauri ta d'ago kanta cikin razana da jin abinda yake fad'a, kuma da alama baya cikin hayyacinsa, domin tafi zaton sumbatu yake yi, " yallab'ai wai me yake faruwa ne, ta fad'a kamar zatayi kuka", kallonta ya tsaya yanayi cike da shauk'in k'ara ganinta a karo na biyu, " Fatima dama kina nan , nayi ta Neman ki sak'o da lungu , a lokacin da na dawo daga k'asar waje naso in zo in da kike amma ban samu dama ba , wayyo gsky Allah yana sona " , ita dai tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, gaskiya itama tayi ta tunanin inda tasan fuskar yallab'ai ashe shine mutumin da ya zamar mata garkuwa kuma jigo a rayuwarta da karatunta, hawaye taji yana k'ok'arin zuba a fuskarta , saurin sanya hannu tayi ta share hawayen da ya fito ta gefen idonta, " cikin rawar murya ta furta, uncle da..da..dama kana nan a raye, ta tambaya tana kallonsa ", gyad'a mata kai kawai yayi kasancewar ya kasa magana ma, suna cikin wannan yanayin Mummy ta dawo tun kafin ta huta Ahmad ya sanar mata wacece Fatima , sosai tayi mamaki , duk da haka ita ma Mummy na yi mawa Fatima kallon sani , chab k'ak'ak'ara k'ak'a, toh ita kuma mummy me take nufi oho.

Suna zaune a haka har magriba ta k'arato , hakan ya tursasa shi tashi ba dan ya so ba ya nufi masallaci, domin gabatar da sallah , su ma nufar toilet ko wacce tayi domin d'auro alwala.

Bayan sun idar da sallah , shi ma ya shigo , abinci su ka ci sosai ya shagalta da kallon Fatima kasancewar tayi girma, shi fa mamaki yake yi yadda ta zama cikakkiyar budurwa, Allah ya taimake shi ya k'ara dawo mishi da ita a karo na biyu, sosai ya ci abinci , sai da mummy ta tursasa masa sannan ya hak'ura ya nufi gidansa cike da farin cikin ganin Fatima.


Ko da ya k'arasa, cike yake da farin ciki, sama ya haura ya nufi d'akin LAILA, a kwance ya same ta a lokacin anyi sallar isha'i shiga cikin band'akin ta yayi, da idanu ta bishi sannan ta juya ta ci gaba da charting d'inta, fitowa yayi ya mata magana akan anyi sallah , nuna masa alamar zatayi tayi da kanta , shi kuma ya juya ya fita ya nufi masallaci.



A chan b'angaren Fatima , sosai ta shagalta da tunanin malamin na ta , kuma yallab'ai, lallai ya mata halarci, bayan ya tsaya mata a rayuwarta ta baya sannan yanzu ya mayar da ita y'ar dangi , ita kam dame ma zata saka mishi ne wai, tambayar da ta gaza amsawa kenan ta kwanta bacci aikuwa ba dad'ewa ya d'auke ta, cike da murnar ganin malamin na ta a karo na biyu.



Shi ma a nashi b'angaren, sosai ya gaza yin bacci , domin tsabar farin ciki, da ganin d'alibar ta sa, sai chan dare ya kwanta, LAILA ta yi mamakin ganin na sa , a cikin farin ciki amma kasancewar ta mai da damuwar wani ba na ta ba, ya sanya ta k'yaleshi kawai , a haka su ka yi bacci.


To fa shak'uwa sosai ta shiga tsakanin yallab'ai Ahmad da kuma Fatima , kullum zai zo in ya dawo daga aiki , ya zauna yayi ta tambayarta labarin bayan rabuwa, ita kuma tana bashi , wani yayi dariya wani yaji tausayinta , shi kansa ya gaza gane kansa game da ita, a farko ya d'auka tausayi ne amma daga baya kuma ya gane soyayya mai k'arfi yake yi mata, chab to fa fans din yallab'ai Ahmad gare ku😍😍.



Ana cikin haka kuma su Fatima suka gama aji biyu, kuma a wannan lokacin zata zana placement, wannan tsari ne daga yallab'ai, an biya mata komai sannan su ka zauna fara exam.

Masha Allahu sunyi exam , kuma Alhamdulillah , sun yi nasara , ita ma k'awarta Halima tare su ka yi , sosai ta yi murna ganin cewar tare zasu ci gaba da Halima.

A chan b'angaren Ahmad , kuwa sosai ya Sanya ayi masa binciken kakanin Fatima anyi sa'ar an samu Wanda ya san kakan nata amma kuma ya tafi fatauci legas sai bayan shekara zai dawo, sosai ya ji dad'in haka, kuma yana yin komai ne ba tare da sanin ita kanta Mummy ba ballantana kuma Fatima.



Achan b'angaren LAILA kuwa sosai hankalinta ya kwanta, ganin mijinta yanzu baya matsa mata wajen hanyar fita, don haka sai ta ranci na kare, kullum bata gida , daga gidan wannan k'awa sai bikin wannan k'awa, ni ko nace uhmmmm su LAILA manya a dai juri zuwa rafi tohm😝.



Suna zaune a falon mummy, Ahmad yana ta satar kallon Fatima, tana sane da kallon da yake bin ta dashi duk ta kasa sukuni , " uhmmmm Mummy please anjima inason daughter ta ki ta rakani unguwa , ya fad'a yana kallon mummy don jin me zatace "," Ina zaku je banason ka koyawa yarinya ta yawo bazata je ba,", " please mummy ba dad'ewa zamu yi ba, da kai ta amsa alamar ta yarda sannan ya juya ya kalli Fatima dake zaune , "ki shirya bayan la'asar , kafin na dawo abinda yace kenan sannan ya juya fita ita ma ta tashi ta shigewarta d'aki domin cika umarnin yallab'ai, kuma malami a gare ta , wato Ahmad............



Please
Share
&
Comments




To be continue.............


🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿

🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸

(True life story)


🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸


KU NA K'ARAMIN K'AIMI FAN'S, INA TARE DA KU NIMA, LUV U ALL 😍😍.



SHAFI NA 29_30

Mummy kuwa, bi Fatima tayi da kallo , tare da wani k'ayataccen murmushi , irin na su na manya wadda ita kad'ai tasan ma'anarsa, sannan ta girgiza kai , ita ma ta mik'e ta shige cikin d'akinta.



A b'angaren Fatima kuwa, tana shiga d'akinta wardrobe ta bud'e, tsayawa tayi tana duba kayan da zata sanya, rasa wanda zata saka tayi , saboda batasan inda za su je ba , sai da ta gama dube dubenta ,har ta mik'e zata kirawo mummy ta taya ta zab'ar kaya kawai sai ta hango wata marron color d'in doguwar rigar abaya , hakan ya sanya ta zaro ta , wadda taji stones kalar gold, sai siririn mayafinta, jaka da takalmi ta zab'o su ma kalar golden da agogo, sannan ta fad'a wanka , ko da ta fito sai da ta gama zafa lotion mai k'amshi sannan ta zura kayan ta yane kanta da mayafin rigar , takalmi ta zura sannan ta rataya jakar ta ta, ta feshe jikinta da turaren "Al' oud Al khalij", sannan ta nufi falon, tana fita yana shigo wa, da idanunsa masu rikitar da ita , a zuciyarsa ya furta masha Allahu , k'arar bud'e k'ofar d'akin Mummy ne ya dawo da shi daga duniyar da ya shiga , sannan ya k'arasa cikin d'akin ya zauna, " Mummy barka da fitowa , ya ce da ita ", sannan ya dubi Fatima wadda ta mak'e a jikin bango kamar zata shige " mu je ko , abinda ya furta kenan sannan ya yiwa Mummy sallama ya nufi hanyar waje" , ganin haka ya sanya Fatima ta bishi cikin hanzari, mummy ce ta musu a dawo lafiya , bayan ta sanarwa da Ahmad kar su kai dare, da toh ya amsa mata sannan ya k'arasa ficewa, ko da su ka k'arasa bakin motar da kanshi ya bud'e mata sannan ta shiga , shima ya zaga ya shiga su ka bar gida bayan gateman ya bud'e musu gate.



A chan b'angaren LAILA kuwa, tana zaune a falonta ita da k'awarta Aliya fire, cike da jin

8 / 14