kwanta bayan sunyi sallama..............
Please
Share
&
Comments
To be continue..........
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸
SHAFI NA 41__42
Washe gari , tun asubah ya tashi , kasancewar akwai aikin da ba'a k'arasa ba a gidan Fatima, kuma ya bar masu aiki , zasu yi aikin kwana, da hanzari ya shirya, k'arfe bakwai daidai ya fita daga gidan bayan ya sanarwa da LAILA cewar zaiyi tafiya, kafin ya dawo ta shirya masa kayansa a jaka,da murnarta ta amsa har sai da yayi mamaki, kasancewar in dai zaiyi tafiya ta dinga k'orafi kenan , yana fita daga gidan ta shiga falo , had'i da lalubar number Aareef , kasancewar ya shaida mata lallai su had'u a yau , dan haka ko da ya d'aga da murnarta ta sanar masa shima yayi farin ciki, sannan ya fad'a mata inda zasu had'u.
A chan b'angare guda bayan ya k'arasa gidan ya tarar da komai ya kammala , saboda ya makara a office ya sanya bai biya gidan mummy ba sai dai ya sanar da ita amgama aikin, saboda ta shaida masa cewar za'a so jere, bayan ya gama sanar mata ne ya wuce office.
A chan gidan mummy kuwa, daga ita sai mahaifiyar Fatima sai kuma aminiyarta , wato hajiya sadiya, kasancewar ta sanar da su dalilin auren d'an nata ya sanya su ma suka yadda da hakan , sannan suka sanya albarka, su da kansu suka yiwa yarinyar ta su jere na gani na fad'a, komai masha Allahu, sai san barka, wannan kenan.
Fatima a zaune a d'aki, yayin da Halima k'awarta tana ta aikin lallashi, " kinga Fatima ki nutsu ki k'watarwa kanki y'anci, kinga dai yadda yanzu rayuwa take , wallahi da ni na samu ya Ahmad da wallahi yaga yadda ake tarairaya, , dan wallahi ko ita LAILAN zata yi mamaki , ki rik'e mijinki hannu biyu biyu , kinji na fad'a miki " , cikin sheshshek'ar kuka Fatima tace " Halima bazaki gane ba ina tsoron LAILA wallahi , saboda irin matan nan ne masu mugun kishi akan mijinta ba abinda bazata yi ba walllahi", " shi yasa na fad'a miki ki jajirce tunda yanzu matsayinku d'aya da ita , a da dai ke ba kowa bace ba amma a yanzu gaji y'ar uwa a gare shi kuma mata , ki sanyawa kanki salama", sosai ta mata nasiha yadda jikin Fatima yayi sanyi sosai ta yaddarwa kanta cewar zata iya , sai da ta ga ta saki jikinta sannan ta kira mai k'unshin da zata mata , dama an gyara mata kai dan haka aka fara yi mata k'unshin.
Sai k'arfe biyar sannan ya samu damar barin office, gida kai tsaye ya nufa, ko da ya k'arasa tarba ta musamman ya samu daga LAILA , yayi mamaki sosai amma haka ya biye mata , ya kammala komai , yadda a b'angaren LAILA ta matsu da tafiyar Ahmad haka shi ma ya matsu da ya tafi , har bakin mota ta raka shi , sai da ta tabbatar ya bar gidan sannan ta juya ciki domin fara shiri, cike da murnarta, hmmmmn LAILA kenan.
Yana k'arasawa bakin gidan, yayi horn mai gadi ya bud'e masa, ya shiga , a lokacin su Mummy sun gama jere sun tafi gida, tsayawa yayi ya jera kayansa a wardrobe sosai tsarin gidan ya burge shi , yana gamawa ya nufi gidan Mummy sakamakon kiranshi da tayi akan cewar yaje ya d'auki matarsa ,aikuwa cikin hanzari ya nufi gidan Mummy, uhmmmm sarakan azarb'ab'i kenan.
Ko da ya k'arasa a lokacin angama shirya ta , ba wani dad'ewa yayi ba , mummy tace su tashi su tafi dare ya fara yi , anan fa aka ga abu domin fafur Fatima ta tubure ba inda zata je, koni sai da na mata k'walla , haka ma mummy da k'yar aka lallab'ata ta shiga motar su ka fice daga gidan.
Ko a hanya ma , kukan ta cigaba da yi , yana sauraronta, duk da yana jin kukan har cikin ransa amma haka ya k'yale ta , a hanya ya tsaya ya siya gasashshiya kaza , da fresh milk sannan su ka nufi gidan .
A chan b'angare guda kuwa, LAILA , kwance akan gadon hotel d'in da Aareef ya kama musu, " wallahi baby kanaji da ni irin sannan garab'asa haka, ta fad'a tana duban Aareef da ke fito wa daga cikin toilet da alama daga wanka ya fito" ai baby kad'an ma kikq gani indai ni ne", murmushi tayi, sannan ta tashi ta fad'a jikinshi daga suka cigaba da aikata abinda su ka zo , wa'iyazubillah.
Ko da su ka k'arasa gidan , da kanshi ya mata jagora har cikin gidan, tana lullub'e da mayafi sai k'amshi take yi , a d'aya daga cikin kujerun ya mata masauki, sannan ya nufi cikin kicin da plate ya fito a hannunsa, ya shiga zuzzuba musu, sai da ya gama sannan ya mata umarni da ta sauka su ci tsabar yunwa ce ta sanyata dole ta sauka su ka fara ci duk da a takure take jin ta, bayan sun gama ya nuna mata d'akinta yace ta shiga tayi alwala , bayan ta gama su ka yi sallah , sannan akayi shirin bacci, toh nima daga nan na janyo k'afafuna na fice daga d'akin baki d'aya, saboda kar ace min nayi gulma, wata k'ara da Fatima ta saki ne ya haddasa ni ba shiri na fice daga gidan a miliyan, don tsabar abin tausayi.
Asubah ta gari amarya da Ango.
Ko da na koma lokacin komai ya wakana, Ahmad zaune a gefen gado yana aikin lallashi , ni kuwa nace tunda ka aikata kuwa sai kayi aikin lallashi , komai shi ya mata , sannan ya barta , tayi wankan tsarki, ya shimfid'a mata darduma , ya jasu sallah, albarka kuwa Fatima ta sha ta gurin Ahmad, gani yake duk duniya yafi ko wanne namiji dace , ya kurbu zumar Fatima daidai gwargwado.
Ko da gari ya waye a lokacin Fatima , zazzabi ya rife ta , Ahmad na zaune yana jinya , yaji ana k'wank'wasa k'ofa a hankali ya mik'e saboda kar Fatima ta farka daga baccin wahalar da take yi , yana zuwa ya ga mai gadin Mummy ne ya bashi basket d'in abincin sannan ya juya ya tafi , shi kuma ya koma cikin falo.
Sai k'arfe goma sannan ta tashi a lokacin ya sata tayi brush ya zuba musu abinci , kunun tsamiya ne sai k'osai sai farfesun layan cikin , da lallashi ya dinga bata , yayin da kunya duk ta addabeta , a haka su kayi kalaci , sannan ya bata magani su ka koma bacci.
A chan b'angare d'aya LAILA sai Washe gari ta koma gida , tare da kyautar da Aareef ya mata , aikuwa suna cikin sallama, da Aareef Allah ya jefo da Dr sadeeq , kasancewar ya kira number Ahmad , baya shiga saboda ko shi kansa bai San yayi auren ba , LAILA da ke tsaye bata lura da shi ba dan haka su ka gama duk abinda zasu yi sannan ta shiga gida , da matukar mamaki a fuskarshi ya juya da mota ya bar k'ofar gidan...........
Please
Share
&
Comments
To be continue............
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸
( True life story)
🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
SHAFI NA 43__44
Toh haka dai Ahmad ya kwashe kwana bakwai a gidan Fatima, suna kwasar amarci da soyayya, tun Fatima najin kunya har ta saba , ta sake tare da taimakon k'awarta Halima, sosai take wayar mata da kai, aikuwa tayi amfani da shawararta ta, sai da ya kammala kwanakinsa, sannan ya koma gidan LAILA badan ya so ba.
A haka dai zaman na su ya kasance cikin walwala, da soyayya, yayin da a b'angare d'aya kuma zaman LAILA da Ahmad, ba'a cewa komai, ita dai ta maida hankalinta ga samarinta yayin da a b'angare d'aya, shi kuma Ahmad yake samun wannan damar in kwanan Fatima ya zagayo, a haka su ka koma makaranta, taci gaba da karatunta, bayan ya shaidawa principal d'in makarantar akan cewar zata yi jarabawar gama secondary a aji biyun senior
Hankalin Fatima ya kwanta , sai Sam barka , suna wata na hud'u da aure Allah ya a zurta , zo kuga murna lokacin da Dr ya sanar musu da wannan sakamakon , wanda a wannan lokacin suna daf da fara jarabawa,sosai ya shiga kula da Fatima cikin so da k'aunar juna , tarairaya ba wadda bata gani, ita kanta idan ta zauna godewa Allah kawai take yi , dan ganin Allah ya sauya mata rayuwarta ta da , da jin dad'i , rayuwarta dai abar sam barka da kwatance.
A b'angare d'aya kuma, Mummy tawa Ahmad magana akan cewar tunda yanzu rayuwar Fatima ta sauya, kamata yayi ya kai ta k'auye domin ziyartar y'an uwanta , a kuma shaida musu duk al amarin da suka faru, sosai ya gamsu da haka, ko da ya koma ya sanarwa da Fatima abinda Mummy tace,tayi murna sosai, ya sanar mata da cewar ana gama jarabawarsu, za su tafi , harda mahaifiyarta.
Fatima a zaune a falo, yayin da cikinta a lokacin ya kai wata bakwai,sallama taji anyi hakan ya sanya ta mik'e da k'yar ta nufi bakin k'ofa kasancewar tayi nauyi, da fara'arta ta bud'e k'ofa," ah aunty Aisha barka da zuwa, wallahi tun d'azu nike jiranki ,ta fad'a tana kallon mak'ofciyar ta ta , wadda suka shigo ita da wata bak'uwa, " ke dai bari Fatima wallahi Aliya ce ta tsayar da ni, kinganta nan k'awata ce sai dai ita bata ji ko kad'an," harara r wasa Aliya ta jefawa Aisha, da sannan Fatima ta matsa musu suka wuce, zuwa cikin falon, da hanzari Fatima ta wuce, domin kawo musu ruwa, Aliya ce ta dubi Aisha cikin mamaki bayan ta yi nuni da hannunta zuwa cikin wani photo,wanda Ahmad ya rungume Fatima aka musu photo, sunyi bala'in kyau sosai kamar ka sace su ," Aisha wannan fa waye, ta tambaya cike da mamaki, " lah ai mijinta ne " , cike da mamaki Aliya ta kalle ta, miji kuma ," girgiza kai tayi sannan tayi shiru, ita kad'ai ta san me take k'issimawa a ranta, Ahmad mijin LAILA shine ya zama mijin wannan yarinyar gashi ma ta lura akwai rabo a jikinta, a hanzarce ta sha ruwan da ta k'agauta ta fita ta sanarwa da LAILA halin da ake ciki, ko da suka gama bata koma gidan Aisha ba ta wuce gidan LAILA.
Tun daga bakin falo take k'wallawa LAILA kira, a hanzarce LAILA ta sauko daga upstair, " haba Aliya ta yaya zaki shigo kina min ihu bayan kinsan ina chan ina hutawa ta"," dallah chan wanne irin hutu , kina hutu amma mijinki yana chan shima yana hutawa " ," bangane ba, ta fad'a tana zare idanu"," toh ki sani cewar mijinki ya k'ara aure ba tare da kinsani ba ", wata uwar ashariya ta doka " ni za'ayi was hauka lallai ma amma ta yaya aka yi kika san cewar Ahmad yayi aure kin tunanin zaiyi aure ba tare da cewar ya fad'a min ba ta fad'a cikin k'araji "," yau da idanuna ma na kalla matar Ahmad harda tsohon ciki "," tsohon ciki fa kika ce tabbas kuwa," , " Aliya rakani in ganewa idanuna domin dai na tabbatar da cewar kina min wasa ne ko kuma gaskiya kike fad'a min , cikin hanzari da tashin hankali ta nufi sama domin daukar mayafinta, sai da ta sauko sannan Aliya ta ja ta , suka nufi mota , Allah Allah LAILA take yi su isa aikuwa ko da suka k'arasa sunyi sa'a mai gadi ya jagaya masallaci , aikuwa cikin hanzari suka shiga , sallama Fatima taji ya sanya ta fito bak'uwar d'azu ta gani , gabanta ne ya fad'i ganin wadda suke tare, " aunty LAILA , ta furta da k'arfi ", LAILA ce ta zare idanu wa take shirin gani kamar wannan mayyar yarinyar nan , aikuwa d'aga idanun da zata yi taci karo da hoton Fatima tare da Ahmad, wani uban hanzari ta daka gami da finciko Fatima , wallahi sai na kashe yarinyar nan , hankali na zai huta, jibgarta ta shiga yi tun Fatima na kuka harsai da ta suma sannan suka k'yaleta , aikuwa jini ya b'alle mata ganin haka ya sanya suka yi shirin ficewa daga gidan.
Ahmad wanda tun yana zaune a office , yaji gabanshi yana fad'uwa, hakan ya sanya ya baro wajen aiki ya nufi gidan Fatima , a bakin gate ya tsaya yana horn, shirin da yaji ya sanya ya fita daga motar ya nufi cikin gida , tin daga k'ofar d'akin ya fara sallama , shirun da yaji ya sanya ya shiga ciki, a kwance ya hango ta , da Sauri ya k'arasa inda take kwance, jijjigata ya fara yi , d'aga ta da yayi ne ya kalli jini na kwance a k'asa , cikin zare idanu, ya shiga girgiza ta yana kiran sunanta," Fatima ki tashi, ki tashi karki mutu , karki mutu bazan iya rayuwa in babu ke ba , ganin haka bazai kai ba ya sanya ya d'auke ta ya nufi mota cikin hanzari ya ta da mota ya nufi asibiti da ita.
Su LAILA kuwa b'oyewa suka yi ganin motar Ahmad ta nufo cikin layin, sai da suka bari ya wuce sannan suka wuce , ta k'yar su ka k'arasa gida suna maida numfashi , bayan sun huta Aliya ta dubi LAILA , "amma kina ganin yarinyar nan bazata fallasamu ba kuwa, ni fa inajin tsoro wallahi ,", " ke ni fa bai dame ni ba Allah yasa ma ta mutu kowa ma ya huta ," " amma kuma idan Ahmad ya sani fa, Aliya ta fad'a ,"," wallahi ko a jikina, ki barmin komai a hannuna , haka dai su ka cigaba da maimaita abinda ya faru, yayin da LAILA zuciyarta fari fes akan abinda ya faru .
A hanzarce ya k'arasa asibitin ,a lokacin Fatima ta jigata , tsananin wahala ya sanya ta farka daga sumar da tayi , suna k'arasawa aka shigar da ita d'akin emergency, ko da likitocin su ka duba , suka gane cewar nak'uda ta kama ta, nan da nan aka shiga bata taimako dan ganin ta samu ta haife abinda ke cikinta, Ahmad da ke safa da marwa , zancen zuci kawai yake yi , lallai duk wanda ya jawa matarsa wannan iftila'in wallahi bazai rabu da duk wanda yayi sanadiyyar fad'awar Fatima cikin wannan yanayin har ya sanyata nak'udar dole, a hanzarce likitan ya fito gami da cewar congratulations, bayan ya mik'a masa hannu " matarka ta haifi yara har guda biyu ma'ana twins , cikin tsananin farin ciki ya ma rasa meke masa dad'i , yama manta da damuwar da yake ciki , ko likitan bai jira ya gama magana ba ya nufi cikin d'akin...............
Please
Share
&
Comments
To be continue............
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
SHAFI NA 45__46
INA BALA'IN YINKU FAN'S, SADAUKARWA GA Y'AN MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION, TARE DA KISHIYAR UWA FAN'S, 😍😍😍😍👌🏻💃🏻
A firgice ya bud'e k'ofar d'akin, a lokacin nurses sun gama gyara ta da babies d'in tsayawa yayi yana k'are musu kallo, yaran kamar ba bakwai ni ba , ganin su yake kamar a mafarki wai ace wannan duk nasa ne , kuma daga tsatson da yafi so , ba shakka yasan Allah kad'ai zai sakawa Fatima amma ba dai shi ba.
Tausayin yaranne ya kama shi, saboda rashin imani , lokacin fitowarsu duniya baiyi ba amma tsabar zalunci sai da aka sanya yaransa suka sha wahala, ya k'udurtawa ransa cewar wallahi kome ake ciki sai ya gano Wanda ya yiwa matarsa haka, kuma yaso kassara masa gudan jininsa.
Tunawa yayi da Mummy hakan ya sanya yayi dialing number na ta , aikuwa bugu d'aya ta d'aya ta d'aga, cikin hanzari ya fara sanar da ita abinda ya faru kama daga dukan da akayi mata , zuwa haihuwar da tayi, sosai mummy ta firgita da jin labari , sunan asibitin ya fad'a mata sannan ya kashe wayar .
A nan kusa da hospital d'in ya fita ya jibgo uwar siyayya , na kayan baby da wanda mamansu zata sanya, bayan kuma akwai a gida .
Ko da ya dawo ya tarar har lokacin suna bacci , cikin kulawa so da k'auna ya k'arasa kusa da Fatima da ke kwance kamar matacciya, anyi mata dressing na wajen da su LAILA su ka dake ta, sanadiyar allurar baccin da likitoci suka mata ya sanya har a time d'in bata farka ba , domin ta samu hutu.
D'aya bayan d'aya ya d'auki yaran hassan da husain, kasancewar nurses d'in sun gama banbanta masa su kowa an lik'a masa sunansa a saman hularsa, Hassan ya d'auka ya masa hud'uba da mahaifin Fatima wato Iliyas ,sannan ya d'auka Hussain ya masa shima kiran sallah da hud'uba ya sanya masa sunan mahaifinsa wato Muhammad, sannan ya jera mata su a kusa da ita .
Hoton yaran ya fara d'auka , sannan yayi posting through WhatsApp, Facebook, Instagram, Twitter da sauransu, aikuwa kan kace me ana ta masa murna Allah ya raya , kiran mummy ce ta shigo wayarsa , hakan y sanya cikin Sauri ya d'aga , ta sanar masa da cewar tana parking space driver ya kawo ta, aikuwa koda ya k'arasa suna tsaye ya musu jagora har zuwa cikin d'akin da suke, sosai hajiya taji dad'in ganin yarinyar ta ta da jikokinta cikin k'oshin lafiya , d'aya bayan d'aya ta d'auka , a nan ya sanar da ita sunan da ya sanya musu , taji dad'i sosai .
Kafin kace kwabo asibitin ya cika da y'an barka , kowa sai sam barka , cikin y'an barkan harda aunty Aisha da Halima k'awar Fatima sai tsiya su ke mata, ita dai Fatima sai murmushi take musu, tana tuna fuskar bak'uwar aunty Aisha, tabbas itace wadda a gabanta LAILA a wanchan karon ma ta illata rayuwarta , kenan a wannan karon ma ita ta kawo LAILA cikin gidan ta kenan , sosai ta shagalta da