Author : Zahra Royal Star Category : True Hausa Novels
RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 18
Marmah na gama girkin, su Tala suka taimaka mata suka jerasa darning table, saboda basu san inda zasu ajeshi ba.
Shiga d'akinta Marmah tayi tana zama tad'an huta domin ta gaji sosai, tashi tayi kawaii ta shiga wanka domin jin kiran salar la'asar, tana cikin yin wanka taji kamar shigowar mutum.
Can taji muryar Ifteesan tana cewa "wai kina ina ne?, ya za'ai ku aje min abincin bak'o a babban parlo, parlon bak'i ya kamata aje min abincin"
Ta idasa maganar dai-dai Marmah na fitowa daga toilet, wata harara Ifteesan ta watsa mata, da yasa da sauri Marmah ta ce "kiyi hakuri, bamu san inda ya kamata mu aje bane, shine yasa ana gamawa aka ajeshi akan darning"
"Mine-mine, sai ana magana, kiyita sukuyar da kai, kega munafuka, to idan kin gama sai zo ki kwaso su, ke d'aya nake so ki kawo minsu parlon bak'i, domin bana son ana min shiga da fice bak'o na ya iso, fatan kin saurari mi nake cewa?"
"Eh naji kuma yanzu zan fito"
Marmah ta k'are maganar cike dajin haushin ce mata munafuka da tayi.
Su Ifteesan anci uban wanka, ana zaune a parlon bak'i, da wani saurayi, yaci uban wanka da manyan kaya, sai wani shishshige mata yake, suna zaune kujera d'aya da juna, kamar zasu had'e da juna, sai jefa mata wani shu'umin kallo yake, kai ka rantse da Allah bai saba ganinta bane, yadda yake binta da kallo.
Harsai da Ifteesan cike da yanga ta ce "Ohh my Abdul, wannan kallo haka, sai kace yau ka fara gani na"
"Yaushe rabon dana ganki, ai na dad'e sai dai ta waya fa, muna gari d'aya amma bakya son gani na"
"A'a fa ba haka bane kasan yanayin Daddynmu ne sai a hankali, baya son wasa, yanzu ma dan ka shirya aure ne, yasa na barka kazo, idan ba haka ba, Daddy zai tamin tabbayoyi ne, idan yaga zuwanka, shi yasa ba wadda muke ba damar zuwa gidanmu, wai da sunan zuwa zance"
"Hakane kuma yana da gaskiya, kuma very soon na shirya auran ki"
Ya idasa maganar yana jefa mata murmushi yana kamo hannunta yana murza y'an yatsun hannunta.
Suna cikin haka Marmah tayi sallama ta shigo kanta a k'asa tunda ta shigo idonta yayi mata tozali da yadda suke zaune kamar zasu manne da juna, ga hannun Ifteesan dake a hannun saurayin.
Marmah ta girgiza kai tana ganin hakan ba waye wa ba ce, a yadda suka zauna ma kwata-kwata bai dace ba wallahi, koda yake daga ganinsa da tayi idonsa shima a bud'e yake, daga shi har Ifteesan d'in, su gani suke nan waye wa ce.
Haka dai ta gama kawo abunda zata kawo ta gaida shi, ya amsa yana binta da kallo harta fice.
"Amma dear wannan kuna kuma, ko y'ar uwarki ce? ban santa ba"
Yamutse fuska Ifteesan tayi tana cewa "wallahi y'ar aikinmu ce"
"Kai amma nayi mamaki batai kama da y'an aiki ba bare y'an K'auye"
"Ai ko y'ar K'auyen ce, kaga dan Allah dai min zancan ta"
Basarwa yayi ganin ranta ya b'aci danda nan ya sakko da ita, suka cigaba da soyayyarsu.
Koda aka gayama Daddy da farin ciki ya iso, Ifteesan tayi mai iso shida Y Khaleefa, suka gaisa sosai da Abdul, Daddy yayi mai tabbayoyi yana basa amsa, inda Ifteesan ta basu waje domin su tattauna.
NARNAH POV
Zaune take a parlonta, tayi uban tagumi, yau kusan wata uku da auransu da Abbas amma kullum ba ranar banza da bai zai zo mata cikin dare a buge ba, kuma kusan kullum saiya mata dukan kawo wuk'a, duk jikinta tab'on duka ne, duk ta rame ta lalace, kuma kwata-kwata ya hanata fita koda k'ofar gida ne, shi yasa yau da gobe asirin da suka mai ya sake shi, sai dai abunda ba'a rasa ba, gashi kayan abinci sun k'are dama tun na auransu ne, garar da aka had'a mata ce, ta k'are kuma yak'i kawo kayan abinci, kullum sai garin kwaki da take ci shima yau ya k'are.
Hawaye ne ke mata zuba a fuska, dafe cikinta tayi dake kukan yunwa.
Jin motsin mutum yasa a zabure ta tashi dan tasan bamai shigo mata a yanzu sai shi, domin ya hana kowa ya rab'eta.
Shigowarsa yasa ta zube a k'asa tana ruk'onsa cewa "dan Allah ka bani abinci wallahi yunwa nake ji, sana ka barni naje na gano Umma ta, tana cikin wani hali bata da lafiya fa"
Wani banzan kallo yayi mata, baice mata komai ba ya fice ya dawo, sai gashi ya shigo rik'e da kofi a hannunsa, zama yayi kan kujera, yana mik'a mata kofin.
Kallon cikin kofin tayi ganin garin kwaki a jik'e harda gyad'a ciki, yasa ba shiri ta fara sha, sai dai mi?, loma d'aya takai bakinta ta furzo da ita, a gigice tana kallonsa.
Ta ce "Abbas garin kwaki da gishiri ne fa"
"Kuma a haka zaki shanye sa tas idan ba haka ba, kinsan sauran wallahi, kuma da kike cewa wai uwarki bata da lafiya, duk ba ita ce ta raba ni da Marmah ba, abar k'aunata, bazan tab'a yafe muku ba, ke baccin ina son d'aukar fansa a kanki, da tuni na sake ki, domin babu digon sonki a raina, kuma bazan tab'a sakinki ba, haka zaki zauna, cikin K'ANGIN RAYUWAR dana saki, itama Mahaifiyar taki abunda ta shuka ne take girbewa tun a nan gidan duniya"
Shuru Narnah tayi tana jin wata nadamar auran Abbas data yi, tana nadamar kwace ma Marmah shi data yi, yanzu wa gari ya waya?, yanzu data je ta sami wadda yake sonta tsakani da Allah da duk hakan bata faru da ita ba.
Wata tsawa daya daka mata yana cewa "maza ki cinye sa na ce, kuma aure zan k'ara domin bazan iya zama dake ke kadai ba, wacce nake so zan auro"
Wani sabon tashin hankali ne ya ziyarci Narnah, ba shiri ta fara tusa garin kwakin tana ci tana kuka, bakinta ba abunda yake sai zafi da zugi, ga cikinta dake murd'awa yana mata ciwo kamar zata shid'e, danda nan ta fara amai, har a jikin Abbas, tashi yayi ba shiri baiyi wata-wata ba, ya tsinka mata mari mai zafin gaske, har saida ta wuntsila, sai gata cikin aman dame-dame, tana kuka, wani dogon tsaki ya kuma ja, yana tsallake ta ya fice da gidan, nan barta tana rusa uban kuka, ta rasa inda zata fara, ga ciwon Mahaifiyarta, da y'an gidansu suke zuwa, domin kawo mata tsegumi, ta rasa inda zata sa kanta taji sanyi.
Ita kanta Hajara hankalinta a tashe yake, abubuwa sun taro sun mata yawa, kullum tana aika wa aje aga wane irin hali d'iyarta take ciki, dan duk wacce tayi aure a gidan, tazo gida, kuma da abun arzik'i ga iyayansu mata, sosai fa hankalin Hajara ya tashi da irin labaran da ake kawo mata dangane da irin zaman da Narnah take yi a gidan Abbas, ga wasu irin k'uraje dake feso mata a gabanta, wadda yasa Hamza gudunta ko inda take baya son zuwa, duk wani tsoronta da yake ji yanzu babu shi, shi yasa data bi ta tada hankalinta, dole saita je gidan Narnah, ya hanata ya ce mudun taje bada yawunsa ba, indai taje daga nan karda dawo gidansa, shi yasa hankalin uwa da d'iyarta a tashe yake kullum, ga ciwo dake cin Hajarar a tsaitsaye, k'uraje kullum k'ara fesowa suke a gabanta, ko a gaban waye sai kiga tasa hannu a gabanta, tana sosawa tana kartar gabanta, wajan harya fara rub'ewa ya fara jagwalewa, wannan ciwon yasa Hajara fara sakin maganganu barkatar, kanta ya fara samun tab'uwa, duk wani laifi da ba'asan tayi ba,ta fara bankad'o shi, yau hankali gobe babu, mutanan gidan yanzu kam basa shakkarta, saima kyararta da suke suna gudunta, data zo waje za'a tashi saboda warin da take, gashi Hamza na shirin yin aure, abunda ya k'ara hargitsa kwanyarta kenan, kuma Mlm ne ya hana Hamza sakinta da tuni ya saketa saboda, bazai iya rab'arta da irin warin da take yi ba.
Hamisu ko ba laifi Habiba ta d'an canza shi, sai abunda ba'a rasa ba, amma sun rage rigimar da suke sosai ada can................✍️
*And ina so na sanar daku duk wadda yake son ayi tafiyar book d'in nan dashi book 1 ya kusa k'arewa, daga na 20 za'a shiga book 2, tohm gsky book 2 na kud'i ne naira #500 ne kacal game buk'atar book 2 akwai sa complete a yanzu haka d'aya turo kud'insa zan tura masa ni kuma Kai tsaye idan kana so zaka iya min magana ta wannan number d'in*
👇
08130479973
Ko kuma ka turo kud'inka ta wannan account number d'in
👇
8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank
Saika turo shaidar biya a number Dana aje sama.
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 19
"Ke bakya gani ne wai?"
Cewar Khairat dake sakkowa sukayi karo da Marmah tana shirin zuwa school.
Marmah tad'an matsa kad'an ta ce "Ohhh kiyi hakuri dan Allah please banga ni bane"
"Ki dai rink'a tafiya a hankali idan ba haka ba, zaki sami mai wanka miki mari ne, mtswwww aikin banza kawai yarinya sai k'iriniyar tsiya, kina tafiya ba kintsi"
Ita dai Marmah da sauri ta rab'a ta wuce domin Y Khaleefa ne yake jiranta.
Tana fita ta hango shi jingine jikin mota, kallonsa take cike da birgewa, yasha shadda ruwan k'asa tayi mai bala'in kyau, manyan kaya namai kyau sosai kamar mi, k'arasowa tayi tana jefa mai murmushi.
Shima murmushin ya sakar mata yana ware mata hannu alamar ta rungume shi, waro ido tayi tana waige-waige, mik'e k'afad'a tayi tana mai alamar kar wani ya gansu.
Dariya ya saki yana k'ara mata alamar ta taho gare shi, ganin alamar da gaske fa yake yasa, Marmah ta tafiya a hankali ta isa gareshi, tana k'arasawa ta kwanta a jikinsa, masauki yayi mata akan faffad'an k'irjinsa ya zagaye hannunsa a k'ugunta, tare suka sauke ajiyar zuciya, d'agowa tayi tana kallonsa, bata san sadda ta ce "Y Khaleefa kayi kyau manyan kaya nama kyau sosai"
Ja mata hanci yayi na fad'ad'a murmushinsa ya ce "da gaske?", d'aga mai kai tayi, ya sake sakar mata murmushi yana rabata da jikinsa ya ja hannunta suka shiga mota, har suka d'au hanyar school d'in hannunsa na cikin nata.
Suna isa dai-dai k'ofar school d'in zata sauka, ya jawota jikinsa yana mata rad'a a kunnanta, yana cewa "kiyi karatu sosai, sana ki rink'a tunawa ke ba kamar sauran y'an matan school d'in bane, ki rink'a tunawa kina da aure, ina da kishi sosai, bare a kanki, ina jin wani irin kishi a kanki, ki kiyaye kinji, y'ar albarka?"
Murmushi tayi itama cike da d'unbin son mijin nata, wadda bata san sadda ya shigeta ba, shima kuma haka, lokaci d'aya suka fad'a son juna.
Ta ce "tohm insha Allah d'an albarka na"
Tana idasa fad'ar haka ta b'alle murfin motar ta fita da sauri, tana d'aga mai hannu, murmushi ya saki yana shafa kansa, girgiza kai yayi yana jin wani irin nishad'i idan yana tare da ita, shifa gaskiya da za'a bashi matarsa su tafi tare, dan gobe ne yake shirin komawa wajan aikinsa, yana buk'atar matarshi kusa dashi, amma yasan hakan bazata yuwu ba, Maminsa ce babbar matsalar.
Washe garin ranar da zai tafi da daddare Marmah tasha kuka, duk ya jagwalgwalata da soyayyarsa mai yatsawa a zuciya, dan sashinsa yasa ta kawo mai shayi, yake sanar da ita, ita kanta bata san sadda ta saki kukan rabuwa dashi ba, a daran ya nuna mata so da k'auna kamar ya had'iye ta, shi yasa da kyar suka rabo idonsa yayi jawur shima, duk miskilancin Y Khaleefa ita kam yanzu baya mata shi, kusan zata iya cewa daga ita sai Daddy suke ganin hak'uransa, sai ko Mami, da safe da zai wuce Marmah bata yarda ta fita ba, bare a gane da wani abun, shi ko Y Khaleefa yaso yasata a idonsa kamin ya tafi, gashi ba waya ne da ita ba, sai su Khairat da Mami da suka fito raka shi harya tafi.
Kwananshi biyu da tafiya, sosai Marmah take kiyaye duk wani abu dasu Ifteesan zasu kyareta, da wuri take gyara masu d'aki sana driver ya kaita, school, satin Y Khaleefa uku da tafiya yazo garin Kano, ba wadda yasan zai shigo garin yaje har school d'in su Marmah sai dai kawai ta ganshi.
Ai ko gaban kowa ta ruga da gudu cike da matsanancin farin ciki ta rungume sa da k'arfi, ta sauke ajiyar zuciya, shima rungume ta yayi yana jin wata sabowar k'aunarta ta rufesa, a yadda yaji bugun zuciyarta kad'ai zai basa amsar tayi kewar sa sosai, da yadda take sauke ajiyar zuciya kad'ai ya isa ya tabbatar ma tana matuk'ar k'aunar mijinta.
Kai tsaye hotal ya kama masu, Marmah ta kallesa cike da tsoro ta ce "Y Khaleefa karfa aga na dad'e fad'a za'ai min a gida"
"Ba wadda zai miki fad'a insha Allah, nima ke kad'ai nazo gani, daga nan zan juya na koma Abuja"
Zaro ido Marmah tayi tana cewa "kamar ya baza ka je gida bane wajan su Mami?",
"Yeah ke kad'ai na zo gani"
Ya idasa maganar yana jawota ta fad'a jikinsa, wani irin sihirtaccan kallo yake jefa mata, itakam da sauri tayi k'asa da kanta tana kwantawa akan k'irjinsa.
Magana ya farayi cike da wata shu'umar muryar mai kamar yana mata rad'a.
"I really need my wife by my side, and I feel like I'm gone"
Tashi da sauri tana kallon kyakkyawar fuskarsa, hannunta tasa tana shafa sajen fuskarsa, danta kawar da maganar da yayi ta ce "This sergeant is beautiful, I love him"
Murmushi yayi yana cewa "mai wayo, hmm ai naki ne ki tab'a yadda kike so"
Murmushi tayi tana k'ara fad'awa jikinsa, d'agota yayi suka fad'a kan gado, ya had'e bakinsu waje d'aya.
Ganin abun zaiyi nisa, danta lura shi yama manta a inda suke, yasa da sauri Marmah ta kwace jikinta tana sauke ajiyar zuciya.
Khaleefa da yayi nisa ya bud'e idonsa yana kallonta, da sauri Marmah ta runtse idonta ganin idonsa yayi ja, tsabar jarabar dake taso masa, ga wani ciwon mara dake taso masa, sai zufa ke yanko masa, duk sanyin AC dake
d'akin, shima kansa yafi so a kawota gidansa abun sai ya fi mai dad'i.
Kallonta yayi yana had'e wani abu a mak'oshinsa ya ce "Please come and find peace, I have nothing to say to you, but please find peace for your husband"
Tausayi ya bata ba shiri ta matsa kusa dashi, da kyar ta cire kunya, amma wani abun saita runtse idonta saboda bata sababa kwata-kwata da wannan irin abun, saida ta tabbatar ta samamai natsuwa sosai, sai albarka yake sa mata.
Da kansa ya maida ta har k'ofar gida ya bata wata waya iPhone 7 ta rik'e ko sun rink'a waya.
Daga cikin motar ya lek'o yadda yaga idonta ya ciko da hawaye yasa yasa ya jawota cikin mota.
Yana ce mata "Oh my baby, don't cry and here's the phone, we'll say hello and if you want to see me, tell me and see me, and bana son na ganki haka"
A shagwab'e ta ce "I won't cry because you don't want me, but I will miss you so much"
"Wow da gaske zakiyi Miss d'ina"
Cewar Y Khaleefa yana jan hancinta, yana kallon yadda take mai shagwab'a, yana matuk'ar son mace mai shagwab'a.
Da kyar suka rabu, sana ya juya ya koma, ji take kamar karya tafi, shima a wajansa hakane, daurewa kawai yayi.
Wayar tasa a school bag d'inta sana tayi sallama a parlon gidan, birki taja ganin Mami na jefa mata wata irin harara.
"Ke daga gidan ubanwa kike?, tun d'azo aka tashi daga school driver yaje d'akko ki aka ce kin taho"
Ifteesan dake sakkowa daga sama ta ce "kuka sani ko tayi saurayi shiya zo ya d'auke ta"
"To bari kiji mu nan gidan ba y'an iska bane, yarana basa yawon banza, dan haka sai kiyaye dan baza'a kaso mana abun kunya a gida ba"
Mami ta idasa maganar tana komawa ta zauna tana jefama Marmah harara.
Ifteesan dake danna computer ta d'ago tana ma Marmah kallon tsaf ta ce "to tsayuwar uban mi kike kuma, marar kunya, ke nan har kinsan bin wani saurayi?, bar wajan nan ko yanzu nazo na sharara miki tafi wallahi"
Marmah da idonta ya cika da ruwan hawaye bata bari sun zubo ba tayi d'akinta, tana jin sadda Ifteesan ke cewa,
"Ni wallahi Mami na tsani yarinyar can, wai mi yasa ma Daddy zai wani d'akko mana ita ne?"
"Ohho mai shima k'ila wani mugun abun sukai mai, sunga ai shi kad'ai keda abun hannu, shi yasa kullum suke mak'alemai, nima nan basan yarinyar can nake ba, dandai ba yadda zanyi ne"
Ranar asabar dasu Marmah sukaje ismilya, su Ifteesan sunyi matuk'ar mamakin wai Marmah ce aka d'auka Malama, ai ko haka suka dawo gida suna sanar da Mami cike da bak'in ciki a ransu, suna mata kallon marar ilimi ashe sune ma take ma kallon sakarkaru, duk da sun fahimci haka, basu daina musguna mata ba, harsai idan Daddy na gidan, ko Y Khaleefa yazo garin suke d'aga mata k'afa.
Rayuwa na gudu, cikin k'ank'anan lokaci Marmah ta gama secondary d'inta inda Daddy yasa mar mata, wata school of hygiene, shekara biyu, zata gama, dai-dai su Ifteesan suma sun kammala karatun nasu, yana so gaba d'aya a had'a ayi hidimar bikin a tare, kuma a lokacin ne zai sanar da Mami..........✍️
*And ina so na sanar daku