Author : Zahra Royal Star Category : True Hausa Novels
saukar ruwa a jikinta.
A zabure ta mik'e tana bin Ifteesan data watsa mata ruwa da kallo, itama dake mata kallon wulak'anci.
"Ke kwanciyar ubanmi kike har yanzu?, Ohho an samu katifa mai laushi, abunka da ba'a sababa, to bari kiji na gaya miki, daga yau bacci bai kama ki ba, gyaran d'akinmu da wankin toilet ya dawo gareki, kamin mu tashi a gyara mana toilet a wanke sa sosai, domin bamu son k'azanta, and abu na biyu, ki tabbatar kin shiga kitchen kina taya so Tala aiki, yanzu ma nazo ne in sanar dake, na tarar dake kina bacci kega isassa, maza kije ki wanke mana toilet, kin wani b'ararraje kina sharar bacci, ai bacci ba naki bane yarinya"
Ifteesan ta idasa maganar tana juyawa zata fice tana gaf ficewa ta k'ara wace "ki tabbatar kin wanke toilet d'in nan da kyau, idanma baiyi ba, wallahi sai kin mai-maita sa"
Marmah bata ce komai ba, da sauri ta shiga toilet d'inta ta wanke bakinta, ta fito da hanzari, ta haura sama, inda take da tabbacin nanne d'akinsu, ta shiga, kallon d'akin take, duk had'uwar d'akin a hargitse yake, ko ina kaya a watse, ba kintsi, sai kace ba mata ke kwana a d'akin ba.
Bata tsaya komai ba ta fara gyaran d'akin, tukun tana gamawa ta shiga toilet shima ta wanke sa tas, a d'an k'ank'anan lokaci ta gama gyara masu d'akunan su, dan ita irin wannan aikin baya d'aga mata hankali tana yin wadda yaci uwarshi a garinsu.
Koda ta sakko ba kowa a parlon kitchen ta shiga suka gaisa dasu Tala, suna labari tana taya su aiki, har suka gama suka jera a darning table, ita kad'ai ce a parlon bayan ta kawo wata kula ta ajiye a darning d'in, taji sallamar Y Khaleefa, cikin siririyar muryarsa.
Sanye yake da wasu farin yadi sai hula dake kansa sunyi mai masifar kyau kwarjinisa ya sake fitowa, tunda taimai kallo d'aya suka had'a ido, tayi hanzarin janye nata, shi ko idonsa na a kanta, yadda yake karantar tsanin nutsuwarta, gaida sa tayi, bakinta na rawa, saboda jikinta ya bata har yanzu kallonta yake.
Zuwa yayi ya zauna kan darning d'in, sana ya amsa gaisuwarta, can ya dube ta ya ce "wannan d'in aikinki ne?, waya saka ki?, kin manta matsayin ki ne?"
Shuru tayi mai, kallonta yayi ya tsareta da ido.
Ya sake cewa "Hajiya am talking to you fa?"
"Aikin ne nake sonyi amma babu wadda ya sani"
"To daga yanzu karki sake yi, ki rink'a tunawa da ko wacece ke"
"Amma fa na sabayi a gida, wannan d'an aikin ai ba komai bane, bana jin dad'in zaman haka nan"
"To ubanta ina ruwanka da aikin da take yi?, baka ji mita ce bane?, ta saba wahala a can K'auyen nasu, kuma ni ce nan na sata"
Cewar Mami dake sakkowa k'asa, bayan taji wani abunda Khaleefa yake cewa, karasowa tayi ta zauna akan darning d'in.
Tana sake duban Khaleefa tana cewa "wai tsaya inama ruwanka da ita?, kaida ba shiga harkar mutane kake yi ba, dan haka bana son wannan shishshigin da ka fara yi mata"
"Amma Mami"
Shuru Khaleefa yayi ganin ta d'aga mai hannu.
Ta ce "amma mi?, bana son jin komai"
Daddy dasu Khairat ne suka iso wajan darning d'in a tare, kowanne ya samu waje ya zauna.
Marmah dake tsaye ta gaisar da Daddy yana amsa mata cikin fara'a, yana tabbayarta ya kwanan bak'unta.
Mami sai kallonsa take cike da jin haushi ganin yadda yake wani sakar mata fuska, yana wani washe mata baki.
Mami takai dubanta ga Marmah ta yatsine baki tana cewa "to Malama tsayuwar mi kike mana a kai?, ki wuce kiba mutane waje, kin wani tsatstsare mutane da ido"
Daddy dake kallon Mami yayi sauri cewa "ban gane tsayuwar mi take mana ba?, ke Marmah zu ki zauna tare damu, na ce miki kamar gidanku ne nan"
"Kamar ya Alhaji ta zauna kusa damu taci abinci?"
Cewar Mami dake jefama Daddy kallon takaici.
Su Khairat suma jin haka yasa suka tsayar da cin abincin suna sauraron mi Daddy zai ce, Khaleefa ko daga kallesa zaka gane baiji dad'in abunda Mamin take ma Marmah ba, ko banza ai yanzu matarsa ce, anya ma Mami zata amita da Marmah a matsayin matarsa kuwa?, yana tsoron ranar da zata sani ne, Allah kad'ai yasan rigimar da za'ai, duk da baya jin komai game da Marmah, bare yaji yana sonta, kawai tausayinta yake ji, dan yaji labarin irin wahalar data sha wajan Mlm, inda yake mai nasihar ya kula da ita, yaji tausayinta, tunaninsa ne ya katse jin abunda Daddy yake cewa.
"Kamar yadda kikaji na fad'a"
Ya sake kallon Marmah dake shirin barin wajan, karma ace ita ta had'a su fad'a,
Daddy ba wasa a fuskarshi ya ce "ke Marmah dawo ki zauna, kici abinci damu, duk wadda yaga bazai iya zama tare da ita ba, yana iya tashi"
Ba yadda ta iya ta dawo taja kujera, a hankali kamar mai tsoron duka, kwata-kwata sai taji ta takura tama kasa cin abincin, ita da Daddy ya kyaleta wallahi, bata saba zama irin haka taci abinci ba, ga kallon da su Ifteesan ke jefa mata, duk sai ta sargu.
Ganin yadda Daddy yasha mur yasa ita kanta Mami bata sake cewa komai ba, haka dai suka ci abincin ba walwala a fuskarsu, ita ko Marmah da kyar tayi loma uku kwakwkwara.
Su Ifteesan na shirin tashi domin wucewa school, da yake BUK suke yi, sun kusa had'a degree d'insu, suka ji Daddy na cewa,
"Yauwa Khaleefa ina so yau kaje kasa Marmah islamiyar su Ifteesan, inda suke zuwa, boko kuma, sai kaje secondary d'in da su Ifteesan suka gama ka sata, nasan za'ayi mata enter biyu, idan sukayi mata, sun son class d'in daya kamata su ajiyeta"
Da to Khaleefa ya amsa.
Sosai fa abunda Daddy ya ce yaba su Khairat haushi, islamiyarsu kuma, wannan ai sai dai ajeta a ajin y'an koyo, ko a bokon ne kuwa, ficewa sukai suna hararar Marmah, da bata san sunayi ba, ita ko sai murna take, itama ta tashi ta shige d'akinta, domin shiryawa.
Daddy yaga d'akin da Marmah ta shiga tuni kawai yayi shuru ne, dankar yaja ma Marmah wata tsanar wajan Mami.
Mami data cika tayi fam, ta kalli mijinta, cike da takaicinsa yadda ya fifita wata akan yaransa, yana son saiya maidata matsayi d'aya dasu.
Ta ce "haba Daddynsu Khairat wane irin kuma makarantar da y'ay'anka sukayi zaka ce a sata, ina laifin a sata ta gwamnati, wannan school d'in da kake biyan kud'i da yawa haka"
"Hmmm Bilkisu kenan, itama ba y'ata ba ce?, kamar yadda zan iya kashe musu ko wana ne dan suyi karatu, to itama haka zan iya kashe, ko wana ne domin ta samu ilimi, kin mata wai matsayinta a waje na ne?, dan haka Bilkisu bana son irin haka"
Shuru tayi cike da jin zafin amsar daya bata, ba yadda ta iya, domin tunda taji ya kira sunanta, kai tsaye tasan ba wasa yake ba..............✍️
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 17
Marmah ce ke fitowa da sauri saboda zumud'in za'a kaita school, ta taho da sauri bata lura ba, Mami ma ta taho, itama tana tafiya da k'arfi kamar zata tashi sama, kawai sukai karo.
Cike da tsananin tsoro Marmah taja baya, zata bud'e baki domin bata hakuri, kawaii taji saukar mari, hakan fuskarta, runtse idonta tayi, tana sa hannunta ta dafe inda ta mareta, wasu hawaye suka wanke ma Marmah fuska.
Jin wata tsawa data buga mata tana cewa "keeeee dabbar ina ce?, ni sa'arki ce da zaki bangaje ni?, na taho kin taho, bazaki ban waje na wuce ba, saboda dama marar tarbiyya ce ke?, shashasha marar kunya kawai, mai ido a sakar ka"
Daddy dake kallon komi ke faruwa, ya had'e wani abu mai d'aci a zuciyarsa, hucewa tayi kanta kenan, kallon Khaleefa yayi yana mai alamar yaje ga Marmah so wuce.
Tashi Khaleefa yayi cike da tausayin matarsa, ya matsa kusa da ita, yasa hannunsa ya kama nata hannun, suka fice daga gidan, kai tsaye mota suka hau suka fice daga gidan.
Suna tafiya a mota, Marmah na share hawaye, ba tayi tsammani ba, taji hannunsa cikin nata, yana d'an murza y'an yatsun hannunta, wani irin abu taji ya fara yawo a jikinta, lumshe idonta tayi, wasu sabbin hawaye na sake zubowa, baice mata komai ba, saboda shima ba gwanin magana bane, idan kinga yayi magana mai tsawo to Mami ce, take ja, domin Mami irin matan nanne masu saurin fushi da fad'a, sai ko idan magana da wani ta zama dole yake yi.
Islamiya suka fara zuwa, nanma saida akai mata enter biyu, sosai Malaman sukai mamakin iliminta da k'ok'orinta, inda har suke tabbayar Khaleefa, cewa "gaskiya wannan k'anwar taka akwai hazak'a, wannan ai sai dai a d'auketa Malama, idan an bamu dama, dama gashi bamu da Malamai mata da yawa, domin gaskiya tana da sani sosai akan karatun addini, zata bada gudunmuwa, ga d'alibai, dan enter biyun da nai mata, tana da sani akan sauran littatafai addini"
Sosai shima Khaleefa ya cika da mamaki, ashe dama da iliminta har su Khairat ke mata kallon sama-sama, sosai ya cika da farin cikin samun mata kamarta, lokaci d'aya yaji zai iya zama da ita ko a yanzu ne, lokaci d'aya yaji ta shiga zuciyarshi ta zauna, yana son mace mai ilimin addini, sosai, tabbas maganar Mlm da yake cemai bazai tab'a dana sanin auran Marmah ba, domin ya yarda da Marmah d'ari bisa d'ari.
Ai ko nan take Khaleefa ya bada damar zata rink'a zuwa domin koyawa d'alibai, amma sai asabar da lahadi, ranakun dasu Ifteesan ke zuwa suma, za'a rink'a kawosu tare, sosai Malaman sukai godiya, inda za'a rink'a biyanta, albashi, ko yaya ne, da Khaleefa yaso subar wani albashi, kyauta zata rink'a koyawa, sai dai Malaman sun nuna basu yarda ba, dole tasa ya amince haka.
Wajan Marmah ma sosai abun yayi mata dad'i, dama tasan k'ila suce hakan, domin bata zauna haka ba, babu inda bata zuwa domin daukar karatu, hatta Mlm tana zuwa wajansa domin sanin wasu littatafan addini.
A bokon ma dai taci enter biyun domin su kansu Mlmn sun jijjina mata, inda kai tsaye aka ajeta SS2, aka mata komai daya danganci school hatta kayan school d'in komai da zata buk'ata sai da aka bata, sana suka taho gida, basu isa gida ba, sai da ya biya wani shago da ita, yayi mata sayayyar kayan ciye-ciye, ai ko sosai tayi murna tana mai godiya, shi ko sai kallon kyakkyawar fuskarta yake yadda take murmushi mai zautar mai da zuciya, sai yaji shima yana cikin wani irin yanayi, yadda ta sake dashi sai surutu take mai, bai hanata ba, bai kyareta ba, itama sai yasa ta k'ara sakin jikinta dashi, tana bashi labarin rayuwar data yi, harta gangaro labarin Abbas da yadda aka rabasu, tana kai iya ta fashe da kuka mai cin rai, daya sa Khaleefa tsayar da motar, ya gangara bakin titi, jawota yayi jikinsa, ai ko ta kwanta luf tana sauke ajiyar zuciya, k'ak'k'amesa tayi tana jin wani irin abu a zuciyarta game dashi, d'agota yayi, ganin hawaye na zuba har yanzu, batai aune ba yasa harshensa ya fara lashe mata shi tas, lumshe ido tayi, sai da ya gama yabi fuskarta da kallo, wani abu na fisgarshi gareta, har baisan sadda ya had'e bakinsu waje d'aya ba, Marmah jin sabon abu a gareta yasa jikinta fara rawa, hannunta dake jagaye da jikinsa tasa ta k'ara damk'e rigar dake jikinsa, tun tana mutsu-mutsu harta daina jikinta ya mutu, sai da ya gaji dan kansa ya saketa, suna suke ajiyar zuciya a tare.
Komawa yayi ya jingina da kujerar motar, yana suke lumfashi, idonsa harya suke launi, kallonta yayi da idonsa masu kaifi da suka fara shiga wani yanayi, da sauri ta sauke idonta a k'asa tana wasa da y'an yatsun hannunta, wata irin kunyarsa ta saukar mata.
Can taji muryarsa mai matuk'ar sanyi da dad'in sauraro yana cewa "ki kwantar da hankalinki, ki daina tunanin wani, yanzu aure ne akanki, kuma insha Allahu zansa ki manta da wai ma kin tab'a son wani, idan bani ba, zansa miki sona a zuciyarki insha Allahu rabbi, kamar yadda zan koyawa kaina sonki, dan har na fara jin wani abu dangane dake"
Ya idasa maganar yana suke lumfashi, saboda dogowar maganar da yayi, itama kanta tayi mamakin maganar dake fitowa daga bakinsa.
Suke ajiyar zuciya tayi a hankali tana cewa "ai ni tuni na fidda Abbas a cikin rayuwata bare kuma a cikin raina, kawai na tuna da abunne harna baka labari"
Shuru yayi bai k'ara magana ba, saima tadar motar da yayi suka cigaba da tafiya, itama kama bakinta tayi ta tsuke, dan tasan ba lallai ya sake magana ba, kuma, ai tama yi mamakin doguwar maganar da yayi yau a tare da ita, lallai yau ta ciri tota.
Har suka isa gida, ita ce ta fara fita, ta nufi babban parlon gidan, koda ta shiga da kayan school d'inta a hannunta tayi karo da su Khairat na zaune a parlon, daga ganin alama sun dawo school ne, suka zube a parlon.
Kallonta sukai Ifteesan ta ce "kee zo nan"
Zuwa Marmah tayi ta ce "gani"
"Yauwa ina so ki shiga kitchen ki had'a min abinci kala uku, da lemo mai dad'i, zanyi bak'o ne wadda zai aure zai zo, dan haka karki sake kiyi min shirme, kin gane ko?"
Amsawa da kai kawai Marmah tayi.
Ifteesan cike da jin haushinta yadda ta wani amsa mata da kai yasa cikin fad'a ta ce "baki da baki ne?, da bazaki amsa min ba?, ko tsabar kin fara raina mutane?"
"To baza tayi ba, marassa kunya kawai, ke bazaki iya shiga kitchen d'in kiyi masa girkin ba, tunda kece wacce zatayi bak'on, idanma bazaki iya ba, kisa su Tala suyi miki mana, dole sai Marmah ce zatayi, ko kun manta matsayinta a gidan nan ne, matsayinku fa d'aya ne, babu wani babbanci, ai ba y'ar aiki bace dan haka bazata yi ba, wallahi kafin nabar garin nan na koma wajan aiki, k'ila sai na koya muku hankali, kun girma amma gaku nan babu tunani"
Y Khaleefa ya idasa fad'ar maganar da shigowarsa kenan yaji maganar da suke mata, yana jefa masu harara, ai ko ba shiri suka tsuke bakinsu suka yi shuru.
Tsaki yaja zai juya ya tafi, Marmah dake shirin barin wajan gabanta na fad'uwa, dan Allah ya gani ita tana jin tsoron taji suna fad'a a kanta.
Suka cinkayi muryar Mami na k'arasowa wajan tana nuna Marmah tana cewa,
"tsaya na ce munafuka"
Tsayawa Marmah tayi gabanta na dukan uku-uku, shima Khaleefa ba shiri ya dagata da fita.
Mami ta juyo wajan Khaleefa tana cewa "wai kai ban gane mi kake nufi da wannan yarinyar ba, mi yasa kike shiga harkarta ne haka?, ko akwai wani abu a zuciyarka dangane da ita?, ko kyanta ne ke rud'arka?, to bari kaji na gaya maka, wallahi idan ma akwai wani abu ne, a ranka, zuciyarka ta fara d'arsa maka a kanta, tun wuri ka gargad'i zuciyarka to, domin bazan tab'a lamunta ba, ka sani basai na sake fad'a maka ba, kuma daga yau karna sake jin ka shiga harkar wannan yarinyar, kuma aiki ne saita yi shi a gidan nan, tunda ba gidan ubanta bane, kuma da kike cewa wai matsayinsu d'aya, ta ina suka zama matsayi d'aya?, sufa gidan ubansu ne, itafa?, daga cin arzik'i"
Mami ta sake juyowa ga Marmah da kanta ke k'asa tana had'iye wani abu mai d'aci a zuciyarta, taji muryar Mamin na sake ce mata "ke kuma daga yau dan Allah su saki aiki bakiyi ba, kiga yadda zanyi dake a gidan nan, sana kikai kayan nan naki, kizo ki wuce, ki fara aikin data saki"
Da sauri Marmah tayi ciki tana aje kayan ta fito ta wuce kitchen domin fara aikin, itafa dan aiki baya b'ata mata rai, da Y Khaleefa zaiji maganarta daya barta tayi masu aikin, bafa raguwa tayi ba, saima k'aruwa da tayi, suda basu iya komai bafa, a haka za'aje gidan miji, ai ko tana tausaya musu, domin mazan yanzu sunfi son matansu su rink'a masu komai, bawai y'an aiki ba, ba komai zaka sa y'an aiki suyi maka ba, bare kuma hidimar mai gidanka.
A parlo kuwa Khaleefa ji yake kamar ya bud'e baki ya ce ma Mami ai yanzu matsayinta ma ya d'ara naso, tunda matarsa ce, amma saiya taushi zuciyarsa, tunda dai Mahaifiyarsa ce, ya bata hakuri, yana ficewa daga parlon.
Su Ifteesan ko dad'i ne ya rufe suna rungume Mami.
Mami ce ta kalli Ifteesan ta ce "ya akai baki sanar dani zakiyi bak'o ba?, da bansa anyi shirya wani abu wadda yafi wadda kikasa ayi masa ba, mi yasa baki sanar dani tun wuri ba?"
"A'a wallahi Mami nima sai muna hanyar dawowa daga school ya kira ni yake shaida min, wai zaizo ya gaida ku ne"
"To ai kinga Daddynku ma baya nan, da kin sanar tun wuri, ai bazai fita ko ina ba, dama burinsa ku fidda miji kuna gama school ayi bikin"
Sauke ajiyar zuciya Ifteesan tayi tana gyara zama tana kallon Mami ta sake cewa,
"Eh kuma hakane, bai sanar dani da wuri bane, amma Mami ki kira Daddyn mana zai baro wajan aikin yazo"
"Eh kuma hakane bari naje sama na kira shi, namai albishir, ke kuma Khairat sai yaushe ne naki zai kawo gaisuwar?, so nake asa muku rana a tare"
Mami ta idasa maganar tana kallon Khairat dake latsa waya.
"Hmmm Mami shima yana nan zuwa, kinsan Abuja yake aiki, daya shigo Kano to danni yake zuwa, zai zo very soon"
"To shikenan Allah ya nuna mana"
Da amin suka amsa, tayi sama domin kiran Daddy ta sanar dashi................✍️
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN