KANGIN RAYUWA BOOK 1 BY ZAHRA ROYAL .txt

Author :  Zahra Royal Star Category :  True Hausa Novels

Chapter   5 / 11

12K to 15K   out of 32.9K words

nasa wuk'a na yankaki kowama ya huta?"




Hamisu dake shigowa gabansa ne yayi wata irin mahaukaciyar bugawa ganin abinda ke faruwa, yana shirin komawa da sauri, har yana tuntub'e, da azama Habiba ta kwace daga shak'ar da uwarta tayi mata ta ce "gashi can shine wallahi yayi min cikin, kuma ba laifi na bane dole yayi min"






Wani irin salati suka sake saki Hajara ta rik'e k'ugu tana cewa "babbar magana ai da yake Kakarku d'aya kuma duk tsatso d'aya yayi ku, abun zaizo da sauk'i"




Ba wadda ya tankama Hajara Sa'ade tada kusa suman tsaye ta matsa kusa da Hamisu batai wata wata ba, ta fara bashi maruka ba k'ak'k'autawa, tanayi tana kuka, tana cewa "Hamisu abunda zaka samin dashi kenan?, Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un, Hamisu ka cuceni ina zamu kai wannan abun kunyar har haka"




Duk jikin su sai yayi sanyi ganin yadda Sa'ade ke kuka.




Maryama itama data share hawaye ta ce "na rantse da Allah Hamisu saika aure ta ko kak'i koka so"




Da wani irin mahaukacin sauri ya d'ago yana kallon Maryama.




Shigowar su Mlm da Mahaifin su Habiba dana Hamisu, kai harma da Hamza, yasa su yin shuru, sai dai aikin gama ya gama sunji komai.






Iro tsabar bak'in ciki bai san sadda ya rarumo wani uban itace ya makama Hamisu ba, yana Allah wadai da halinsa, yana cewa "ai Maryama basai ma kince ya aureta ba, wallahi dolanshi ne, tunda shi ya lalatata, kuma ciki gara da baki zubar dashi ba, sai an haife shi, kuma tana haihuwa, za'a d'aura auran"




Mlm ya rasa bakin magana Mamman ko yana shirin kamo Habiba ya rufeta da duka, da sauri Mlm ya dakatar dashi, yana cewa "dukanku mazan ku biyoni sashi na ina son ganinku, harda kai Hamisu"




Gaba d'aya Mlm suka rufama baya, a tsakar gidan ko sai maida magana ake, ganin abun zai dawo na b'acin rai da gori yasa Maryama jan yaranta suka shige d'aki.






Zaune suke gaban Mlm ya kalli Hamisu tsaf ya ce "Hamisu miye kaje kayi haka?, da kasan kana son aure miye yasa bazaka zo ni ka gaya min ba?"




Zunburo baki Hamisu yayi yana k'unk'uni wajan cewa "yo Mlm ba sai da na nuna cewa auran nake so ba, anyi min ne?, ni kuma shine yasa naje na nemarwa kaina mafita..... Wani mari da Iro ya kaima Hamisu yasa shi yin shuru da sauri Mlm ya d'aga mai hannu,


Da sauri kuma Iro ya ce "Mlm daka kyale ni nama yaron nan hankali, wallahi mu zai zauna yana gaya ma maganar banza haka"




Mlm dake kallon Iro ya ce "ai gaskiya ya fad'a, ni ai bansan wannan zancan ba, da tsaf ba'a zo ga wannan halin ba, mi yasa daya nuna yana son aure bakuyi masa ba?, yanzu rashin yin hakan mi ya jawo?"




Shuru gaba d'aya parlon yayi, Mlm ya gyara zama yana cewa "tabbayar ku nake?",




Iro ne yayi k'arfin halin cewa "Mlm ayi hak'uri, tabbas muma munyi kuskure"




Mlm ya ce "abinda zance yanzu dole a bari ita Habibar ta haihu, idan yaso sai a d'aura auran, kai gaba d'ayama y'an matan dake gidan nan, za'a had'a a ranar ayi bikinsu kowama ya huta, yanzu daba abun na gida bane, ina kukasan abun zai kai?, sana abu na gaba, karna sake naji maganar nan ta fita koda nanda k'ofar gida ne, kai hatta Sule (Daddy) ban yarda an sanar dashi ba"




Mamman ne ya d'ago ya ce "amma saboda mi Mlm?"




"Saboda bana so ma matarsa taji, dan nasan kunsan ba son danginsa take ba, a hakan ma ya aka k'are bare taji wannan abu daya faru"






Hamza ne ya ce "hakane kuma Mlm amma kasan komin dad'ewa yana iya sani, kamar zaiji babu dad'i ana waresa"




Shuru Mlm yayi can ya nisa ya ce "da wannan dan wannan amma dole ce tasa za'a b'oye masa, kuma insha Allahu abun zamuyi shi a sirrance ne, Allah zai kawo mana mafita, dan haka ko wannan ku, ya sanar da yaransa mata, su tabbatar sun fiddo da mijin aure, nanda lokacin da Habiba zata haihu"






Hamisu dake k'unk'uni shifa bazai auri Habiba ba, dan yanzu jin wata tsanarta yake har cikin ransa.




Mahaifinsa ne ya k'ara kaimai wani marin cike da jin haushinsa ya ce "ai ko mutuwa zakai na rantse saika aureta, mutunan banza kawai"






Tashi yayi ya fice yana ayyana yadda zaici uban Habiba mudun ta bari aka kaita gidansa..........✍️


*K'ANGIN RAYUWA*






*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*






*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*








SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973








Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u












Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.










*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*














*EPISODE* 9






Tun daga wannan lokacin aka hana Habiba fita koda tsakar gidan nasu ne, idan ba wani abu daya zamu dole saita fitan ba, saboda tana fita wasu daga cikin mutanan gidan zasu fara zund'inta suna magana k'asa-k'asa.




Marmah ko tafe take a hankali kamar wacce bata son taka k'asa, ta dawo daga bakin tasha daga tallar da Hajara, ta nace sai ta rink'a yi.




Yamma tayi sosai dare ya fara k'unnu kai sauri take ta isa gida kamin a fara kiran sallah.


Tazo dai-dai k'ofar gidan nasu, kamar ance ta d'aga kanta ta hangi Narnah tsaye da Abbas d'inta suna tad'i, a yadda ta gansu suna dariya suna murmushi, kai daga ganso zaka ce masoya ne.




Saura kad'an tayi tuntub'e ta fad'i, tsabar yadda take binsu da ido, cike da tsananin bugawar zuciya ta k'ara matsawa kusa dasu, wani irin zazzab'i ne taji na neman rufeta, ta tabbata an rabata da Y Abbas kenan, mutunan da take matuk'ar so, duk fad'in garin, duk yawan wadda suke cewa suna sonta, shine kad'ai ya tsiri tuta a zuciyarta.




Batai aune ba taji Narnah ta buga mata tsawa tana cewa "kee mayya karki cinye mu, ai dama na ce miki duk duniya Abbas baida matar da zai aura sama da ni, dan haka Abbas ya miki nisa, sai kije ki nemi dai-dai dake, koda yake Umma ta ce wadda ta zab'a miki na nan zuwa gobe da safe, dan haka da'aAllah Malama kallon ya isa haka, karki cinye mu nida Honey na"




Wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga bin kumatunta Marmah, ganin yadda Abbas ya nuna halin ko in kula da ita, gani ma take kamar nunawa yake bai san tsayuwarta a wajan ba, "k'alu Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un" kawai take mai-maitawa a zuciyarta.




Ba shiri tayi cikin gidan, danjin kuka na neman kwace mata.




Tana shiga gidan ko tsayawa ta kaima Hajara cinikin tallar da tayi mata bata yi ba, kai tsaye d'akin daya zamo a nan take kwana yanzu ta shige, bayan ta aje sauran kayan tallar data dawo dasu.




Tana shiga ta zube akan tabarmar da take kwana a kullum, wani irin kuka ya sark'eta, tana tushe bakinta, k'ank'ame jikinta tayi, ta cigaba da kuka marar sauti mai matuk'ar cin rai, tayi kuka sosai har taji kanta kamar zai rabe gida biyu, tsabar yadda yake sara mata.


Jawo zani tayi ta lullub'e dashi dan wani irin sanyi take ji, wani zazzafan zazzab'i ya rufeta, danda nan jikinta ya d'au wani zafi rau kamar wuta, sai rawar d'ari take.




Mahaifiyarta ta tuna, da ace ta nan da wani abun bai sameta a yanzu ba, sai dai tasan Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i, kuka ta k'ara saki, mai sassayan sauti tana matuk'ar kewar Mahaifiyarta.






Wani irin wahalallan bacci ne ya d'auke ta, tana cikin yin baccin daba dad'in shi take ji ba, taji saukar ruwan sanyi a jikinta mai bala'in sanyi, wata irin zabura tayi, danda nan jikinta ya kama kyarmar sanyi, gafgaf, har hak'oranta na had'ewa waje d'aya, kallon Hajara tayi dake tsaye kanta tana jijjiga, tsabar tsanar Marmah da take ji har bata san sadda ta kai mata wani mangari ba.


Marmah daba wani k'arfi jikinta ta tafi ta bige da wani kututturan icce ta bige kanta dashi, daya sata sakin wata uwar k'ara, kanta dake ciwo ya k'ara yin wani dum, ji take kamar kan nata ba'a jikinta yake ba.




Hajara ta buga mata tsawa tana cewa "to makira al'gunguma, ina kud'i na?",




Da sauri Marmah ta raromo k'unshin kud'inta ta mik'a mata, kwata-kwata halin data shiga ne ya mantar da ita, bata je takai mata kud'inta ba.




Sai da k'irga su ya kai sau uku tukun ta maido dubanta wajan Marmah ta nunata da yatsa tana cewa "da nufinki ki cinye kud'in komi?, makira, kuma ki bud'e kunnanki da kyau kiji ni, gobe wadda zai aureki ko na ce wadda na zab'a miki zaizo, saura idan yazo ki nuna masa halin akuyancin naki, kuma na rantse miki mudun iyayanki maza suka tabbaye ki, shin kina sonsa, kika tsake baki amsa da eh kina sonsa ba, hmmm Marmah kenan, kinsan Allah na rahira saiya fiki jin dad'i, dan rantse miki sai kin gwammace dama uwarki bata haifeki ba"




Shuru Marmah tayi zuciyarta na wata irin bugawa, kamar zata tsaga k'irjinta ta fito, ta kasa cewa k'ala.




Sai Hajara dake mata kallon tsana ta sake cewa "baki jin abinda na ce ne?, kikeyi k'unnan uwar shegu dani, y'ar iska marar tarbiyya"




Ba shiri har bakin Marmah na rawa ta ce "naji Umma"


"Yo karda ma Allah Ubangiji yasa kiji mana, jikinki ne dai zai gaya miki, kika sake kikai min ba dai-dai ba, dan wallahi sai na k'ara d'ai-d'aita rayuwarki, a K'ANGIN RAYUWAR nan dana saki, to wallahi kikai min shirme, sai na k'ara saki wadda yafi wannan da kike ciki, idan k'unne yaji gangar jiki ta tsira"




Tana gama fad'ar haka ta fice tana jan dogon tsaki.




Marmah share hawayen dake zubo mata tayi, duk da tana sharewa wasu ne ke faman zubowa ba k'ak'k'autawa, sauke ajiyar zuciya tayi tuna ledar maganin da Mlm ya sai mata, yasa da sauri ta jawota ta b'alli magani tasha, Allah yaso harda na zazzab'i da ciwon kai ya sak'o mata, hakan yasa danda nan tasha, kamin wani d'an lokaci zazzab'in ya fara sauka zufa ta fara rufeta, ciwon kanma ahankali-ahankali yatai sauka, wani bacci na neman d'aukarta, har yanzu idonta na hasko mata Abbas d'inta da Narnah, a yadda suke soyayya suna tad'i, girgiza kai tayi, tana saurin rufe idonta da k'arfi, tana ma Mlm addu'a dan idan badan shi ba, da K'angin rayuwar da zata shiga sai yafi haka, saboda yawanci shike sai mata sabolun wanki dana wanka, wani lokacin wajansa take zuwa idan an hana ta abinci, shike sai mata, da abubuwan da ba'a rasa ba, shi yasa daya ganta yake karantar wane hali take ciki, wani lokacin ba sai ta tabbaya ba yake sai mata, shi yasa take matuk'ar son Kakanta, Mlm tun yana ma Hamza fad'a akan rashin kulawar da yake ba Marmah harya gaji ya daina sai dai ya bisa da addu'a, dan a yanzu yasan an shiga tsakanin Y'a da kuma Uba.




Washe gari da safe Marmah ta tashi ta fara ayyukan gidan nasu, duk fad'in gidan haka take zagewa ta share shi tas, tun bata sababa harya bi jikinta, tana gama sharar kuma ta fara uban wanke-wanken gidan yadda kasan shagon saida kwanoni, tana yi tana hutawa saboda zazzab'in da tayi jiya, so har yanzu ba wani k'arfi a jikinta.




Tana cikin yi Habiba ta fito, cikinta harya fara tasawa, tabi Marmah da kallo, kamar na tausayi, tana tsaye saiga Hamisu ya fad'o gidan ko sallama babu, ai ko yana hango Habiba ya nufi wajanta yana nunata da yatsa yana cewa,




"Yauwa dama tuni nake son ganinki, kinga Habiba kika sake aka d'aura auran nan dani dake, wallahi Allah na rahira sai ya fiki jin dad'i, dan sai kin gwammace dama baki tab'a sanina a rayuwa ba, tun wuri ya kamata kije ki zubar da cikin nan, dan bazan tab'a son abinda kika haifa ba wallahi"




Habiba dake kallonsa sama da k'asa ta aje butar dake hannunta, dama band'aki zata shiga, shine yasa ma ta fito.


Ta nuna sa itama da hannunta ta ce "to sannu ubana, na ce sannu ubana, ka bud'e kunnanka da kyau kaima kaji ni, kaga wannan cikin nan gani nan bari ne wai an kama kazar mayya, sana idan na aurekan an kaini gidanka domin Allah karka barni da rai kaji?, dai-dai nake kai fa Hamisu, na fika d'anyan kai duk yadda kake tunanina na wuce nan, dallah matsa ni kaban waje kona hanb'arar dakai a wannan wajan"




Marmah dake duk'e tana wanke-wanke sosai fa abun yabata mamaki domin ko bata san mike faruwa ba, addu'ar shiriya kawai tayi masu ta ci gaba da yin abunda ke gabanta, duk da can cikin zuciyarta abun ya tab'a ta, wannan abun kunya har cikin family naso, "kai Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un" kawai take anbata a cikin zuciyarta.






Hamisu dake kallon Habiba ya kasa ce mata komai, sai binta yayi da ido harta shige b'an d'aki.




Juyowa yayi zai fice ya hangi Marmah dake wanke-wanke, baiyi wata-wata ba, ya rarumo dutse ya saita goshin Marmah ya jefa mata shi.


Ai ko ya sameta a dai-dai goshin nata, da wani irin sauri ta tashi tana dafe goshin nata, sai hawaye shaaaa, tana kallon Hamisu, miye tamai haka zai mata wannan muguntar?, take tabbaya a zuciyarta.




Can taji muryarsa yana son huce haushinsa a kanta yana cewa "to tsananniya makira, shine kin wani kasa kunne kina sauraran abunda muke cewa, ai dama ke na durka ma cikin aka bani ke"




Da azama ta k'ara ware idonta akansa bata san sadda bakinta ya furta "Ubangiji Allah ya kiyashe ni, da fad'awa irin wannan k'addara, kuma aniyarka tabika wallahi, wannan ai mugun fata ne......... Shuru tayi ba shiri tana tushe bakinta, dan bata san ta fad'a bama, ganin yadda Hamisu ya cika yayi fam, ganin yana nufo wajanta, yasa da azama zata juya domin guduwa, sai dai charaf ya ruk'o................✍️


*K'ANGIN RAYUWA*






*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*






*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*








SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973








Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u














Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.












*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*














*EPISODE* 10


Kuka Marmah ta saki tana ba Hamisu hak'uri, ganin yadda ya kama tsintsiyar hannunta, batai aune ba ya sakar mata wani gigitaccan mari, yana murd'e hannunta ta baya.


Wata irin k'ara ta saki ta azaba.


Kawu Mamman dake shigowa cikin gidan, ganin abinda Hamisu ke shirinyi yasa ba shiri ya matsa kusa dasu, Hamisu baisan da tsayuwarsa ba, sai dai yaji saukar mari shima a kumatunsa, ai ko ba shiri ya saki Marmah dake kuka, sauke ajiyar zuciya tayi tana komawa gefe, tanama Allah godiya daya kawo mata Kawu Mamman, dan Allah ya gani yanzu tsoron Hamisu take ji, tunda yayi mata jakin duka.




Hamisu ne ya juyo yana bin Kawu Mamman da wani irin kallo.


Kawu Mamman daya tsaya akansa yana cewa "ko zaka rama ne?, marar kunyar banza marar kunyar wofi, ai duk ina kallon mike faruwa, ubanmi tayi maka zaka kama bugunta?, ko tsabar cin zali ne, kai gaka tsohon mugu, wai kai ko kunya ma baka ji ne?, dallah b'ace min da gani ni, dan idan ina ganinka na rantse wani bak'in ciki nake ji, duk irin halin daka sa mutane baka dubaba ka daina abunda kakeyi, wato saima abinda yayi gaba kenan?, to Ubangiji Allah ya shiryeka, idan kana da rabon shiryowar"






Ya idasa maganar yana nufar sashin Mlm.


Hamisu dake daskare waje d'aya, yak'i motsawa bak'in ciki ya dabaibaye mai zuciya, yana nan tsaye, Marmah ta lallab'a ta fad'a d'an d'akin da take kwana.




Har Habiba ta gama ta fito Hamisu na nan tsaye, kallonsa tayi tana tab'e baki, duk taji abunda ya faru bayan shigarta band'aki tana tafiya ta kusa shiga d'akinsu ta ce "idan bakai wasa ba dai, a haka zaka k'are solob'iyo kawai, kai in banda k'addara mi zanyi dakai fisabilillahi, ai ka cuce nima wallahi"




Tana fad'in maganar tayi shigewarta d'aki ta barshi da jin haushi biyu, juyawa yayi buguzin-bugunzin ya fice daga cikin gidan.






Marmah na zaune a d'akinta tana faman linke y'an suturinta daba wasu bane, ta tsinkayi muryar Hajara na faman kiranta.




"Kina ina ne wai?"


Cewar Hajara dake shigowa d'akin Marmah.




Marmah dake saka hijab, ta ce "gani Umma"




"Yauwa kinga abinda nake so dake, ki fita waje, ga Dangana can yazo, shine wadda ya nuna yana sonki, kuma shine wadda zai aureki, dan haka maza ki fice yana jiranki k'ofar gida"




Marmah dake tsaye a daskare tayi mutuwar tsaye, bakinta na kyarma wajan furta,




"Dangana kuma?, Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un badai Danganar data sani ba, mai mata biyu, gason y'an matan tsiya ne dashi, ga gidansa da garda-gardan mata da maza, ga matansa y'an bala'i ne, ita ko ina zata kai Dangana"


"Kware kuwa au ashe ma kinsan sa har haka, harkika karanci irin rayuwarsa haka, kinga abun zaizo da sauk'i ma"




Hajara ta idasa maganar tana mata kallon raini wayo.




Hannu Marmah ta d'ora a saman kai, tana zubewa k'asa ta kama k'afafun Hajara tana cewa,


"Dan girman zatin Allah ki taimaki rayuwata Umma ina zankai rigimar iyalansa, Dangana ba sa'an yina bane, indai Abbas ne wallahi na rantse miki na barma Narnah shi ai tuntuni, ki taimaki rayuwata karki had'ani aure da Dangana"




Ta idasa fad'ar haka tana sakin kuka.




Wani murmushi Hajara ta saki tana cewa "yarinya kenan ai idan kinga baki auri Dangana ba, sai dai idan bana raye, a wannan duniyar, amma mudun ina duran duniya sai kin shiga gidan Dangana, karma ki b'ata bakinki wajan bani hak'uri, domin ko bayi zanyi ba, kuma banza janye k'udurina ba, kuma da kike cewa, wai kin barma Narnah Abbas, ke kin isa ki bar mata shi, inahh ai da k'arfin ikona nasa Abbas ya dawo da soyayyar da yake miki akan Narnah, domin ke baki dace da irin

5 / 11