KANGIN RAYUWA BOOK 1 BY ZAHRA ROYAL .txt

Author :  Zahra Royal Star Category :  True Hausa Novels

Chapter   3 / 11

6K to 9K   out of 32.9K words

k'ara sauke ajiyar zuciya ta ce "na rantse Ya Khaleefa d'an rigima ne, karkiji yadda zuciyata ke harbawa, ita kuma Mami harda cewa wani munyi kewarshi, nidai wallahi bana so ya dawo, kwata-kwata komi kayi shi a wajansa kayi laifi"




Ifteesan ta amshe da cewa "hmm ai ni abinda yake ban tsoro ma a tare dashi idan ya fad'i magana koda baki ji ba, tofa kin kad'ai dan bazai maimaita miki ita ba, sai ya mula ya munmule tukun, gashi Mami tasa shi ya kusa dawowa"




Ifteesan ta kwab'e baki duk jikinsu yayi sanyi, ga zuwa K'auye da aka tilas tasu zuwa gobe.






HAJARA POV




Shigewa d'akinta tayi da Marmah a hannunta tana zuwa ta dungure ta waje guda, yarinyar ta saki kuka domin yinwa take ji, kallonta Hajara tayi cike da tsana tasa d'an yatsa ta dungure mata kai, tana cewa "kee jarababbiya kin ishemu da kuka, Allah ji nake kamar na shak'eki ki mutu kibi uwarki kowa ma ya huta, shegiyar yariya da kyau kamar y'ar aljanu"




Ta idasa maganar tana sakin tsaki tashi tayi tana harkar gabanta duk kukan da Marmah keyi hakan baisa ta aje abunda take yiba, baiwar Allah tun tana kukan har wani wahalallan bacci ya d'auke ta, jin shuru Hajara ta saki tsaki tana k'ara cewa "da karda ma kiyi shurun ko mutuwa zakiyi da yinwa sai ubanki ya kawo abinda za'a baki, nidai ba nono zan baki ba, a'ato".








Bishira ce ta fito daga d'akinsu ita da y'ar uwarta Habiba ance wata shegiyar kwalliya za'a fice talla, daga yin mutuwa amma su ko a jikinsu daga su har uwarsu, Maryama dake masu kirari tana kod'asu har suka shiga zaurar gidan suna faman washe baki.




Hamisu ne ya taho bai lura dasu ba kawai yaji an bangaje, tsayawa yayi yana nuna Bishira da yatsa cike da jin haushin yaran ya ce "keee dabbar ina ce bakya gani ne?, kuna tafiya sai kace mahaukata",


Wata uwar hararara Habiba ta banka mai tana murgud'a mai baki, Bishira dake mai wani kallo na raini ta rik'e k'ugu ta ce "to sannu mai hankali kai akwai ma wadda ya kaika rashin hankali, ai cikin mahaukatan garin nan kaine lanba d'aya, mai shaye-shaye har an gaya mai rashin hankali".




Batai aune ba ya matso kusa da ita yana d'auke ta da wani kyakkyawan mari tasssss tassss, wata irin mahaukaciyar chafka ta mai ta chakumo wuyan rigarsa, itama kamin ya sauke hannun nasa itama ta wanke shi da nata marin, tana sakin shi ta hankad'eshi gefe, kamar wani kayan wanki.






Wata shewa Habiba ta saki tana cewa "kai amma y'ar uwata na rantse kinmin dai-dai, shashasha kawai marar hankali",




Tasowa yayi a zuciye yana nuna kanshi da cewa "kaiii ni ne marar hankalin?".




Wata shewar suka sake saki suna cewa a tare "yo kaine mana akwai wani ne dake tsaye a nan bayan kai?, hankalin ne da kai?, ai kowa yasan mai shaye-shaye da neman mata basu cika hankali ba, ni wallahi kama cucuni dana had'a jiki da kai Allah ya isa na kuma wallahi bari ma ka gani".




Bishara ce ta idasa maganar ta k'arshe tana sakin wani uban kuka tayi cikin gidan nasu da gudu, tana kururuwa, yadda kasan ana yankan naman jikinta.




Dukansu mutanan gidan ba shiri suka fito, Maryama ko har tuntub'e take wajan fitowa, tana tayi saurin isa kusa da Bishira tana jijjaga tana dudduba jikinta sai faman tabbayarta take miye ya same ta.




Habiba dake shigowa tare da Hamisu daya saki baki yaga wane irin shirri, Bishira ke son k'ulla mai.




Itama Habiba kukan munafurci ta saki tana nuna Hamisu.




Ba shiri Maryama ta matso kusa da Hamisu taci kwalar rigarsa tana cewa "to tanbad'and'e ubanmi kayiwa yara na?, na rantse da sarkin dake busan lumfashi zan sharara maka mari idan baka gaya min abunda kayi musu ba, haka nan dai baza su shigo gidan nan a haka ba, zaka yi magana ko kowa d'an iskan yaro kawai"






Sa'ade ce tazo ta bangaje Maryama tana cewa "keee Malama dagata na ce abun ya isa haka, ban haifi d'an iska ba, na gaji da irin abubuwan da ake ma yaro na a cikin gidan nan gaskiya, mi yasa ba zaki iya tabbayar yaran naki ba sai shi?".


Hajara dake tsaye ta rik'e k'ugu tana murmushin jin dad'i tana so taga ya za'a k'are.




Bishira ce ta k'ara sakin kuka tana cewa "Mama wallahi Hamisu d'an iska ne, munzo fa fita zaure shine na d'an bigeshi ban gani ba, na basa hakuri, amma kawai ya mare ni yana rungume ni yasa hannunsa cikin rigata yana matsa min nono Na........




"Innalillhi",




Gaba d'aya suka d'auka da cewa.




Wani kukan kura Maryama tayi tana zanfga ma Hamisu wani gigitaccan mari, ba shiri yayi baya-baya zai fad'i, da mugun sauri Sa'ade ta taro shi, tana taroshi ta matsa kusa da Habiba itama tana zafga mata mari tasssss tassss kake ji...........✍️


*K'ANGIN RAYUWA*






*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*






*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*








SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973










Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u








Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.












*EPISODE* 5




"Kutumar uba, keee shine kika mareta?"




Cewar Maryama dake rungume da yaran nata sai kuka suke kamar wasu yaran goye.




Sa'ade dake tsaye kansu ta ce,


"An mareta d'in ko zaki d'au mataki ne?, ashe babu dad'i, ni da kika mari nawa d'an"




Tana gama fad'ar haka taja Hamisu cikin d'aki tana mai mitar ya daina shiga shirgin wannan gidan.




Watsewa akai sai Hajara dake tsaye ta saki wani tsaki "mtswwww aikin banza kawai, kai amma fa, Maryama kin ban mamaki, harki tsaya waccan kucakar matar ta mari Habiba, ai wallahi da ni aka tab'o da tawa d'iyar, yau da ansha kallo hmm"




Ta idasa maganar tana yin kwafa tayi shige cikin d'akinta.




Inna Khande dake tsaye har yanzu ta matsa bakin murhu domin d'ora sanwa, dan Daddy yayi mata waya suna tafe, shi yasa bata cika shiga dama harkar gidan ba, su Inna Suwaiba ko danba da nasu ake ba shi yasa sai dai suka tsaya kallo, dan basu cika shiga harkar jikokin nasu ba.




Da yawan mutanan gidan jin labarin Daddy na hanya yasa kowa fitowa suka fara taya Inna Khande aiki, sai nan nan ake da ita, kallonsu kawai Inna Khande keyi tana murmushi, dan tasan da biyu suke mata wannan abun, saboda sunsan mudin Daddy yazo garin kowa sai bashi kud'i masu yawa, su k'ara jan jari, bata tab'a hanasa ba, ita kawai idan aka zagi yaranta ne ko aka tab'a su, nanne fa zakuyi bata kashi da ita.




A wajan Marmah baiwar Allah da kyar Hamza ya sayo mata madara saboda Kwata-kwata an kauda hankalinsa daga gareta, madarar ma da aka kawo sai da Hajara ta fara ba Nana d'iyarta tasha ta more tukun sauran data rage, ta d'akko Marmah dake tsutsar hannu, ta dungura mata madarar, tana bata tana faman zaginta, ji take kamar tasa mata guba taci ta mutu kowa ma ya huta, yadda kasan ta rik'e garwashin wuta haka take ji.






A sadda su Mami suka iso suka shiga cikin gidan, Mami da yaranta ba abinda suke sai yatsine baki suna tafiya a hankali cikin gidan suna bin mutanan gidan da wani d'an iskan kallo, suma kansu mutanan gidan duk d'okin zuwansu sai suka sha jinin jikinsu, kai tsaye d'akin Inna Khande suka sauka ba laifi d'akin Inna Khanden an gyara shi sosai har ban d'aki anyi mata cikin d'akin nata, kuma duk aikin Daddy ne, babu abinda baya ma uwarshi, duk wani kayan more rayuwa yasa mata a d'akin, shi yasa koda su Mami suka shiga d'akin sai suka saki jikinsu sunata labari da Kakarsu, Mami ko sai danna wayarta take, mutanan gidan sai shigowa suke suna gaida ita, da kyar take amsa gaisuwar, harta gaji da amsawa sai dai ta d'aga kai kawai tana yatsina.






Hajara ko tana fitowa ta saki wani shegen tsaki tana mita a fili tana cewa


"Kaji y'ar iskar mata sai wani d'agin kai take, tana ma mutane iskanci, kai jama'a dama fa mutanan birnin nan basu cika mutumci ba, aka ce, ai ko na shaida wajan matar Sule"




Hadiza dake zaune akan dakalin d'akinta ta amshe da cewa "hmm Hajara kema kya fad'a, kuma da take wannan d'agin kan mijin nata dai shima d'an K'auyen ne, baki ga yaran Sulen ma ko kallo basu ishi mutane ba, suma an koya musu wulak'anci da tsirfa da iyayin tsiya"






"Sayi ma wadda ya shiga harkar su ai, dan wallahi nikam bana d'aukar wulak'anci a'ato, harsu gama kwanakinsu basai in ta k'ara gani na bama, shegiyar mata ita ba kyau ba sai wani faman tab'e baki take, tana cika tana batsewa",


Cewar Hajara dake tsaye ta rik'e k'ugu, sosai fa abunda Mami tayi musu bai mata dad'i ba.




Hadiza ko dariya ta saki tana cewa "kai Hajara karfa ajiki a'ato, dan kinsan gidan nan saboda abun duniya ai ake mata wannan biyayyar, da ace bata dashi ko mijin nata baida shi, ai ko kallon su baza'ayi ba".




"Yo dama waze kalle su Hadiza?, ai dan abin duniya yanzu ake abu, anayin abu ne dan son a sani, ni da nice a matsayin Mamin na rantse miki k'ila sai nayi abunda yafi nata ma, ko ina d'ayan yaron nan nata mai shegen miskilancin tsiya?, da shegen kyau kamar aljani shima kamar ba cikin tsatsun nan ya fito ba, Allah yadda kasan bature wannan yaro"




Hajara ta idasa maganar tana ayyana ina ma Ya Khaleefa ya kasance siriki a gareta dan dukansu mutanan gidan sunsan waye Ya Khaleefa, yana matuk'ar birgesu, sosai ba kad'an ba, shi yasa indai zaizo K'auyen da yawan y'an matan garin ke tururuwa zuwa kallonsa, shi kuma gashi baya son hayaniya, sai dai ya shige cikin mota yana faman tsaki.




Itama kanta Hadiza shuru tayi tana hasaso abinda Hajara take tunani itama tana ma d'iyarta fatan samun miji kamar Ya Khaleefan.




Da safiyar ranar su Mami suka je suka gaida Mlm, sai jan yaran yake a jiki.




Da kyar da kyar dai suka idasa sati d'ayan suka wuce Kano inda Daddy ya cika mutanan gidan da alkhairin daya saba, musu, suna ta murna, inda sosai yaso ya amshi Marmah amma fufur Hamza ya k'i, inda Mami ma ta bigi k'irji tana mai surutu, danmi ma zai ce ya wani d'auki yarinyar mutane, wai ruk'o, itafa bata jin zata iya rik'e d'an wani, ba nata ba, kawai dai yarinyar ta bata d'an tausayi kad'an, kamin Daddy ya fara cewa wai zai d'auketa, yana furta haka taji ta tsani yarinyar, dan idan akwai wa'inda ta tsana to dangin mijin nata ne, bata so su rab'eta ko kad'an, bare susan wane hali suke ciki, daga yaranta sai danginta, Daddy ko kallonta kawai yake cike da takaicinta, yayi alk'awarin koba yanzu ba, saifa ya d'auke Marmah koda ta fara girma ne sai dai Mamin tayi duk yadda zatayi...................✍️


*K'ANGIN RAYUWA*






*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*






*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*








SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973










Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u








Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.








*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*












*EPISODE* 6






A kwana a tashi har shekaru Goma sha uku sun waci inda a wannan shekaru abubuwa, da yawa sun faru, sosai Marmah ta fuskanci kalubale daban daban a wannan shekaru, tunda ta fara tasawa tana da jikin girma idan ka ganta saika rantse tayi shekara goma sha tara ko sha takwas ne, amma shekaru sha uku ne da ita, jikinta ya k'ara murjewa ga uban Hips dake gareta ga cikakkun nonuwa wadda suka cika k'irjinta, tubarkalla, kota ina Marmah ta zama cikakkiyar budurwa, ga tsananin kyanta dake k'ara fituwa, danma wahalar da take ciki tana b'oye wani kyan nata.




Tana shan wahala wajan Hajara dan ko, waje d'aya suke kwana da Narnah, zata malala fisarin kwance tun suna shekara uku zuwa hud'u, mai yawa har ya tab'a Marmah da safe idan Hajara ta gani saita kama Marmah da uban bugu, har sai taga bata iya d'aga hannunta, tana zaginta tana kwashe mata albarka tana cewa ai ita ce tayi fitsarin, duk sanyi duk zafi aka zata wanke kayan fitsarin tana kuka.




Duk wasu ayyukan gidan sai dawo kanta, da Inna Suwaiba ta fara tausaya mata, tunda Hajara ta fuskanci haka, ta fantsama wajan Bokanta, ya rufe ma Inna Suwaiba baki kwata-kwata bamai tausayin Marmah, an shafa mata bak'in jini, gata tunda ta taso ta fuskanci Mahaifiyarta bata a raye dan kuwa Hajara saita kira sunan A'i sana ta dark'ara mata zagi, shi yasa tun tana goye ta fuskanci Hajara ba ita ce ta haife ta ba, duk gidan a waje d'aya ne take jin dad'i wajan Kakanta.




Tsaye Marmah take a bakin turmi tana wani uban surfe na masara da za'ai tuwon dare da ita, kusan tiya uku, tsayawa tayi da dakan, tana rik'e k'ugunta, duk'ewa tayi tana dafe k'irjinta yadda taji yana mata ciwo kamar zai rabe gida biyu, daka kalleta danma tana da tsawon k'afa girman jiki, dan ko girman jikinta yafi k'arfin shekarunta.




Batai aune ba taji maganar Hajara kanta tana cewa,




"Kee tsayawar uban mi kike?",




Da masifar tsoro da bugawar zuciya ta mik'e tana cewa "a'a Umma bana jin dad'i ne shi yasa na d'an tsaya na huta",




Wata muguwar hararara Hajara ta makama Marmah kamin ta ce "to makira kin wani langwab'e, wai baki jin dad'i, to ubanwa kejin dad'i nufinki?, to aiki ne dai ke jiranki ga wanke-wanken gidan nan can na jiranki, idan kin gama kuma ki maza-maza ki d'ora min sanwa idan ba haka ba kuma jikinki ne zai gaya miki",




Wasu irin hawaye ne suka shiga zuboma Marmah akan kyakkyawar fuskarta, tana duk'awa har k'asa kusa da Hajara ta kama k'afafunta tana cewa,


"Dan Allah Umma kiyi hakuri wallahi bazan iya d'ora k'atuwar tukwainyar can ba, shi yasa k'irjina ke ciwo saboda d'aukarta da nakeyi",




Wata shegiyar hanb'ara tayi mata da k'afarta, Marmah har saida ta wuntsila ta kifa a k'asa, Hajara ta d'an duka inda Marmah take yashe a k'asa tana hawaye, tana cewa "to bari kaji na rantse koda k'irjin naki zai rabe gida biyu sai kinyi sanwar nan, makira al'gunguma harda wani kukan munafurci, da'aAllah tashi ki kama abinda ke gabanki ko kija ma kanki mugun duka yanzun nan wallahi",




Da sauri Marmah ta tashi tana goge hawayen dake sintiri akan kumatunta ta fara dakan cike da k'arfin hali, ga gadda-gaddan y'an mata a cikin gidan, babu abinda suke sai zaman banza, da yawan banza, wadda sun girme ta nesa ba kusa ba, amma baza a iya sasu aiki ba sai ita.




Cike da k'arfin hali take aikin harta gama surfen ta d'ora ruwan tuwon, ta d'au masarar ta nufi wajan nik'a.




Tana tafe tana faman tunanin rayuwar da take yi ace Babanta bai damu da damuwarta ba, sai dai ta y'ar uwarta, komai ya samu ko ya sayo to na y'ar uwarta ne, tunda ta taso da kyar yasa ta a makaranta itama wani lokacin da kyar Hajara ke barinta zuwa ita kad'ai dama ke zuwa, y'an matan gidan nasu dama tuni sun daina zuwa suna idasa furamari karatun naso ya katse, sai yawan tallah da suke yi da tsayawa da samari, ko wacce aure take so, dan har ana shirye-shiryen auran da wasu.




Batai aune ba taji muryar Abbas saurayinta mai k'aunarta tun tana y'ar mitsitsiyarta d'an Sarkin garin ne Abbas shi kad'ai ne a gidansu ana ji dashi dan har birni aka fidda shi yayi karatunsa mai tsawo, da yawan y'an matan garin suna mugun sonsa, suna burin ace sun aure shi, amma ita Marmah Allah yayi mata farin jini ko a makarantar boka ko Islamiya, saboda Marmah tana mugun kok'ari, da anyi abu ta hadda ce kenan tun tana shekara uku ta sauke Al'qur'ani mai girma, duk fad'in garin kusan ita ce kad'ai ta tab'a dagewa harta tayi karatun addini mai zurfi, ba irin wahalar da bata sha ba, dan Kakanta Sani ya tsaya mata dan yana mugun tausayinta, wani lokacin idan ya shigo cikin gidan yaga an tsareta da uban aiki, dan kar taje makaranta, shike rufe mutanan gidan da fad'a ya tasata gaba har Islamiya, tana jin dad'in haka, shi yasa take bala'in son Kakanta.




Inda Hajara ke mugun jin haushinsa tayi-tayi Bokanta yayi maganinsa amma uban ya gagara, domin ko Mlm yana da ruk'o da addu'a, shi yasa ta kasa galaba a kanshi.






Abbas daya tsaya a kanta yasa hannunsa yana ja mata hanci, da sauri ta dawo hayyacin ta d'an matsawa gefe tana jefa mai murmushin nan nata mai kashe mai zuciya da ruhi, dariya yayi yana sa hannunsa ya amshi buhun dake kanta dake d'auke da masara.




Ya ce "kaii bakya jin nauyin masarar nan, ai ta miki nauyi, ina sauran y'an gidan naku da baza'a aike su ba sai ke?"




"Hmm Ya Abbas kenan, kana yawan maimaita min irin haka kuma kasan ai dai ba aiken nasu ake ba saini ya kamata ka rik'e hakan a ranka"




"Kinsan Allah na k'agara na aureki ko na d'auke ki daga gidan nan naku, kina ban tausayi wallahi"




Dariya Marmah tayi ta ce "kaii Ya Abbas duka nawa nake?, duka fa shekara ta sha uku fa ai ban isa aure ba, kuma kaga ina da burin yin karatu mai zurfi, ko zaka barni nayi karatun?",




Dariya ya saki shima yana cewa "eh man zan barki mana, ai tunda nayi karatu kema sai kinyi insha Allahu, kuma da kike cewa baki isa aure ba a hakan?, hmm idan aka kawoki gidana zan nuna miki kin isa ai"




Dariya ta sake saki tana sa tafin hannunta ta rufe fuskarta.




Haka suna tafiya suna raha har sukaje inda ake nik'an sukayo suka dawo, a hanyar su ta dawowa ne, Narnah ta dawo daga tallar shinkafa da take yi a bakin tasha dake garin, kamar ance Marmah ta juya taga Narnah a k'ofar gidansu tana kallonsu tana girgiza kai, cike da bak'in

3 / 11