Author : Zahra Royal Star Category : True Hausa Novels
daran ta kasa gane kansa, da akazo wajan ma'amular aure kuwa, da zafi-zafi Abbas ya rink'a tafiyar da Narnah ba wata nuna soyayya tasha azaba iya azaba, kuma yana gamawa ya sauka daga kanta ko ci kanki baice ba, tana kuka da neman ceto, duk yadda take kallon Abbas zai bata kulawa ya riritata sai taga sab'anin haka.
Haka nan dai ta daure ta gyara jikinta, zuwa safiya jikinta da kasanta sunyi tsami, dan ko tafiya da kyar take yi, da kyar ta fito parlo, ganin Abbas yashe a k'asa yana ta sharar baccinsa, kamar an tsikare shi ya tashi, tana ma Narnah wani kallo kamar yau ya fara ganinta, sai can ya ce "ke ina kalacin safe na?"
Wani kallo Narnah tayi mai tana cewa "kamar ya daga aure jiya nifa amarya ce kuma ma bana jin dad'i bazan iyayi ba, jiya duk ka gajiyar dani"
Tashi yayi yana dafe kansa jin yadda ya sara mai, dan jiya wani abokinsa ya basa wasu kwayoyi yasha wai na rage damuwa ne, don tun ranar da akace an kauda hankalinsa daga Marmah ya shiga wata matsananciyar damuwa, shi yasa ya had'u da wani abokin banza yake d'orasa a harkar shaye-shaye, shi yasa jiya ya afkama Narnah ba wani tausayi.
A ranar da daddare ma Narnah abunfa ya fara bata tsoro, da rana komai ta ce mai yi mata yake, koda zata gaya mai magana ne kuwa, bazai ce komai ba, amma da zaran yasha yayi mak'is zaizo mata a buge.
Tushe hancinta tayi jin wani warin giya na feso mata ganin Abbas ya nufo inda take, tana shirin guduwa ya chafkota, ya had'ata da bango, yana faman shinshinar ta, wani irin mai ne ya taso ma Narnah jin Abbas na niyar kai bakinsa cikin nata, ai ko ta kwararamai shi a fuska, bai san sadda ya kwasheta da wani gigitaccan mari ba, ya rufeta da duka baji ba gani, ya kuma taushe ta a nan tsakar d'aki ya haye kanta, saida yayi mata kaca-kaca saida ya tabbatar ya biya ma kansa buk'ata sana ya sauka daga kanta ya zubewa a jikinta ya kwarara mata wani amai itama mai shegen wari, Narnah ta kasa koda d'aga hannunta ne sai uban kuka take, ga k'asanta dake mata zafi kamar ana yankarshi, dama ba wani warkewa tayi ba, jiya daya fara saninta, dama bata dad'i ya biyar da itaba.
A cikin kwana biyu Narnah duk ta rame saboda azabar da Abbas yake gana mata, mundun yana cikin maye, ubanta yake ci la'ada waje, harsai mayen ya sake shi ne, take yin yadda taso dashi, ta rasa yadda za'ai ta hanashi shaye-shaye.
Irin wannan rayuwar ke faruwa a gidan Narnah, gashi auran ba wani dad'ewa yayi ba, bare tasa ran fita taje wajan uwarta, kota samo mata mafita.
A wajan Habiba ko, itama dai babu wani jin dad'i saboda tunda aka kaita bata ga Hamisu ba, sai a kwana na biyu yazo mata a buge shima, amma da yake tasan kansa rufe d'aki tayi ta barsa a waje sai faman d'ora mata ashar yake yana zaginta, bata damuwa ba, tayi kwanciyarta, sai washe gari tana fitowa ta gansa yashe a k'asa, aiko bata tsaya komai ba ta d'ebo ruwa masu sanyi ta watsa mai a jiki.
Wata irin zabura yayi yana tashi yana d'ora mata zagi, dariya ta saki tana kallonsa ta ce "kai ko kunya baka ji jibeka da'aAllah kamar wani d'an bori"
Cike da b'acin rai ya dubeta yana cewa "kee dankin rainani ni zaka watsa ma ruwa?, kuma jiya shine kika rufe min d'aki, d'akin na uwarki ne da zaki rufesa?"
"Kai Hamisu dakata karka sake karka soma k'ara zagar min uwa, kuma d'aki na rufe indai zaka rink'a zomin a buge wallahi bazan tab'a bari ka shigar min d'aki a haka ba"
"Ke dalla rufe min baki an zageki d'in ko akwai abunda zaki iya?, y'ar iska kawai wacce ta gama tanbadewarta a waje, har wani abun arzik'i ne a d'akin naki?"
Dariya Habiba ta saki tana shewa da cewa "y'ar iska ko y'an iska, ka rink'a sa munjaye Malam, waya b'ata ni d'in inba kai ba, ai kaine babban d'an iska"
Tana rufe baki ya d'auketa da mari, ai ko shima baiyi aune ba, ta d'auke shi da nata marin, kallon juna suke ido cikin ido, nuna kansa yake yama kasa magana, sai Habibar ce ta ce "kware na mare ka mana, ubanwa yasa ka fara mari na, kaifa bari kaji na gayama, nice dai-dai dake dama, idan kayi min dubu saina rama, kasan dai ba fin k'arfi kayi ba, saboda k'arfin naka duk ya k'are wajan shaye-shaye, taba da wiwi, da giya duk sun tsotse sa, to ka bini a sannu, dan banza tab'a bari kayi min wulak'anci ba ban rama ba wallahi"
Zage-zage sukai tayi har makwafta sun fara jiyo su, k'arshe Habiba ta shige d'aki tana bugamai tsaki.
Hakace take kasancewa a gidan su Habiba itama, cikin kwana biyu babu wani jituwa a tsakaninsu, kullum tunda akai auran kwana uku kenan, kullum cikin rigima suke, idan yaso samun wani abu daga Habibar saiya kama lallab'ata, to tsakanin mata da miji sai Allah, saita yarda su biyama kansu buk'ata, itama da yake tana son kasancewa tare dashi, saboda Hamisu yasan takan mace wajan kwanciyar aure, shi yasa yake gigita Habiba, daya zo yake mata wayo, su sha sha'aninsu, sai kaga a kwana ba rigima rana d'aya kuma, suyita rigima, da zage-zage da tunama juna asiri wani lokacin har sai makwafta sun shigo suna basu hak'uri.
Ko wanne gida dai ana zaune k'alau amma banda gidajan nan guda biyu, na Narnah da Habiba...........✍️
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 15
Sati na zagayowa Daddy da Khaleefa sukazo d'aukar Marmah, sosai Mlm yayi mata nasiha tana zumda hawayen rabuwa dashi, domin bata san miye zata taras ba, a can, tana ji a jikinta akwai sauran k'alubalen a tare da ita, tunda tun kan tasan wacece ita, take samun labarin Matar Daddyn yadda ake cewa girman kaine da ita, bata son y'an K'auye.
Tunda suka d'au hanya ba wadda ya sake cewa uffan, gara ma Khaleefa tunda ya kalleta sau d'aya bai sake koda duban inda take ba, a zuci yake tunanin, yanzu wannan yarinyar harta isa wani aure?, yana da tabbacin k'annansa mata sun girmeta nesa ba kusa ba, su ba'ai musu auren ba sai ita, koda yake haka al'adar K'auye take, tab'e baki yayi yana k'ara kallonta ta k'asan ido, a hakanma yana da tabbacin girman jiki ne da ita, shi yasa kallo d'aya baza a iya cewa, ga shekarunta ba, itama tun a wajan Mlm data ji ya kirasa da Khaleefa, saida ta girgiza da ganin dama shine ya amshi auranta?, shin ina zata kai wannan d'an gayun mai ji da kansa, tana gani fa ko kallo bata isheshi ba, tana da tabbacin, ko kalar fuskarta bai sani ba, gaskiyar magana tana da aiki ja a gabanta.
Shi ko bata san ya kalleta tsaf ba, har kallon ya wuce misali, shi kansa saida yayi zargin kansa, yana jan dogon tsaki, har saida Daddy ya dube shi, murmushi Daddy ya saki, yana basarwa shima, danshi ya lura da irin kallon da yake ma Marmah, shi kansa Daddy yasan bata inda Khaleefa zai iya cewa Marmah batayi ba, saboda yarinya ce, mai shiga rai.
Tunda Marmah taga sun shigo Kano taji wata irin fad'uwar gaba, bawai fad'uwar gaba wacce wani abu zai sameka nan take ba, a'a fad'uwar gaba ce, wacce tajita can k'asan zuciyarta, kallon garin Kano take, cike da sha'awa da birgewa, tunda take bata tab'a fita tabar garinsu ba, koda wajan K'auyensu ne, bare ta shigo birni, sai dai taga y'an gidansu na fita suna zuwa, ita wake gareta ma bare ta ce zataje wajansa?, koda akwai ma, tasan Hajara bazata tab'a bari taje inda suke ba.
Tunaninta ne ya katse dai-dai sun iso wata unguwa mai d'auke da gidaje masu mugun kyau, daka kalli tsarin unguwar kai kasan ta masu hannu da shuni ce, wani rantsatstsan gida wadda ya amsa sunansa gida taga sun nufa, shi kanshi get d'in gidan abun kallo ne, tasbihi take a zuciyarta, tana ayyanawa a zuciyarta dama akwai irin wannan gidajan a duniya?, bata k'ara tsinkewa da lamarinba saida suka shiga harabar gidan, sosai Marmah tasha mamaki ganin irin tsarin gidan, kamar na turawa, har suka tsaya ta fito daga cikin motar tana kallon gidan, danba k'aramin birgeta yayi ba, tsarinsa da kyansa.
Daddy ne ya kamo hannunta yana k'ara tuna mata yadda zata zauna gidan, saifa tayi hakuri, saboda shi dai ba mazauni bane har Khaleefan, tana jinsa gabanta sai fad'uwa yake.
Har suka shiga rantsatstsan parlon gidan wadda yaji kayan alatu, da kayan more rayuwa, ga parlon na fitar da wani sahihin k'amshi, mai kwantar da hankali, ba abunda Marmah take sai bin Parlon da kallo, cike da d'unbin mamaki a ranta, dama haka Daddy yake da kud'i?.
Tunaninta ne ya katse, a sadda ta wurga ido, taga wasu mata matasa wadda suke ji da wanka, da gayu, suna zaune akan kujerun parlon, d'aya na danna waya, d'aya kuma computer.
Sai sana Khairat, da Ifteesan, suka lura da shigowarsu, ai ba shiri, suka saki k'arar murna suna zuwa suka rungume Daddynsu, bama su nufi Y Khaleefa ba, saboda wani shegen kallo daya watsa masu.
Marmah dake gefe, tana masu kallon sha'awa, inama itama, haka suke da Mahaifinta.
Daddy daya sake su, yana murmushi, yana tabbayarsu ina Mami?, kallon Marmah suke cike da rashin sani, sai kuma taga sun tab'e baki, suka koma suka zauna, suna ba Daddynsu amsar cewa Mami na sama.
Kamin su rufe baki, ma saiga Mami na sakkowa daga kan bene, tundaga sama Mami ta lura da Marmah dake zaune yanzu a rakub'e waje d'aya, Daddy na zaune akan kujera, sai Y Khaleefa daya fice ya nufi part nasa, Daddy na ma Marmah magana, ta saki jikinta, ai nan kamar gidansu ne, ta tashi ta zauna kan kujera, Marmah da kanta ke a k'asa ta girgiza kai kawai, danta lura mutanan gidan sai mata kallon banza suke.
Mami data idasa sakkowa tana faman jefama Marmah wani kallo, wadda Marmah kallo d'aya tayi mata ta hango tsanar y'an K'auye a idonta, kai harda ma fuskarta data nuna.
Tana idasa k'arasowa kanta a k'asa ta gaida ita, maimakon ta amsa saita jefoma Daddy tabbaya da cewa,
"Daddyn yara wannan fa wacece?"
"Ki zauna mana ai zanyi miki bayani"
Zama tayi tana d'ora kafa d'aya kan d'aya tana cewa "ina sauraranka"
Gyara zama Daddy yayi yana fuskantar Mami, fuskarsa ba wasa.
Ya ce "wannan dai yarinyar da kike gani y'ar uwata ce domin ko d'iyar k'anina ce, wacce can baya naso amsarta tun tana jaririya, to yanzu ma na taho da ita ne domin na rik'eta, ta samu ilimi, a takaice dai ta dawo nan da zama dundundun"
"Daddy kamar ya ta dawo da zama dundundun ban fahimce ka ba?"
Murmushi ya saki yana harbo jirginta yana cewa "kamar yadda kikaji na fad'a, ai ba wani yare nayi miki magana dashi ba, kuma nasan kin fahimce mi nake cewa, dan haka na gama yanke hukunci, ai dai gidana ne, kuma y'an uwana suna ikon duk sadda sukazo su zauna a cikinsa"
"Amma dai gaskiya ba'a nan gidan ba, haka kawai bansan yarinya ba, bamu san halinta ba, kawai ka wani kwasota wai ta zauna tare mu"
Mami ta fad'a cike da jin haushin Daddy, tana banka ma Marmah dake jin komai harara, zuciyarta sai bugawa take cike da tsoro.
Daddy daya tashi yana sake jaddada mata cewa, "na gama maganata, ku kuma"
Ya nuna su Ifteesan dake zaune wajan har yanzu sun kasa kunne suna sauraro, ya nunasu da yatsa yana cewa "karna ji wani abun wulak'anci ya fito daga wajanku, a tare da Marmah, kuma ku nuna mata, d'akinta dake kusa da naku, a sama"
Yana gama fad'ar haka ya juya yana hayewa sama, yana cema Marmah ta shirya da anjima, zaisa driver ya kaita tayo sayayya.
Ai ko yana shigewa, Khairat tayi saurin cewa "wai Mami kinji mi Daddy yake cewa, wai a bata d'aki kusa damu, kenan kamar matsayinta d'aya damu, gaskiya ni bazan zauna waje d'aya da ita, jibeta fa wata y'ar K'auye k'azama da ita"
"Kema kenan ni gaskiya bana had'a hanya da irinsu, dan ina kallonsa kamar zubar da daraja ne"
Ifteesan ta idasa fad'ar haka, tana makama Marmah harara.
Marmah tayi saurin kallon jikinta, ita dai bata ga wata k'azanta ba.
Mami dake kallon Marmah ta ce "dalla ku rabu dashi, ba gidan ubanda zata zauna min a sama, d'akin dake k'asa na saukar bak'i a nan zata zauna, ina laifi ma"
"Yauwa Mami hakanma yafi wallahi, ke tashi ga d'aki can ki shiga nanne d'akinki"
Khairat ta fad'a tana jefama Marmah wani banzan kallo.
Marmah tashi tayi jikinta a mugun sanyaye, tana son b'oye hawayen dake neman zub'o mata, tana gaf da shigewa, Mami ta dakatar da ita da cewa, "Kee ki bud'e kunnanki da kyau kijini, ba hutu ya kawoki gidan nan ba, aiki zaki fito duk abunda yarana suke so ki tabbatar kinyi shi, karki sake a kawo min k'ararki, dan haka saiki kiyaye, idan kinyi masu laifi kuma, bazan hana su hukuntaki ba, babu ruwana dan haka saiki kiyaye, and kuma ki tsaya iya matsayinki, bana son shishshigi, a harkar gidana, zaki iya wucewa ki ba mutane waje"
Da sauri ko Marmah ta shige d'akin, tana sauke ajiyar zuciya, dan Allah ya gani ma wata irin shakkar Mami take, dan Mami tunda take mata magana fuskarta a murtuke, babu wasa, ga wani kallon k'ask'anci da suke jefa mata, duk sai taji ta muzanta.
Kallon d'akin tayi ita harga Allah, d'akin yayi mata shegen kyau, tunda ga katifa babba a k'asa da waduruf harda madubi, sai toilet, ita gani take wannan ma ya isheta, ba abunda ya mata dad'i ma irin yadda Daddy yayi mata albishir d'in sata makaranta, yafi komai mata dad'i, shi yasa data tuno saita manta da abunda su Mami sukayi mata.
Sai wajan yamma Daddy yasa akai Marmah shopping, yasa Tala ta raka ta, mai aiki, ai ko a cikin motar, Tala da surutun tsiya sai labari take ba Marmah, har suka d'an saba, koda sukaje shagon sayayya Marmah kasa daukar komai tayi, saita zama bak'auyar k'arfi da yaji, ita dai ba sanin wasu kaya tayi ba, bare harta zage ta zab'a, sai Tala ce ta zage tana zab'ar mata kaya masu mugun kyau da tsada, tunda saida Daddy ya gaya mata y'ar uwarsa ce, ai ko ta zab'ar mata kaya masu mugun yawa, dan har saida Marmah ta kwab'eta da cewa ta barso haka, ai sunyi yawa ma kayan, tukun Tala ta dakata, da jidar kayan.
A gajiye suka dawo gida kai tsaye d'akin Marmah aka wuce da kayan.
Bayan Marmah ta huta, tana zaune tana kallon kayan cike da farin ciki take d'agasu, sai murna take, kawai taji an banko d'akin ko sallama babu, Mami ce da y'ay'anta biye da ita, zabura Marmah tayi ta tashi tsaye gabanta na fad'uwa.
Marmah bata san hawa ba bata san sauka ba, taji Mami ta tsinka mata mari tana nunata da yatsa tana cewa "wato kinga kud'in banza kenan?, shine yasa kikaje kika jido wa'innan uba-uban kaya, saboda kud'in bana ubanki bane, baki san ciwonsu ba"
Kuka Marmah ta saki tana girgiza kai, kamar ta sani take ma Tala fad'an kayan sunyi yawa.
Canta ta tsinkayi maganar Ifteesan dake d'aga kayan tana cewa "kan uban can, Mami, wai kinga tsadar kayan nan kuwa?, ai komu iya kayan da muke sawa kenan"
"Kwasu min rabin kayan masu tsadar ciki, ku barma matsiyaciyar, sauran, na rantse baki sa kayan nan duka, idan ba halin tsiya zaki nuna ba, miye na daga zuwa, har kinsan ki zab'o wa'innan kayan, wato ke idonki a bud'e yake kenan, munafuka, kin wani tsare ni da ido"
Mami ta idasa fad'ar maganar tana jefama Marmah wata uwar harara, Marmah dake girgiza kai tana son yin magana, domin kare kanta, Mami ta kwatsa mata tsawa da cewa,
"Dalla rufe min baki munafuka, ubanmi zaki ce min?, ke gaki kinga dukiyar banza ko?, to ta Allah ba taki ba, duk wani mugun sharrinku ya koma muku, idanma turoki danginsa sukai, kiyi barbad'anci dasa ido"
Har suka gama mata wulak'anci suka kwashe kayan Marmah bata k'ara yunk'urin magana ba, suna fita ta zube kan katifa tana rusa kuka..................✍️
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 16
Da kyar Marmah ta tashi ta shiga toilet ta wanke idonta daya kunbura saboda kukan data sha, bata k'ara fita koda parlo bane, tana rakub'e a d'akinta, abinci ma sai dai Tala ta kawo mata, tana nuna tausayinta danta ji abunda su Mami sukayi mata, taita ba Marmah hak'uri.
Marmah ko murmushi kawai tayi, inda sabo ta saba da irin wannan wulak'ancin tun a garinsu, tunda inda ta fito d'inma da yawan mutanan can kyararta suke, to danmi zata ji haushi?, kawai zuciyarta mai saurin rauni ce, kuma dama tana da saurin kuka.
Washe garin ranar Marmah wani mugun bacci ya d'auke ta, bata san ma gari ya waye ba, saboda taji dad'i canjin wajan kwana data samu, da a k'asa take kwana, laushin katifa yasa ta makara, tunda tayi sallar asuba ta koma bata tashi farkawa ba, sai da taji