Author : Zahra Royal Star Category : True Hausa Novels
su Abbas ba, irinsu Dangana ne suka dace dake"
"Innalillahi dan Annabi Umma karki bari a aura min Dangana, bana sonshi wallahi, ki kawo min wani zan aura amma banda Dangana dan Allah"
"Keee ki rufe min baki na ce, ai ko mutuwa zakiyi saifa anyi auran nan, idan yaso ki mutu da auran Dangana a kanki, amma auransa ba fashi kinji na gaya miki, tunkan na hanb'arar dake a nan wajan ki tashi kije yana can yana faman jiranki, sauran idan kinje ki gaya mai maganar banza, ni kuma maganar ta dawo waje na kiga yadda zanyi dake, a cikin gidan nan"
Marmah ta dage sai kuka take wiwi kamar ranta zai fita, shikenan za'a tarwatsa mata rayuwa, itakam mita tsarewa Hajara ne?, a rayuwarta, take son sata a K'ANGIN RAYUWA har hakane?.
Can ta tsinkayi muryar Hajara tana k'ara cewa "zaki tashi ki wuce ko kuwa, saina lakad'a miki na jaki?".
Ba shiri Marmah ta fice daga d'akin tana share hawayenta wasu na k'ara zubowa.
Hajara dake fitowa itama tana faman mitar cewa "kaji mun y'ar iskar yarinya, da kilbibi, ai tukun na ma yarinya, dan baki san yadda nak'i jinin bud'e idona na kalleki bane, da baza ki tsaya ma rok'ona ba, babu abinda zai canza a zuciyata dangane da irin tsanar da nayi miki".
Haka Marmah ta fita k'ofar gida, tana fitowa kuwa ta hangi Dangana tsaye bakin wata bishiya dake k'ofar gidan nasu.
Yana hangota ya fara washe jajayan hak'uransa, yana dariya, a zuciyarsa yana cewa "kai amma fa Hajara na gode miki, wannan zuk'ek'iyar budurwa haka, na tsinci dame a kala"
Marmah data tsaya nesa dashi tana makamai wata uwar hararara, da manyan idonta kamar zasu fad'u tsabar yadda take hararar sa.
Washe baki yayi yana cewa "ki k'araso mana masoyiya",
Cike da tsiwar da bata san ta iya ba ta ce "bazan k'araso d'in ba, wai kai baka ji kunya ba, kike shirin aure na, ni ka dubeni da kyau, kafa yi jika dani, Dangana kaji tsoron Allah ka fita daga rayuwata, na rok'eka"
Marmah ta idasa maganar tana had'e hannayenta waje d'aya alamar rok'o.
Wata y'ar iskar dariya Dangana ya saki yana cewa "yarinya kenan ai idan kinga na fasa auranki, to mutuwa ce ta dauke ni, amma mudun ina lumfashi, yarinya sai kin zama tawa"
"Au haka ka ce?, to bari na daina lallab'aka amma ka sani, na rantse komi nayi ma kaine ka sayeshi da kud'inka, kuma bazaka tab'a samun abunda kake kwad'ayinsa akai na ba, insha Allahu"
Ta idasa fad'ar haka ta juya tayi shigewarta gida tana jamai dogon saki, bata tsaya jiran mi yake cewa ba.
Shiko sai b'ab'atu yake yana murna ya samu y'ar shila, duk abunda ta gayamai baiji wani haushi ba...............✍️
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 11
Tana shiga gidan ta taradda Hajara k'ofar d'akinta tana zaman jiranta.
Hajara ganin Marmah ta shigo hannu rabbana, yasa ta tashi tana maka mata hararara, tana cewa "ke ya zanga haka?, ina y'ar k'unshin ledar, da ake yoma y'an mata, idan sauri yanzo zance, ko kuwa bak'in hali kika nuna kik'i amsa?"
Da sauri Marmah ta girgiza kai tana cewa "a'a Umma wallahi nidai bai bani komai ba"
"Ke dalla rufe min baki, bama sai kin tsaya kin saurare shinba tukunna, waike mi yasa bazaki daina bak'in hali da bak'in ciki ba?, tona rantse da Allah duk sadda ya sake zuwa baki tsaya da kyau kin saurare shi ba, harya baki abun duniya, kika shigo gidan nan hannu rabbana, zaki sani ne"
Girgiza kai kawaii Marmah tayi hawaye sun cika idonta, ita ba wannan ke damunta ba, wannan kaddararran auran da Umma Hajara ke shirinyi mata shi yafi komai tsaya mata a zuciya, haka tana tunani harta k'arasa d'akinta tana shiga ta rakub'e waje d'aya, yadda taga Dangana, waishi zata aura yasa ba shiri ta fashe da kuka, tana tusa kanta a tsakanin cinyoyinta.
Rayuwa na tafiya da gudu kwanaki na komawa kamar wuni watanni na komawa kamar sati, sati na komawa kamar kwana d'aya.
Haka ce take kasancewa a ga Marmah gani take kamar ranar mutuwarta na k'ara matsowa ne, saboda yadda taga anata hada-hada a gidan naso, na shirye-shiryen auran dasu, kowaccen su ana mata gyara amma ita banda ita, saima tallar da take zuwa har yanzu, sai ko fargabar da take ciki, na auran Dangana, da kullum yake ci mata rai, shi yasa a wannan tsakanin dukta fita hayyacinta, ta rame ta figi, gashi kullum ya dameta da zuwa, yana mata wasu maganganun shirmensa, gaba d'aya iyayansu maza kamar an kauda hankalinsu daga gareta bare wani ya lura cewa bafa san Dangana take ba, kowa ya kasa ganin aibun Dangana, dan har an amshi kud'in auran y'an matan gidan nasu harda nata ma, dama Mlm ne take sa rai shi kuma hidima sunmai yawa, ga kwana biyun nan baida ishishshiyar lafiya, gashi tana tsoron gargad'in da Hajara tayi mata, shi yasa kullum cikin kuka take, da tsananin fargaba.
Inda Mlm ya kira Daddy ya sanar dashi auran yaran da za'ai, Daddy yayi mamaki sosai kuma yayi fad'a danmi ba'a sanar dashi tun wuri ba, gashi yanzu baya k'asar shida iyalansa dan har ayi bikin basa nan, dan bikin bai wuci saura wata d'aya ko biyu ba, domin Habiba ta shiga watan haihuwarta, kuma tana haihuwa da sati biyu ko d'aya akeso ayi bikin, inda Mlm ya ce ba matsala karya damu, daga baya yazo, idan suka dawo, inda shi kuma Daddy kwata-kwata baiji dad'i ba, haka nan dai ya turo kud'i masu yawan gaske ya ce ayi ma y'an matan kayan d'aki, zai sa kuma a kawo kayan abinci da za'ayi anfani dasu a bikin, sosai Mlm yaji dad'in hakan yana tasa mai albarka.
Yauma Marmah na zaune tana aikin tunanin da yanzu ya zame mata jiki, ita ba wata k'awa gareta ba bare takai mata kukanta, shi yasa abun yayi mata yawa, zuciyarta tayi nauyi da yawa, ta rasa inda zata amayar da abinda ke cikinta kota samu sassauci.
Jin muryar Hajara a kanta tana cewa "ke wai bakiji ana miki magana ne?"
Tashi Marmah tayi gabanta na fad'uwa, yanzu indai taga Hajara gabanta muguwar fad'uwa yake.
Har bakinta na kyarma ta ce "Umma banji bane wallahi"
"Keni ki tashi da'aAllah Dangana ne yazo yana son ganinki, ance dama yana zuwa kwana biyu sai kice ace mai baki zuwa, ke gaki mai kunnan k'ashi ko?",
Shuru Marmah tayi dan Allah ya gani ta tsani Danganar nan ko ganinsa bata sonyi, ya addabi rayuwarta.
Bata ce komai ba ta fice ranta babu dad'i.
Ai ko yana tsaye yana hangota ta fito, ya fara washe mata baki kamar yadda ya saba, nesa dashi ta tsaya kamar yadda takeyi aduk sadda yazo.
Da kyar ta bud'e baki ta ce "wai kai da'aAllah Malam, baka da zuciya ne a k'irjinka?, tunda kake zuwa ban tab'a sauraranka ba, saima k'ara tsanarka da nake ji a zuciyata, kai bazaka hak'ura ka fita a rayuwata bane?"
Dariya ya saki yana cewa "ai duk abunda zakiyi min bana tab'a jin haushi, saboda ina matuk'ar sonki"
Da sauri Marmah waigo tana bankamai wata uwar hararara tana cewa "kai ko kunya ma bakaji kake fad'an irin wannan kalaman, toni kaji da kyau bana sonka, kuma bazan tab'a sonka ba, mai budurwar zuciya kawai"
Ta idasa maganar tana niyar juyawa ta wuce cikin gida.
Ba shiri ya matsa kusa yana aje mata ledar dake hannunsa yana cewa "masoyiya kenan ai bazan tab'a jin haushinki ba komi zakiyi min kuwa, sana ga wannan ki shiga dashi, sana biki fa sai k'ara matsowa yake, har yanzu baki fara tabbayar dame-dame kike buk'ata ba"
Juyowa tayi a fusace ji take kamar ta wanke shi da mari, ta ce "bana buk'atar komai, daga gareka indai akan wannan bikinne, kuma wannan abun dakake kawowa ma, ka sani ban tab'a anfani dashi ba, dan haka ka daina wahalar da kanka wajan kawowa"
Ta idasa fad'ar haka kawai taji wani abu ya tsaya mata a wuya na bak'in ciki, har bata san sadda ta fashe da kuka ba.
Kallonsa take ganin shi ko a jikinsa saima wasu surutai da yake mata, yasa ta fisgi ledar tayi cikin gida, danta lura Dangana baida zuciya a k'irjinsa.
Koda ta shiga cikin gidan inda Hajara ke zaune tana kwashe shinkafa da wake ta sana'arta da takeyi, ta aje mata ledar tana niyar barin wajan,
Hajara ta maka mata hararara tana cewa "ke zo nan ina kuma zaki?"
Marmah da bak'in ciki ya cika mata zuciya ta ce "Umma ba inda zani mana"
"To kuma naga kina niyar tafiya, ko nufinki ba zaki tallar bane?, ubanwa zaije min tallar nufinki?, ai idan kinga kin daina zuwa tallah to satin bikinku ne ya kama, kinji ma na gaya miki"
Shuru Marmah tayi bata k'ara cewa komai ba, dama kwanakin nan rashin maganarta ya k'aru, dama ita ba gwanar magana bace.
Tana gama had'a mata komai ta d'auki tallar ta fice, tana cikin tafiya kawai taji an tsaya mata a gaba, da sauri ta d'ago tana duban y'an matan dake kallonta suna jefa mata wani shegen kallo, kallo d'aya tayi musu ta shaida Y'ay'an Dangana ne, y'an mata ne guda biyu, sun girmeta nesa ba kusa ba.
Suna jijjiga tsabar rashin kunyar dake cinsu, wata ta nunata da yatsa tana cewa "ke kece wadda Babanmu yake son aurowa?, ke wacce irin zuciya ce dake?, ki dubemu da kyau kina tunanin kishi da Iyayanmu mata damu kanmu abu ne mai sauk'i, to ki bud'e kunnanki da kyau kiji mu, tun wuri kije ki soke auran nan idan ba haka ba kuma, kika sake kika bari wallahi kika shigo cikin gidanmu, wallahi kinji na rantse saiya fi miki kabari dad'in zama, dan haka tun wuri kasan abunyi"
D'ayar ce ta amshe da cewa "ke Hansa'u kema ke tsayawa lallab'ata, dan Allah idan kin cika ke y'ar rigima ce, to ki shigo gidan namu, wallahi sai mun lallasaki, shi Baba baccin ma baida zuciya mi zaiyi da wannan kwailar domin Allah"
Marmah dake musu kallon mararsa tarbiya, sai da suka gama tsaf sana ta ce "ni da zakuje ku sami uban naku ma ya hak'ura da nemana da yake, da naji dad'i, ku kalleni da kyau nayi sa'ar auran ubanku ne?, ai kusan hanyar jirgi daban ta mota ma daban, dan haka bani zakuyi ma wannan gargad'in ba ubanku zakuje ku sama, danni in banda k'addara da kuma anfi k'arfina, na rantse kunsan nafi k'arfin ubanku"
Wata irin kururuwa d'ayar tayi tana shirin kaima Marmah mari, da azama Marmah ta rik'e hannun tana mata kallon baki isa ba wallahi.
Marmah dake kallonta ganin sai wani huci take tana kallonta, Marmah ta ce "ki shiga hankalinki da alama nima baki san wacece ni ba, duk abunda kuke tak'ama dashi, na damaku na shanye, tabbas inada hak'uri amma aka kaini bango, ban iya rigima ba, dan haka ku shiga hankalinku, ni ba sa'ar yinku bace"
Tana gama fad'ar haka ta zagaye su ta wuce, ta barsu sake da baki, cike kuma da mamakinta, suda akeba labarinta, bata magana, hak'uri ne da ita.
A wajan Marmah ko k'arfin hali ne kawai ta aro tasama kanta, bata tab'a tunanin zata iya yin maganar nan mai tsawo har haka ba, dan tana wucesu sai da ta sauke ajiyar zuciya, wasu hawayen ba'kin ciki na zub'o mata.
Harta gama tallar ta dawo gida ba wani walwala a fuskarta, abunda Y'ay'an Dangana sukai mata ya tsaya mata a zuciya.
Sai gashi tana shiga gidan ta k'ara taradda da abunda yasa mata bugawar zuciya............✍️
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 12
Domin tana shiga ta taradda mutanan gidan sunyi ciccirundo a kusa da d'akinsu Habiba da alama nak'uda take.
Dan yadda Marmah taji yadda Habiba ke ihu tana kuka, samun waje tayi ta zauna zuciyarta na faman bugawa, yanzu da Habiba ta haihu shikenan bikinsu ya kusa kenan?,
Can kuma sai tausayin Habiba ya kamata, tana zaune saiga Hajara ta nufo wajanta tana cewa,
"Bani kud'i na ke"
Marmah dake zaune ta mik'a mata bata ce komai ba, saida ta k'irga kamar yadda ta saba sana ta saki wani tsaki tana cewa "Ohhh ni haba Habiba kin cika raki da yawa sadda kikaje kika lik'ema k'aton banza kuna kwasar dad'i a tare wani ya sani ne"
Ba wadda ya jita bare harya samu mai biye mata, Marmah dake kallonta, ta girgiza kai, ganin Hajarar ita ko a jikinta, sab'anin mutanan gidan, da yawansu fuskarsu cike take da tausayin Habiba.
Habiba dake cikin d'akin Mahaifiyarta ta kwance tsakiyar d'akin, tana murk'ususu, Maryama na rik'e da hannunta, tana, mata sannu, Inna Indo dake taimaka mata tana cewa "daure kinji, ki daure kiyi nishi mai k'arfi"
Jujjuya kai Habiba tayi maganarta bata fita sosai tsabar wahalar data sha tana cewa "Inna bazan iya ba, k'arfi na ya k'are, wayyo Allah mutuwa zanyi"
Sosai fa hankalin mutanan dake d'akin ya sake tashi can Bishira dake share hawaye ta ce "wai Mama baza'a kaita asibiti bane?"
"Ke wane irin asibiti kuma?, ana zaune k'alau, Allah ya rufa mana asiri wannan abun kunyar data yi bai fita cikin gari ba, yanzu idan aka kaita asibiti ai asirinmu ne zai tuno"
Maryama ta idasa maganar tana sharce gumi itama, duk da ta fara sarewa da Habibar yadda ta kasa iya tab'uka komai, tun tana nishan iya k'arfinta har k'arfin nata ya k'are.
Tunda yamma ake abu d'aya har dare ya fara kutso kai, iyanzu Habiba kod'an yatsa bata iya d'agawa, ga kan yarinya ya fara fitowa, itakam Habiba harta sare da wannan duniyar, Maryama sai kuka take ita sa Bishira, jin Habiba na cewa su yafe mata.
Cikin wani ikon Allah kuma, wani k'arfi yazo mata, tana yin wani uban nishi jariraya ta fad'u macece, sai dai kana kallon yarinyar zaka san bata zo da rai ba, domin ba kukan nan da jarirrai keyi babushi, su Inna Khande har d'an bugun yarinyar sukai, ko da ranta, sai dai tuni yarinyar dama ta mutu a ciki, saboda an raini cikin ba shan wani magani bare zuwa asibiti awo, dan yarinyar harta fara sandarewa, Allah nema ya taimaki Habibar da bata rib'e mata a ciki ba, shi yasa ita kanta Habibar tasha wuya wajan haihuwarta, domin yarinyar bata motsi, bare ta taimaka mata wajan fitowarta duniya.
Mutanan gidan sunyi farin ciki da mutuwarta, bare da aka gaya ma mazan hamdala ma sukai suna ma Allah godiya, a cikin gidan akayi rami aka sallaceta aka binneta ba wadda yaji ba wadda ya gani, daga su sai su.
Ta b'angaran Habiba ko kuka tayi shi dan Allah ya gani taji tana son komiye ma ta haifa tunkan yazo duniya, tana kuka tana rok'on Mahaifiyarta ta yafe mata, itada Mahaifinta, duk ta zama wani iri tana nadamar biyema son zuciya da tayi, gashi nan tun kan aje ko ina ta fara gani, ko wannan azabar wahalar data sha ai izina ce a gareta, ashe haihuwar ba sauk'i ne da ita ba, ashe haka iyayansu suka sha irin wannan wahalar wajan kawosu duniya, ai ko dole Allah yayi fushi da kai, idan har ka sab'a musu.
Haka dai ta ture komai aka fara shirye-shiryen biki sosai Maryama ke gyara y'ay'anta, bare Habibar inda Allah ya taimaketa sati na zagayowa taga jinin haihuwar ya d'auke.
Inda Hajara ma ke gyara d'iyarta, Marmah ko ba wadda ma ya damu da ita bare har a gyarata, y'an uwan Mahaifiyarta sunzo, sai dai Hajara ta hanasu koda ganin Marmah ne, saima ta amshe kayan da suka kawoma Marmah na bikin babu abinda basu saya mata ba, na dangane da abunda uwa take ma y'arta idan auranta ya tashi.
Sai dai Hajara ta handame komai ta had'ama Narnah da shi, koda ta sami labarin kayan d'akin da akai ma y'an matan gaba d'aya da kud'in da Daddy ya turo, sai da ta had'a munafurci, a ranar da za'aje jere, ta hana a nufi da kayan Marmah gidan Dangana kai tsaye, aka wuce dasu wajan masu yin Furnitures, aka sauya su aka bada mararsa kyau, wadda basu da k'arko, sauran kud'in kuma, aka k'ara saima Narnah wasu kayan dasu.
Haka akaje jere gidajan y'an matan kowacce gidanta ba laifi bare na Narnah nanne fa aka sha kallo irin gidanjan y'an birni Abbas ya gina, kuma yana so bayan bikin ya d'auki matarsa su wuce Kano, inda yake aikinsa, sosai yake rawar k'afa a bikin, kai daka kallesa kasan ma baya cikin hayyacinsa, domin yadda su Hajara da d'iyarta ke tatsarsa kud'i, da bashi umarni, jikinsa na kyarma yakeyin komai.
Gidan Habiba ko bayan layinsu ne Mlm ya bada gidansa su zauna, a nan akayi mata jeranta, sai ko Bishira, da aka je wani gari dake hayin K'auyen, ita ce kawai aka fidda daga garin duk sauran cikin garin ne, gidan Marmah shine k'arshe, ansha tashan k'ananun maganganu a wajan matan Dangana, ba wadda ya biye musu, akayo jere aka dawo, d'aki d'aya ne dai, da kyar ma kayan suka amshe d'akin, har wasu na cewa "gara da Hajara ta canza mata kayan d'akin, dama tasan talaka zata aura, da haka za'a kawo wa'innan kaya masu mugun tsada, da kyau, a wannan K'urk'uk'un d'akin.
Sosai aka dawo gida ana maganar gidan da za'a kai Marmah, duk bidirin da ake banda sanin Iyaye maza, dan har kayan da aka canza ma Marmah basu sani ba.
Marmah kuwa kwana take kuka,