Author : Zahra Royal Star Category : True Hausa Novels
sosai ta k'ara fita daga hayyacinta, kowacce cikinsu na murna amma banda ita, idan ta kallesu sai taji sha'awa inama ace itama, masoyinta zata aura wadda take so, duk da baza tai damuwar nan ba, sosai idonta ya zurma ta rame sosai dan idan ka kalli ramar da tayi sata baka tsoro, sai ido tayi zuru-zuru.
Ana gobe d'aurin aure aka kawoma kowacce lefe, Habiba kuma Mlm ne yayi mata komai, cikinsu babu wacce lefenta baiyi ba, saima na Narnah ya d'ara na kowacce, sai na Marmah shine k'arshe, akwati biyu ne, bama wadda yake tashi.
Anata bud'a ana shewa, su Hajara ganin komai aka kawo na d'iyarta sai yafi na kowa, nanfa ta k'ara d'agawa tana sakin maganganu da habaici.
Marmah ko y'ar uwar Mahaifiyarta Kharima tazo tana ta lallashinta ta kawo mata kayan da zata sa da bikin tana bata hak'uri ta daure ta amshi k'addararta hannu biyu-biyu, sai sana Marmah tad'an samu sauk'i, amma duk da haka kullum cikin kuka take, gashi dama Kharima tunda tazo Hajara ke yab'a mata bak'ar magana, sukayi kaca-kaca, tun ranar bata sake dawowa ba, taba dai Marmah hak'uri, tayi mata nasiha sosai.
*WASHE GARI RANAR D'AURIN AURE*.......✍️
*Mu ha'du a gobe idan Allah ya kaimu*🙄🤪
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 13
Washe gari ranar d'aurin aure Marmah na k'udinddine a d'an d'akinta, jikinta yayi zafi rau, zazzab'i ya rufeta, gashi sai faman kuka take, ita d'aya, tana iya jiyo hayaniyar y'an bikin da suka cika gidansu, sauran amare an ware masu wajansu daban a cikin gidan kasancewar babban gida ne, sai basu je ko ina ba, duk a nan cikin gidan suke komai nasu, inda zasu zauna, ita ko lek'a wajan ma batayi ba.
Dan harta ji an fara mata surutun girman kaine da ita, tak'i fitowa cikin jama'a, sai dai sam ba haka bane, auranne yazo mata a yadda batayi zato ba, bata tab'a tunanin zata rasa Abbas ba, sai gashi a d'an k'ank'anan lokaci komai ya ruguje mata.
Tana tunanin zuci hawaye masu zafi na bi mata fuska.
Kowa na gidan nata hada-hada su Hajara k'irjin biki, sai nan-nan ake an kasa zaune bare tsaye, kwata-kwata tama manta da wata Marmah, ta yarinyarta kawai take, yadda kasan ita kad'ai ce wacce ake bikinta, su Narnah a shiga waccan kaya a cire waccan, tasa kaya sun kai kala biyar, a safiyar ranar dai, anata tsokanar amare, ko wacce na shiga da fita.
Habiba ce ma ta lura bata ga Marmah ba, ai ko da hanzari ta nufi d'akin da take, tana zuwa ta ga irin halin da take ciki, cike da tausayi, ta tada ta, tana cewa "Marmah mike damunki ne haka, ko wacce amarya ta shirya cikin kaya masu kyau, amma ke shuru, gashi har an kusa d'aurin auran ma, dan k'arfe sha d'aya dai-dai ake daurawa"
Gaban Marmah ne yayi wani irin bugawa dassss, har sai da wasu irin hawaye suka sake bin kyakkyawar fuskarta, data rame kamar ba ita ba, tama kasa cewa komai, domin ko babu abunda zata iya cema Habiba, saboda ta tuna mugun gargad'in da Hajara ta bige mata, ba abunda keci mata rai irin wannan auran.
Haka nan dai ta lallab'a tayo wanka, tazo ta zab'i cikin kayan da Kharima ta kawo mata, wata shadda ta d'auka wacce tasha ado da duwatsu, shadda kallo d'aya zakayi mata kasan ta d'inku, kuma mai tsada ce, ita kanta Habiba sai da ta kalleta ta sake kallonta, tana yaba kyan da tayi mata, danma duk ta rame, tayi duhu, ita kanta Marmah sai ta k'ara jin k'aunar dangin Mahaifiyarta, tasan da ace wajansu ta taso, tabbas da zata gata iya gata.
Koda ta fito waje, suna gaisawa da mutane, sai tsukanarta ake itama, sai dai tayi murmushin yak'e kawai, Hajara ko tana kallonta cike da jin zafin ganinta ta warware, so tayi ta ganta ranga-ranga, harda sa wasu kaya, bata san da kayan ba, ai da wallahi saita amshe su.
Jawota Hajara tayi tana mata kallon sama da k'asa tana cewa "keee munafuka, ina kika samo wa'innan kayan kuma?"
"Umma Aunty Kharima ce ta kawo minsu"
"Ahh lallai cewa zakiyi munafuka ce ta kawo miki su, inba munafurci ba, mi yasa ba'a nuna min ba, kema harda ke munafuka ko?, ko da yake ai gadon munafurcin kikayi can wajan dangin uwarki"
Runtse ido Marmah tayi tana jin zafin maganganun Hajara bata ce komai ba, zata juya ta tafi taji maganarta tana cewa "kuma ki kwaso kayan gaba d'ayansu ki kawo min d'aki na wallahi baki sake sasu, kinyima kanki, ni za'a munafurta"
Ko ci kanki Marmah bata ce ba, bare tasan ran zata ce dan Allah tabar mata kayan, taje ta d'akko kayan taje d'akinta ta aje mata su, a d'akin taga Narnah ana sake sa wasu kayan.
Narnah dake kallon kayan jikin Marmah cike da jin haushinta ta kalli Hajara dake shigowa yanzu ta ce "Umma ita kuma wannan banzar ina ta samo kaya haka?"
"Inafa zata samo su inbadda munafukan dangin uwarta sune suka kawo mata, itama da yake munafuka ce ai kinga bata nuna min ba"
Wani dogon tsaki Narnah taja tana sake cewa "to kuma ubanmi kikazo yi a d'akin nan?"
Juyawa Marmah tayi domin ficewa taji muryar Hajara naba Narnah amsa tana cewa,
"Cewa nayi ta kwaso duka kayan data kawo mata ta kawo min su nan"
"Tohm saboda mi Umma ai da kin bar mata tsiyarta kawai"
"Inbar mata a ina?, ai wallahi tunda ta munafurce ni bata ba k'ara sasu, sun kuma zama haramiyarta, gara naje na zubar dasu kona bayar dasu, dana bari ta sake sakawa, nifa na tsani naga yarinyar can cikin warwala ko cikin sutura mai kyau, bare har ta rink'a jin farin-ciki nafi son ganinta kullum cikin K'ANGIN RAYUWA"
Dariya Narnah tayi tana cewa "ai Umma nima nan wallahi na tsani yarinyar can, ji nake dama ba ubanmu d'aya da ita ba".
Haka dai sukayi ta zagin Marmah da bata san sunayi ba, dan tana fita ta samu waje ta rakub'e ta zauna, tana tunanin data sabayi a kullum.
Gaba d'aya gidan ne ya d'an d'auki shuru, jin mai shalar d'aurin aure ya fara sanar da wadda aka fara d'aurawa, danda nan gidan ya kaure da bud'a, shalar k'arshe ce ta girgiza jama'an gidan, hatta Marmah sai da ta mik'a a zabure, Hajara ko afujajan ta fito daga d'aki, ita da Narnah.
Narnah ce tayi k'arfin halin cewa "Umma kodai banji dai-dai bane, da waye kuma aka d'aurama aure da Marmah"
Mai shalar ne kamar yasan suna wasuwasi ya k'ara wage baki wajan k'ara cewa,
"D'aurin aure na k'arshe shine an d'aura auran Khaleefa Suleman Sani Mai Goro, da amaryarsa Aysha Hamza Sani Mai Goro, akan sadaki naira na gogar naira dubu d'ari uku cif lakadan ba ajalan ba"
Gaba d'aya fa gidan sunyi muguwar girgiza anma rasa bakin magana, Marmah ko ba abunda zuciyarta take sai muguwar bugawa kamar zata tsak'e k'irjinta ta fito, wani irin masifaffen tsoro ne ya rufeta.
Hajara da tayi suman wucin gadi sai da mutane suka jijjagata ana watsa mata ruwa, tana dawowa hayyacinta ba inda ta nufa sai wajan Marmah, batai wata-wata ba shak'e mata wuya tana cewa "wato da had'in bakinki aka canza wannan d'aurin auran ko?, to gara na kashe ki da inga wannan ranar wallahi"
Ba shiri y'an uwan Hajara suka b'anb'are ta daga jikin Marmah da idonta ya fara kakkafewa, tana shirin sumewa, tari ne ya sark'e Marmah bayan Hajara ta sakar mata wuya, ta duk'e a wajan tana sakin kuka mai cin rai, tana tunanin waye kuma Khaleefa?, waye haka ya fanshi auranta a wajan Dangana?,
Da kyar aka janye Hajara y'an uwanta sukayi d'aki da ita, wata y'ar uwarta ta kalli Hajara tana cewa "Hajara kanki d'aya kuwa?, ya za'ai ki rink'a nuna wannan k'iyayya a gaban mutane, ki bari ki fuskanci abun mana daga baya kin d'au mataki"
Sauke ajiyar zuciya Hajara tayi tana girgiza kai tana cewa "Inahhh wallahi bazai tab'a yuwu ba, wannan yarinyar ce za'a ce ta auri Khaleefa"
Y'ar uwar Hajara wacce ta tayi magana daga farko mai suna Halima, ta sake cewa "wai waye Khaleefan nan ne?, daya sa duk kikabi kika tada hankalinki haka ne?"
"Kinsan kuwa waye shi?, d'an gidan Sule ne, yanzu duk garin nan waye baisan Sule ya tara dukiya ba, shi kanshi yaron nasa yana da abun duniya, kinganshi kuwa?, gashi da kyau dan birni, gashi da iliminsa, babu abunda yaron nan ya rasa a nan gidan duniya dai, kinga yadda y'an mata ke rubibinsa a can birnin ma, wai amma a rasa wacce za'a bashi aure sai waccan y'ar iskar yarinyar, shin mi yasa ba'a bashi Narnah bane?, wai yama akai hakan ta faru ne?"
Halima ce ta dafa Hajara jin sai zaro zance take har tana son sakin layi yasa Halima cewa "shin koma dai wanene ki nutsu ki kwantar da hankalinki, mazan gidan su shugo ai zakuji ya akai auran ya dawo kansa ko?"
"Ya za'ai na kwantar da hankalina iyee Halima, kinsan mi kike fad'a kuwa"
"Tohm ya kike so na ce miki Hajara anfa riga anyi d'aurin auran nan, ki kwantar da hankalinki daga baya sai ki d'au koma wane irin mataki ne, amma yanzu idan kina nuna haka, ai zaki iyasa shakko a zukatan mutane"
Ba yadda Hajara ta iya haka yasa tayi shuru tana sharce wani uban gumi, zuciyarta cike take da mugunta da tsanar Marmah tsantsa, wacce ta linka ta da, sai had'iyar zuciya take.
Ai ko su Inna Khande sukam sunji dad'in wannan had'i kawai sunja bakinsu sunyi shuru ne gudun tashin hankali, dan sunsan Hajara y'ar bala'i ce.
Hamza suna shigowa ta jawoshi ko kunyar mutane babu ta sashi a d'aki ta kori kowa dake d'akin ta rufesa da tabbaya.
Tana cewa "Mai gida shin ya akai auran haka naji Marmah an maida mata aure da wani sab'anin Dangana?"
Hamza ya gyara tsawuyarshi yana murmushi daka kalleshi kasan yana cikin farin ciki ya ce "eh hakane abunda ya faru shine, wajan d'aurin auran ashe Sule (Daddy), ya wakilta Khaleefa zuwa d'aurin auran nan, saboda shi kad'ai ne bai biso k'asar waje ba, yana aikinsa a Abuja, amma Daddy ya sashi zuwa domin ya wakilce sa, ana cikin d'aurin aure Khaleefa ya kira Daddy a waya video call yana kallon komi ke wakana, a sadda aka zo gana Marmah Daddy na ganin angon, shi duk daukar Daddy ma banda Marmah ga masu yin auran, nanfa ransa ya b'aci ganin wadda zamu ba auranta, inda ya nemi alfarmar a maido auran akan d'ansa Khaleefa, shi kansa Khaleefan ya girgiza dajin haka, amma da yake yaro ne mai biyayya yasa ya amince, duk da bai san ko wace yarinyar ba, inda Dangana yaso tada tarzoma, a wajan d'aurin auran, shi kuma Daddy ya basa mak'udan kud'ad'e wadda suka linka hidimar da yayi ga auran, ai ko danda nan Dangana yayita washe baki, yana cewa yabar ma Khaleefa, ganin irin kud'in da aka basa, nan take aka d'aura auran, inda Daddy shine ya bada sadakin Marmah, dan Mlm shi kansa sai lokacin yaga Dangana kwata-kwata bai dace da auran Marmah ba, Mlm yayi farin ciki sosai da wannan had'in"
Hamza ya idasa maganar yana kallon yadda Hajara ke mai wani shegen kallo, wata uwar hararara ta banka mai tana cewa "kai kuma sai kai tsaye ka amince mai makon a maida auran Khaleefan ga Narnah, idan yaso ita Marmah sai a bata Abbas d'in dama ai tana sonsa"
Da sauri Hamza ya ce "mi kike cewa?"
Da sauri Hajara ta rik'e bakinta jin tayi katob'ara, sauke ajiyar zuciya tayi jin bai fahimceta ba.
Murmushin yak'e tayi tana cewa "a'a babu abinda na ce cewa nayi abun yayi"
Murmushi kawai Hamza ya saki yana ficewa daga d'akin dan mutane nata jiransa a waje.
Yana fita Hajara ta zube a k'asa tana sabbatu tana cewa "Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un, kai jama'a wai mi yasa bance Narnah ita ta auri Danganar ba, da nasan auran Khaleefa zai iya dawowa kanta, da sai mu nuna kamar auransa zatai da gaske, itama fa da yanzu Daddyn ya tausaya ma Narnah ya bata auran d'ansa, kai wayyo Allah na ji uban sadakin da aka sa ga auran waccan Marmah banzar"
Sai surutai take wata maganar ma bata san tana zarota ba, har saida Narnah ta shigo d'akin itama kanta jikinta yayi sanyi ganin uwarta a haka, lokaci guda duk ta fita hayyacinta...........✍️
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 14
Narnah ta dafa Hajara tana cewa "Umma dan Allah ki kwantar da hankalinki, tunda kinga nima wadda na aura mai kud'i ne, tunda babu abinda ya rasa"
"Kee in kwantar da hankalina fa kike ce?, mi Abbas d'in yake dashi?, ke kinsan waye Khaleefa kuwa?, ai bazaki tab'a had'asu da Abbas ba, ai tazarar ma tayi waya tsakaninsu, inahhh ai wallahi ko zanyi yawo tsirara na rantse da sarkin dake busan lumfashi, sai na raba auran Marmah da Khaleefa tabbas tunda baki sameshi ba, sai dai kowa ya rasa wallahi"
Narnah dai bata k'ara cewa komai ba, danta lura Mahaifiyarta tayi nisa bata jin kira.
A wajan Khaleefa ko tunda aka d'aura auran yake jin zuciyarsa wani iri, yana cikin mota zaune ana d'aura auran ya baro wajan ya dafe kansa, dake sara mai, ya d'ago kyakkyawar fuskarsa da take cike da damuwa, Khaleefa kyakkyawan matashi ne ajin farko k'ak'k'arfan namiji, tsayayye ingarma daka kalli jikinsa yadda yake a murd'e, k'irarsa daka kalla kasan yana motsa jikinsa, fari ne amma ba can ba, ga wani saje daya kewaye fuskarshi wadda ya k'ara mai kyau da cikar zati, sanye yake da bak'in yadi wadda ya k'ara mai wani mugun kyau, mai fisgar mutum, lumshe idonsa yayi masu zara-zaran gashi ga girarsa dake da yawa kamar zata had'e da y'ar uwarta, idonsa ne ya d'anyi ja kad'an saboda damuwar daya shiga, sosai fa yake shakkar Mami idan taji wannan zancan yaya zata d'auke sa.
Yana cikin tunani yaji ringing d'in wayarsa, da sauri yakai dubansa ga wayar a hankali ya d'au wayar ganin Daddy ne ke kiransa.
Da sallama ya amsa wayar, daga cikin wayar Daddy ya ce "Khaleefa ka kwantar da hankalinka nasan abun yake damunka akan Maminku ne ko?, ni nan insha Allahu idan lokacin sanar da ita yayi ni zan sanar da ita, karka damu, ai ni nasaka kayi auran, bawai yin kanka bane, so hakan karya dameka kaji"
Sauke ajiyar zuciya yayi cikin muryarsa mai sanyi ya ce "to Daddy insha Allah amma ita yarinyar yaushe zata bar nan d'in?"
"Karka damu insha Allah sati mai zuwa zamu dawo idan mun dawo zanmu zo da kai garin mu taho da Marmah, a matsayin rik'eta zanyi dan har yanzu nasan yarinyar bata gama karatu ba, ba lallai ma tayi karatun ba, idan yaso a sadda ta gama karatunta ta k'ara zama budurwa sai ayi bikin tarewarta gidanka"
Lumshe idonsa yayi yana jin sanyi a zuciyarsa, da ba yanzu Mami zata san zancan ba, sallama sukai inda yake shaida ma Daddy shima yanzu yake shirin barin garin zai biya ta Kano, zai hau jirgi zuwa Abuja, inda yake aikinsa.
Sai da yaje wajan Mlm sukai sallama ya gayamai sati mai zuwa zasu zo da Daddy domin tafiya da Marmah, ya gayamai kad'an daga abunda suka tattauna da Daddyn, shima Mlm yayi na'am da abunda Daddy ya ce, sai da Mlm ya tsareshi yaci abinci sana sukai sallama, yaso yaga Marmah a ranar, sai dai jama'a sunyi yawa a cikin gidan, dama wajan gidan.
Sai wajan dare aka kai ko wacce amarya d'akinta, sab'anin Marmah dake rakub'e a d'akinta tana kuka kamar ranta zai fita, bata san makomar auran nan, da akai mata ba, bata san waye angon ba, tana addu'ar Allah yasa shine mafi alkhairi a gareta.
Tana ji tana gani aka fitar da kowacce amarya daga gidan aka nufi gidan kowacce, Habiba ce ma k'arshen kaiwa, su Mlm ne suka bata mota aka kai Habiba, wadda angon ma yana can yawonsa, kwana biyu ba'a ganinsa a gidan.
Haka taji sun dawo suna ta zancan gidan Narnah yayi kyau sosai, ko wacce ma dai sai san barka, amma na Narnah ya zarce na kowacce, amma duk da haka, Hajara bata farin ciki, ba abunda take ma Marmah sai fatan tsiya, tana zaginta, da kwashe mata albarka, sai kace ita tasa aka aura mata Khaleefan.
Washe garin ranar tunda asubahi Hajara ta fice daga cikin gidan ta nufi wajan Bokanta, koda taje Bokan ya tabbatar mata da cewa "bazai iya raba auran ba, amma yarinyar akwai sauran k'alubale a gareta domin Mahaifiyar yaron bazata sota ba, kawai ta rabo da irin k'alubalen da zata fuskanta ma a can"
Ai ko jin abinda Boka ya ce yasa Hajara cikin farin ciki, tunda dai Marmah bazata tab'a jin dad'in uwar mijinta ba, ai ko bata ba kwanciyar hankali, wahala kawai zata sha, shi yasa Hajara ta baro wajan Boka cike da farin ciki.
Tunda aka kai Narnah Abbas bai shigo ba, sai wajan sha biyun dare, kuskuran da Narnah tayi tana waya da Hajara ta furta sunan Marmah, Abbas yaji, yana ji yaji kansa yayi wata irin sarawa, yana son tuna ina ya san mai sunan nan?, ganin kansa ya matsanta masa da ciwo idan yana son tuna wacece mai wannan sunan.
Kwata-kwata Narnah a