Author : Zahra Royal Star Category : True Hausa Novels
ciki a ranta tasa d'an yatsa a bakinta tana cizawa, cike da tsananin kishin Marmah a ranta, dan Allah ya gani batun yau ba ba tun yanzu ba Narnah ke nuna tana son Abbas, kai bama shi kad'ai ba duk wadda zai nuna yana son Marmah itama saita ce tana sonsa, Marmah tasha barma Narnah abu koda tana so, idan ma bata barmata ba, koda tsiya koda arzik'i sai Hajara ta rabata da abun.
Gaban Marmah ne yayi wata irin mahaukaciyar bugawa, har sai da ta dafe k'irjinta.
Ganin Narnah ta k'araso kusa dasu tana jefama da Marmah wani d'an iskan kallo, ta nunata da yatsa tana cewa,
"Algunguma, dama abunda kikeyi kenan idan an aike ki, kina yawo da samari suna lallatse ki, to na rantse da sarkin dake busan lumfashi, yau sai kin gane shiyi ma ruwa ne, y'ar iskar yarinya kawai...... Kamin ta idasa rufe baki, taji an d'auke ta da wani gigitaccan mari, da wani irin sauri Marmah ta d'ago tana duban Abbas dake huci, jikinta ne ya kama kyarma cike da tsananin tsoro, Marmah har bakinta na kyarma wajan cewa,
"Na shiga uku Ya Abbas mi yasa ka mare ta, kasan mi wannan marin zai jamin kuwa?, daka barni da bala'in dazan fuskanta na gani na da kawai tayi da kai, innalillhi wa'innan ilaihar raju'un".
Ta fad'a tana sakin wani marayan kuka, tana bin Narnah da kallo ganin yadda take murmushin mugunta ta rik'e fuskarta dai-dai inda Abbas ya mareta, kallonsa tayi ido cikin ido ta ce "hmm wannan marin da kayi min kaci darajar ina sonka, duk cikin sonka ne da nake yi kai da baka isa tafiya wajan nan salin alin ba, wallahi kaci darajar ina sonka, amma wacce kake ikirarin wai kana so, a kanta zai k'are, danna rantse baka mari banza ba, kuma ka rubuta aje ni d'in nan nice wacce zaka aura...............✍️
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 7
"Kee ni sa'anki ne zaki tsaya kina gaya min wannan maganganun?, banzar naki"
Abbas daya idasa maganar yana tsare Narnah da ido, ko kallonsa batai ba, ta juya da sauri ta shige cikin gidan nasu.
Juyowa yayi ganin yadda Marmah ke kuka duk'e a k'asa, da sauri ya d'agota, ba shiri ta ya tashi tana goge hawayen dake sintiri akan kumatunta, tana nuna sa ta ce,
"Ya isa haka, Y Abbas dan Allah kabar wajan nan yanzu, tun kamin wani ma ya k'ara ganinmu, in k'ara jama kaina wata masifar",
"Amma ya za'ai na tafi na barki a haka nasan dole sai anyi miki wani abu na b'acin rai, ni gaskiya bazan iya tafiya na barki a wannan yanayin ba, nina ja miki komai ina ganin bai kamata na tafi na barki a wannan halin ba"
Da sauri ta ce "Y Abbas zan iya d'aukar komai duk wani wulak'anci naso, na saba da hakan, amma shedar da aka fara min ta neman maza tana sa zuciyata a wani mugun bak'in ciki, ka tafi kawai"
Ganin yadda take kuka kamar mi yasa Abbas juyawa ya fara tafiya yana yi yana waigenta, yadda kasan daga lokacin bazai sake ganinta ba, harya b'ace ma ganinta.
Juyowa tayi ta nufi zauran gidan zuciyarta na lugudan bugawa, ta kusa shiga harabar gidan kawai taji tayi garo da mutum, wata irin zabura tayi tana komawa baya, ganin Hamisu a gabanta yana jefa mata wani d'an iskan kallo, yana lashe baki.
Kallonsa take k'irjinta na bugawa sosai, tsabar tsorantar da tayi.
Can ta tsinkayi muryarsa irin ta gaggun y'an iska yana cewa "Ohhh wato dama abunda kiki yi kenan?, yawon banza a aike ki, shine sai kin lab'e wajan maza su latse ki, ai daba sai kinje wani waje ba, kawai ki taho waje na, ni nan sai na biya miki buk'atar ki, ba tare da kowa ya sani ba"
Ya idasa maganar yana kamota ya had'ata da jikinsa, wani shegen wari ne ya ziyarci Marmah kamar warin giya kamar kuma warin taba ko wiwi, ba shiri ta k'ara sakin kuka, tana son turesa iya k'arfin tana cewa "ka cika ni Y Hamisu bana so irin haka, ni ba y'ar iska bace, ban tab'a iskanci ba, dan Allah ka kyale ni bana so"
Ta idasa maganar bakinta na rawa da wani irin kuka mai tab'a zuciya, ba tai aune ba taji hannunsa akan k'irjinta yana shafawa iya k'arfinsa yana murzawa, yana faman cewa "ke y'ar iska a hakanne kike ikirarin cewa wai maza basa latsa ki, dan uwarki, to ko kink'i ko kinso na rantse sai na ratsaki, saina d'and'ana zumarki".
Wani irin tuk'ukin bakin jiki ne ya ziyarci Marmah har bata san sadda ta ware hannunta ta hankad'e shi tasa tafin hannunta tana d'auke sa da wani gigitaccan mari har guda biyu ji kake tasss tassss.
Wata irin zabura yayi yana ware idonsa a kanta yana nuna kansa,
"Keee ni kika mara?"
Kuka kawai Marmah keyi ba bakin magana bak'in ciki ya hanata magana ma kwata-kwata.
Batai aune ba taji ya kama gashin kanta da k'arfi, ya gwara kanta da bango, wata irin azaba ce ta ziyarci Marmah har k'okan kanta, wata irin k'ara ta saki wacce bata fita sosai, jefar da ita yayi k'asa, yana sa hannunsa, a k'ugunsa ya kwanto bel, d'in dake d'aure a waddonsa, bai tsaya wata-wata ba ya fara jifgar Marmah baji ba gani.
Ihu take tana birgima k'asa sune har tsakar gida yana mata wani shegen duka, ai da saurin mutanan gidan suka fiffito, ganin irin dukan da yake mata hakan baisa wani ya ce danmi ba.
Hajara data k'araso wajan, itama cike da jin haushin Marmah saboda Narnah ta gaya mata komai, yasa ta d'akko wani dutse ta buga mata shi a kai, da sauri Marmah ta rik'e wajan ganin jini na zuba dan da nan goshinta ya fashe, ya kunbura.
Hajara ta ce "ai wallahi kamin dai-dai dama kaine wadda nake nema yau ya lallasa min wannan y'ar iskar yarinyar shegiya ballagaza kawai, y'ar iska mai bin mazan banza, tunda aure kike so to sha kumurin ki za'a miki, ni nan zan kawo miki mijin daya dace dake",
Ta k'ara matsawa kusa da ita amshi bulalar dake hannun Hamisu, ta daddage iya k'arfin ta a dai-dai gadon bayanta ta zafga mata bugu, harsai da Marmah ta gantsare tana sakin wani irin kuka.
Hajara ta k'ara cewa "amma ki bud'e kunnanki ki jini, ko zanyi yawo tsirara, na rantse da Allah Marmah, bazan tab'a bari ki auri wani ba a rayuwa, kuma Abbas keda shi har abada daga yau, na sake jin an ganki da wani namiji ba wadda nice nan na zab'a miki ba, na rantse miki, sai kin gwammace dama ba'a haife ki ba"
Tana gama maganar ta jefama Hamisu bel d'insa ya amsa yana cewa "waifa ganinta nayi zauran gidan nan da wani saurayi yana latsa mata nono, shine na fara mata fad'a, shine da yake y'ar hannu ce harda sa hannu ta mare ni, ni ko shine na nuna mata nima d'an tashan ne"
Tashi Marmah tayi tana girgiza kai hawaye sai zuba suke, gaba d'aya jikinta rad'ad'i yake mata, duk Hamisu ya fasa mata jiki.
Inna Suwaiba dake kallon komai ba damar tayi magana dan yanzu gaba d'aya gidan shakkar Hajara suke idan aka cire Inna Khande, da ita bama ta wajan danko fitowa bata yi ba, bare tasa baki, ayi mata rashin kunya.
Marmah zatai magana, domin kare kanta daga wannan bak'in sharri da Hamisu ya mata, bata kai ga magana ba, Hajara tasa hannu ta buge bakin tana cewa "imin shuru makira miye zaki ce mana?, al'gunguma, wacce ta iya tsaro zance, ke har kina da abunda zaki ce ma mutane, kuma yau baza ki kwanar min a d'aki ba, d'akin uwarki data zauna zaki koma dan bazan zauna da mazinaciya ba, y'ar iska"
Wasu hawaye ne suka k'ara zuboma Marmah bakinta na rawa muryarta na kyarma tana cewa "Um..Um....Umma wallahi ban tab'a iskanci ba, Umma d'akin itace ne fa aka maida shi"
Ta fad'a tana jin wani bak'in ciki a ranta yadda aka maida d'akin Mahaifiyarta wajan aje itace, da tsunmokara.
Hajara dake zafga ma Marmah hararara cike da tsana da kyara ta ce "kware kuwa, ko baza ki koma ba?, ai ko ban d'aki ne ya koma sai kin tare a can sai kin koma wallahi, kinji na rantse miki, inba ni ba ma, ubanwa zai iya rik'e ki, dan haka maza-maza kizo ki kwashe kwamutsanki ki kai so can, kuma kazo ki tankade garin nan wallahi yau ke ce zaki tuk'asa, koda zaki fad'a a cikin tukwanyar ne"
Kuka Marmah ta k'ara saki, kukan da ba hawaye, tsabar yadda take kuka tun d'azo yasa hawayen ma k'afewa babu so, sai idonta da yayi jawur.
Hajara dake kallonta ta ce "baza ki tashi ba?, kai Hamisu k'ara mata wani dukan, dan Allah kabarmin ita kwance na ce".
Hamisu kamar jira yake ya fara jifgarta kamar Allah ya aikosa, dama da biyu yake mata wannan uban bugun, tak'i basa had'in kai, amma yaci alwashin wallahi saifa ya d'and'ani zumar wannan yarinyar, tun tana k'arama yake kwad'ayinta, bare yanzu da yaji luntsuma-luntsuman nonuwanta masu taushi kamar auduga, ga yarinya da bazaune kamar ita ta k'era kanta.
Tun Marmah na iya kare kanta wajan dukan da Hamisu yake mata harta kaiga ko d'an yatsa bata iya d'agawa, tun tana kukan neman ceto harta gaji, sai wata ajiyar zuciya da take saukewa Narnah dake tsaye itama wajan dariyar mugunta kawai take ma Marmah, Bishira da Habiba duk da ba wani shiri suke ba, ba k'aramin tausayi ta basu ba, kwafa Habiba tayi tana kallon Hamisu, tana magana a zuciyarta.
"Kenan Hamisu so yake ya lalatama Marmah rayuwa, kamar yadda ya ribace ta ya lalata tata rayuwar ya manta mike tsakanin su ne, tabbas idan baiyi a sannu ba, wallahi ta gaf da tuna mai asiri, ita zai yaudara"
Ta idasa maganar zucin tana fad'awa cikin tunani a sadda Hamisu ya ribace ta.
Kwanakin baya da suka wuce.
Habiba ce tsaye a harabar gidan nasu, babu kowa a gidan sun tafi wata barka, dake wajan K'auyan su, dan lokacin harda Bishira aka tafi sai ita d'aya aka bari tana wankin kayan Mamansu, daga ita sai wani guntun zani, ta duk'a tana faman wanki, dan idan ta duk'a har k'asanta kana iya hangowa, gashi ko wando babu a jikinta.
Hamisu ne ya shigo cikin gidan yana hard'e kafafuwa waddonshi ya cika yayi fam abar girmansa ta mik'e samb'al, dama ya kwaso jarabarsa tun a waje, yana zuwa ya hangi Habiba dake duk'e tana wanki, baiyi wata-wata ya matsa kusa da ita, yana sa hannunsa a dai-dai k'asanta a dai-dai y'ar tsakarta ya matse yana shafawa yana luliyawa, wata irin tsabura Habiba tayi tana juyowa tana shirin kwasa mai mari, wata shafa da yayi ma nonuwanta, yasa ba shiri ta k'ara rungumesa tana lumshe ido, zatai magana yasa d'an yatsa ya tushe mata baki yana cewa,
"Shittttt ai kina so kiji dad'i ko, ni zan rink'a biya miki buk'ata"
Turesa take sonyi tana cewa "kai yaushe kaji na ce ina son jin dad'i?"
"Hhhhh yarinya kenan na tab'a ji mana kuna zancan keda Bishira, kinga yanzu kin samu a gida, babu wadda zai san tsakaninmu, kawai ki manta muji dad'in mu"
Sauke ajiyar zuciya tayi shed'an na k'ara zugata, dama gashi Hamisu ya kanainayeta sai faman shafa sassan jikinta yake, duk inda yasan zai taso mata da sha'awa, nan ne yake tab'awa, har bata san sadda ta k'ak'k'amesa ba, ya sureta sai zaure inda d'akinsa yake.
Tun daga wannan lokacin ya lalata Habiba, koda yaushe suna tare suna shek'e ayarsu, sun manta da Allah na kallonsu, har basu ankara ba, ciki ya shiga, sosai suka shiga tashin hankali, inda daga nan suka fara fad'a Hamisu ya ce su zubar dashi ita kuma tana tsoro, dan taji ance har mutuwa ake, inda da kyar ta amince, a zatonsa ta zubar da cikin ne shi yasa ya fara baya-baya da ita, yana nuna mata halin ko in kula, shine yanzu yake shirin b'ata Marmah.
"tabbas Hamisu ka d'akko dala ba gammo, tunda ka lalata ni na rantse da sarkin dake busan lumfashi saika aure ni, babu mijina a duniyar nan sai kai, ni nasan abunda zanyi"
Ta idasa maganar zucin tana dawowa tunanin data lula, tana nadamar biye ma son zuciya da tayi, da kuma biye ma Hamisu da tayi, Allah kad'ai yasan irin tashin hankalin da za'ayi a wannan family, idan wannan abu ya fito, babu yadda zatai ne dole Hamisu ya girbi abunda ya shuka, wallahi.............✍️
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* 8
Sallamar Mlm ce ta tsayar da Hamisu daga bugun da yake ma Marmah.
Da sauri Mlm ya k'ara so kusa da Marmah, yasa hannunsa yana d'aga ta yana cewa "subhalllahi, Hamisu miye tayi maka haka, kake mata wannan uban dukan?",
"Yo Mlm taddata nayi da wani k'ato a zaure yana shirin b'ata mata rayuwa"
Da sauri Marmah ta shige jikin Mlm tana girgiza kai bakinta yayi mata nauyi.
Kallonsa Mlm yake yi cike da tsananin mamaki yana cewa "Hamisu Marmah ce ka kama da k'ato?, anya baka sha wani abun ba yauma?, to ni dai nasan jikata bazata tab'a iya aikata abunda kake fad'a ba"
Ya sake juyowa ga mutanan gidan ya sake cewa "dan bakwa sonta gidan nan shine ko a samu wadda zai tsawatar mai, saboda Allah dubi irin bugun da kayi mata, kayi dai-dai kenan?, kai wake bugunka haka iyee?, kai akwai wadda ya kai ka rashin ji a cikin gidan nan ne".
K'unk'uni Hamisu ya fara yi yana sa k'afa ya fice daga gidan, yana ai kama da Marmah wani kallo, na ina nan hak'e dake, kuma zamu gamu ne.
Da sauri Mlm ya fice da ita daga cikin gidan suka nufi kyamis, suna isa shi kansa mai kyamis d'in ya girgiza da ganin irin bugun da akai ma Marmah, cike da tausayi ya bata magunguna, ya wanke mata ciwokan da aka ji mata, yana mata addu'ar samun lafiya, haka suka taho cike da tausayinta Mlm keta bata hakuri, yana cewa,
"Jikata kiyi hakuri kinji komai mai wucewa ne zaki ga watan wata rana kamar ba'ayi ba, ki daure ki cinye jarabawarki Allah ya k'ara miki hak'uri",
Hawaye Marmah ta share bata ce komai ba, sai faman had'iyar zuciya da take, haka har suka k'arasa gida Mlm sai da ya biya ya sai mata lemo da kilishi, suka shiga sashin sa ta k'ofar waje, da yake zaka iya shiga sashin Mlm ta wata k'ofa dake waje harka b'illa cikin gidan, shi yasa bai cika sanin mima tsakar gidan nasu yake ciki ba, saboda ko fita zaiyi ta k'ofar waje yake fita ta cikin sashinsa.
Sai da Mlm ya tabbatar ta cinye abinda ya sai mata, tasha magani, sana ya k'ara mata nasiha akan hak'uri, sana ya barta ta wuce cikin gidan.
Koda ta shiga gidan kayanta taje ta kwaso daga d'akin Hajara tana kaiwa d'ayan d'akin Mahaifiyarta wadda yanzu ya zama na ajiye itace, d'akin duk yayi k'ura ga warin kayan wanki da ake tumawa a ciki, da kyar ta daure ta d'an gyara wani wajan inda zata samu ta kwanta, ga cinna ku duk sunma d'akin yawa, haka nan tasa wata yagaggar tabarma ta aje kayanta a kai.
Fitowa tayi waje jin Hajara na kwala mata kira da k'arfi.
Da bugawar zuciya ta fito ta ce "gani"
Wani kallo tayi mata na sama da k'asa ta ce "tunda bakiyi tuwon rana ba, maza ga shinkafa can da wake, kije ki dafa ta, kizo idan kin gama ki wuce tallah, dan Narnah ta gama zuwa tallah wallahi, daga yau kece wacce zaki koma zuwa, kamin a aurar daku a tare, ko wacce ta gama gabanta"
Wata irin fad'uwar gaba ce ta ziyarci Marmah, cike da k'arfin hali taje ta kama aikin data sata, tana yi tana hutawa, ga wani hakki dake taso mata, zuciyarta tayi nauyi, haka dai harta gama ta d'au tallar ta wuce.
Habiba ce duk'e tana kwarara wani uban amai ba k'ak'k'autawa, Maryama dake tsaye kanta cike da tashin hankali ta d'agota tana faman mata kallon tsaf, wata irin kururuwa ta buga, da yasa mutanan gidan fitowa ba shiri.
Hadiza dake tsaye ta tab'e baki tana cewa a hankali,
"Komi ke shirin faruwa ne yau kuma yau zamu sha kallo da alama"
Maryama tada rik'e Habiba tana zare mata ido ta ce "keee d'ago ki dube ni nan",
D'agowa tayi tana zubawa uwar tata ido duk ta galabaita ta rame, Bishira dake tsaye ta ce "haba Mama baki ganin bata da lafiya ne?, kike mata ihu"
Bata tankama Bishira ba ta sake kallon Habiba ta ce "ubanwa yayi miki wannan abun kunyar dake jikinki?,
Gaba d'aya mutanan gidan suka d'auki salati, suna cewa,
"Innalillahi abun kunya kuma"
Inna Indo da gabanta ke lugudan bugawa ta matso kusa tana cewa "ke Maryama wane irin abu kike haka?, a bainar nasi miye kike tuhumar y'arki dashi haka?,"
Maryama dake tsaye cike da bak'in ciki ta ce "kinga Inna ki barni da ita yau wallahi ciki ne da ita ba tun yanzu na fara lura da ita ba, yau saita gaya min Ubanda suke shashanci dashi"
Kuka Habiba ta saki ta duk'e k'asa sai uban kuka take mai cin rai, cike da bak'in ciki Maryama tasa hannu ta shak'o wuyanta tana cewa "zaki gaya min uban waye yayi miki cikin nan ko kuwa, sai