Author : Zahra Royal Star Category : True Hausa Novels
duk wadda yake son ayi tafiyar book d'in nan dashi book 1 ya kusa k'arewa, daga na 20 za'a shiga book 2, tohm gsky book 2 na kud'i ne naira #500 ne kacal game buk'atar book 2 akwai sa complete a yanzu haka d'aya turo kud'insa zan tura masa ni kuma Kai tsaye idan kana so zaka iya min magana ta wannan number d'in*
👇
08130479973
Ko kuma ka turo kud'inka ta wannan account number d'in
👇
8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank
Saika turo shaidar biya a number Dana aje sama.
*K'ANGIN RAYUWA*
*(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
SHARE FISABILILLAHI
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Follow the K'ANGIN RAYUWA HAUSA NOVEL CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029Vaa4Njl4SpkNAtqcRa3u
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Masu tabbaya daga farko please kuyi FOLLOWING CHANNEL D'INA, zaku samesa tun daga farkon, saboda turowa kullum daga farko da ake yawan tabbayata akwai wahala amma duk wadda yayi following zai gansa daga farko a channel d'in.*
*EPISODE* *END END END*
*IT IS THE LAST PAGE I WILL TYPING A LOT*
Duk wata wahalar RAYUWA da tsangwama Marmah ta gansu, a shekaru biyun data yi a gidan Mami, amma data jure ta kauda kai, sai gashi komai ya kusa shigewa ya wuce.
Cikin nasarar rayuwa ta gama school d'inta inda tana gamawa ta samu aiki asibiti, sai dai Y Khaleefa ya nuna baya ra'ayi kuma ya nuna mata ba'a Kano zasu zauna ba, zai samar mata wani aikin a can Abujar.
Gaba d'aya an fara shirye-shiryen bikin su Ifteesan, kwana biyun ta samu sauk'in bak'ar maganar da suke yab'a mata, domin kullum basa gidan, suna gyaran jiki, gobe suna kasuwa, a sayo wannan a sayo wancan, gida ya fara d'aukar harami, Marmah itace suke sa duk wani aiki, Y Khaleefa yana jin ciwon abun, amma babu yadda zaiyi ne, saboda yana sa baki Mami ke gwalashe shi, ya zuba musu ido kawai, domin Daddy yaune yake shirin sanar da Mami, ita kanta Marmah a firgice take, tun safiyar ranar bata fito daga d'akinta ba, saboda tana jin sadda Daddy yake cewa yana son ganin Mami a sashinsa.
Cike da farin ciki ta shiga sashin Daddy ta d'auka ko wani abu zasu tattauna wadda ya danganci bikin su Khairat d'in.
Zama tayi kusa dashi tana cewa "Daddyn yara ina cikin mutane ka aika a kira ni, ko wani abunne ya taso kuma?"
"A'a ba wani abu bane, dama akwai abunda baki sani ba, kuma ya kamata ki sani, wadda zan sanar dake yanzo, za'a kawo wani lefe akwati goma sha uku za'a kaishi can garinmu domin dangi su gani"
Dakatar dashi tayi da sauri tana cewa "lefe kuma?, kuma akai shi garinku, to akan mi?"
"Shine nake so ki tsaya ki saurare ni ko"
"To ina jinka ai"
Sosai Daddy shima ya canza fuska babu wasa ya fara sanar da ita duk abunda ya faru dangane da auran da Khaleefa yayi da kuma wacce ya aura.
Tunda ya fara magana harya kai aya, Mami ke kallonsa, sake da baki, ko motsi ta kasayi bare ta ce wani abu.
Kawai gani yayi ta tashi ta fice daga part d'in ta nufo part d'inta da mugun sauri yabi bayanta.
Mami tana shiga parlonta tayi hanyar d'akin Marmah, da k'arfi ta banka k'ofar d'akin ta shigo, su Ifteesan da dawowarsu kenan daga wankin kai, sukaga Mami tayi d'akin Marmah kamar bata cikin hayyacinta yasa suka rufa mata baya suma.
Sai dai Mami tana shigowa d'akin ta iske Marmah zaune kamar tasan sai tazo d'akin, ba shiri Marmah ta mik'e tana kallon Mami a tsorace.
Mami bata b'ata wani lokaci ba, ta matsa kusa da Marmah tana d'auketa da wani gigitaccan mari, tassssss, ta nunata da yatsa bakinta na kyarma tana cewa "wato abunda nake zargi akanki ya tabbata kenan?, akwai manufar zamanki a cikin gidana kenan, kinsan komai kenan?"
Girgiza kai Marmah keyi tana ja baya amma duk da haka sai da Mami ta k'ara kai mata wani bahagon mari, wadda har yasa Marmah zubewa k'asa.
Wata tsawar ta kuma buga mata tana cewa "harda had'in bakinki kika aure min d'ana, ki dube ki da kyau, d'ana ba sa'an auran irinku bane, to na rantse da Allah sai ya sake ki yau-yau d'in nan"
"Idan kike sake kike k'ara furta kalmar Khaleefa ya saki Marmah to tabbas kema, ki rubuta ki aje sai kin barmin gida na"
Ja da baya su Ifteesan suke ba shiri jin muryar Daddy a bayansu, cike da d'unbin mamaki suke kallon abun, yanzu wannan yarinyar ce matar Y Khaleefa, duk cin mutumcin da sukai mata dama da auran Y Khaleefa akanta, amma bata nuna komai ba, bare ta nuna d'agawa, jikinsu ne yayi sanyi, lokaci guda daga Ifteesan d'in har Khairat suka ji Marmah ta basu tausayi, da sune a matsayinta da yanzu wata maganar ake ba wannan ba.
"Kamar ya ban gane ba Alhaji, akan wannan abar kake cewa wai yau na barma gidanka akanta?"
Cewar Mami tana nuna Marmah cike da b'acin rai a fuskarta ji take kamar ta shak'e Marmah, saboda tsabar yadda take jin tsanarta a ranta.
"Kware kuwa kuma idan kina ganin wasa kisa Khaleefan ya sake ta kiga matakin dazan d'auka, kuma a ranar da za'a kai su Ifteesan gidajan mazajan su a ranar Khaleefa zai d'au matarsa su wuce Abuja, dan acan na basa gida, kamar yadda nayi ma y'ay'ana hidimar biki itama haka zanyi mata, dan haka tun wuri idan zaki samawa zuciyarki ruwan sanyi ma kiyi, domin mudun ina raye, ke koda na mutu ma, ban amince Khaleefa ya saki Marmah ba, idan ko yayi haka ban yafe masa ba".
Wani irin juya ido Mami tayi tana kallonsa lallai ta k'ara yarda dangin Mijinta sun wanke sun bashi yasha yo idan ba haka ba, ubanwa yake ma irin wannan gatan idan basu ba.
Fuuuuu Mami ta wuce kamar zata tashi zama, su Khairat jiki a sanyaye suka fice daga d'akin sai Daddy dake ba Marmah hakuri, yana ce mata komai ya kusa zuwa k'arshe.
Marmah dake kuka ta d'ago tana cewa "amma Daddy sai yaushe ne Mami zata soni?"
Shafa kanta yayi yana samata albarka yana cewa "zata soki, insha Allah very soon"
Yana fad'ar haka yabar d'akin zuciyarsa babu dad'i.
Mami zarya kawai take a d'akinta ta kasa zaune bare tsaye, su Ifteesan ne suka shigo suna cewa "Mami dan Allah ki kwantar da hankalinki komai zaiyi dai-dai"
Kallonsu tayi cikin fad'a ta fara cewa "wai ni Daddynku yau yake cema na bar gidansa idan na k'ara magana akan na tab'a danginsa"
"Amm.... D'aga musu hannu tayi tana cewa "ku tashi ku bani waje naga alamar kuma ta gama daku, maganar banza zaku gaya min, tama k'ara b'ata min rai"
Tashi kawai sukai suka bata waje.
Khaleefa kuwa ta fuskar Mami kawai ya gane akwai matsala, Daddy ya sanar da ita kenan, dan ko gaida ta yayi bata amsawa saima ta d'auke kai, duk da haka bai fasa bata hakuri da gaishe ta ba, amma duk sadda zai mata magama saita yarfa shi, kota danna mai ashar duk akan Marmah.
Haka dai aka fara biki ba wani sakin fuska ga Mami koda akazo kai lefen Marmah y'an uwan Daddy su gani, tunda ba'ayi mata lefen tun time d'in ba, Mami ta hana kowa cikin danginta zuwa, sai d'ai-d'aiku sukaje kai lefen.
Inda Marmah taga canji wajan su Ifteesan, duk wani gyara sai suka rink'a jawota jikinsu anayi da ita, duk da haka dai, bata wani sakewa dasu.
Tofa tunda aka kai lefen gidansu Marmah, nanfa kallo ya koma sama, ba wadda bai girgiza da ganin irin uban lefen da aka narkama Marmah ba, a sadda aka kawo lefen Hajara lokacin y'an hankalin na kai, ta girgiza ainon, bak'in ciki ya kusasa zuciyarta bugawa, danda nan ta fara sakin maganganu barkatar haukan ya motsa, tana tunama kanta asiri duk abunda tayi ranar saida ta fad'eshi kaf, da kyar aka janyeta daga wajan a ranar Hamza ya saki Hajara, furincin daya sata ta k'ara hartsewa, tana cire kayan jikinta, tana fisge gashin kanta, y'an kawo lefe sunga tashin hankali, da kyar aka d'aure Hajara wani d'aki.
Koda wa'inda suka kawo lefe suka dawo suna bada labarin Hajara, sosai Marmah ta girgiza dajin abubuwan da Hajara ta aikata mata wadda bata sani ba, sosai ta rink'a kuka kamar ba gobe, koda Mami taji ta ga yadda Marmah ke kuka, da irin abunda taji yarinyar ta fuskanta a cikin rayuwarta, duk sai jikinta yayi mugun sanyi.
Shi kanshi Khaleefa yayi mamakin jin abunda aka kaita ma Marmah, zuciyarsa ta k'ara kamuwa da tsananin tausayin matarshi, sai kuma ganin Mami ta dawo tana amsa masa gaisuwa, ta rage kyarar Marmah da take yi, sai dai ba wani sosai take sakar mata fuska ba, amma dai tana mata magana cikin dad'in rai, a hakan ma Marmah ba k'aramin dad'i taji ba.
Ranar juma'a aka d'aura auran su Ifteesan, kuma a ranar kowacce aka kaita gidanta, Khairat Abuja sai Ifteesan cikin garin Kano, a tare aka je kai Marmah da Khairat, da wasu dangin Marmah y'an uwansu na gida, dan harda Habiba aka je Abuja.
Sunsha kallo fa gidan Marmah sun girgiza da ganin irin kayan da Daddy yayima Marmah, komai iri d'aya da y'ay'ansa yayi mata, kusan d'akuna hud'u ne sai parlo biyu, sai kuma wani parlo na sakar bak'i, gida fa yayi masha Allah sai san barka, su Habiba haka aka baro Abuja Marmah ta cikasu da abun Arzik'i naban mamaki..
Haka suka dawo gida suna bada labarin irin dukiyar da daular da Marmah take ciki a yanzu, da garin da aka kaita, garin masu kud'i.
Koda labari yaje ma Narnah kuka ta rink'a yi tana sake nadamar abunda tayi ma y'ar uwarta, a ranar ma sai da Abbas yayi mata shegen duka, yana mata gorin, ai gashi sunyi mata bak'in ciki, sai kuma gashi Allah ya maida mata mafiyin wadda suke ganin ai yafi k'arfin Mamarh.
Marmah sosai take ba Mijinta kulawa yadda ya kamata, shima haka yana riritata kamar kwai, yana nuna mata so, ji take kamar ita kad'ai ce tayi dacen miji a duniya.
Sati uku da yin auran su Ifteesan, matsaloli suka fara k'unnu musu kai, ita Khairat mijinta ya ce taje ta koyo girki, da dabarun zama da miji, danya lura bata iya komai ba, ita kuma Ifteesan tunda aka kaita ta lura ashe mijin data aura d'an k'arya ne duk wasu kud'in da yake zuzutawa yana da su ashe k'arya yake mata, to itama dai bata iya komai ba, ta ce ya d'akko masu y'ar aiki, shi kuma ya ce baida halin d'akko y'ar aiki sai da taje ta koyi yadda zata kula dashi, bazai iya da irin halinta ba, idan ba haka ba kuma ya sake aure, tana ji tana gani.
Tunda suka gaya ma Mami hankalinta yake tashe, sai dai Marmah data ji wajan Mijinta yake gaya mata, ta ce mai ya kawo mata su suyi wata d'aya a wajanta zata koya masu komai da ikon Allah.
Koda Mami taji haka, taso tayi wata magana amma saita basu damar tafiya gidan Khaleefan.
Cikin ikon Allah dama sun samu fahimtar juna da Marmah, cikin farin ciki da kwanciyar hankali ta rink'a koya masu komai, da yake iyawar suka zo yi, sai suka mai da hankali wajan koya, kamin ma wata d'aya ba laifi sun iya wasu abubuwan, nanfa sukai ta k'ara ba Marmah hakuri dama ashe haka masu aiki suke wahala, amma da idan sukai masu aikin basa ma ko gode masu, lallai sunyi kuskure babba, ashe da ba gata ake nuna musu ba, da sai dai su ci su kwanta, inda Marmah ta nuna musu ita dama bata rik'e su a ranta ba, Aunty sama Aunty k'asa suke kiranta dashi yanzu, ba abunda Marmah keyi sai godiya ga Allah.
Koda suka koma gidajan mazajan su sosai suka ga canji, sosai suka k'ara ganin kulawa daga wajan mazajan nasu, inda suka kira Mami suna fad'a mata, sosai Mami ta kira Marmah tana mata godiya harda sa albarka.
Itama Marmah cike da farin ciki take amsa mata tana cewa "ai babu komai yiwa kaine"
Sosai ta k'ara ganin darajar ta, ta k'ara jin sonta a ranta, saboda ta kyautata ma yaranta.
One year later........
A wannan shekara d'aya data wuci abubuwa da yawa sun faru, ciki harda mutuwar Mlm, sosai Marmah taji mutuwar Kakanta dan har suma tayi, da kyar Khaleefa ya shawo kanta, koda suka je garin, saita zama abar kallo, wacce ake ji da ita, kowa so yake ya rab'eta, kuma dama Marmah bata da ruwa bare wulak'anci, tayi ta kyautata ma y'an uwanta, data ji irin zaman da Narnah take da mijinta da kanta ta rok'i da Khaleefa ya barta taje gidan Narnah, ya kuma barta taje sai da tayi kuka ganin yadda Narnah ta koma, Narnah itama tana kuka tana rok'on ta yafe mata, Marmah ta ce dama ita tuni ta yafe mata, ta sake rok'on ta yafe ma Mahaifiyarta Hajara, sai dai Marmah ta kasa cewa komai, hakan yasa Narnah tayi shuru tasan dama ba lallai ta yafe mata dan yanzu ba.
Koda Abbas yazo shima sai da yayi kukan jin Marmah na rok'on sa ya sassauta ma Narnah haka nan kodan ita, inda ya ce insha Allahu zai sassauta mata, abunda yake mata, kamar yadda ta nema, amma ta sani darajarki taci.
Abbas ya rage wasu abubuwan da yake ma Narnah, yanzu har yana barinta fita, taje gidansu, taga Mahaifiyarta dake cikin hauka tuburan, inda Abbas ya sake auro wata matar wayayya y'ar boko nanfa sai dai Narnah ta zama y'ar kallo.
Zaune Marmah take a jikin Khaleefa a babban parlon Mami sunzo Kano kawo ma Mami ziyara, da yake duk k'arshen wata suna zuwa Kano, su duka suna had'uwa a gidan Mami su Ifteesan, Khairat nada ciki, sai Ifteesan dake goyan d'anta namiji.
Kallonsa Marmah tayi cike da shagwab'a ta ce "nima Y Khaleefa ina so"
Kallonta yayi yana ja mata hanci ya ce "mi kake so?"
Ta nuna cikin Khairat.
Dariya yayi ya ce "insha Allah kema very soon zaki samu naki, amma sai kin bari na k'ara dagewa da abun nan, kin yarda mu rink'a yi sau uku a rana uhum?"
Da sauri ta ce "eh wallahi na yarda indai zamu samu baby muma"
Dariya ya saki yana cewa "kai wannan yarinyar waya koya miki rashin kunya wai?"
Rufe fuskarta tayi tana dariyar itama.
Haka wannan ahali suke kasancewa a kullum cike da farin ciki wata rana kuma akasin hakan, yau da gobe sai Allah, har Allah yasa itama Marmah ta samu tana rabon.
Sosai cikin ke wahalar da ita laulayi take mai wahalarwa komi ta ce saita amayar.
Duke take a toilet tana kwarara amai, da sauri Y Khaleefa ya shigo toilet d'in yana kamata ya wanke mata baki, yana mata sannu, d'aukar ta yayi kamar baby yayi d'aki da ita, yana faman mata sannu.
Suna shiga ya shinfid'eta a gado yana d'akko mata abinci ko zata samu ya zauna, tab'e baki tayi cike da zallar shagwab'a ta ce "bazan iya ci ba"
"Ki daure ki ci kinji baby na?"
"Wallahi banzan iya ci ba ko k'amshinsa bana sonji fa baki na d'aci yake"
Da sauri ya maida abincin ya d'akko zuma yana lakuta mata a baki da haka yad'an samu ta samu bacci, bayan ta samu bacci yana kallonta cike da tausayin mata a ransa, lallai mata sun cancaci a jinjina masu.
Sosai wannan cikin da Marmah ta samu ya k'ara mata fitina da rigima, haka dai Khaleefa ya rink'a biye mata, har Allah yasa ta sauka lafiya, ta haifo d'anta namiji mai kama da ubansa sak, karku so kuga irin farin cikin da wa'innan ahali suka shiga, bare Mami ji take kamar ta goya Marmah danso, dama ga Mami da son yara, inda yaro ya ci sunan Mlm wato Sani, amma an b'oye sunan ana kiransa da Mubeen, a gidan Mami tayi wankan arba'in d'inta ta samu kulawa sosai, tayi kuma wayon arba'in amma da kanshi Khaleefan ya kaita, basu kwana ba, suka wuce Abuja.
Haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu cike da son juna da zuminci da y'an uwa, Marmah bata tab'a mantawa da y'an uwanta ba, kullum cikin kyautata masu take, haka ma dangin mijinta su Ifteesan sosai suke zuminci, babu nuna kyashin juna ko hassada.....................✍️
Alhamdulillah Thumma Alhamdulillah
Yabo da godiya su tabbata ga Allah tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Annabi Muhammad Rasulullahi Sallalahu Alaihi Wassalam. Alhamdulillah na gode Allah da ya bani ikon rubuta wannan labarin ina addu'ar Allah ya sa mu amfana da shi.
*NICE DAI TAKU ZAHRA ROYAL STAR INA K'AUNAR MASOYA NA A DUK INDA SUKE*
*SAI MUN HAD'U A BOOK 2 AKWAI SAURAN LABARI A GABA AMMA BOOK 2 NA KUD'I NE, KUNDAI JI YADDA BOOK 1 YAYI ARMASHI, KARKA BARI KARKI BARI A BAKU LABARI, AKWAI SAURAN RINA A GABA, KU DAI KU KASANCE TARE DA NI*
*And ina so na sanar daku duk wadda yake son ayi tafiyar book d'in nan dashi book 1 ya kusa k'arewa, daga na 20 za'a shiga book 2, tohm gsky book 2 na kud'i ne naira #500 ne kacal game buk'atar book 2 akwai sa complete a yanzu haka d'aya turo kud'insa zan tura masa ni kuma Kai tsaye idan kana so zaka iya min magana ta wannan number d'in*
👇
08130479973
Ko kuma ka turo kud'inka ta wannan account number d'in
👇
8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank
Saika turo shaidar biya a number Dana aje sama.