TATTALIN SO Complete Hausa Novels by Surayya.txt

Author :  Surayya Category :  Home Of Novels

Chapter   3 / 18

6K to 9K   out of 51.6K words

ba, ita da gidan wanta "ai ban isa na koreta ba." yamata shiru bai sake ce mata komai ba daman tasan ba zai sake magana ba, don ya fiya miskilanci, baya son yawan magana.

*** ****
karfe shidda 'yan makaranta sun dawo, suna cin abinci ba dadewa akayi mangariba, suna idar da sallah hajiya ta rungumo zainab jikinta tana shafa kanta, tace "zainab yanzu fa yayanki zai zo zai tafi dake gidansa, zaki ci gaba da zama acan."
zainab tasa kuka tace, nidai hajiya bazan jeba nace, yai tamin fada koma ya dokeni, hajiya tace bazai dokeki ba, kuma fada ma ya daina yi miki. Kije ki zauna kinji zainab? Ta make kafada, um-um, ni ba zanje ba."
suna haka taji yo sallamarsa, da sauri ta tashi da gudu tai cikin dakin hajiya. Aliyu ya shigo ya sake gaida hajiya, hajiya tace masa "zainab dai tace baza taje ba, ka ganta can harda kuka."
ya kwala mata kira ta fito a tsorace, tazo ta durkusa a gabansa
yace "shine kika ce bazaki gidana ba? Ta girgiza kai alamar cewa, a'a yace to meye nayin kukan? Yi min shiru. Tasa hannunta ta toshe bakinta ta hadiye kukan.
Yace ki goge hawayenki kije, kiyi wa Abba da daddy sallama." tace to, ta goge fuskarta. Ta shiga bangaren su umma ta tarar da Abba da umma da ummi suna falo, Abba yace yaki 'yata tazo ta zauna a jikinsa." yace menene naga idonki alamar kinyi kuka? Tace bakomai, Abba sallama nazo inyi muku zan koma gidan yaya."
Abban yace "zainab bana son abunda zai takuraki, in bakya son zuwa ni zansa ya kyaleki kiyi zamanki." tace a'a Abba zanje." yace to shikenan zainab, Allah yayi miki Albarka, kici gaba da maida kai da kokari a makaranta, tanan ne zaku fi shiri da yayan naki kinji 'yata?
Tace "to Abba nagode." ta mike ta shiga wajen daddynta, ta daura kanta akan cinyarsa tana kuka. Yasa hannunsa yana shafa kanta yace "kiyi hakuri zainab, nasan bakya son tafiya. Zainab ko yaushe kina raina, dana ganki saikin tunamin da mamanki. Zainab du ina tausaya mana ni dake na rashin mamanki.
Kiyi hakuri zainab kiyi zamanki, nasan zai rikeki da amana kamar ni. Kiyi masa biyayya shida matarsa, banda rashin kunya kinji? Tace "to daddy zan kiyaye." ya bude firij ya dauko rubutu a roba ya bata, ungo shanye rubutunki maganin tsari da kariya daga shaidanu." ta karba tayi bisimilla ta shanye, ya karba yasa ruwa ya dauraye mata, ta karba tasha, ragowar ya zuba a hannunsa ya shafa mata a kanta da fuskarta.
Yaita mata nasiha mai shiga jiki, yace ta daina kuka ta tashi taje su tafi." hajiya dasu ni'ima su sadik har gindin mota suka rakota suna hawaye tana hawaye.

Surayya
[1:23PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**11

HAJIYA tana rungume da ita tana rarrashinta suka bude mata gaban mota ta shiga, ta dunkufar da kanta akan gwiwoyinta tana ci gaba da kukanta kasa-kasa, Aliyu ya sallame su du yaraba musu kudi, yace su koma gida, suna tunanin 'yar uwarsu wai anrabata da gidansu kenan.
Ya kalleta au baki daina kukan ba? Tayi saurin hadiye kukan nata, ta goge idanuwanta. Tafiya kadan suka isa gidansa, suka fito har daki ya kaita, "nan shine dakinki, talatuwa zata rinka taya ki kwana." dakin yayi kyau, a yau dinan ya sayo mata gadon silba da madubi, sai kwaba ta jikin bango, sai labuye da jan kafet, shikenan ba wani shirgi, sai toilet aciki dake gefe, tace "to yaya." ya fita ya nufi sashinsa, zainab itama ta shiga dakin aunty mansura.
Zainab ta kwantar da hankalinta tana zaune a gidan yayanta, tsakaninta da abinci saita ga damar ci, ko yaushe yayan nata yana cikin siyo musu ice-cream, youghot su biskit da cakulet, da yake abinci bai dami zainab ba, ita hakan saya fiye mata dadi.
Ita kuwa mansura ta fiya lalaci da sangarta, bata wani iya girki ba, shikuwa Aliyu dan gaye ne mai aji, gashi da kyankyami, don haka bazai iya cin abincin mai aiki ba.
Don haka inya zo garin ma saidai yaje gida yaci abinci, don a gidansa inna laraba ita take yin girki. Babbar mace ce amma da kwarinta, don bata wuce yin aure ba, sai 'yar budurwa wato talatuwa, ita take yi mata shara dasu goge-goge da gyaran gado, inta yi baki ta kula dasu. Don wata wauta ta mansura dai-dai da mijin ma inya nason wani abu sai dai ta kira talatuwa.
Don haka ma ko meye ya gwammace yayi da kansa, abinci kuwa saiya je gidansu sannan yaci. A gidansu su umma har fada suke yi masa, don me zai rinka baro girkin matarsa baya son ci.
Sai dai yayi murmushi kawai yace musu bakomai. Bama yanzu da mansura take fama da laulayi. Da safe yana zaune a falo da wando iya gwiwa da farar shirt, yana lumshe idanuwarsa kamar mai jin barci. Mansura tana zaune kusa dashi tana cin wainar kwai da dankalin turawa, ta zuba shayi a kofi yana ta turiri, gashi yayi kauri da hadin madara da naskofi da dai sauransu.
Zainab ta fito sanye cikin shirin makaranta, ta durkusa ta gaishe da yayan nata da mansura. Ta mike a gurguje take, dan takusa makara. Ta dauki shanyin gaban auntyn nata tadan kurba, tace "wai aunty wannan kaurin ai yayi yawa, bakya tsoron ya kulle miki ciki?
Mansura tayi dariya tace, laifin babynku ne ba ruwana. Zainab tayi dariya tace ai, "ai gwanda ki dinga ci sosai don ki haifa mana katon baby in rinka daukarsa da kyar." ta nufi firij ta dauko ice-cream da youghot da cake, tazo ta wuce su da sauri saboda yayan nata, tace aunty natafi makaranta." kafin tayi magana Aliyu ya kirata "zainab."
tayi saurin juyowa tare da amsawa, a sanyaye tace na'am yaya." zo nan. Ta dawo ta durkusa a gabansa. Yace haka zaki tafi makaranta baki karya ba? Tace yaya zanci cake da ice-cream da youghot a mota." yace wato har yanzu kina nan dakin cin abincin ki ko sai kayan kwadayi? Ke wace iri ce ne? Da safe ma sai kin sha sanyi bazaki ci abinda zai dumama miki ciki ba?
Mansura tace wallahi haka nake fama da ita, bata son cin abinci, daga shan kayan zaki sai shan kayan sanyi." yace ina break din nata? Mansura ta kwalawa talatuwa kira, tace mata ina break din zainab? Talatuwa ta shiga dakin zainab da sauri ta dauko break din data kai mata, yanda ta ajiyeshi haka yake, ko budawa bata yiba. Ta ajiye a gaban zainab din.
Aliyu ya kalleta yace to maza ki cinye shi yanzun nan." idonta yayi rau-rau alamar sonyin kuka. Shikuwa sai ya jingina da kujera ma ya lumshe shanyayyun idanuwansa kamar zaiyi barci. Ba yanda zata yi, haka ta rinka tura dankalin nan da kwai tana shan ruwan shayin.
Cikinta ya cika taji kokarin yin amai take yi, tace a hankalin cikin sanyin muryanta, "yaya ya dago kai yayi mata wani kallo, bata iya fada masa komai ba, ta sake sunkuyar da kanta, ya sake lumshe idonsa.
Haka taci gaba da ci tana hawaye, saida ta cinye du. Dakyar ta iya tashi tsaye, tace yaya na cinye, na tafi? Ya bude ido daya yayi mata alama da hannu wai ta tafi. Ta fice inda direba yake jiranta ta shiga ta tafi.
Mansura tace gaskiya Aliyu kana matsawa yarinyar nan, da nice saika bata min rai kace ina takurawa kanwarka." ya bude ido daya yace karki manta shekaranta goma sha daya, yanzu ta shiga sakandari aji daya, har yanzu ita yarinya ce, idan bana matsamata taci abinci sai yunwa ta kamata."
ta tabe baki tana gunguni, "in rashin cin abinci ne ai a wurinka ta gado, tunda kaima baka cin na gidanka." ya kwanto akan cinyarta yace, kiyi min da kanki mana, du rashin dadinsa ai zanci. Amma zaki rinka sa tsohuwar mutane wahalar girki, sannan kisa wata yarinya daban itace mai bani abinci, kallon yarinyar nan kadai tayar min da zuciya yake."
ta zumburi baki bata ce komai ba, ya shafa cikinta yana cewa, "i luv u baby, yaushe zaka iso kaga daddynka? Tace ai kuwa zai jima baiga daddyn ba, sai nan da wata biyar." ya gyada kanshi, Allah kawo minshi lafiya."
tadan rankwafo kanshi tace, "Aliyu dan Allah zaka danyi min tausa?

Surayya
[1:23PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**12
ALIYU dan Allah zaka danyi min tausa?
Yace nikuma me zakiyi min? Tace
bakomai." yace to kyaleni bacci nake ji."
ta ture masa kansa akan kujera, tace to
dagani naje na kwanta." yau alhamis karfe biyu direba ya dauko zainab daga
makaranta, saboda yau basuda islamiya,
shiyasa basu kai shidda ba. Ta shigo
tana jan jakartata, ta zube a falo tace
"wash! Aunty sannu da gida, ya
bybynmu? Mansura tace gashi nan dai yana ta min
zillo.
Aunty ki bashi abinci yaci yunwa yake ji,
inya ci zai daina yi miki zillo." ai naci
abinci zeey, kin zata ni irinki ce sai anyi
min dura ina kuka? Zainab tayi saurin mikewa, bari na tashi kada ya shigo ya
ganni anan ya kuma sani cinye abincin
daya fi karfin cikina." tayi dakinta suna
dariya.
Da mangariba ni'ima tazo gidan, sukayi
tsalle suka rungume juna suna masu jin dadin ganin juna, kamar ba dazu suka
rabu a makaranta ba. Suka zauna a falo
suna dariya. Ni'ima tace auntyn mu ina
wuni, ya babyn namu?
Lafiyarsa kalau gashi nan yana jinki."
ni'ima tace zainab kinsan gobe ne fatin zara'u yusuf shidda na yamma, ya zamuyi
wajen tafiya, don yanda muke da zara'u
dole ne mu fasa fatin nan?
Zainab tace, wallah yaya ni'ima ina so in
rakaki, to amma ya zamuyi da yaya, dama
ya tafine da sauki, to shi sai ranar littinin da safe zaiyi sammakon tafiya kaduna
kan bakin aikinsa." ni'ima tace, "ai dolene
ma kije zainab, tare fa nayi mana ankon
fatin, har gwagwaron, har takalimin da
not din iri daya ne. Kuma yanda zara'u
take sonki, ke wallahi kin fiya tsoro, ba sai kice masa zaki zo gida ba sai muyi
tafiyar mu ta gida." mansura tace amma
ni'ima anyi saurin yiwa zara'u kawarki
aure da wuri, shekararki sha bakwai fa?
Koda yake daga ganini zara'un nan ta
girmeki, Allah ne dai ya hada kaunarku." ni'ima tace shekara biyu fa ta bani, yanzu
da ita fa zamuyi candy, wai mijin zai
barta ta karasa a gidansa."
to saurin na meye? Inji mansura, saura
wata shidda fa kuyi candyn, da ya kyaleta
ta karasa ba shikenan ba." ni'ima tayi dariya tace tsoro yake yi kada ayi masa
kwace, tafiya samari daya wa."
talatuwa ta shigo tana jera musu abinci,
ni'ima ta bude jalof din taliya ce da
farfesun kifi. Ni'ima tace zubamin jalof
din kadan da farfesun." talatuwa ta zuba mata.
Zainab kuwa farfesun kawai ta diba, ta
debo musu fantar gwangwani a firij.
Ni'ima tace, zainab wai ke wace iri ce?
Ban taba ganin makiyin abinci ba sama
dake, yanzu kuma inkinci wannan shikenan saida safe ko?
Tace "a haba yaya zai taho mana da
cake da icream. Ni'ima tayi tsaki tace,
shikenan abincin naki." tace don Allah
aunty ki rinka yi mata fada, shiyasa
kullum gata nan kamar a busheta ta fadi. Mansura tace ai tasan karonsu da
yayanku, saina shiga gaya masa
tukunna." talatuwa ta dawo da tangaram
a rufe, da gasasshiyar kaaza aciki da
mansura tasa agasa mata.
Ni'ima tace kai aunty ni aida nasan da wannan ai bazan ci farfesun ba, ba
ruwanki aunty, abinda kike so kici shi zaki
ci. Muma dai Allah ya aurar damu, ina
daga kwance aita yimin komai." mansura
tayi dariya tace, ke kuma abunda yake
baki sha'awa kenan. Suka fara cin kazar suna hirarsu, zainab ta fara cire
hannunta waita koshi, ni'ima da mansura
kuwa har kashi saida suka taune.
Ni'ima ta kwalawa talatuwa kira tazo,
"gani. Kije ki gayawa direban gidan nan
gani nan fitowa zai kaini gida." talatuwa ta fita da sauri. Ni'ima ta mike tana yafa
mayafinta da jaka, zainab ta rike
hannunta tace, "don Allah yaya ni'ima ki
bari sai anjima kya tafi kinji?
Tace a'a zainab gwanda na tafi, kinsan
yanzu yaya yana kan hanyar dawowa gida, kada ya gane ni nazo najaki ya
hanaki zuwa goben." tace to shikenan
saina zo goben. Ta rakata har mota ta
tafi. Sannan ta dawo ciki ta wuce dakinta,
alwala tayi ta tayar da sallar ishsha. Aliyu
ya shigo ya wuce dakinsa, sai da ya watsa ruwa ya dan shafa lotion a jikinsa,
yasa kananan kaya, ya fito falo yana
kallon tashar zee-aflam, suna wani
tsohon film mai kyau.
Mansura tana gefensa tana cin tufa,
zainab ta fito daga daki ta durkusa a gabans, tace, yaya sannu da zuwa." ya
amsa a hankali. Taci gaba da
tsugunnawa tana so ta tambayeshi zuwa
gida gobe ta rasa ta ina zata fara.
Ya kula da ita yasan akwai abunda take
so ta tambaye shi, don haka sai yaci gaba da kallonsa ya dauke kansa daga
bangaren tana zaune tana zaune tana
wasa da yatsun hannunta, tace "yaya.
Yace "uhm! Ba tare da ya kallo taba.
Saita yi shiru ta kasa cewa komai.
Shikuwa yana jingine da kujera ya lumshe ido yana kallo kamar ma baisan
da zamanta a wurin ba, ta sake cewa,
yaya don Allah gobe zanje gida. Yace me
ake yi a gidan? Tace bakomai. Yace to
bazaki jeba."
ta sunkuyar da kanta sai hawaye kawai itada bata da wahalar yin kuka. Mansura
tace don Allah ka kyaleta taje." yayi mata
shiru kamar baiji abinda tace ba.
Mansura tace, ni tsiyata dakai kenan, sai
ayi ta ma magana kayi shiru kana jin
mutane kamar wani kurma. Ko motsi bayyi ba balle yasan dashi take. Zainab
ta mike a hankali zata wuce daki, ya
kirata "zainab." ta juyo da sauri tare da
amsawa na'am yace "don nace bazaki
jeba shine kike kuka?
[1:23PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**13
TA juyo da sauri tare da amsawa na'am.
Yace "don nace ba zaki gidan ba kike
kuka?
Tayi saurin girgiza kai. Yace bakida baki?
Tace a'a ta koma ta durkusa a gabansa tace, "yaya dama bikin kawar yaya ni'ima
za'ayi, shine zan rakata."
yace "to me ya hanaki ki gaya min
gaskiya? Tace, "don Allah yaya kayi
hakuri ba zan sake ba." ya jinjina kai.
Tace yaya naje goben? Ya daga kai. Amma kada kiyi dare." tayi murmushi,
"yaya nagode, Allah ya saka da Alheri."
tamike ta shige dakinta tana murna. Da
safe a makaranta zainab take gaya wa
ni'ima yaya ya barta zata zo. Ni'ima tayi
murna, tace "to ki taho da wuri dai. Bayan sun tashi daga makaranta, karfe biyar na
yamma ni'ima ta bugo wayar mansura
tana neman zainab.
Zainab din tana karba ni'ima tace, "haba
zeey, ki sauri kizo man biyar fa tayi.
Zainab tace, "nayi wanka na gama kwalliya, yaya nake jira ya fita nasa
kayana na taho. Tace baya barki ba ki
fito ki taho kawai mu tafi.
Tace mata, cewa fa yayi kada na dade, to
kinga gwanda yasan ban taho da wuri ba.
Tace eh to gaskiya hakane. Yauwa kingan shi can ma ya fitarsa,
yanzu direba zai kawoni.
Wajen fatin ya hadu, ango da amarya
sunyi kyau kamar fure, sai walwali suke
suna sheki. Ni'ima sai kaiwa da komowa
take a matsayinta na babbar kawa, du inda tayi kuwa zaki ga idanuwan samari a
kanta, saboda ni'ima ta zama budurwa
kyanta ya kara fitowa, ga gwalli ga iyayi.
Su masu sabis da aka dauka sunata
kaiwa mutane abinci dasu swan, lemon
kwali dana gwangwani. Jama'a suna cin abinci Ali jita ya saki kida, tuni zakin
kidansa yasa jama'a suka fara kada kai.
Amarya da ango suka shiga filin rawa,
nan fa kawaye da abokan ango 'yan
uwan amarya da 'yan uwan ango, aka
shiga filin rawa aka rinka watsi da naira kamar ba a san zafin nema ba.
Hankalin zainab ya tashi ganin har
takwas na dare tayi, ta rinka damun
ni'ima ta taho su tafi gida. Ni'ima tayi
tsaki, waike meye hakane? Ki bari agama
basa mu tafi ba. Zainab tace um-um yaya ni'ima, kinsan
halin yaya, kizo mu tafi, ni'ima tace ke
wallahi kin fiya matsala, saika ce wata
matar aure, kita faman jin wannan
tsoron, bafa abunda zaiyi miki. Tace um-
um, nidai kizo mu tafi bana son bacin ran yaya, wallahi du saina ji na damu." dai-
dai lokacin da Ali jita ya saki cashiyar
karshe ni'ima ta riko hannun zainab suka
fice suka shiga motarsu, direba ya kawo
su gida. Saida aka sauke zainab sannan
ya wuce da ni'ima gida. Yana zaune a falo yayi zaman nasa na
kasaita kamar wani basarake, ya lumshe
ido daga gani tunani yake yi, mansura
tana kwance da littafi tana karatu, zainab
tayi sallama ta shigo, mansura ta amsa
sallamar tare da cewar "kun dawo? Tace mun dawo aunty." tace yaya sannu da
gida." ya bude ido daya yace sai yanzu
kuka ga damar dawowa? Bance ku dawo
da wuri ba? Ta marairaice, "don Allah
yaya kayi hakuri bazan sake ba." ya daga
kai "shikenan tashi kije. Ta mike tana hamdala a ranta da abin yazo da sauki.
Ranar littini da asuba Aliyu ya nufi
kaduna bakin aikinsa, sai kuma ranar
jumma'a da yamma zai dawo. Kwanci
tashi asarar mai rai, cikin mansura ya
shiga wata tara harda kwanaki, tana zama dakyar tashi da bisimillah.
Ranar jumma'a da mangariba Aliyu ya
iso, bai samu wata tarba ba, sai dai
mansura ta langwabe masa bata da
lafiya, sai kuka take yi masa. Shikoma du
ya wani rikice, don shi kukan yaro ma baya so bare na babba.
Ya kwasheta suka nufi asibiti, raki take yi
da ihu tana murkususu acikin motar.
Zainab kuwa sai hawaye take yi, tana
cewa aunty kidaina ihu salati zakiyi.
Tun a motar Aliyu yayi waya gidan su mansura da gidansu. Suna isa asibiti aka
shigar da mansura dakin haihuwa, Aliyu
yayi tagumi yana sauraron ikon Allah,
yayinda zainab ta dukufar da kanta acikin
gwiwarta tana kuka kasa-kasa. Tana
tuna lokacin da suka kawo mamanta acikin irin wannan halin, wanda
haihuwarce sanadiyar mutuwarta,
'yan gidan su mansura sun zo. Yart da
kishiyar babarta. Can saiga ummi tazo,
zainab ta tafi ta kankame ummi tana
kuka, ummi ta rinka shafa kanta tana rarrashinta. Wani ihu da suka ji mansura
tayi shine dai-dai da dan ya fado. Nurse
din ta garzayo da gudu tazo ta
kwantsama musu labarin haihuwa, tuni
kowa ya washe baki ya daga hannu sama
yana yiwa Allah godiya. Sun shiga dakin anata yiwa juna barka
da yaba kyan yaron. Aliyu ya rungumeshi
a jikinsa yana maiyi masa addu'a da
fatan Allah ya raya shi.
Washe gari da safe ka sallamesu
kasancewar mai jego kalau da ita da babyn. Gidan ya cika da 'yan barka 'yan
uwan Aliyu dana mansura.
[1:24PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**14
GIDAN ya cika da 'yan barka 'yan uwan
Aliyu da 'yan uwan mansura. Sadiya ta
taho tinkis-tinkis dana ta tsohon cikin,
ni'ima da zainab suka rungumota suna
murnar ganinta. Dakin mai jego sai kamshi yake. Kowa yazo barka zainab ce
zata karbeshi da farin cikinta, ta dakko
masa jaririn. Ko yaushe yaro yana
rungume ajikinta, kamar kada ta bawa
kowa." ranar kwana hudu aka kawo
kayan barka a katuwar akwati, kayan jariri ne tsala tsala masu kyau, da dan
jeans da shet na yara, takalma, safofi,
fidoji, saitin shawul da tawul, barguna
masu laushi.
Kaya ne masu kyau da tsari duk 'yan
waje. Sai karamin akwati kayan mai jego ne, turmin super holllan biyu, leshi biyu,
shadda galila mai tsadar guda daya,
kowanne da mayafinsa, sai takalma

3 / 18