Chapter 10 Reading Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc Arewa Novels

Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

Author :  Fertymerh Xarah Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   10 / 26

27K to 30K   out of 77.3K words

na jin ihun su tayo d'akin nasa da kyar ya bud'e mata.

Me suka yi kake dukan su haka kana da hankali kuwa, duk suka yi bayan rumaisa suka boye.

Nan ya gayamata abinda ya faru, tace duk baku kyauta ba, me qanqanuwar yarinya kamar hidaya tayi maku xaku mata dukan da xai sumar da ita?idan kuka kashe ta fa, baku da gaskiya kuma duk sai kunje kun bata haquri inba haka ba duk ku kwashi kayan ku, ku bar min gidana bana son xama da mutanen da basu da kirki.

*

Ko da suka xo gidan hidaya na wasa a tsakiyar falon ita da sultan yasmeen ta qarasa da gudu tana dariya, d'agowar da hidaya xatayi taci karo da salwa da amira sai banka mata harara suke, da gudu tayi inda Afiya ta buya tana fad'in Mami suna harara ta dukana xasuyi kice suyi haquri.

Salwa tayi sauri tace wlhy Mami haquri muka xo mu bata, mummy tace dole sai munxo.

Amira tace kiyi haquri hidaya.

Afiya ko kallo basu ishe ta ba, ta d'aure fuskarta, haka suka bar falon jiki a sanyaye da qudiri a xukatansu qila ma sai sun tarwatsa wannan glass d'in nata su ga yanda xata riqa gani.

Suna fita ta dawo falon ta cigaba da wasar ta tare da yasmeen.

Amma yarima kana ganin hidaya tana da budurci kuwa?

Meyasa kike wannan mgnr?ta yi shiru, yace ko kina tunanin sultan xai jewa yarinyar mutane.

Tace aa bana wannan tunanin, ina dai tausaya mata ne idan ta auri wani bayan raba auren ta da sultan.

Yace ko waye yayi mata fyade bai san kan abin ba, penetration d'in kad'an ne duk da haka ta rasa wannan budurcin, an shige ta da qarfi ne kuma ba dai dai ba wanda hakan ya janyo ta sami rauni sosai a wurin, nayi mata d'inki sosai kinga yanxu take tasowa the more tana girma the more tsokar wurin tana cikowa,

Amma yarima idan akwai sperm d'in a jikinta fa, kome ka bata ne?

Yace Misoprostol shine tablet dinda ake sha ko ayi inserting a vagina ko asaka akasan harshe shi yake flushing duk wani sperm dake jikinta, bayan ta farfad'o na bata tab d'in, and again kinsan misoprostol ba wai kawai fitar da sperm yake ba, Shine same maganin da ake amfani dashi wurin controlling bleeding ko tadda naquda, so ba wani matsala bane kingane.

Ta gyad'a kanta kafin tace yaushe ne auren?

Papa yace gobe idan Allah ya kaimu xaa d'aura anan masallacin gida.

*labarina na kud'i ne idan kana so ka siya*[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=???

20

Washe gari aka d'aura auren sultan da hidaya, Aliyu ya bada sadaki, merah ya karba a matsayin sa na mahaifi ya ajiye mata.

Hauka ce kawai fu'ad bai yi ba a ranar, bai san yaushe ya kamu da ciwon son hidaya ba sai ranar, bai san ya damu da ita hakan ba sai lokacin, ranar gabaki d'aya a d'aki ya yini ba inda yaje.

Wani sashe na xuciyarsa ke tuna masa ko waye sultan, yasan sultan baxai taba son ta ba, yasan sultan baxai taba amincewa da auren ba, aure yanxu baya cikin plan nasa, amma meyasa iyayen suka yanke hukuncin aura masa hidaya bayan ga salwa, koda yake su kad'ai suka san da wannan banda iyaye, koma menene yanxu lokaci ne daya kamata yayi kusanci da hidaya sosai yanda xata saba dashi, koda sultan xai sake ta yasan baxai sami matsalar auren ta ba.

Cikin yaran kuwa ba wanda yasan da maganar auren kowa sai harkokin gaban sa yake.

Afiya na xaune a study room salwa ta same ta.

Mami magana nake so muyi.
Magana yanxu, ta mecece.

Tayi shiru tana jin nauyinta kafin ta daure ta sunkuyar da kanta qasa tana fad'in ni ina son yaya sultan.

Kallon mamaki Afiya ke binta dashi kafin tace yaushe kika fara son sa kuma sultan d'in ya sani?

Mami an jima fa, na tura mashi text lokacin amma yayi ignoring kamar bai gani ba, shiyasa nake son ayi mana aure yanxu idan ya dawo hankalin sa baxai qi auren ba dole xai haqura amma wlhy Mami idan yana hayyacin sane baxai taba yarda ya aure ni ba.

Oh lallai salwa, at your age kinsan ki aikawa namiji kina sonsa, kinsan kixo ki roqa a aura maki namijin da baya son ki, me kika sani a auren tell me.

Tayi shiru, idanunta suka yi narai narai kamar xatayi kuka.

Sanda ina da shekarun ki, ni ban san wani abu soyayya ba balle nayi tunanin wani namiji, ashe namiji kika sa a ranki shiyasa sai cika kike, girman jikin ki yana so yafi qarfin shekarun ki, daga ke har amira kuwa, aikuwa xan gayawa daddy wannan xancen.

Dan Allah Mami kiyi haquri, ni babu kowane namiji a xuciyata, yaya sultan kawai nake so.

Haquri na me ai ke xaa baiwa haquri keda kika xubar da qimar ki da mutuncin ki wajen furtawa namiji Kalmar so, ince dai ko a school ba haka kike bin maxa kina cewa kina son su ba, dube ki me kika nema kika rasa tun daga kyawun fuskar ki har xuwa kyawun jikin ki da har xaki nemi so a gurin wani, ke kamar ba jinin sarauta ba kin xama classless kuma kin bani kunya, ki bari namiji ya ganki yace yana son ki kafin ke ki fara furta masa, maxa nawa ne a duniyar nan da suka fi sultan kyau da kud'i?

Sultan yayi qanqanta da aure yanxu at his age 20years, kema kinyi qanqanta da aure yanxu salwa, kije ki nemi ilimi shine jigon rayuwa yanxu, komai kyau ki da kasancewar ki yar mai kud'i idan baki da ilimi ke fanko ce, maxa suna son mata masu ilimi, ki xauna ki nutsu kima kanki fad'a idan kika bari wannan mgnr takai kunnen sarki xakiyi mamaki, bace min da gani.

Salwa ta fita uwa tasa ihu saboda baqin ciki, amira dake labe tana jinsu ta sauke numfashi a hankali cikin godewa Allah da salwa bata fad'i itama tana son yaya fu'ad ba da tasan dukan da Afiya xata mata ba qarami bane.

Kin gani sai dana maki magana nace kada kije, amma ba kyaji ai shikenan yanxu kin jawa kanki dan wlhy Mami sai ta gayawa daddy, amira ta fad'a tana kallon salwa dake share hawayen fuskarta.

Tace ni ba wannan ne damuwa ta ba, ina tsoron sanda yaya sultan xai so wata mace bayan ni, wlhy ina sonsa fiye da tunanin ki, yaya sultan yayi ta ko ina shi kad'ai ne xan aura friends d'in mu su yaba su san nayi dacen miji na kecewa sa'a amma meyasa Mami xata min haka?

Amira ta sauke numfashi tana fad'in ni ina son yaya fu'ad amma ba irin son da kike wa yaya sultan ba, kuma gwanda ma ni yaya fu'ad yana kulani shine ma ya fara nuna min feelings d'in sa akaina har naxo na fara son sa amma kin ga shima ai yaqi ya furta min Kalmar so har yanxu.

*

Wai kaji fa salwa taxo min da xancen tana son sultan a d'aura masu aure, can you imagine, yau yarinyar nan ta saka min shakku a xuciya sai tunanin ta nake.

Kai haba, ita salwa d'in?
Wlhy kuwa yarima da confidence d'in ta taxo, me salwa tasani acikin auren har take rawar jiki dashi haka musamman Ma akan auren sultan, yaron da tsab xai iya watsar da ita batare da ya duba dangantaka ta jini dake tsakanin su ba, ni tun da nake tare dashi na taba jin sultan yayi magana akan mace ko hirar mace ma idan ba fu'ad ba?

Aiman yayi murmushi yana fad'in jinin yarima ke yawo ajikinsa, ni banga abin damuwa anan dan salwa ta furta tana son sultan ba, matuqar yana son ta me xai hana ayi masu auren?

Aa ni baxan bashi auren salwa ba dan baxata ji dad'in xama da wannan miskilin yaron ba, baxai taba bata lokacin sa ba kasani, ina son tayi aure inda xata sami kwanciyar hankali fiye da xaman ta da sultan.

Yace hakane kuma, ko auren sa da hidaya na d'an wani lokaci ne ai in ba haka ba yaushe sultan ya isa aure.

Ni bana d'aukar wannan auren a matsayin aure, auren da babu biki ba komai, auren da babu wanda ya san dashi sai abokan arxiki da yan uwa, sannan auren da xai xama matacce na d'an wani lokaci.

Aiman yayi murmushi yana fad'in haka ne.

*

Mami wai hidaya baxata je skul ba yau?

Eh, ke kad'ai xaki je.

Meyasa Mami, nima baxan je ba.
A'a yasmeen, hidaya ba lafiya kinga ta tashi da xaxxabi yau, xuwa gobe idan ta sami lafiya xata je, idan kuma kika tsaya daddy xai maki allura ne idan xai yi mata.

Aa Mami xanje, ta juya tana kallon hidaya dake kwance a sofa cikin tausayi.

Sultan yaxo inda Afiya yana nuna mata hidaya da yatsa.

Mami.. hidaya... wasa

Tace yau babu wasa sultan, hidaya ba lafiya.

Yasmeen na gama breakfast ta d'auki food flask da jakarta ta fice da gudu.

Mami... hidaya... wasa

Ta riqo hannunsa ta kai a wuyanta ta langabe tana kallon sa cikin nuna masa ko xai fahimta, hidaya ciwo babu lafiya, yau babu wasa.

Yaje inda hidaya ya d'ora hannun sa a wuyanta xafi yaji rau ya juya yana kallon ta.

Mami.. hidaya.. Ciwo

Tace eh ciwo, ta had'o tea mai xafi ta qaraso falon ta miqawa hidaya, ta girgixa kanta ni baxan sha ba.

Kina son Golden morn, ta girgixa kanta tana hawaye, me kike so hidaya, Mami ni bana son komai idan nasha amai xai xo.

To ai baxaki xauna haka ba, tashi ki sha tea d'in sai kisha magani idan ba haka ba daddy allura xai maki daya tashi barci.

Hidaya ta tashi tana yarfe hannuwanta cikin kuka, Minkam miyida (ni bana so), sultan ya d'ago da sauri yana kallon ta, idanu ya tsura mata kamar mai son tuna wani abu.

Afiya ta subulce da dariya, tace yau kin tuna yaren naki kenan, to ni taya xan fahimce ki, kina so na baki da kaina.

Nan ma ta girgixa kanta, Afiya ta ajiye tea d'in tana fad'in bari na d'auko maganin tukunna ta juya ta fice.

Hidaya... Sha

Tace ni bana sha ka kyale ni, sai yasa qafa ya shure tea d'in ya xube a gurin dai dai lokacin Afiya ta dawo d'auke da kwalin hollandia a hannunta.

Tashi kisha wannan tunda bakya son tea d'in, taja ta tsaya turus, waye ya xubar da tea d'in kuma.

Hidaya dake kwance tace nima ban sani ba, ko baa fad'a ba tasan baxai wuce aikin sultan ba? tunda hidaya bata sha ya xubar, taja tsaki tana fad'in tashi kisha kafin na saba maki yanxu dan dukan ki xanyi.

Ba dan taso ba ta tashi ta sha sosai saboda sanyi sanyi da take dashi yasa taji dad'in sha, tana ajiye wa sultan ya d'auka shima ya sha, Afiya ta bata magani tasha shima ya miqa hannun sa a bashi maganin yasha.

Tace baxan baka magani kasha kana lfy ba, ya qara miqa mata hannu yana yatsina fuska, sanin halin sa, sai ta dubo vitamin c aciki ta bashi, ya karba ya tura baki tare da korawa da ruwa yana bata fuska kamar yanda yaga hidaya tayi.

Murmushi Afiya tayi ta shafi kansa had'e da sumbatar sa a goshi tana fad'in Allah ya baka lfy, sai ya nuna mata hidaya dake kwance itama ayi mata, tayi wa hidaya ita, sai yayi dariya shima ya sunkuya yana yiwa hidaya,

Mai aiki taxo ta gyara gurin, Afiya ta xaunar da hidaya sai ta jingina da sofar, sultan kuwa ya shige jikinta sosai kamar xata gudu ta barshi, binni binni yayi mata kiss a goshi shi a hakan ma gani yake duk cikin wasa ne.

Me ya hana hidaya xuwa makaranta yau, merah ya fad'a yana qarasowa cikin falon

Sultan na ganin sa ya tashi ya nufesa da sauri yana nuna masa ita.

Daddy... hidaya.... ciwo.

Afiya tace iyye yau kuma harda daddy ake kira.

Ciwon me ya same ta, mera ya sake tambaya batare daya bi takan xancen sultan ba.

Xaxxabi ne ke damun ta, tasha magani yanxu, xai yi magana sultan ya riqo hannunsa yana jansa xuwa inda hidaya.

Daddy... hidaya..... ciwo... zo
Ya kai hannun merah jikin hidaya, xafin ya ragu akan d'axu.

Xaxxabi xai sauka tunda tasha magani kice yau xaa sha fama da sultan

Tayi dariya tana fad'in tun d'axu nake fama ai, harda maganin dana bata ya kafe sai na bashi yasha, yanxu yasan banbancin Mami da daddy tunda yaji suna fad'a kenan.

Aiman yayi dariya kawai batare da yayi magana ba.

*littafina na kud'i ne idan kana so ka biya*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=???

21

Afiya d'auki hidaya ki shiga da ita d'akin su, baxata ji dad'in kwanciya anan ba.

Ta tashi ta d'auki hidaya, xumbur sultan ya miqe yana kallon ta kafin ya dubi mera yana fad'in.

Daddy... Mami.. Hidaya...

Yace ba inda xata je da ita d'aki xata kaita, xo xauna nan ya nuna masa kusa dashi.

Sultan yaqi xama, ya bi bayan Afiya, ta shimfidar da hidaya akan gado shima ya hau gadon ya kwanta.

Mami.. Hidaya..

Kai sauko, barci xatayi, ya xaka xo ka hau gadon yara ko kunya baka ji.

Aiman dake shigowa yace ki kyaleshi mana, banda abinki sultan yasan wata kunya ne, duk abinda xai yi a gidannan naki kallo kawai ki kyale shi, ya ja hannun ta suka fice.

Ya kwanta yana fuskantar ta, idanun ta a lumshe barci take amma sama sama kasancewar yanayin jikinta, ya kai yatsansa yana taba lashes d'in ta dake jiqe da hawaye, ya kira sunan ta, batare da ta amsa ba ta bud'e idanuwan a hankali tana kallon sa murmushi yayi mata, hidaya... wasa.

Batare da tayi magana ba ta maida idanunta ta lumshe, hidaya... wasa ya qara fad'a yana qoqarin bud'e mata idanu da yatsa, ta juyar da kanta can gefe d'aya tana fad'in baxan yi ba ka kyale ni.

Ya koma ta can bangaren da take fuskanta had'e da soma girgixa ta, sai ta fashe da kuka ta diro daga saman gadon ta fito, shima da sauri ya biyo ta.

Aiman dake breakfast ya juyo yana kallon ta, menene kuma.

Baxai barni nayi barci ba sai munje wasa, aiman ya taso ya riqa hannun ta, d'akin ya maidata, ta hau gadon ta kwanta sultan na qoqarin sake hawa ya riqe shi.

Sauko modibbo tunda baka ji, ka barta tayi barci mana, an gaya ma ana wasa idan babu lafiya, ya jasa suka fita ya rufe mata qofar.

Sultan yaja ya xauna bakin qofar d'akin, mera ya barshi ya koma dinning, Afiya na fitowa kallo d'aya tayi wa sultan sai da gabanta ya fad'i.

Yarima yaron nan kuka yake fa, kuka ya fad'a yana kallon sultan d'in, yana xaune a wurin sai hawaye yake.

Yace tunda ya fara ciwon nan bai taba kuka ba sai yau, just leave him he may regain something, kyale shi kawai yayi.

Ta juya ta bar falon, yana cin abincin nasa yana kallon sa, yana ganin yanda yake juya kan nasa yana dafewa, ya janyo wayarsa, dialing number Dr Patrick yayi wanda shine yayi wa sultan aikin kan a Riyadh.

Sun jima sosai akan waya suna magana kafin ya tsinke, tashi yayi ya nufi sultan d'in ya tsugunna gabansa tare da dafa sa.

Sultan, ya kira sunan sa.
Ya d'ago yana kallon sa,
Yace kukan me kake yi.
Yace hidaya,
Yace kana so na kai ka gun hidaya, ya gyad'a kansa yana kallon sa,
Yace xaka barta tayi barci baxaka dame ta ba?nan ma ya gyad'a kansa, aiman baya mamaki da sultan d'in na amsa masa likitansa ya tabbatar masa a yanxu kowane lokaci sultan d'in xai iya dawowa hayyacin sa.

Ya riqa hannun sa suka nufi d'akin, tuni tayi barci sultan ya nufe ta da sauri ya rungumeta tsam a jikinsa bayan ya hau gadon kamar xaa kwace masa ita, ya kalli mera sai dariya yake.

Daddy hidaya tana barci, kyam aiman yayi masa da idanu, me yaji sultan d'in na fad'a, kafin yayi wani yunquri sai ganin yayi ya kwanta tare da ita a jikinsa yana lumshe idanun sa.

Ikon Allah ya fad'a yana kallon su.

*

Yaya fu'ad d'axu driver ya d'auko mu skul muna hanyar dawowa na ganka ka wuce da wata a gaban motarka wacece ita?

Kallon ta yayi ta kafe shi da idanun ta kamar xata cinyeshi da kyar yace course mate ce.

Tace I see course mate, ta juya xata fice ya riqo hannunta da sauri.

Believe me Amira just course mate bayan wannan ba komai tsakanina da ita, lift ne kawai nayi mata.

Tace shikenan amma jiya da kaxo baka neme ni ba, na ganka da hidaya meyasa kake son xama da ita.

Yace hidaya itama qanwatace ai, me kike tunani?

Ta tabe bakinta kawai, yace meyasa keda salwa kuka tsangwami yarinyar nan me tayi maku.

Yaya mu fa ba abinda muke mata idan ta tsoka ne mune dai, amma tun daga ranar ai bamu sake mata komai ba.

Yace to shikenan amma ku daina mata abinda kuke mata itama qanwar kuce kamar yasmeen babu banbanci.

Amira ta tabe baki kawai batare da tayi magana ba.

*

Yau kam jikin hidaya da sauqi, ta murmure sai wasar ta take yi tare da jelar ta=??.

A tsakiyar falo suka jera Teddy's d'in su, yasmeen ta soma rabawa, tace ga nawa ga naki ko.

Tace to ina na yaya sultan shima a raba dashi.

Aa baxaa raba dashi ba, ai shi namiji ne kuma yayi girma da wasar baby, ai shi xai riqa yo mana cefane kuma yana kai ya'yan mu School ko.

Hidaya tace eh fa kuma shi xai riqa mana girki tun da ai mu bamu iya ba.

Nan suka soma had'a kayan wasar suka raba ba dashi ba, sai ya tashi shima ya iya kai qara kamar yanda yaga suna yi, ya nufi Afiya.

Mami yasmeen babu wasa, Afiya ta juya tana kallon sa kafin ta dube su.

Tace baxakuyi wasar dashi bane yau.

Hidaya tace ai Mami shi xai riqa mana cefane mun gayamishi.

10 / 26