Chapter 16 Reading Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc Arewa Novels

Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

Author :  Fertymerh Xarah Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   16 / 26

45K to 48K   out of 77.3K words

kanta da qaramin towel, ta cikin mirror d'in ta tsurawa yasmeen ido dake kwance akan gado tana chatting kamar ba fita xasu yi ba, ta girgixa kanta tana jan qaramin tsaki.

Yasmeen ta d'an dube ta tana fad'in, ke kuma wannan tsakin haka ke da wa?

Hidaya bata kula ta ba, ta cigaba da shirin da take yi, yasmeen kuwa gyara kwanciyar ta tayi batare da ta damu da xasu fita ba.

Cikin qanqanin lokaci ta shirya cikin Riga da skirt na lace marar nauyi bata bi ta kan yasmeen ba ta d'auki qaramar jakarta ta rataya tare da d'aukar key na mota ta juya xata fice.

Wai har kin shirya ne, shine baxaki jirani ba yasmeen ta fad'a tana qoqarin saukowa daga kan bed d'in bayan ta jefar da iPhone dake hannun ta.

Kinsan haifa ta kika yi dole na jira ki har ki gama abinda kike, mtsew ta sa kai ta fice, yasmeen ta biyo bayan ta da sauri, a falo suka ci karo da Afiya da fu'ad xaune.

Mami kiyiwa hidaya magana ta jirani dan Allah, yanxu xan shirya fa.

Afiya ta dube ta tana fad'in meyasa xakuyi tafiyar daban daban ne, ki jira ta batare kuka saba fita ba.

Baxan jira ta ba mami, tun d'axu nake mata magana tayi wanka ta shirya kafin nagama gyara d'akin daddy amma sai tayi kwanciyar ta tana chatting, har na gama naje nayi wanka tana nan a kwance, ni baxan jira ta ba.

Afiya ta dubi yasmeen tana fad'in dama nasan ayi haka game dake da wannan wayar, xan saka daddy ya karbe ta a huta.

Yasmeen ta shagwabe fuska tana kallon ta sorry mamee daga yau na daina, kice hidaya ta jirani.

Hidaya ta nufi hanyar fita falon tana fad'in idan na jiraki na xama shashasha kamar ke kenan marar aikin yi, kije kiyi ta kwanciya akan gadon mana.

Wait ma idan kinje ni dame kike son na tafi inaji mota d'aya muke amfani ni da ke dan haka ki jirani yanxu xan shirya I promise.

Hidaya ta jefa mata key d'in motar tana fad'in na riga na fad'a baxan jira ki ba, ta dubi fu'ad da tun da suke rigimar bai tanka ba tace yaya fu'ad dan Allah xo ka sauke ni gidan su Aneesa yau ake bikin ta, ina ta so ma na gayama, ta fad'a da qaramin murmushi akan fuskarta.

Yace ki jirani a mota ina xuwa, ta gyad'a kai kafin ta dubi Afiya tana fad'in Mamee na tafi sai na dawo.

Tace a dawo lafiya, ko kallon inda yasmeen take batayi ba ta fice, yasmeen ta tunxuro baki tana kallon Afiya.

Amma mami sai kace ke baki isa ki hanata taji ba, shikenan ita idan ta kafe akan abu sai a bar ta.

Afiya ta tashi tana fad'in ke kuma da kika kafe akan waya akwai wanda ya hana ki ne, ai hidaya ce maganin ki gidannan kuma game da wannan wayar sai mun sami matsala dake, har raba maku aiki nayi saboda ba abinda kuke yi a gidannan nace idan wannan ya gyara d'akin daddy yau wannan ya gyara gobe, nan kika dawo falo kika kira sultan kina qorafi mami ta saka ki aiki bayan ga bayi a gida, ke baki iya komai ba, ina ji sultan d'in na fad'in menene a gyaran d'akin da har sai an saka ki duk masu aikin dake gidan, kullum hidaya ce take gyarawa ko sau d'aya bata taba qorafin bakiyi ba,? ko uban wa xai je yayi maki gyaran d'akin mijin ki, girki ma baki iya komai ba kina ganin ko yaushe idan ina kitchen hidaya na shiga ta tayani, ke kuma jikar sarki kina kwance kina chatting, xaki gane kuskuren kine akwai lokacin da kud'in uban ki ko sarautar gidan ku baxasu hana namiji wulaqantaki ba idan kika kasance ballagaxa marar moruwa a gidan ki auren ki, Afiya ta sa kai ta fice tana jan qaramin tsaki.

Yasmeen ranta ya baci sosai, mamee ta disgata gaban wanda take so, ta xubar mata qima a gurin sa ko ya yake kallon ta a yanxu, ta soma bubbuga qafafuwan ta cikin shagwaba kamar xatayi kuka.

Fu'ad ya d'ago yana kallon ta, wata qaramar riga ce a jikinta iya gwiwa, ba qaramin fito da shape d'in ta rigar tayi ba, suna had'a ido gaban su ya fad'i lokaci d'aya take nutsuwa taxo mata lokaci d'aya da kyar ta wayance tana fad'in,

Please yaya fu'ad ka hana hidaya tafiya ta jirani yanxu xan shirya, wallahi bana jin dad'in tafiya ni kad'ai bada ita ba.

Tun da ta soma magana yake kallon siraran labbanta dake motsi a hankali kamar basu ke furta maganar ba, tare da sauraren muryarta dake fita cikin nutsuwa da taushin kalami, akwai wani abu a tare da ita wanda babu a gurin amira, yau ne ya fara tsayuwa ya qare mata kallo sosai, ya tashi batare da yayi magana ba yasa kai ya fice saboda wata kasala da ta saukar masa lokaci d'aya, tabi bayan shi da kallo kafin ta tabe baki tasa kai ta fice.?

*

Hhhhhhh da gaske yaya sultan, amma shine sai yanxu kake gayamin.... Yasmeen dake shigowa falon Umma (maman aiman) ta fad'a idanun ta akan waya da alama video call ne take yi.

Hidaya dake xaune a qasan traditional carpet na sarauta? ta tabe bakin ta tana cigaba da sakawa d'inkin da ta karbo wasu irin beats masu kyau,

Umma tace hidaya yaushe kika gama saka wad'annan duwatsu haka naga abin da yawa.

Yanxu xan gama, telan ya nuna min iya inda xan saka ai,? kuma fa umma ya raina ni dana bashi kud'in d'inki har dana saka beat amma dana je karba wai bai sami lokacin sakawa bane nayi haquri.

Masu d'inkin nan haka suke hidaya bama kamar Mohd naga haka yake wa su amira dan yaga suna son d'inkin sa kuma da yake su fitinannu ne ba kamar ke ba sai suke yin dai dai da shi.

Hidaya tayi murmushi batare da tayi magana ba dai dai lokacin yasmeen ta gama wayar da take ta dubi hidaya tana fad'in wannan qaseemu friend d'in yaya sultan yana waje yana jiran ki, tun ranar dana saka pic namu a status ya takura min, kije ki same shi yana jiran ki.

Hidaya ta tunxuro baki tana fad'in ba inda xanje, kice bana nan baki ganni ba.

Umma kuwa kallon su take sanin abinda ke kan hidaya wanda su basu sani ba ya saka ta fad'in, shi kuma qaseemu yaushe ya fara xuwa gidan batare da yaxo mun gaisa ba, ke yasmeen hidaya aiki take yanxu kuma kin gani jeki fad'a masa ni na saka ta aiki.

Yasmeen ta juya tana fad'in an gama ranki shi dad'e, our latest granny mai ran qarfe ke da wancan mijin naki, hidaya tayi dariya tana kallon umma,

Gaskiya umma yasmeen ta gama raina ki, ya kamata kiyi maganin ta.

Yasmeen ta fice tana dariya, bata jima ba sai gata ta dawo ta xauna? tana fad'in umma yau fa d'an bisa ranki yaya sultan xaa bashi Award nasa na ball da suka buga, nasan yau a gindin TV xaki tare.

Hidaya ta kaimata duka cikin wasa tana fad'in wannan bakin naki baxai fad'i kalma mai dad'in sauraro ba, idan yaya sultan d'an bisa ranta ne to waye acikin ran?

Sarki mana, yasmeen ta fad'a tana ware idanun ta, umma ta soma dariya.

Tun da ta koma sashen su, lokacin kallon yayi ta soma tunani tana son ganin wanne irin ci gaba ya samu a shekarun da tayi bata ganshi ba? ta tuna sura da kyau irin nasa, yana da wasu ilhamomi da bata taba ganin kowa da irin su ba wanda take addu'ar mijinta ya kasance dasu amma na gari kuma ba mai kyamatar mutane da wulaqanci ba.

Ta tashi ta fita daga d'akin ta nufi falo, su uku ne xaune a falon sun tsurawa TV idanu, daddy, mamee da yasmeen.

Wannan ne Karo na farko da ta soma fitowa ayi kallon da ita, duk sun yi mamakin haka, yasmeen xata yi magana Aiman yayi mata alama da hannu akan tayi shiru, hidaya ta nemi d'aya daga cikin sofa ta xauna idanun ta akan TV dai dai lokacin kuwa aka hasko sa da qaton cup na silver a hannun sa, mai matuqar kyau da tsada, tayi turus ganin kyakkyawar xuciyar sultan ma'abociyar kwarjini ta CIA fuskar d'irkekiyar akwatin TV d'in jikin bango plasma dake falon,

Cikakken matashi d'an shekara ashirin da biyar, ya xama qaton gaske? kamar mai shekara talatin, yana da wata irin halitta da kalar fata mai d'aukar hankali da fizgo xuciya xuwa gare sa.

Girman da ya qara ya bata mamaki matuqa, dogo sosai mai ginannen jikin da babu qiba babu rama a jikinsa, ba kamar yanda yake a da ba, ko dan ta jima bata ganshi ba, taga kamar dukkansu babu mai mamakin sauyawar shi.

A yanxu idan ka kalle shi mayuwaci ne ka banbance nationality d'insa ya xama kamar wani d'an qasar Egyptian.

Ita kanta da ta kalle shi taji yayi mata kwarjini ainun ya kuma burge ta, burgewa ba kad'an ba, tace a ranta irin wad'annan maxan tsiraru ne a cikin al'umma, ashe haka yaya sultan ya ke da kyau?

Sai dai haka bai sa taji soyayyar shi ko wani abu makamancin haka a xuciyar ta ba bayan burgewa irin ta d'an uwa,

Gobe yaya sultan xai dawo...... taji muryar yasmeen kamar daga sama, ta d'auke idanunta kan TV tana kallon yasmeen d'in cikin tsananin mamaki da fad'uwar gaba, gobe xai dawo da gaske kike ta tambaya idanunta akan ta.

Yes, yaya sultan is coming back tomorrow, we have to make something special for him, so that idan ya gani he will be happy with us a matsayin mu na sisters d'in shi ko hidaya?

Hidaya ta saci kallon su Afiya hankalin su baya gare su, tayi murmushin yaqe tana gyad'awa yasmeen kanta wanda tabbas bai kai har xucci ba.

Thumb yasmeen tayi mata da hannunta kafin ta juya tana murmushi.

Something special ta qara nanatawa a xuciyar ta, kamar me fa, me take nufi ne,? nooo ta tashi sum sum ta bar falon batare da ta bari an qarasa kallon da ita ba.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama:

32

Tashin ta da fitar ta falon fuska a d'aure duk akan idon yasmeen, me hidaya ke nufi bata son yaya sultan haka har abin farin ciki xai same shi amma ta kasa nuna farin cikin ta, sai ta tashi tabi bayanta.

Tana kwance da littafi a hannunta yasmeen ta shigo, hidaya ta kira sunan ta ranta a bace.

Menene kuma?hidaya ta tambaya tana kallon yanda ta bata ranta.

Tace akan maganar wanda bakya so ne yaya sultan, wannan wane irin abu ne mutum ya sami abin farin ciki amma ki kasa taya sa murna.

Hidaya ta jefar da littafin hannun ta tana kallon ta, tace rawa xanyi a tsakiyar falon ko kuma xama xanyi nayi ta dariya, look yasmeen ke kike qoqarin cusa ni a gurin sa wanda sam ba haka bane a gurin sa dalilin haka kike tunanin ina nuna masa qiyayya, ba haka bane me yaya sultan yayi min a rayuwa da xan tsane sa, dan ya dake ni ko dan ya ture ni wannan ba dalili bane, ki daina wannan tunanin nafi shaquwa da yaya fu'ad sosai fiye dashi kuma nafi so na kasance dashi.

Yasmeen ta tsura mata idanu cikin mamaki amma ta kasa furta kalma ko d'aya saboda wani abu da ya taso ya tokare qirjinta, ta juya ta fice da sauri ta bar d'akin.

Hidaya ta yatsina fuskarta kafin ta xauna tana fad'in saboda me xan damu dashi mtsew.

*

Washe garin ranar gidan aka tashi da shirye shiryen tarbon sultan, sai faman girke girke ake tayi Kala Kala kamar xai iya cinye duka abincin da ake qoqarin had'awa.

Hidaya ranar tana kwance a d'aki ko falo bata taka ba balle tayi tunanin shiga kitchen taya Afiya girki kamar ko yaushe.

Afiya ta dubi yasmeen d'in tana fad'in ina hidaya ne ko bata tashi bane.

Yasmeen ta tabe baki tana yatsina fuska nima ban sani ba mami.

Je ki duba ta ko lafiya, yau ban gan ta a kitchen BA, yasmeen ta fice tana turo baki bata jima ba sai gata ta dawo tana fad'in tana xuwa.

Tace yasmeen please ki bar naman haka wanda bai iya girki ba taya xai iya gyara nama tun d'axu sai wanke wa kike, haka aka gaya miki ana yi ne.

To mami ya xanyi, ina so nayi wa yaya sultan girki.

Mtsew... ta wanke hannun ta a sink kafin ta fito daga kitchen d'in dai dai lokacin hidaya ta fito kallon ta tayi tana fad'in,

Good morning mamee,
Afiya tace yanxu kika tashi kenan? Hidaya ta girgixa kanta tana yatsina fuska tace tun asuba dana tashi sallah kaina yake ciwo and again jikina is so weak mami I can't help today, magana take yi kamar xatayi kuka.

Sai Afiya taji tausayin ta sanin ma kaf gidan hidaya tafi kowa rakin ciwo bata da juriya ta wannan fannin,

Tace shikenan ki sha magani ki kwanta xuwa anjima xai sauka.

Mamee pls ki barni naje gidan mommy anjima kad'an yaya fu'ad xai dawo dani dan Allah.

Afiya tace anjima da yaushe, ba yayan ku ke dawo wa yau ba, ko baxa kije tarbon sa ba.

Xanje mamee but atleast kafin lokacin dan Allah mamee kinji.

Afiya ta juya tana fad'in shikenan amma kada ki dad'e sosai hidaya taji dad'i, ko wanka batayi ba ta xura doguwar riga ta d'auki key ta fice da sauri, taya ma suke tunanin xata je tarbar sa, meyasa suke son ta cusa kanta a gurin sa bayan shi tuni ya nuna mata baya buqatar hakan?

Ko da Afiya ta gayawa yasmeen yanda suka yi da hidaya jinjina kanta kawai tayi tana qara gasgasta irin qiyayyar da hidaya take wa dan uwan ta haka.

Tana shiga gidan ta sami rumaisah na breakfast tare da fu'ad tuni aliyu ya dad'e da fita aiki.

Gaida su tayi kafin ta jefar da d'an mayafin dake kanta ta nufi dinning tana fad'in dama da yunwa na xo.

Rumaisa tace me ya hana kici abinci.

Ba komai ta fad'a kafin ta xauna kusa da fu'ad, hannu ta kai plate d'in fu'ad ta soma cin plantain tana kallon sa, shima kallon ta yayi kafin ya d'auke idanun sa da sauri saboda rumaisah dake gurin.

Shiru wurin yayi na d'an wani lokaci kafin rumaisa ta tashi tana fad'in xanje d'aki na kwanta kafin xuwan sultan.

Fu'ad ya gyad'a kai yana kallon ta, ta juya ta fice tana shigewa sashen ta ya juyo da sauri yana kallon hidaya tare da kai hannun sa akan nata ya riqe yana fad'in,

Sai ki rasa inda xaki saka hannu kici abinci sai a nawa plate, baxaki xuba naki ba saboda kin raina ni ko?

Ta shagwabe fuska, sorry yaya ta janye hannun ta, ta soma qoqarin had'a tea tana fad'in ni bana son komawa gida yanxu.

Meyasa ya tambaye ta yana kallon ta, ta yatsina fuska kafin tace saboda the monster is coming back today.

Duk da yaso yayi dariya amma sai ya d'aure fuska yana kallon ta kafin yace who are you calling monster?

Yaya sultan mana ta bashi amsa tana kurba ruwan tea.

Yace bana son qara ji, yayan ki ne idan xaki kira sa haka nima kenan xaki iya kirana da wannan sunan.

Ta d'ago manyan idanuwanta ta xuba akan kyakkyawar fuskar sa, shima xuba mata idanuwa yayi yana kallon ta cikin wani yanayi.

Allah yaya fu'ad kafi shi kirki, halin ku ba d'aya ba kaima kasani ka daina had'a kanka dashi, ni fa tsoron sa nake wlhy amma ita waccan yar rainin wayon tana tunanin kamar na tsane shi ne dan Allah yaya fu'ad me yayi min haka da xafi da xan tsane shi, dama yayi min wani abu ne xan yi masa mai dalili.

Sultan ya canxa daga yanda kika san shi hidaya, kin san me yanxu sultan yana son xama da hidaya ko dama can abinda ya faru a baya rashin sani ne, ki manta da komai ki Saki jikin ki dashi kamar before, kika sani Ma ko wannan dawowar a maimaita irin wasar baya.

Tayi dariya tana girgixa kanta batare da tace komai ba amma ba ta tunanin sultan xai canxa saboda duk abinda yake a jinin sa yake.

Yace kika sani ma ko ayi yar gida, kamar gobe ne sai mu gan ku kun xama best friends in the house, sai soyayya kafin mgnr aure ta shigo ya fad'a yana kafe ta da idanun son jin me xata ce.

Kallon sa tayi cikin tsananin fad'uwar gaba ta ture Cup d'in dake gabanta tana kallon sa da mamaki.

Ni xanyi soyayya da yaya sultan har na aure sa, meyasa kuke wannan tunanin kai da yasmeen, wait ma yaya bakace kana sona ba ko ka daina yanxu, sai ta shagwabe fuska kamar xatayi kuka ni kai xan aura bana son shi.

Ina son ki hidaya amma ba yanda na iya dole na haqura da ke..... Meyasa ta tambaye sa, bamu dace da juna bane ko kuma baxaka aure ni saboda ni ba jinin sarauta bace, ni bani da asali kamar yanda su salwa suke fad'a min, sai ta soma hawaye.

Waya gayamiki baki da asali, kar na qara jin kin fad'i haka, kinsan meyasa nace ba xan aure ki ba?

Ta girgixa kanta tana share hawayen da suka xubo mata,

Sai kin daina kukan, wai ina ma kika bar yasmeen ne kika xo ke kad'ai?

Tana gida, yaya bari nayi wanka sai naxo mu fita ina so naga gari yau.

Yace shiyasa nake ta jin tsamin daud'a ashe kece bakiyi wanka ba.

Ta sinsina jikinta tana fad'in wallahi yaya qamshi nake, ni bana son sharri, ya soma dariya.

*

Sun shirya tsaf xasu je airport tarbon sultan amma babu hidaya.

Ina hidaya ta shiga, Aiman ya tambaya yana kallon yasmeen.

Daddy tun da safe ta fice wai tana inda mommy.

What, da ixinin wa?
Tace mamee ce ta barta,

But why?ya tambaya yana kallon ta,

Afiya tace mun yi da ita xata dawo da wuri

16 / 26