Chapter 2 Reading Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc Arewa Novels

Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

Author :  Fertymerh Xarah Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   2 / 26

3K to 6K   out of 77.3K words

barmu ki tausaya mana muna tsananin buqatar ki a tare damu.

A hankali bakinta ke motsi baya jin kome take fadi, ya kai kunnensa dai dai bakinta dai dai lokacin numfashin ta na tsaya cak.

Wata qara da jaririyar ta callara ya dawo dashi daga suman xaunen da yayi dai dai lokacin wata irin fad'uwar gaba ta riski sultan da nayi matuqar firgitashi wanda sai da hankalin iyayen nasa ya koma kansa.?
[11/20, 10:25 AM]Ummi Tandama:
*SULTAN MERA*
Haske writers Association
?Fertymerh Xarah=???
*is not free pls, idan baka biya ba dan Allah kada ka karanta*
A hankali yake tafiya yana danna wayar sa tamkar wanda baya son taka qasa, duk bayi da masu aikin gidan dake gaidasa ba wanda ya d'ago ya kalla illah hannu kawai da yake d'aga masu alamar yaji.

Falon kakansa ya nufa wato sarki, kai tsaye ya nemi iso aka masa, ya shiga fuskar nan tasa ba walwala.

Ya sami guri ya xauna had'e da tankwashe qafafuwan sa yana kallon sarki.

Mami tace kana nemana, me kuma akace nayi.

Modibbo iyayen naka basu koyama gaisuwa bane, sarki ya fad'a batare da ya kalle sa ba.

Sultan ya tunxuro baki, kamar baxai yi magana ba sai kuma yace na same ka lafiya.

Wanna ce gaisuwa? Ya qara tsuke fuska cikin bacin rai da d'aga murya yace good afternoon, sai a sannan sarki ya kallesa yaga sai wani cika yake yana batsewa yayi murmushin sa mai qayatarwa yana fad'in,

Wai ni na damu dana ga sultan ne shiyasa na tura neman sa, tun da suka xo bai xo na ganshi ba ashe nayi laifi ne.

Sultan ya dube sa yana fad'in dan Allah granny meyasa xaka tilastawa daddy sai mun dawo Nigeria, banda xafi da talauci menene acikin qasar taku.

Kaji ja'irin yaro, ni kake gayawa haka, waye bai San asalin buzu ba, inace anan qasar aka haife ka.... Yayi saurin katse sa tare da fad'in,

Amma baa cikin ta na tashi nayi rayuwa ba, ni bana son wannan qasar dan Allah ka barni na koma.

Idan raina ya baci da kai game da qasar nan wallahi baxaka koma ba, xaka xauna nan tare da yar uwar ka Ameera, ka kiyayeni.

Sultan yayi shiru bai qara magana ba sanin halin kakan nasa, magana d'aya ya xartar da hukunci kuma dole abi, illah xuciyar sa dake quna.

Sarki ya jawo kayan abincin dake gabansa yana fad'in, kacokan na saka aka ma abinci daban dana su yarima, saboda kai na daban ne a gurina, kasani kaf cikin jikokina nafi son ka akan kowa amma duk acikin su ba wanda baya jin magana ta kamar kai.

Matso kaci abinci, xamuyi hira idan ka gama ina so na baka wani labari game da rayuwa da yanda ka dauki kanka, Sam mahaifinka ba haka yake ba, ko sanda yayi quruciya bai kyamaci talakawa ba ballantana qasar sa ta gado.

Sultan ya dauke kansa gefe, yana jin sanda sarki ya soma bud'e dishes din, qamshin abinci ya daki hancin sa, sai a lokacin ya tuna tun da suka sauka qasar bai ci komai ba saboda fushin da yake da kowa, ya saci kallon abincin, Sinasir ne da miyar ganye, beef sausage, da stuffed atomy, nan da nan cikin sa ya dauki wani kuka, ba dan ya so ba ya matsa ahankali kusa da sarki inda shi da kansa ya soma bashi da hannunsa cikin kulawa irin ta jika da kaka.

Bai dauki dogon lokaci tare da sarki ba ya fito dauke da makullin motar sa, duk gidan shi kad'ai ke hawan motar sarki ba wanda yake baiwa makulli idan ba sultan ba.

Kai tsaye ya nufi motar Qirar Opel Astra baqa wuluk sai sheqi take, gidan Ammi ya nufa (mahaifiyar Afiya) ya jima sosai a gidan kafin ya nufi gidan Aliyu, ko da yaje fu'ad baya gidan sai ya xauna tare da rumaisa yana bata labarin Phoenix ba kamar Nigeria ba.

Hidaya..... Ina kika shiga hakane,

Baffa gani xuwa ina neman xani na ne ban gani ba.

Ya qarasa shiga cikin d'akin yana kallon yanda take lalaben inda xata ga xanin nata, yace yaushe kuma kika cire kayan?

Wanka nayi baffa, naji xafi yayi yawa baxan iya jira har ka dawo ba.

Ya qarasa kusa da ita had'e da riqo hannunta yana murxawa a hankali sai ga datti kamar wacce ta shekara batayi wanka ba, a hakan take cewa wai wanka tayi,

Yace dame kika yi wanka?
Baffa bansan inda xan ga sabulu ba sai nayi da ruwa kawai.

Yace to ki cire rigar kixo na miki wanka akwai datti a jikin ki bari na had'a ruwan wankan, ya fita.

Yana cikin had'a ruwan sai gata ta fito tana tafiya a hankali, ba komai jikin ta sai pant, ya riqo hannunta suka nufi toilet.

Basu jima ba ya fito dauke da ita sai dariya take da yanayin yanda ya dauko ta, bayan ya gama shiryata ya dube ta yana fad'in,

Hidaya mai kyau ce ko ba kwalliya, kin ganki kuwa,

Ta tunxure baki tana fad'in baffa yaushe xaka je birni ka siyo min kayan kwalliya da kamin alqawari.

Yau xan cika wannan alqawarin hidaya bari na shiga kasuwa naje na siyo maki, kada kije ko ina xan turo maki su Asiya su tayaki xama.

Ta soma tsalle cike da farin ciki, baffa ka siyomin harda sabbin slippers kaga wannan nawa ya tsufa ba dad'in tafiya.

Sai me kuma kike buqata,
Ka siyo min kuma kayan birni masu dad'i tare da irin wannan alawar da ka taba kawo min.

Ya tashi ya dauki kud'in sa ya saka cikin hular kayan sa ta fulani kafin ya maida hular akai ya saka, ya d'auki sandar sa ya fice.

Fu'ad shiru yayi yana kallon sultan tun dax'u da yaxo yake mitar wannan qasar tasu abin har ya soma bashi haushi.

Man tashi muje ka rakani xan karbo saqo kasuwa.

Wace kasuwa xan raka ka, da sauka ta yau a gari sai kuma naje wata uwa kasuwa sai kace gurin kirki.

Ba cikin kasuwa bane, ni me xanje yi cikin kasuwa, kasan saqon me xan karbo?

Sultan ya girgixa kansa batare da yayi magana ba.

Yasmeen ta aike ni fa kuma dole sai mun je tare da kai.

Mtsew sultan yaja dogon tsaki, shiyasa ta raina ka, taya yarinya yar shekara goma xata aike ka kaje har kake rawar jiki haka.

Qanwatace idan ta nemi abu nayi mata dole ne, rayuwar ka daban tawa daban, yanxu dai roqon ka nake ba dan yasmeen ba, kuma ba dan na isa ba, ka taimaka ka raka ni.

Baffa ya gama siyayyarsa duk abinda ya gani na wasa ko naci wanda ya birgesa ya siyawa hidayarsa, a gaggauce ya fito kasuwar yana neman abokin tafiyar sa da suka xo tare Buba,

Ko ina Buba ya shiga haka shi da ba gari ya sani sosai ba, ya soma waige waige bai gansa ba, ya d'auki kayan sa had'e da sandar sa ya qara gaba.

Dai dai gurin wata baqar mota ya tsaya, ya d'ora kayan sa akai, sai ga mai kankana yaxo wuce wa, ya tuna yanda hidaya ke mutuwar son ta, ya siya mata ya siyawa kansa yana sha, yayin da ruwan kankanar ke xuba a motar.

Duk abin nan da baffa keyi sultan na xaune cikin mota yana kallonsa cike da bacin rai musamman yanda yaga ruwan kankanar ke bata masa mota, har tsigar jikin sa ke tashi saboda kyankyami, wannan bafillatan ya raina masa wayo.

A fusacce ya fito cikin motar batare da tunanin komai ba ya d'auki kayan baffa ya soma wurgi da su, baffa ya juyo cikin xafin nama ganin waye mai wannan aikin na wulaqanta masa kayan hidaya, yayi qoqarin riqo sultan.

Da sauri sultan ya matsa tare da nuna sa da yatsansa cikin bacin rai,

Kul, kar ka soma tabani da wannan qaxamin hannun naka, kai wane irin daqiqin bafillatani ne, dubi yanda ka bata min mota.

Koda baffa baxai iya maida masa da hausa ba tabbas yaji abinda sultan din ya fad'a, dalilin haka baffa ya cakumo sultan din cikin xafin nama, tsananin bacin rai ya saka sultan dauke sa da Mari batare da tunanin komai ba, baffa ya d'aga hannun xai rama, fu'ad yayi saurin dakatar dashi, isowar sa kenan.

Sultan yace da ka barshi ya mare ni din, dana nuna masa ko ni waye da qarfin mulkina anan garin, wallahi summa tallahi wannan hannun sai na saka a gutsire shi ba uban da xai hukuntani akan wannan.

Jikin baffa yayi sanyi, nan da nan wata kwalla ta taru a idanuwansa yana kallon sultan, banda kud'i da rashin tarbiya taya qaramin yaro kamar wannan xai tsaya ci masa mutunci haka har ya kai ga marin sa.

Fu'ad ya fisgo sultan tare da dukan qirjinsa, baka da hankali xaka Mari dattijon mutane, akan wane dalili, mtsew ya juya yana kallon baffa ya riqo hannunsa.

Baba kayi haquri dan Allah, Allah yasa ka fahimci mgnr da nake ma naga kamar baka jin yaren namu.

Da kyar baffa yace ina ji kad'an ba komai, cikin wata hausa tashi ta koyo.

Fu'ad yaje yana tattara masa kayan sa da sultan ya watsar, yana tsaye yana kallon yanda sultan ke sinsinar rigarsa saboda ya riqasa, ya bude motar ya d'auko gorar ruwan faro ya xubawa jikinsa.

Fu'ad kallon sa kawai yayi ya girgixa kansa cikin jin haushin d'an uwan nasa kafin ya bawa baffa kayan yana qara bashi haquri, ya d'auko kud'i ya bawa baffa.

Baffa yaqi karba, ya juya ya fice jikinsa a sanyaye batare da ya tsaya jiran buba ba, yana ganin dalilin sa hakan ta faru dashi tabbas da bai tsaya jiran sa ba da wannan wulaqanci da cin fuska bai ci karo dasu a yau ba.

Fu'ad ya dube sa cikin bacin rai yace ya kamata ka sani shi musulmi a duk inda yake d'an uwan musulmi ne, mu dasu bamu da wani banbanci, meyasa a rayuwa kake wulaqanta talaka, su suka yi kansu ne ko kai kayi kanka ne.

Fad'a kake min saboda wannan qaxamin, just look yanda ya bata motar nan har yake d'aga hannu yace xai mare ni, chab, ya ciji labbansa na qasa tare da shafar sumar kansa xuciyarsa na masa xafi ya shiga motar batare da ya qara sauraren fu'ad ba.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERA*


Haske writers Association


? ?Fertymerh Xarah=???






*is not free pls, idan baka biya ba dan Allah kada ka karanta*



Bayan kwana bakwai da rasuwar halimatu aka rad'awa yarinya sunan mahaifiyar ta suna kiranta Hidaya.

Ba yanda yan'uwa ba suyi ba akan ya bada yarinyar aje da ita can cikin dangi a sami wanda xai shayar da ita, yaqi amincewa da mahaifinsa ya matsa sai ya fashe da kuka mai tsanani wanda dalilin haka aka bar mishi ita.

Bayan kwanaki suka tattara suka koma cikin qauyen su.

Afiya kuwa tun ranar da ta haihu da kwana biyu Aiman yasa suka dawo gida Nigeria saboda biki, xo kaga murna gurin yan uwa da abokan arxiki.

Duk shagalin bikin da ake sultan ko a jikinsa sai Ma ya fice daga gidan ya nufi gidan Aliyu da Rumaisa inda yaron su Fu'ad wanda ya xame masa babban aboki kuma d'an uwa indai yana Nigeria.

Yarinya taci sunan Ammi, mahaifiyar Afiya idan baku manta ba suna kiran ta da yasmeen.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da dad'i ba dad'i, Hidaya tana samun kulawar mahaifinta sosai, kashin ta, wanka, wanki, fitsarinta duk shine, bai yarda da kowa ba indai akan yar'sa ne, bai yarda kowa ya kula masa ita ko ya dauke ta ba.

Maqota manya da yara yan uwansa fulani suna son d'aukar hidaya saboda yarinyar akwai shiga rai sosai, duk wanda yaxo ganin ta tabbas a hannunsa xaka ganta ka tafi.

Jeji da ita yake xuwa, wani xubin ya kan goyata ne yayi yawo da ita acikin jejin tare da dabbobin sa, mutane tun suna masa dariya har suka xo suka daina saboda bai taba kulawa dasu ba,

Kullum xai dafa madarar shanu ya bata, baya son kukan ta ko kad'an duk da bata da fitina, idan tana rashin lafiya tamkar shine ba lafiya komai qanqantar ciwo dole sai ya dage an bashi gado a qaramin? asibitin su dake garin.

Kowa yasan hidaya yar gidan ma'awiya, kowa yasan soyayya da kulawa dake tsakanin yarinyar da mahaifinta.

Lokacin da ta soma rarrafe a lokacin mahaifinta ya fuskanci bata gani, bai yarda da xargin sa akanta ba har sai da ya kaita asibiti aka duba ta aka qara tabbatar masa tabbas makauniya ce.

Fadin irin halin da ma'awiya ya shiga a ranar baxai fadu ba, yayi kuka har ya gode Allah, dalilin haka wata soyayya da shaquwa ta qara shiga tsakanin shi da ita, ya dauki lokacin sa da rayuwarsa kacokan ya damqa wurin kula da ita, tun da ta fara bud'e baki tayi magana ya koya mata da ta kira sa baffa.

Wasa wasa rayuwa ta soma ja, yau gashi hidaya tana shekara goma cif a duniya.

Yarinya ce mai haquri sosai, bata da yawan magana ko neman fitina gurin abokannin wasan ta idan sun xo gidan, tana yin komai nata a natse, idan ka ganta xaka rantse idanunta basu da matsalar komai domin a bud'e suke farare qal dasu, xaka ga dariyar tane idan tana xaune da mahaifin ta bayan shi sai dai murmushi ya had'a ka da ita kawai.

ita wata irin miskilar yarinyace da wuya ka fahimci inda tasa gaba domin fuskarta bata nuna abinda ke xuciyarta komi girmansa da muhimmancinsa koda xata cutu.

An haifeta a gidan, ta taso cikin gidan tayi rayuwa acikin gidan tun tana koyon xama, rarrafe, har tafiya shiyasa lungu da saqo na gidan ba inda bata sani ba, ba inda baxata shiga ba kai tsaye batare da sandar ta, ta dogarawa ba, idan ka ganta da sanda a hannu tana tafiya tabbas ta fito waje ne, a hakan take taimakawa mahaifinta ta tsar nonon shanu ko madara, wani lokacin ma ta kan taimaka masa gurin d'aure dabbobin idan sun dawo jeji.

Xakuyi mamaki idan nace maku a wannan shekarun nata tayi kusa hardar qur'ani saboda yanda baban ta ke xaunar da ita a koda yaushe yana koya mata tun tana qanqanuwar ta, tabbas bata gani amma babu ayar da xaka janyo mata a qur'ani bata karanta ta ba sai kuwa wadda bata kai ba.

Bata San wani harshe ba a rayuwar ta bayan nasu na fulani, duk ruggar basu da bahaushe ko mai yare da hausa, manyan ne kawai ke hausa sama sama saboda suna shiga gari tallar nono amma mafi yawan yaran d'if suke.

Baffa yau xan bika jeji, na jima banje ba yau ka barni naje.

Kiyi haquri har xuwa wani lokaci Hidaya bana son kina fita ko kad'an, sannan gasu Asiya duk xasu xo su taya ki xama kuyi wasa anan ko bakya farin ciki da xuwan da suke yi na dakatar dasu.

Ina yi baffana, ina kuma jin dad'in kasancewa dasu shiyasa nake da burin fita dasu tallar nono a rugar Ard'o, yaushe ne xan fara baffa?

Xan kaiki rugar ard'o amma ba dan ki siyar da nono ba, rugar kakan ki ce ai na gayamaki mahaifin maman ki.

Aa baffa ni nafi so naje tare dasu Asiya, ina so naje tare dasu muna wasa a rafi kullum suna bani labari.

Su idanun su masu lfy ne sabanin naki kada ki biye masu.

Baffa ni sai yaushe xan fara gani? Yayi shiru yana kallonta kafin yace duk ranar da Allah ya sauke ikon sa akanki, bani da wannan burin a yanxu kamar na ganki da idanun ki kina gani kamar kowa a wannan rugar, xan iya salwantar da duk abinda na mallaka domin na sama maki lafiyar idanun ki idan har aka tabbatar min da cewa xaki gani.

Tayi murmushi a hankali tare da riqo hannunsa tace baffa ni babban burina a rayuwa shine naga wannan baffana mai sona, nabi baffana duk inda xai je ina biye dashi sannan kuma na ganni tare da qawaye na muna xuwa rafi wasa.

Da yardar Allah idan ina numfashi a rayuwar nan burin ki xai cika Hidaya, ta tashi tana tsalle kafin ta lalaba ta haye bayansa tana fadin baffa yau duk baka goya ni ba, ni baxan sauka ba.

Ya tashi da ita yana murmushi yana juyawa da ita cike da farin ciki.

? ? Kyakkyawa ne matuka, dogo fari amma farin nasa ba mai irin hasken nan bane, fari ne daya cakud'e da gogayya cikin jin dad'i? hutu da wayewa irin ta yan boko, ma'abocin fad'in qirji da alamun qarfi ta ko ina, abin alfaharin kowacce mace, har maxa yan'uwan sa suna yaba shi.

*SULTAN AIMAN MERA* kenan mai shekaru 20 kacal a duniya, kasancewar sa d'an wasar buga ball ya saka jikinsa wani irin girma da qarfi da xakayi tunanin ya wuce shekarunsa.

Ba miskili bane dan bashi da shariya ko rashin qin magana idan aka masa,? sai dai shi mutum ne da baya son wasa ko dariya da yara musamman da baya son raini ko kad'an??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????, abu kadan yana amusing din sultan, a very jovial and loving personality.

Xaune yake gaban mahaifin nasa fuskarsa a cunkud'e da alama baya cikin walwala daga yanayin fuskarsa,

Dad kayi haquri ka barni anan, na fi son kasancewa ta anan qasar akan Nigeria please.

Na riga na gama magana gobe Nigeria xamu je, almost 2years an a half rabon da muje qasar mu, kuma ba wai nace baxa mu dawo bane ai xamu dawo inaji hutu kuke yi ai a skul ko kana da wasar da xaka buga ne mu jira ka.

Ya girgixa kansa a sanyaye, tamkar ya fasa ihu yake jinsa.

Asibitina tana buqatata sosai bayan wannan Ma mai martaba ya nemi da mu koma na d'an wani lokaci idan kunyi resuming school xaka iya dawowa ba wai ina nufin xamu koma gida Nigeria da xama baki d'aya bane na canxa ma makaranta.

Sai a sannan ya sauke numfashi kad'an kafin ya tashi yayi hanyar dakin sa.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERA*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=???

6


Yanda yake sharara gudu a titi sai kayi tsammanin tashi sama xaiyi, fu'ad kallon sa kawai yake kafin ya girgixa kansa a

2 / 26