Chapter 20 Reading Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc Arewa Novels

Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

Author :  Fertymerh Xarah Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   20 / 26

57K to 60K   out of 77.3K words

da a duniyar nan da xan sadaukar wa farin cikina, ina son hidaya fiye da komai a rayuwata dalilin ta na banxar tar da tawa rayuwa saboda na faranta mata, kuskuren ka d'aya a guna na aurawa sultan ya'ta, baffa ya cigaba da kuka, duk falon kallon sa suke da mamaki.

Waye ya lalata min rayuwar hidaya har yau ban sani ba, bansan waye wannan da yayi sanadiyar raba ni da hidaya ba, na d'auki hidaya na kaima lokacin da take matuqar neman taimako lokacin da duk soyayya ta a gare ta baxan iya taimaka mata ko ceto ta daga halin da ta fad'a ba, lokacin da kace xaka ma hidaya aikin idanu na baka amanar ta idan baka manta ba, ka karbi amanar kana fad'in xaka had'a hidaya da yar wurin ka saboda sa'annin juna ne, nayi amfani da wannan damar ta hanyar damqa maka hidaya a wannan lokacin da nima ina neman taimako dan ina gab da rasa rayuwata,

Na barka da hidaya na roqi mutanen da ka turo su kula dani da su gayama na mutu yan uwana sun tafi dani, a lokacin na bar asibitin cikin yaqinin cewa hidaya xata sami rayuwa mai kyau da inganci, xata dandani jin dad'i da gata kamar sauran ya'yan masu kud'i wanda ni bani da qarfin da xan bata wannan jin dad'in, na tafi ba dan bana son kasancewa da ita ba sai dan bani da abinda xan tallafi rayuwar ta dashi har ta sami ilimin da nake mafarkin ganin ta dashi, na siyar da komai nawa wanda nake da na had'a kud'in domin nema mata lafiyar idanu, idan na bada kud'in duka tabbas babu wani sauran abu da hidaya xata ji dad'i a gurina, na yarda na rungumi qaddarar da taxo min na fyaden da aka mata sannan na d'auki yin rayuwa babu hidaya, xan iya xama ni kad'ai na kula da kaina idan na sami abinci naci idan ban samu ba na xauna da yunwa to amma baxan jure ganin hidaya a wannan yanayin ba dalilin haka na bar maka ita.

Tun daga lokacin ban qara d'ora idanuna akan hidaya ba duk da ina bibiyar rayuwar ta, motar da ake kai su makaranta ake d'auko su tana da glass baqi wanda baka iya hango wanda ke ciki duk yanda na kai ga labewa domin naga hidaya ban taba hango ta a motar ba, idanu da xuciya a koda yaushe suna kwadaituwa da ganin hidaya, na tashi xaucewa saboda rashin ta har naji baxan iya ba xanxo na d'auke ta sai kuma xuciya ta ta rinjayi hakan, gidan da nake xaune anan sune suke kula dani kuma sune suka taimake ni wurin sama min lafiyata a wancan lokacin, na gayamasu ina da yarinya amma ta bata, a shekarun baya da suka wuce shekara biyar ban qara d'ora idanuna akan hidaya ba sai kwanakin baya na gane hidaya daga lokacin da ta bud'e baki tayi magana, 'ai kasan Dr aiman merah to ni yar sa ce babu ta yanda xan cutar da wannan tsohon' farin ciki a xuciyata a wannan lokacin baxai misaltu ba shine ya hanamin magana, hidaya ya'tace wannan ta koma haka, hidaya tawa ce da mota take tuqawa, me xanyi banda na godewa Allah, tsananin farin ciki ya saka jikina rawa sanda nake cikin motar ina shan kankana, kuma na bata motar da gangan saboda na ga canjin rayuwar da hidaya ta samu xai saka ta kyamaci talaka sai naga sabanin haka daga gare ta wanda ta nuna min a lokacin mota ba tafi mutum daraja ba kamar yanda sultan ke d'aukar mutum talaka kamar takalmin sakawar shi, daga lokacin na kasa samun nutsuwa ina so na karbi hidaya ina so na kasance da hidaya har tsawon rayuwa ta, had'uwata ta biyu da sultan Allah ne ya had'a kamar yanda ya had'a mu a farko kuma ka sake min rashin mutunci irin wanda ka min a baya, ka jefeni da kud'i kana ikirari babu abinda kud'i baxai baka a rayuwa ba, babu abinda xaka nema ka rasa tunda kana da kud'i mahaifin ka yana da kuma kakan ka Ma yana da, a yau xan gyara ma kuskuren ka na cewa ba duka abinda kake so a rayuwa kake samu ba ta hanyar kud'i domin ka rasa hidaya, kud'in ka baxa su iya siyen hidaya ba kuma babu ta yanda xaka iya samun hidaya ko da kai d'in xinari ne, ya juya yana kallon aiman.

Likita bani da abinda xan biya ka ko bakin da xan gode Ma akan amanar da ka riqe hannu biyu ba tare da cutarwa ba tabbas ka kula da hidaya Allah kad'ai xai iya biyan ka, wanda yayi wa hidaya fyade har yau ban san shi ba ban san kuma inda xan ganshi ba sai dai ina da shaida har yanxu ta dalilin wannan xoben da kuma wayar hannun sa.

What, daddy wannan xobe nane shine nake gayama ya bata, x..... yayi shiru sakamakon mari da aiman ya d'auke shi da shi, shut up idiot.

Baffa ya nuna sa da yatsa kai kuma, dama kaine kayi mata fyade innalillah me nayi ma a rayuwa kake bina da abu marar kyau haka, hankalin hidaya ya tashi sosai an taba mata fyade kuma sultan ne sanadi, hidaya ta tsurawa sultan idanu wanda tuni ya susuce tabbas ta tuna wannan ranar ta tuna wannan lokacin ta tuna abinda ya faru a wannan daren wanda bata gane illar haka a tare da ita ba sai yanxu, nan take taji xuciyarta na mata xafi taji babu wanda ta tsana a rayuwar ta sama da sultan tabbas shi ba alkhairi bane a gare ta.

Afiya tace taya xaku saka yaro gaba kuna xagi da masa qaxafi haka kai ka daka ita wannan ta daka akan wane dalili me yayi maku ta fad'a tana kallon aiman

Aiman ya juya yana fad'in ina xuwa, d'akin sa ya nufa bai jima ba ya fito d'auke da wata qaramar akwati, a gabansu ya bud'e ya ciro kud'i cikin leda da aka boye su, ya jefawa baffa yana fad'in wannan shine kud'in da ka bada ayiwa hidaya aiki, ya fito da wasu yana jefa masa, wannan kuma kud'in sadakin hidaya ne da aliyu ya biya dubu 100 cif, sai kuma ya fixgo sultan da qarfi cikin bacin rai tare da tura sa gurin baffa yana fad'in, wannan shine d'ana sultan, tsatsona wanda jinin Aiman Merah ke gudana a jikinsa, ko duniya da abinda ke cikinta xasu taru akan sa suna tsine masa baxan guje sa ba saboda ina son sa fiye da yanda kake son yar ka, ko sau d'aya ban taba gudun sa ba ko tsere masa saboda gaxawata ta wani fannin, da dad'i ko babu dad'i ina xaune da iyalina domin kare su, ni ina da yaqinin cewa sultan ne yayi wa hidaya fyade tuni na dad'e da sanin haka.

A raxane suke kallon sa, ba ma kamar sultan d'in da kusan fad'uwa a gurin ya tashi yi.

Afiya ta soma kuka tana fad'in sharrin da xaka masa kenan kamar ba....

Yace kimin shiru bana son jin komai daga gare ki, ya ciro awarwaro guda uku yana nuna wa baffa, yace wannan awarwaron na waye.

Baffa yace na hidaya ne tabbas na ta ne kakanta ard'o ya saka mata su a lokacin dana kaita gurin sa.

Aiman yace guda nawa ne?

Baffa yace guda hud'u ne,

Aiman yace ka kawo min hidaya da awarwaro uku a hannun ta, biyu a d'ayan hannun ta, d'aya a hannu ta guda, ina d'ayan ya shiga.

Baffa ya girgixa kansa cikin tunani yace ban sani ba kuma ban lura daga yaushe d'ayan ya fita daga hannun ta ba,

Aiman yace fine, lokacin da ka kawo min hidaya kafin na karbe ta tabbas naga wayar sultan a gaban aljihun ka, ban kawo cewa wayar sa bace a lokacin beside ma hankalina duka yana gida matata ta kirani a waya sultan baya gida a wannan daren.

Na karbi hidaya da amanar ta a gurin ka na juya na barka a gurin da cewa nurses su kula da kai, Dr Fulani bata qasar a yanxu ta d'auki annual leave da itace xata bada shaida a yanxu cewa akan idanunta ka bar asibitin da qafafun ka haka ta gayamin, dalilin ka na guduwa ka bar yar'ka ban sani ba amma na dad'e ina mamakin haka, sanin kana raye yasa ban taba gayawa hidaya baffanta ya mutu ba sai dai nace xai xo kace xaka xo kuma nasan dama xaka xo tunda gashi ka xo d'in,

An kawo sultan baya numfashi kuma a maballin aninin rigar sa na sami wannan d'ayan awarwaron ya maqale sai dai ya katse wanda rabin duwatsun duk sun xube, na d'auki awarwaron naje na gwada dana hannu hidaya duk iri d'aya ne, kuma hidaya tana qamshin turaren sultan, idan sultan ne yayi wa hidaya fyade kenan kaine wanda ya illata masa rayuwa, you make my son disabled, ya dawo bashi da wani amfani ya xauna tamkar jaririn goye komai sai an nuna masa an koya masa, wannan mahaifin yaron da ka nakasawa d'a shi ka baiwa amanar taka y'ar kuma ya riqe ta da hannu biyu batare da hantara ko tsangwama a gidannan ba, na kula da ita na bata sutura na bata ci da sha na bata ilimi da duk wani abin jin dad'i na rayuwa dai dai da rana d'aya ban taba banbanta ta da abinda na haifa ba, na nema mata lafiya da kud'in jiki na batare da ko kwandala acikin kud'in ka ba bayan nasan mahaifin tane? sanadiyar lalata rayuwar tawa d'an, ina da iko a qasarnan tsab xan iya saka a nemo min kai a duk inda kake fad'in qasar nan kuma ina da hanya da dama da xanbi na gano asali da yan uwan hidaya duk banyi ba, koda sarki yace xai saka ayi bincike a wannan qauyen ni na hana a ranar saboda na riga da nasan komai wanda babu wanda ya sani, daga baya naje na gayawa sarki komai akan abinda sultan yayi wa hidaya da dalilin da ya saka nake son riqe ta kuma na aura masa ita, da ba dan sarki yasan da maganar fyaden ba babu ta yanda xai amince da sultan yayi aure a wannan shekarun nasa, na dannewa xuciyata na boye wanda ko matata bata da masaniya akan wannan na sani komai daren dadewa xaka nemi hidaya xaka kawo kanka.

Na dage da tursasawa matata amincewa da auren hidaya saboda shi kad'ai xanyi na ceci tata rayuwar daga quncin da xata fad'a duk ta auri wani namijin daban, sultan shine yayi mata fyade kuma shine ya cancanci xama da ita, nayi masa uxuri a lokacin saboda nasan wannan fyaden shine na farko a garesa daga yanda yayi amfani da ita, bayan samun lafiyar sa na tambaye shi meya faru a wajen party yace ba komai, na qara tambayar sa fu'ad ya gayamin ya fita daga gurin bai da lafiya meya faru daga lokacin still ya kafe akan ba komai kuma sai na barshi kar na qarfafa bincike na akan sa nasan with time gaskiya xata yi halin ta, kana aibata tarbiyar sultan ga y'ar ka nan itama ta nuna min kalar nata tarbiya ta hanyar d'aukar hannu ta mari babba batare da nuna kawaicin ta a gurin mahaifiyar sa ko kuma ni ba, xaka iya d'aukar hidaya ku tafi shikenan, duk sanda ka ke son takardar sakin hidaya xaka iya xuwa ka karba.

Baffa ya d'auki sadakin ya ajiye masu anan yana fad'in auren da ban yarda dashi ba bana so baxan karbi sadaki ba,ya cire xoben hannun sa ya jefa ma sultan yana fad'in waya kuma na siyar na kashe kud'in,? ya d'auki nasa kud'in ya riqa hannun ta yana fad'in xo muje, cikin kuka ta juya tana kallon mera,

Daddy dan Allah kayi haquri, aiman yace ki bi mahaifin ki ya fimu son ki, ta juya tabi baffa batare da tayi magana ba.

Sultan ya yunqura xai bi su Afiya ta riqo sa tana fad'in, kyale su dama an xauna an tsara wannan drammer ne saboda aci xarafin ka, tsawon shekara biyar suna tsara wannan game d'in aka cutar da xuciyar ka ta hanyar saka maka soyayyar wannan marar tarbiyar, ni na yarda da kai nasan babu wata hanya ta mace da kasani baxaka iya ma kowa fyade ba.

Sultan ya fad'a jikin ta yana fad'in help me mamee ina son hidaya, ki dawo min da ita daddy baxai taimaka min ba.

Afiya tace taya xai taimaka ma bayan dashi aka had'a baki domin a cutar da kai, shekara biyar an rasa wanda yayi fyaden sai yau kuma ace kai, Allah ya saka ma.

Aiman murmushi yayi yana kallon su.....

#TeamAiman
#TeamBaffa

*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*
[11/20, 10:24 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*


*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*
38

Dariya kake tunda ka barsu sun tafi, halin da yaron ka xai shiga ko a jikin ka?

Yasmeen ta fashe da kuka ta bar falon da gudu haka amira ma jiki a sanyaye ta bar sashen nasu.

Aiman ya dube ta yana fad'in saboda me xan hana su tafiya, fyade fa yayi wa yar sa, rasa budurcin yarinyar nan ba abinda baki ce ba a gidannan ba irin maganar da baki fad'a ba yaron ki baxai auri mace ba Virgin ba ashe yaron naki shine ya d'auke mata budurcin baki da labari, wannan dalilin yasa na kafe akan lallai sai na aurawa sultan hidaya, meyasa a lokacin baki qarfafa? sai kinji dalilin auren sultan da hidaya ba duk na xo maki da mgnr a tunanin ki yarinya kamar hidaya ta isa ta kula da sultan ne, tasan yanda xata kula da kanta ballantana wani sultan, me tasani a rayuwa balle wani aure, nayi maki wasa da hankali saboda sanin halin ki nace warkuwar sultan tana tare da hidaya kuma banyi qarya ba itace sanadi, taya sultan xai cuci yarinya kamar wannan sannan ya tafi a banxa, ni na tursasa masa son hidaya da kaina gashi nan ki tambaye shi, tun bayan xuwan sa Phoenix bai qara mgn akan hidaya ba idan xai yi magana da kowa kuwa a gidannan lura da haka ya saka na fara tura mashi pics d'in ta tare da yasmeen ko kuma nata ita kad'ai, sannan ina qara tuna masa wahala da yarinyar tayi domin sa, sannu sannu sai ya fara magana akan hidaya baxai tambaye ni ita ba sai dai ya tambayi yasmeen, sanda yaxo yace min yana son hidaya ni na qarfafa mashi akan yaje ya nemi soyayyar ta ina so ta amince mashi kinsan dalilina na yin haka saboda ina son sultan ya san rayuwa, yasan akwai da babu, yasan abu xai iya xama naka ko kuma sabanin haka, yasan daraja da qimar mutum ko waye shi, ya san qunci da xafin rayuwa ya kuma san akwai abinda qarfin iko ko kud'i baxa su baka a rayuwa ba, duka wad'annan sultan bai san su ba, abinda kawai ya sani xai sami duk abinda yake so kowane lokaci idan ya nemi hakan sannan shi talaka bashi da wata qima a idanun sa komai girman sa da tsufan sa, can you imagine kamar sultan ya d'aga hannu ya mari wannan dattijon saboda mota, motar banxa, wannan ba tarbiya ta bace wannan rainon gimbiya Afiya ne da ta gudu da shi.

Sultan ya dube sa yana fad'in amma daddy kaine kace xaka tsayamin akan ko me nake so...

Aiman yace ban gayama idan na sami sa hannun ka a mai batawa hidaya ba xaka gamu da fushina, ban gayama haka ba last time, sannan ranar da ka farfado ban tambaye ka me ya faru a wannan qauyen ba kace ba komai, da a lokacin baka boye min ba ka gayamin gaskiya xan san ta yanda xan bullowa al'amarin kafin a kawo wannan lokacin.

Amma daddy ni baka ji meyasa na aikata hakan ba.... Aiman ya katse sa yana fad'in I don't care na sani yanxu ka riqe sanin ka ko ka gayawa mahaifiyar ka, kai kama aikata ne mahaifiyar ka taqi yarda da hakan saboda idanuwan ta sun rufe da soyayyar ka ta kasa gano kuskuren ka, ni nan qage aka min ta tattara kayan ta da kai ta gudu abinta, bata damu da halin da xata saka iyayen ta ko kuma mijinta ba, taje ta baka wannan tarbiya kaxo ka aikata laifin da kaima taka matar ta guje ka kamar yanda mahaifiyar ka tamin so yanxu itama xata dandana taji wannan xafin ya yake,? yanxu lokaci yayi ka fuskanci rayuwa kaje ka nemi yafiya da soyayya a Karo na biyu gurin hidaya I wish you all the best, xan yi murna idan hidaya ta amince Ma amma ni ba hannu na acikin wannan al'amari yanxu.

Cikin bacin rai Afiya ta soma fad'in eh na gudu dashi d'in, shekara nawa nayi tare dashi acan, inace a hannun ka ya girma, meyasa xan ga laifin sa ko na ga kuskuren sa bayan shine ya share min hawayen da ka saka min, shine wanda ya fara furtamin Kalmar so, mamee I love you, banji wannan kalami a gurin ka ba sai daga baya, shi nake hawaye ya saka hannu ya share min cikin damuwa, shi nake gani naji farin ciki da duk wata damuwa da ka samin ta kau saboda me xan guje sa bayan a lokacin da ka qini he stand by my right, ya'ya nawa aka yiwa fyade aka gudu aka barsu, wasu Ma basu gudu ba an san dasu kuma aka barsu suke rayuwa balle shi ba guduwa yayi ba wani al'amari ya sami rayuwar shi wanda wannan shine sanadi, dan mugun ta kasan wanda ya aikatawa yaron ka haka ka kyale shi yake rayuwa har ka barni nake kulawa da y'ar sa wallahi kaci amanata aiman, kai kake gayamin da bakin ka budurci ba komai bane idan haka

20 / 26