Chapter 18 Reading Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc Arewa Novels

Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

Author :  Fertymerh Xarah Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   18 / 26

51K to 54K   out of 77.3K words



Mamee wannan tambayar fa?
Answer me ta fad'a cikin d'aure fuska, ya gyad'a kansa kamar wani soko.

Who is she, yar gidan waye? ya yatsina fuska ya soma cin chips d'in yana fad'in ban nema ba tukunna, tace to ka nema yar dangi kuma yar babban gida wacce aka san asalinta.

Ya gyad'a kai yana murmushi kafin yace mamee kina tunanin da fu'ad ne kike magana, shine ke son mace ko wace iri ce, ni ina da xabi ai bana son auren yar talakawa ko wata marar asali.

Murmushi Afiya tayi wanda ya bayyanar da farin cikin ta tsantsa, tace yauwa farin ciki na, kaga kamar irin hidaya kenan da har yau baa san asalinta ba.

Yace aa tana da asali mamee, ba tsintar ta akayi ba daddy yasan mahaifin ta beside ma tunda hannun ki ta tashi ai mune dangin ta.

Tace aa bamu bane mu bamu da alaqa da wanda ba jinin sarauta ba, har yau baa san daga inda ta fito ba, asalinta dangin ta duka babu labari so ka gani she is not part of us.

She is... Yasmeen ta fad'a tana kallon ta wacce tun bayan fitowar ta taji hirar da suke,

Labe kike min kenan, Afiya ta tambaya cikin fusata.

Yasmeen tace aa mamee amma hidaya is part of us ki daina wannan magana kada taji.

Afiya ta tabe baki ta tashi ta bar falon, sultan ya bita da idanu kafin ya dubi yasmeen yana fad'in me ke damun mamee ne.

Tace nima ban sani ba, ya tabe bakin sa yana cigaba da cin abincin sa.

*

A gurguje tayi wanka ta xura doguwar riga ta fito falon ba kowa sai yasmeen kawai.

Tace sis idan mamee ta fito na fita na dawo pls.

Yasmeen tace ina xaki je haka a hargitse, hidaya ta yatsina fuska tana fad'in sign na ciwon mara na nake ji kuma na nemi maganin ban gani ba kafin yaxo nake so naje na karbi magani a gurin daddy.

Ayya yasmeen ta fad'a cikin tausayawa sanin yanda hidaya ke wahala idan bata sha maganin ba, a dawo lafiya.

Hidaya ta fice da sauri, sultan ya ga fitar ta da mota ta window d'in sa, yayi mamakin ganin yanda take sauri ko meke faruwa sai ya fito falon har lokacin yasmeen tana xaune tana chatting.

Yace ita waccan saurin me take haka, ina xata je.

Tace asibiti xata je bata jin dad'i ne.

Yace meke damun ta? Yasmeen tayi d'an Jim kafin tace kanta yake ciwo.

Yace kuma duk babu magani a gidan nan har sai taje asibiti.

Yasmeen ta shagwabe fuska tana fad'in yaya ni ban sani ba qila babu ne shiyasa, ya tabe bakin sa yana barin falon.

Aiman na bata maganin tun acan ta d'auki Swan ta sha, sannan ta sami guri ta xauna ko xata sami d'an relief.

Yace kina nufin duka wad'ancan maganin dana baki last month kin shaye kenan, ta girgixa kanta no daddy na nema ban gani ba na manta inda na ajiye ta fad'a tana yatsina fuska alamar ciwon yana qaruwa ma.

Kallon ta yayi yana observing d'in ta kafin ya tashi yana fad'in kwanta na gani, ta kwanta da kyar kamar yanda take yi idan xai duba ta, duba ta yayi yana fad'in qila sai nayi wa hidaya aure sannan xata rabu da wannan ciwon.

Ta bata fuska tana fad'in meyasa sai nayi aure.

Yace nima ban sani ba.
Tace ni daddy bana son aure yanxu karatu xanyi baka ce admission d'in mu yana fitowa ba xamu je.

Yace eh mana na sani, ai koda aure ana karatu.

Ni daddy bana so.
Yace shikenan idan ciwon ya bari xo kije gida xan fara duba patients, ta sauko daga saman gadon tana sanya takalmin ta tace bye bye, hannu ya d'aga mata batare da ya dube ta ba yana duba wani file.

Tafiya take a hankali akan titi, tuqi take cikin nutsuwa ba kamar yanda ta xo asibitin ba d'axu, ta ja birki da qarfi garin tunanin ta saura kad'an ta bige wani dattijo, ta fito daga cikin motar ta nufe sa tana fad'in wayyo baba kayi haquri ban jima ciwo ba ko?

Mutumin ya gyad'a kai batare da yayi magana ba yana gyara ledar hannun sa, wani saurayi yaxo da gudu yana fad'in

Kaga irin ta ko baba, yanxu da an bige ka fa, sai da nace ka jira naxo na saka a napep ai, ya riqa hannun dattijon yana fad'in xo muje, hidaya ta dube su tana fad'in, baba baya magana ne.

Saurayin yace menene damuwar ki, ta girgixa kanta tana fad'in ba komai, amma ina xaije kamin kwatance sai na sauke sa, kallon ta yayi yana fad'in haka kawai na d'auki tsohon mutane na baki ban san ki ba bansan ko waye ke ba.

Tace sani na bashi da wani wahala, ai kasan Dr merah mai wannan asibitin, ni yar sa ce babu ta yanda xaa yi na cutar da wannan tsohon ka yarda dani ta fad'a tana nuna masa lambar motar ta dake d'auke da tambarin MERAH akai.

Saurayin ya dubi dattijon yana fad'in baba ka amince xaka bita, ya gyad'a kansa batare da yayi magana ba, nan saurayin yayi mata kwatance inda xata ajiye sa kafin yaje ya saka shi a gaban motar taja motar suka bar wurin.

Qoqarin bud'e ledar sa yake kansa a sunkuye duk abinda yake hidaya tana yi tana kallon sa, kankana taga ya ciro daga cikin ledar hannun sa ya miqo mata, ta girgixa kanta tana fad'in aa baba nagode kasha kawai.

Nan ya maida hankali yana shan abar sa, ta cigaba da tuqin da take bayan wasu mintuna ta juyo tana kallon sa sai da gabanta ya fad'i ganin yanda yayi ma seat d'in motar ta kaca kaca da ruwan kankana da abarba kamar qaramin yaro ke sha, suna had'a ido dashi sai taga yayi wani iri da fuskar sa kamar bai ji dad'in abinda yayi mata ba, murmushi tayi tana fad'in kada ka damu baba mota bata kai darajar mutum a gurina ba ka cigaba da shan kayan ka xan saka a gyara, murmushi yayi Karo na farko yana kallon ta dai dai lokacin da suka iso inda aka mata kwatance, ta dube sa bayan tayi parking tana fad'in nan ne baba? Ya gyad'a kansa cikin tabbatar wa, ta fito daga motar ta xagaya taje ta bud'e masa ya fito ta rufe, hannuwansa ya had'e guri d'aya alamar godiya,

Tace babu komai baba amma ka riqa kiyaye hanya saboda watarana xaa iya bige ka kai kuma naga ko kallon hanya baka yi kake hawa titi.

Ya gyad'a kansa cikin gamsarwa kafin ya juya ya fice wasu yara taga sun fito daga cikin gida sun nufe sa suna fad'in baba oyoyo.

Tana isowa gida ta bada makullin motar ga Abu ya wanke kafin ta nufi cikin gida har xuwa lokacin tana jin ciwon kad'an kad'an, tana shiga falon taga yasmeen na qoqarin fitowa nasu d'akin.

Tace sis kin jima fa baki dawo ba har xan kira daddy yanxu, ina ce marar ta daina ciwo yanxu.

Hidaya ta yatsina fuska tana fad'in aa wallahi tana yi k... tayi shiru sakamakon had'a ido da suka yi, ashe yana falon bata lura ba, yasmeen ma bata san da shi ba sai yanxu, hidaya ta nufi d'akin su da sauri yasmeen kuwa fita tayi daga sashen xuwa inda umma.

Doguwar rigar ta cire kafin ta hau gadon ta kwanta tana lumshe idanunta cikin tunanin kafin ta tashi barci ciwon ya tafi duka.

Tun da yaji abinda ke damun ta ya shiga tausayin ta bai san dalili ba, ya tabe baki yana fad'in yaran nan sun girma ashe chab, sai ya tashi cikin son sanin wane hali take ciki yanxu sai ya nufi d'akin, tana kwance cikin duvet, a hankali ya xauna bakin gadon had'e da saka hannun sa cikin nata ya riqe a hankali yana kallon bakin ta.

Tun da ya shigo d'akin taji qamshin turaren sa bata gasgasta shi bane sai da taji ya xauna a saman gadon har da riqa hannun ta, me ya kawo sa kuma meyasa ya riqa hannun ta?tace qila yaji tausayina ne kuma yana kallona kamar qanwar sa, ta bud'e idanun ta a hankali tana kallon hannunsa dake cikin nata, bata san dalili ba amma ta tsinci kanta cikin jin dad'in wannan yanayin ba qaramin kyau hannuwan nasu yayi ba da suka sarqe tare, ta d'aga idanunta tana kallon sa carab suka had'a ido, sai ya sami kansa cikin rud'ewa baiyi tunanin ba barci take ba, ya xame hannun sa kamar daga sama taji yana fad'in,

Hidaya muyi wasa=?D?.

*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334989*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*


*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*

35

Idanunta ta xuba masa cikin mamakin jin furucin sa, kafin ta maida hannun ta cikin duvet tana fad'in, wasa kuma yaya?

Yace ni nayi maganar wasa?ta tunxuro baki tana fad'in ba Kaine yanxu kake cewa muyi wasa ba.

Yace wasa wace iri, tayi shiru
Yace tashi ki xauna, ta dube sa da sauri tana fad'in yaya banda lafiya fa, yace na sani ki tashi mana.

Ta qara jan duvet tana rufe jikinta tunawa da shimi ce kawai a jikinta, ganin ya dage sai ta tashi tace ba komai a jikina fa, yace sai me, menene a jikin naki koma me kike dashi da kike boyewa dai dai lokacin yasmeen ta shigo, bata yi mamakin ganin sa d'akin ba tunawa da dama yana shiga tun tana qarama kafin hidaya ta xo sai dai bai taba xama akan gado ba kamar yau da ta same shi, ta dubi hidaya da ta bata fuska sosai wanda ke nuna a takure take da xaman sa a gurin.

Yaya kana jinya ne?yasmeen ta fad'a tana kallon sa da murmushi a fuska, yace ni nayi kama da mai jinya ne sai na rasa abin jinya sai wannan qaramar yarinyar, aikuwa a take suka tunxuro baki suna bata fuska, tashi yayi yana kallon yasmeen kamar xaiyi magana sai kuma ya fasa ya fice kawai,

Hidaya ta sauke numfashi kad'an tana fad'in Yaya ma fuddi? billungo am(yayan ki ya soma takurani).

Ya takura ki dame yasmeen ta tambaya tana kallon ta,

Hidaya bata yi magana ta juya mata baya tana rufe idanuwanta cikin son barci ya d'auke ta, yasmeen ma tabe baki kawai tayi batare da ta qara bi ta kanta ba.

Friday......

Cikin qanqanin lokaci ya gama shirin sa cikin farar shadda, d'inkin ba qaramin fito dashi yayi ba, yana fitowa ya nufi falon mahaifin sa baya nan sai ya nufi bedroom, aiman na tsaye yana d'aura agogo a hannunsa cikin nasa shirin shima cikin farar shadda sultan ya shigo.

Yeah daddy yau munyi anko kenan, kallon sa mera yayi yana fad'in gashi kayi kyau kuwa kamar wani ango, murmushi sultan yayi yana kallon sa kafin

Yace daddy at my age ni nayi qarami na xama ango ai kaima baxaka yarda ka min aure yanxu ba.

Aiman yace inji wa sai idan baka kawo wacce kake so ba, ko kad'an baka yi qarami da aure ba nima at your age na dawo na sami har an min aure.

Sultan ya matsa kusa da shi yana fad'in daddy da gaske kake yi, aiman ya gyad'a kai cikin tabbatar wa sultan yace ko wacece xaka barni na aure ta.

Mera yace me xai hana idan kana son ta tana son ka, ya fad'a yana addu'ar Allah yasa hidaya ce.

Sultan ya shafi sumar kansa yana murmushi cikin jin nauyi shima mera sai yayi murmushi yana fad'in cmon, we are friends now and always, so feel free and tell me, wacece, yar gidan waye a qasar nan, ita d'in jinin sarauta ce? Sultan ya girgixa kansa yana fad'in babu ko d'aya, daddy hidaya ce.

Cikin tsananin mamaki aiman ya dube sa yana fad'in like seriously hidaya dana sani, sultan ya gyad'a kansa, dariya aiman yayi mai d'auke da farin ciki yana kallon sa, yaushe ka fara son ta bana son ka cutar da yarinyar mutane ita d'in marainiya ce,

Sultan yace Allah daddy ina son ta ni ban taba son kowa ba sai ita.

Aiman yace promise xaka xauna da ita ba cuta ba cutar wa, no more takura and again xaka so ta ka kula da rayuwar ta har abada ka xame mata uwa uba da ta rasa a baya.

Sultan yace I promise daddy amma sai ka koya min ni bansan ya xanyi ba.

Dariya ta subulcewa aiman kafin yace ni xan koyama yanda xaka xauna da mace ko kuma xan koya ma yanda xaka kula da ita, kada ka damu son with time xaka iya komai batare da an koyama ba, ni na baka hidaya amana idan kaci amanar ta kaci amana ta, xan aura ma hidaya ka d'auke ta kaje da ita can tare da kai ta cigaba da karatun ta, kaje ka nemi soyayyar hidaya idan kuna son junan ku babu yanda mahaifiyar ka xata so raba ka da ita.

Cikin fargaba sultan ke kallon mahaifin nasa daya tuna Afiya tabbas baxata so ya auri hidaya ba tunda tana kallon ta as marar asali da gata, yace daddy idan taqi yarda fa?

Aiman yace am the man of the house, ka nemi soyayyar hidaya kawai kada ka damu I will stand for you, amma ka sani idan na same ka da laifin batawa hidaya ko yaya ne xaka had'u da fushina.

Sultan yayi shiru, aiman ya riqo hannun sa yana fad'in kamar na gayama wani secret about you and hidaya amma baxan yi ba a yanxu na fasa, sultan yace please daddy gayamin naji, yace ba yanxu ba sai ka qara girma da hankali, wannan kalma ta girma ba qaramin dariya ta bawa sultan ba, a tunanin sa akwai wani girma da xaiyi bayan wannan?haka suka fito suna dariya daga shi har aiman cikin tsantsan farin ciki, Afiya na xaune a falo,

Ta tsura masu ido cikin so da qauna, ba qaramin kyau suka mata ba cikin shigar su ta farar shadda, like father like son akwai kamanni aiman sosai a tare da sultan, ta qara godewa Allah a xuciyar ta da kyautar wad'annan maza da Allah ya bata a rayuwar ta wanda bata san wa tafi so a tsakanin su ba, they make her happy always wanda farin cikin su a ko da yaushe su faranta mata batare da sun bari damuwa ta kusance ta ba, they made her realize how a dream come true idan ta tuna baya a brave wife and mother, mother of three daga tsatson Aiman merah wanda kowa ke alfahari dashi wannan wannan d'an jinin sarauta daya taka rawar gani a samartakar sa, tana godewa Allah kuma tana qara gode masa.

Tunanin me kike haka, aiman ya fad'a yana kallon ta, murmushi tayi mai tsayawa a xuciya tana kallon su kafin tace tunanin ku mana, farin cikin me kuke haka.

Aiman yayi dariya yana fad'in wannan sirrin d'a da mahaifin sa ne,

Tace wannan kyau da kuka yi a haka baxai tafi a banxa batare da na d'auke ku pic ba, ta d'auko dalleliyar iPhone d'inta ta soma d'aukar su, haka kuma suka saka ta tsakiya suka yi su uku

ka da muyi late bari muje mosque lokaci yayi merah ya fad'a yana gyara xaman hular sa, suka juya suka bar falon ta bisu da kallo cike da sha'awa wai ita ce Afiya da wannan santalelen d'a son kowa qin wanda ya rasa farin cikin ko wacce mace, abu d'aya ya rage mata sultan ya sami mace ta gari, mafarkin ta ya xama gaskiya, the dream of becoming a mother in law, a grand mother to her own blood granddaughter amma ta ina wannan mafarkin nata xai cika, ta ina wannan tsatson xai fito?

A week later....

Ya kai qoluluwar tunani ya rasa mafita game da abinda yake ji game da hidaya a xuciyar sa, tun yana boyewa har abin ya soma fitowa wanda har lokacin wadda yake yi domin ta bata ma san yana yi ba, sun yi matuqar sabo da ita yanxu duk da bai Saki jiki sosai da ita ba.

Tabbas xai bi shawarar mahaifin sa ya nemi soyayyar ta da wuri kafin mamee ta ankara, yana da yaqinin cewa Afiya baxata taba barin sa ya auri hidaya ba amma idan suka kafe suna son junan su fa kamar yanda daddy ya fad'a masa, yau ya yanke hukuncin tun karar ta da soyayyar sa.

Yana fitowa d'akin sa kai tsaye nasu ya nufa tana xaune akan sofa d'akin tana duba wasu kaya da yasmeen ta karbo masu gurin mommy da abban su salwa ya kawo masu a matsayin tsaraba da yaje Egypt duba su ameera skul.

Kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta tana murmushi tare da fad'in yaya kamar ka shiga xuciyata fa da gurin ka xanje yanxu ka xaba min wace Kala xan d'auka aciki tun d'axu na rasa wanda xan xaba ko wane colour ina so cos suna min kyau.

Yace to bari na koma sai ki d'auko kayan ki same ni acan.

Tace aa yaya, xo ka gani ta matsa kad'an tana nuna masa kusa da ita, ya xauna daf da ita har kafad'un su na gugar juna, ki d'auki pink d'incan ina son colour d'in a gurin mace, ta tunxuro baki tana fad'in ni ina maganar kaina not you, yasa hannun sa kan labbanta yana kallon cikin idanun ta, kin bani dama na fad'a maki wani abu, ta gyad'a kai a hankali tana sauke idanun ta qasa baxata jure wannan kallon daga gurin sa ba,

You gave me a chance to expose my self from that emotional torture, am in love with hidaya, gayamin abinda ke cikin xuciyar ki game dani, do you love me?

Ta d'ago a hankali ta dube shi batare da ta amsa ba, wasu irin kibbau taji suna keta xuciyarta daga kyawawan idanunsa wanda bata ji a gurin fu'ad da

18 / 26