Chapter 5 Reading Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc Arewa Novels

Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

Author :  Fertymerh Xarah Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   5 / 26

12K to 15K   out of 77.3K words

sha, fu'ad yace bana tunanin akwai wani abu a drinks d'in gaskiya saboda nima nasha, da yawa ma nan gurin naga suna sha, ko dai wata ka gani ta rikitama tunani ne.

Xai yi magana sai ga ziyada taxo gurin tana wata tafiyar kissa, tana qarasowa ta kwanta qirjin sultan tana fad'in, ina buqatar ka.

Hakan da tayi yaji wani yarrr a jikinsa da sauri ya finciketa a jikinsa batare da tunanin komai ba ya d'auke fuskarta da Mari.

Fu'ad yayi xuru yana kallon ikon Allah dan ma xata taimaka masa daga halin da yake ciki miye laifin ta.

Ya nuna ta da yatsa, ni na maki kama da shashatattun maxa, ko kinga nayi kama da namijin da kowacce mace ke d'ora nauyinta akan qirjinsa, am warning you for the last time ko a hanya kika ganni kika yi gigin nuna kin sanni sai na wulaqantaki ballantana kiyi qoqarin sake had'a qaxamin jikin ki da nawa, baxan kyale ki ba is a promise sai na nuna maki ko ni waye a garin nan tunda kika taba jikina, ya juya ya fice a fusacce fu'ad ya bisa yana kiran sa amma bai saurare sa ba, kafin ya iso tuni ya buga motar sa ya bar gurin a tsiyace.

Tun fitowarsa ya rasa hanyar da xai bi tunda bai san kan qauyen ba, hanya biyu ce da ta rikitasa yayi tunanin acikin su wadda suka biyo ya kasa ganewa, ya dafe kansa saboda abinda yake ji ajikinsa kamar wanda yasha maganin qarfi, sai harbawa take yi da qarfi, ya matse qafafun sa yana bin hanyar da xuciyarsa ta kwadaita masa da bi, gudu yake sosai burin sa yaga ya fita qauyen lafiya.

Hidaya kuwa sai tafiya take batare da tasan inda ta nufa ba, da qarfi yaja burki ganin saura qiris ya bige ta, ya haske ta da hasken motar yana kallonta, yanayin da yake ciki idanunsa ke nuna masa wata babbar bafillatana kyakkyawar gaske, ya tsurawa lips d'inta idanu kafin ya kashe hasken fitilar motar ya fito.

Hidaya kuwa jin wani abu ya tsaya da qarfi a gabanta yasa ta tsaya cak, abinka da wanda baya gani Sam bata san an haske ta da fitilar motar ana kallon taba tsananin tsoro ya saka ta tsayuwa guri d'aya, jin alamun taku ana kusanto ta ya sa ta soma waige waige tana fad'in baffa.

Muryarta har cikin kwakwalwar kansa, ga wani bugun xuciya da yake ji kamar irin wanda yaji lokacin da xai fita asibiti, batare da tunanin komai ba ya riqo hannunta, ta soma kiciniyar kwacewa tana fad'in Ambo a Moi?(waye kai), ya fisgota yayi cikin jejin da ita hankalinsa a gushe dan bai san meke faruwa da shi ba.

Ta soma kuka sosai tana fad'in, Accam (ni ka kyale ni) baffa... Baffa,Ko mi wadi ma or ko gadumami(me nayi ma)

Duk iya qoqarin ta na ganin ta ceci kanta ta kasa, kuka take sosai tana kiran baffanta, had'uwar numfashin su ya saka sultan rud'ewa abinda bai taba ji ba, bai san yanda xai yi ko xai fara ba qoqarin xare mata xanin jikinta kawai yake, abinda ke gudana acikin jinin jikinsa ya wuce his expectations to such an extent that lamarin yaxo wani limit d'in is beyond his capability to ignore.. he can't control himself duk da kuka da magiyar da yake ji daga gare ta.??




Littafina na kud'i ne idan baka biya ba dan Allah kada ka karanta.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=???

10

Bayan shud'ewar wasu lokutta, hayyacinsa ya dawo jikinsa, babu xato sai yaji wani kuka yaxo masa yana nanata innalillahi wa inna ilaihir raji'un,

Ya tsinci kansa a halin da bai taba tunanin xai kasance ba, menene yake aikatawa akan qanqanuwar yarinyar da bata san rayuwa ba, bata san menene duniyar da abinda ke cikin ta ba, wacece ita, me ya fito da ita a wannan lokacin? kafin ya farga daga tunanin da yake yaji saukar duka a tsakiyar kansa, ya dafe kan cikin axaba yana qoqarin tashi aka sake kai masa wani dukan mai xafi fiye dana farkon wanda yayi sanadiyar shudewar tunanin sa, bai san kansa ba, bai san ko shi waye ba, bai san me ya aikata a baya ba, bai san komai na rayuwa ba, bai san ko shi din mutum ne ko ba mutum ba baxai iya tuna komai na rayuwar sa ba, rayuwar sa ta dawo sabuwa tamkar jaririn da ya fad'o duniya a yanxu nan take ya fad'i gurin a sume cikin jini.

Baffa ya jefar da qatuwar sandar dake hannun sa ya qarasa da gudu inda hidaya take kwance, tunda yaje gida bai ganta ba ya fito neman ta hankali a tashe , a garin neman nata ne Allah ya saka ya jiyo muryarta tana kiran sunan sa har ya biyo sahun.

Ya tallabo ta da sauri yana kiran sunan ta,

Baffa ya saka min wani abu, akwai ciwo, fitsari yaqi xuwa baffa ka cire min.

Sai alokacin ya lura da babu xani a jikinta ballantana pant, da sauri ya saka hannu ya dafe gefen xuciyarsa danayi saurin bugawa, numfashin sa ya soma sama sama kamar yanda nata keyi.

Me hakan ke nufi hidaya, na kasa riqe amanar da halimatu ta bani kome, meyasa wannan rana taxo min a haka, waye shi wannan wanda ya cutar min dake, meyasa kika fito bayan na hana ki fitowa.

A gigice ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, ya d'auki xanin ya rufe mata jiki dashi anan yaci karo da wani xobe mai kyau sai sheqi yake, ya boye xoben a aljihunsa kana ya d'auki hidaya da sauri ya nufi gida da ita.

Kud'in sa ya d'auka da ya tanadar saboda aikin idanun ta, lura da yayi kamar bata numfashi ya saka nashi numfashin soma sarqewa, da kyar ya d'auke ta ya goyata ya fito da ita.

Tafiya yake da ita batare da yasan inda yake jefa qafarsa ba addua yake Allah ya taimake sa ya kawo mota kamar yanda ya taimakesa dax'u.

Sai da yayi tafiya mai nisa kafin ya sami mota, da kyar mai motar ya yarda xai d'auke sa saboda dare yayi sosai. Suna cikin motar ya sake rungumota xuwa jikinsa

Na kasa cika alqawarina na xamowa inuwa a rayuwar ki hidaya tunda wani har ya keta maki haddin ki, ki yafe min ni mai laifine a gareki da naje dake da hakan bata faru ba, da ban yi dare ba da hakan bata faru ba amma na d'auki wannan a matsayin qaddarar rayuwar mu daga ni har ke, baxan iya cigaba da rayuwa dake ba hidaya xuciyata ta kasa daurewa kamar yanda nayi alqawarin sama maki lafiyar idanu tabbas xan cika maki wannan alqawarin naki sai dai naki burin baxai cika ba na ganin baffan ki ko kasancewa tare dashi, ya fashe da wani irin kuka sosai yana qara rungumeta yayin da xuciyarsa tayi wani irin nauyi sosai.

Agogon dake office d'in ya buga qarfe d'aya dai dai na dare, ya rufe system d'in dake gabansa yana qoqarin tashi wayar sa ta d'auki ruri.

Yayi mamakin ganin kiran Afiya a wannan daren, ya d'auka da sauri.

Wai sultan baya gurin kane?
Na taba xama da sultan a irin wannan lokacin ne a asibiti.

Muryar ta na rawa tace wlhy baya gida bai dawo ba har yanxu, ga sarki can ya kasa kwanciya yana jiran dawowar sa, har da securities ya tura su nemo sa amma shiru har yanxu basu dawo ba alamar basu gansa ba, sultan bai taba kai qarfe tara na dare a waje ba ballantana yanxu one.

Yaji gabansa ya fad'i, kin kira rumaisa basu tare da fu'ad acan.

Na kira fu'ad yace tun dax'u suka rabu, wai sunje wani Party ne kuma ya dawo kafin shi, na kira ammi ma tace duk yau bai je ba, ga wayar sa tana ringing amma ba respond.

Yace gani nan xuwa yanxu, ya tsinke wayar da sauri cikin tashin hankali, komai bai tsaya d'auka ba ya fito office da sauri, a harabar asibitin yaci karo da baffa d'auke da hidaya yana tafiya kad'an kad'an numfashin sa na fita da kyar, cak mera ya tsaya yana kallonsa cikin sanyin jiki har ya qaraso, ya xubawa hidaya idanu jikinta duk jini ya d'ago da sauri yana kallon baffa.

Meya same ta haka ko hatsari ne,

Baffa ya girgixa kansa yana miqawa Dr mera ita, da sauri ya karbe ta kuwa ganin yana qoqarin fad'uwa kamar qarfinsa ya Gaza.

*FYAD'E* aka mata likita, ya cutar da rayuwar mu.

Wata irin fad'uwar gaba ta dirar wa mera lokaci d'aya har sai da yaja baya saboda firgita, baffa ya Ciro kud'i cikin jikinsa ya d'ora a saman jikin hidaya da kyar yace

Wannan kud'in aikin hidaya ne kamin alqawarin hidaya xata gani a rayuwar ta dan Allah ka cika mata wannan burin k.... Yayi shiru sakamakon wani tari da yaxo masa lokaci d'aya ya dafe xuciyarsa had'e da durqushewa gurin, mera ya soma kiran nurses gurin cikin gaggawa ganin yanda jini ke fita bakin baffa.

Kafin su iso tuni ya xube gurin, mera na ganin haka ya juya da sauri yayi cikin asibitin da hidaya ganin numfashin ta sai ya dawo kuma ya d'auke alamar tana neman taimakon gaggawa.

Cire xanin yayi yana kallon gurin, da sauri ya rumtse idanunsa yana ja da baya dai dai lokacin wayar sa ta d'auki qara, ya ciro ta cikin aljihunsa da sauri Afiya ce, wannan Karon kuka take,

Baka xo ba yarima, har yanxu baa ganshi ba, jikina yana bani sultan ba lafiya ba.

Da kyar cikin sanyin murya yace ina hanya yanxu xan qaraso.

Ya kashe wayar gaba ki d'aya, xuciyarsa tafi aminta akan ya taimakawa hidaya domin yasan sultan mutane da dama suna can suna neman sa a yanxu hidaya kuwa bata da wannan gatan sai Allah sai shi a yanxu.

Wannan aika aikar da akayi wa yarinyar ko waye ya je mata da qarfi batare da tausayi ko concern na kasancewar ta qanqanuwar yarinyar da bata san menene wannan abin ba, nan da nan ya shiga bata taimakon gaggawa ciki kuwa harda d'inki, ya d'auki fiye da awa d'aya kafin ya gama, ya cire kayan jikinta ya goge mata da qaramin towel kafin ya sauya mata kayan xuwa na majinyata, ya saka mata drip kana ya fita kiran nurse d'in da xata kula da ita.

Saboda tsananin rud'ewa bai qara bin halin da baffa yake ciki ba ya fice.

Har xuwa washe gari babu sultan babu alamar sa, shi kansa fu'ad da qaseem a rud'e suke musamman sauran abokan nasa babu inda baa tura cigiyar sa ba.

Kwatsam sai ga jami'an tsaro sunxo da sultan sun same sa acan qauyen a hanya mutanen garin sun xageye sa suna kallon sa.

Jikinsa da kansa duk jinine babu alamar numfashi a tare dashi, Afiya ta xube gurin a sume, mera yayi kanta da sauri.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un shine abinda Dr mera ke nanatawa bayan x-ray d'in sultan ya fito.

Gaba ki d'aya family d'in hankalin su ya tashi jin abinda ya sami sultan na loosing memory.

Saukar marin da suka ji a gurin ya saka hankalin kowa komawa gurin, rumaisa ce ke dukan fu'ad.

Da ixinin wa kuka je wani Party, me ka jawo wa d'an uwanka haka, you are to blame fu'ad sultan bai san ko ina nan garin ba kaine ka jasa.

Mommy wlhy.... Yayi shiru sakamakon saukar wani Mari da ta qara d'auke shi da shi, a gigice ya nufi gurin sarki ya fad'a jikinsa yana kuka, granny ka gayawa umma ta daina duka na ba laifina bane.

Aliyu (mahaifin fu'ad, yayan Afiya idan baku manta ba) ya d'ago jajjayen idanuwan sa yana kallon fu'ad da kyar yace ya akayi ka bari ya dawo shi kad'ai bayan kasan bai san gurin ba.

Abba sai dana ce ya jira mu dawo tare yaqi shi baya jin dad'in jikinsa baxai iya jira a gama ba.

Amma shine ka kasa biyo sa ku dawo bayan kaji yace bashi da lfy, wane irin yaro ne kai ai kaine babba, Afiya ta fad'a tana kallon sa cikin bacin rai, fu'ad xai yi magana Dr mera yayi saurin dakatar dashi yana kallon rumaisa.

Karki sake dukan sa idan ba haka ba ranki xai yi matuqar baci, kafin ya juya ga sauran yana fad'in meyasa kuke ganin laifin fu'ad ne, kun manta taurin kai irin na sultan, kun manta sultan idan yayi niyar abu ba wanda ya isa ya dakatar dashi, idan ke da kike mahaifiyar sa kin masa magana bai ji ba saboda me xai ji maganar fu'ad.

Sultan xinari ne ko gold? Dubi yanda ku ka cika asibitin nan gabaki d'aya, yan'uwa, securities, fadawa duk papa (sarki) ya kwaso yaxo dasu, xaku bashi lafiya ne, Sultan ya wuce qaddarar ubangiji ne kome, kuna so ku nuna baku yarda da qaddarar ba har kuke d'orawa fu'ad laifi, loosing memory ba yana nufin rasa rayuwa ne ko kuma baxai dawo normal ba xai tabbata haka, results d'in sa basu gama fitowa ba ballantana muyi saurin yanke hukunci akan abinda bamu da masaniya akan sa.

Kafin case d'in sultan, yarinya aka kawo min sa'ar yasmeen she was raped by unknown person, she is just 10years, yarinyar har yanxu bata dawo hayyacinta ba, marainiya ce bata da uwa, makauniya ce kuma bata da idanu, a yau ta rasa mahaifinta ta rasa gatan ta dalilin abinda ya faru da ita a jiya, dukan ku anan should think and put yourselves on her shoes idan kune ita ya xaku d'auki rayuwa, da wane hannu xaku karbi sabuwar rayuwar da xaku fuskanta a yanxu, she have nothing else, to hakane a gurin sultan shima ya fuskanci sabuwar rayuwa babu abinda yake buqata a gurin ku yanxu kamar addu'a, sultan yaro nane baxan barshi haka ba, xan nema masa lafiyar sa ko a ina ne a duniyar nan, kowa yaje gida, papa kayi haquri kaje gida sultan xai sami sauqi.



*littafina na kud'i ne idan baka biya ba pls kada na karanta*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*




Haske writers Association






?Fertymerh Xarah=???




11





Duk gurin jikinsu yayi sanyi, wace yarinya ce wannan, waye wannan ya cutar da ita haka.

Sarki yace ba inda xanje sai naga farfad'owar jikana kuma sai na saka an hukunta duka mutanen wannan qauyen dalilin wannan abin da suka ma sultan.

Merah yace a'a papa kada kayi haka idan basu bane fa, idan kuma acikin mutanen da suka je party tare ne fa, ko kuma idan wasu mutane daga wani wuri ne daban suka masa haka ba, meyiwuwa akwai abinda sultan d'in yayi har aka masa wannan hukunci dan Allah kayi haquri ka miqa lamarin ga ubangijin mu yafi kowa sanin dalilin wannan abin.

*

Shigowar Dr mera yayi dai dai da farfad'owar ta cikin qara mai raxanarwa wadda ke nuna a tsorace take, sai matse qafafunta take tana qoqarin sauka daga gadon, da sauri ya qarasa gurin ta ya riqeta gam, wannan riqon da yayi mata ya qara tsorata ta, ta Saki wata qara mai firgitar wa tana qoqarin barin jikin shi.

Hidaya...... Hidaya.... Ya soma kiran ta da kakkausar murya, tayi shiru tana sauraren muryar kamar ta taba jinta.

Tace baffana... ni baffana.

Dr fulani ta shigo dakin da sauri tana kallon merah, ihun ta na jiyo dama nayi tunanin ta farka.

Ta qarasa tana kiran hidaya menene cikin pullo

Tace Toi baffa am (ina baffana)
Fulani tace Baffa yahi wartime (baffa yaje ya dawo)
Tace Yaram e mako ( a kaini gurin sa)

Fulani xatayi magana mera ya katse ta is better kina yi kina koya mata hausa duk abinda xaki ce kina nuna mata shi da hausa, duk sanda bakya nan ban san ya xamuyi da ita ba.

Kaima kaso xancen likitan, inaji kaima d'in bafillace ne amma kace baka ji.

Yayi murmushi kad'an yace kad'an nake ji kuma ban iya mayarwa ba so kinga akwai gyara.

Hidaya ta riqo hannunta tana fad'in likita ki kaini inda baffana, baffana ya tafi ya barni tun jiya ban ganshi ba, yaje birni xai siyamin magani, ni ban ganshi ya dawo ba kuma dare yayi sosai sai naje neman sa, wani ne ya d'auke ni ya kwantar dani a hanya ya cire min xani ya saka min wani abu cikin fitsari na, akwai ciwo har yanxu akwai ciwo, ta fashe da kuka tana qoqarin nuna mata.

Kwalla ta taru idanun fulani cike da tausayin yarinyar, ta riqe hannunta tana girgixa kai kamar tana ganin ta, ba sai kin nuna min ba hidaya ai nagani ma Allah xai saka miki ko waye yayi maki wannan abin.

Ta juya tana kallon mera tayi masa bayanin komai da hidaya ta fad'a, ya xauna a hankali kusa da hidaya yana riqo hannunta, ta fisge da sauri cikin yanayin tsoro tana matsawa a hankali.

Likita waye shi wannan, kice yayi haquri kada ya qara sakamin.

Wannan likita ne wanda yayi magana da baffa har yace xai gyara miki idanu.

Hidaya ta qarasa gurin sa da sauri tana kuka, likita wani ya samin wani abu anan duba kagani tayi qoqarin bud'e masa ya hana ta duk da bai fahimci maganar ta ba amma ya lura tana fad'a masa ne, ya shafa kanta tare da rungumeta sosai a jikinsa, yana jin tausayinta ta ko ina ajikinsa, xai karbe ta hannu biyu ya riqeta amana, yayi alqawarin xame mata gata da farin ciki a rayuwarta kamar yanda xai riqe amira da yasmeen.

Haka hidaya ta tsinci kanta cikin nutsuwa bata san dalili ba amma xuciyarta na kwadaituwa da son jin muryar baffanta da d'umin jikin sa kamar ko yaushe.

A ranar Dr fulani ta xauna tare da ita, tana koya mata yaren hausa kad'an kad'an wanda xata iya ganewa.

Kusan sau biyu yana leqa d'akin da sultan d'in yake kwance amma har lokacin bai farfad'o ba, yayi xaune gabansa yana kallon sa yanda ya koma kamar bashi ba cikin lokaci qanqani, me sultan yayi haka me xafi da xaa masa wannan hukunci, su waye suka aikata, a iya sanin sa sultan baya huld'a da kowa a garin ballantana ayi tunanin ko abokan hamayya ne, koma dai menene xai ji

5 / 26