Chapter 3 Reading Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc Arewa Novels

Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

Author :  Fertymerh Xarah Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   3 / 26

6K to 9K   out of 77.3K words

ransa yana fad'in Allah ya kyauta.

Dai dai gate din gidan su fu'ad yayi parking batare da yayi yunqurin shiga gidan ba, fu'ad bai kula sa ba ya fita daga cikin motar yana Jan tsaki, a fusacce ya qara Jan motar da qarfi ya bar unguwar.

Yanda ya shigo gidan xai tabbatar maka ba lafiya ba, cikin gidan ya nufa, akayi sa'a kowa na babban falon ya shigo ba sallama, duk suka xuba idanu suna kallon sa cikin mamaki yanayin shigowar sa.

Tafiya yake da sauri batare da ya d'aga kai ya kalli kowa a falon ba, ya saka hannuwansa da qarfi yaja rigar dake jikinsa nan take ta rabe gida biyu, yana qoqarin hawa step, Afiya tayi saurin dakatar dashi.

Kai mahaukacin ina ne xaka shigowa mutane falo haka ba sallama ballantana gaisuwa, me ya hau kanka ne haka? Yayi shiru batare da ya tanka ba,

Ba magana nake maka ba? ta fad'a cikin tsawa tana kallonsa, ya juyo yana kallonta idanunsa sunyi jawur,

Meya same ka haka, xaka min magana ne ko sai na d'auke ka da Mari yanxu.

Ya bud'e idanunsa sosai yana kallonta da kyar ya bud'a baki
Yace Mami gaban yaran can kike min ihu haka salon su raina ni.... bata bari ya qarasa ba ta sauke masa lafiyayyun yatsun ta a kuncin sa,

Wannan ce tambayar da nake maka, xaka amsa min ne ko sai na qara ma.

Ya shafi kuncin sa yana haqiye wasu yawu da kyar cikin bacin rai, ya motsa bakin sa a hankali wanda ita kad'ai ke jiyo abinda yake fad'a,

Yace ba abinda ke damuna,
Saboda wane dalili xaka shigo mana falo ba sallama, ba gaisuwa, don't you have respect for that?

Cike da bacin rai ya juya yana kallon mutanen dake falon, ina wuni ya fad'a da karfi kafin ya haura sama batare da ya qara kallonta ba cikin sauri dan kar ta samu damar dakatar dashi.

Afiya tayi shiru, ta rasa wane irin yaro ne sultan, ta juya ta qarasa cikin falon, ina ma Aiman na nan da qila xai mata maganin sa,

Yana shiga sashen sa ya sakawa qofar falon key, kana ya nufi d'akin sa, kai tsaye toilet ya shiga acan ya cire komai nasa ya wurgar, shower ya sakar wa kansa tare da lumshe idanuwansa, wannan toxarcin da Mami ta masa yayi mugun bata masa rai fiye da abinda d'an fulani yayi masa, a gaban su yasmeen da Amira xata mare sa, yanxu ya xasu riqa kallon sa?

*

Baffa naji dad'in da ka sauya min slippers d'innan, amma kaine xaka riqa min kwalliya da wadannan kayan saboda ni ban iya amfani da su ba.

Jin yayi shiru tun dax'u da take ta faman surutu ya saka ta riqo hannunsa,

Jikina ya bani akwai abinda ke damun baffa, ta matsa a hankali had'e da xama a saman qafafun sa,

Baffa meya same ka, ka gayamin naji.

Batare da tunanin komai ba ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar da ita.

Tayi shiru tana sauraren sa, abinda ke xuciyarta tabbas baxaka iya karantashi a fuskarta ba, saboda ita wata irin yarinyace da baka gane inda ta dosa, a shekarunta tabbas ta gane ko waye wannan yaci xarafin mahaifinta, meyasa ya mare sa,

Baffa kayi haquri, ka daina tunanin sa kaji, kace idan mutum na saka damuwa a xuciyarsa xai kamu da wata cuta, ni bana son wani abu ya same ka har ka barni, ta qanqamesa sosai tana hawaye.

Qamshin turaren dake jikinsa ta shaqa a hankali ta d'ago kamar wadda ke kallon sa,

Baffa wannan turaren na jikin ka fa, a ina ka samu.

Cikin son kauda damuwar dake xuciyarsa yace inaji turaren wannan marar mutuncin ne dana had'a jiki dashi, tun dax'u turaren ke damuna nima.

Ta qara shaqa turaren cikin son sanin turaren sosai,

Baffa watarana xan rama maka marin da yayi ma kayi haquri kaji.

Yayi murmushi yana kallonta, banda abin hidaya ina xaki gansa ki rama min, keda ba gani kike ba taya xaki same sa.

Tace baffa xanje na neme sa a birni, dama kasan sunan nasa ne abin xai xo min da sauqi, amma ni sai na rama ma idan na ganshi, sai na saka shi cikin damuwa kamar yanda ya saka ka, ta qara shaqa qamshin turaren tana fadi, amma baffa wannan turaren akwai dad'i ba irin namu bane, ina so ka siya min shi.

Shikenan hidaya xan nema na siya maki tunda kina so komai tsadar sa koda kuwa xan siyar da shanuwa d'aya ne na siya maki.

Kinga na tuna ma dax'u da muna tafiya tare da buba yake bani shawarar naje dake babban asibitin birnin abuja a duba idanun ki wataqila xaa dace Hidaya.

Tayi murmushi tana laluben fuskarsa, ya riqo hannunta yana taya ta murmushin kamar tana ganin sa,

Tace baffa Allah yasa xan gani a rayuwata, nayi toxali da wannan fuskar ta baffana bani da wani buri a rayuwa ta kamar wannan yanxu, ko yaushe wannan burin nawa xai cika.

Insha Allah bada jimawa ba, kiyi ta addua Allah yasa mu dace amma ni a yanxu ina tsoron sake shiga birni, baxan boye maki ba Hidaya na kasa tunanin wannan wulaqanci da yaron nan yayi min, qaramin yaro ne da bashi da tarbiya, kud'i sun gama gurbata rayuwar sa, yanxu kamar wannan yaron ya isa a datse min hannu batare da hukuma ta d'auki mataki akan sa ba.

Baffa nace xan rama maka ai, idan na fara gani xanje birni na neme sa nima xan wulaqanta shi acikin mutane kamar yanda ya wulaqantaka, xan saka shi damuwa baffa har kuka sai na saka sa dalilin wannan marin da yayi Ma.

Yayi dariya batare da ya qara magana ba yana sauraren surutun nata mai tattare da tatsuniyar gixo abin ka da yaro ta inda xata je neman mutumin da bata sani ba, bata san kalar sa ko muryar sa ba har taje rama masa marin da aka masa.

Hidaya tayi lamo a jikinsa tana shaqar qamshin turaren da ya gama xama a kwakwalwar kanta fiye da tunanin mai karatu a hakan barci yayi awon gaba da ita.
[11/20, 10:20 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=???



7




2days.......


fu'ad yana gidan tare da sultan a d'akin sa.

Man wannan yarinyar fa ta matsa akan ka ta dame ni.

Wace yarinyar fa,
Wannan yarinyar mana da muka had'u a gurin party jiya kuma na gayama ai na santa sosai a skul din mu.

Mtsew sultan yaja dogon tsaki yana cigaba da chatting din sa kafin yace, na rasa meke rud'a ku akan mata, na rasa dalilin da yasa kuke kasa samun nutsuwa a duk lokacin da idanun ku suka yi toxali da mace, musamman ma Qaseem, ni babu wannan macen da xata rud'a ni a rayuwata.

Fu'ad ya tabe baki kafin yace, saboda xuciyarka har yau bata da nutsuwar da xata duba Ma wacce ta dace da kai ne shiyasa kake wannan tunanin, mata ai abin so ne, kai nifa at this age wlhy idan xaa min aure ina so I don't care.

Aure? Sultan ya maimaita yana kallon sa da mamaki, aure yanxu at 20, kayi me da auren ko xaka xauna matar tayi rainon ka ne?

Fu'ad yayi murmushi yana kallon sa, yayi qasa qasa da murya kamar wani xai jiyo su, aure fa akwai dad'i kasan me yasa, yesterday I made my first kiss, so sweet, ashe haka abin yake, ni fa ban taba xuwa party da ya min dad'i kamar na jiya ba,

Sultan ya tabe bakin sa yana fad'in wai kaji dad'i, kana murna da yin hakan kenan, you are right, is better ayi ma auren nan da wuri kafin ka janyowa family din mu abin kunya a duniya.

Fu'ad ya bata rai, baxaka gane me nake nufi ba, just try it once kaji, nifa ban taba sanin haka ake ji ba, gsky aure nake so.

Hmmm chab, ni aure yanxu Allah ya kiyaye, soyayya ma I don't have time for it talk less of marriage, babu yarinyar da xanyi wa rawar jiki haka, just look at you kamar wani mahaukaci sabon kamu, kiss kawai kayi kaxo kana hauka anan, ni ka kyaleni da wannan shirmen naka pls.

Naji na bar wannan maganar, muyi maganar yarinyar Ziyada, ta had'u itama akwai aji g... Sultan yayi saurin katse sa, babu aji a gurin macen da duk ta furtawa namiji so kafin shi, wannan ba kalar macen da ta dace dani bace.

Wace kalar mace ce ta dace da kai fu'ad ya tambaya cikin fusata,

Ina son mace same age dani ko na bata 2 to 3years haka, doguwa kamar ni, chocolate colour ba fara ba, mai gashi, manyan idanu, marar jiki haka kamar jikin yasmeen is ok, wadda tayi xurfi acikin ilimin boko cos ni da na had'a master's d'ina ba abinda xanyi da kwallin, na fison kwallon nan fiye da komai a rayuwa ta yanxu,? before nake gudun ta but for now ba abinda yake da muhimmanci a gurina kamar ita, and again ta kasance yar babban gida bana son na auri mace gidan su ba kud'i taxo tana min kwadayi da sata a gida, wani abu da baka sani ba game da auren yar talaka kakakaf lalurar dangin su duk kaine, bayan sata da xaa rinqa yi ma a gida har kashe ka mace zata iya saboda ta gaji dukiyar da ka tara.

Fu'ad yace kai man, ni duk wannan lissafin da kake banji kace kana son mace mai nutsuwa da tarbiya ba, yar gidan mutunci, nifa wlhy komai talaucin mace da lalacewar gidansu indai tana da tarbiya tana da ilimi, ga kyau, ga gaba ga baya ba abinda xai hana min auren ta, ina son mace mai boobs suna matuqar burgeni sosai.

Ni na auri yar gidan talaka har na xauna da ita Allah ya tsare ni na kawo mutuwa gidana, kai me kasani acikin rayuwa banda kiss ka rungumi mace what else kuma ka sani, relax maxa babu abinda ya kai kud'i mutunci da daraja a rayuwar nan, sannan babu abinda kud'i baxai iya yi ba, kaga jiya yanda mutane ke rububin ganina, kowa yana so yayi pic da d'an wasan kwallon nan but I was afraid with them bana so ina had'a jiki dasu cos mutanen qasar ku ba amana.

Fu'ad ya tashi yana fad'in, akwai abinda kud'i baxai iya siye ba sultan, akwai abinda kake so da qauna kake burin mallakar shi da dalolin kud'in ka amma baxaka iya samun sa ba, ni na gayama haka.

Naji malam fu'ad, Mr kisser, sai kuma yayi murmushi yana kallon labban fu'ad.

Wai wace irin mace ce wannan har ka yarda ka had'a baki da ita, nifa yanxu na soma kyankyamin ka saboda kowa a gurin ka, ka d'auke shi tamkar kayan sakawar ka, ni ina son xama da mutum da ya san kansa sosai banda kai cousin d'ina ne da tuni mun raba hanya da kai.

Wanda yayi nisa baya jin kira, Allah ya shirye ka, ni xan sauka qasa ina so naga Amira.

Ka jirani xamu je asibiti yanxu, dad yana nemana tun dax'u.

Fu'ad ya fice yana fad'in idan ka shirya ina jiran ka.

Sultan ya d'auki wayoyin sa da key na mota ya sauka, tunani yake yau basu yi magana da Mami kan maganar tauraruwar sa ba, kwanan nan biyu ta daina kusanto shi ko me hakan ke nufi, sai kuma ya tabe bakin sa.

*

Farin cikin dake d'auke a xuciyarta a yau baxai misaltu ba, a duk lokacin da baffa ya kalli fuskarta yaga wannan murmushin a tare da ita ya kan rasa inda xai saka kansa saboda jin dad'i.

Duk wannan farin cikin naki nine na saka ki haka, ina so na xama sanadin farin cikin ki a koda yaushe matuqar ina Raye.

Tace ina so na saka baffana farin ciki kamar yanda yake sakani a koda yaushe, farin cikin sa shine nawa.

Hakane hidaya, ina so kiyi karatun boko ki nemi ilimi ta kowane bangare, ina son duniya tayi alfahari dake, kinga nan qauye ba kowa ke karatun boko ba, nima ba dan ina shiga gari ina ji da gani ba baxan San amfanin sa ba, ina so ki xama malamar makaranta mai koyarwa, mutane su sami ilimi ta hanyar ki hidaya, ki cika min wannan alqawarin.

Ta tunxuro baki tana make kafadar ta, baffa ni baxanyi wani karatun boko ba aure xanyi, Asiya ta gayamin aure xaa yi mata, haka ma dije aure xatayi sai ni kad'ai kake so nayi ta xama.

Ya tsura mata idanu cikin mamaki kafin yace menene auren hidaya?

Tayi shiru tamkar mai naxari kafin tace nima ban sani ba baffa amma naji suna fad'a xasu yi aure su barni da samarin su, ni waye saurayina baffa, ko ni bani da mai sona ne.

Babu mai son ki a wannan halin da kike ciki, ke baki san aure da abinda ke cikin sa ba hidaya, ni bani d'aya daga cikin mutanen dake aurad da ya'yan su da wuri, karatu nake so kiyi ki fito daban da kowa a qauyen nan ki xamo abin kwatance a gurin kowa ki cire mgnr aure a xuciyar ki yanxu.

Ni baxan cire ba baffa, nima sai kamin aure kamar su Asiya nayi sabon gida da sabon d'aki.

Murmushi yayi yana kallonta kafin yace tashi mu tafi idan kin gama shan furar, bana so lokaci ya qure mana bamu isa da wuri ba.

Ta tashi da sauri tana neman inda ta jingina sandar ta, tace a yau karo na farko xanje birni, idanuwana baxa su ga komai ba, sai dai zan jiyo qamshi da sautin birni, a hakan ma na godewa Allah sosai na kuma godewa baffana, baffa xamu je babban asibiti ne.

Eh wanda aka kwatanta min kenan, ya riqa hannun ta suka fito daga gidan kana ya rufe suka tafi.?
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=???

8

Kusan minti talatin da xuwan su office d'in amma Dr mera bai kula su ba, sai ta kan patients d'in sa yake.

Suna xaune, wata mata ta shigo tare da wata budurwa a bayanta, kallo d'aya xaka masu ka tabbatar kud'i sun xauna a gurin su tun daga yanayin suturar dake jikin su,

A hankali budurwar ke bin office d'in da kallo kafin ta sauke idanunta akan su fu'ad dake xaune, cikin murya qasa qasa ta dubi maman ta,

Wow, mom kinga wasu guys acan sun had'u wlhy, maman ta juya tana kallon su.

Yarima dake xaune caraf yaji abinda yarinyar ta fad'a ya maida hankalin sa gurin su sultan, abu suke kallo a waya Sam hankalin su Ma baya gurin.

Maman ta xauna tana murmushi sanin yarima, likitan tane sosai indai yana garin, sun san juna, cikin sakin fuska suka gaisa yake tambayar ta ko jikin ne,

Tace aa Hafsat na kawo, ya juya yana kallon yarinyar cikin d'aure fuska, yace meke damun ki.

Wata kunya da nauyi taji, ta saci kallon su sultan da har yanxu basu san da xaman ta a gurin ba kafin ta kalli mahaifiyarta, mom ki gayamasa da kanki ni baxan iya ba.

Murmushi matar tayi kafin ta soma yiwa Aiman bayanin yanda tayi mata bayani kafin su xo.

Kai tsaye yace infection ne ke damun ta,

Infection d'in da suka ji an kira ne ya saka su d'agowa suna kallon mutanen dake xaune a gurin aiman.

Dr yace Hajiya kuje da ita gurin Dr iman ko Dr fulani ki gayamasu ni na turo ki, idan yarinyar tana discharging duk ki fad'a masu. Yayi hakan ne saboda su sultan dake gurin.

Suka tashi, Hafsat ta kasa daurewa ta dube su cikin murmushi tace hey... tana d'aga masu hannu.

Sultan ya dauke kansa kamar bai gani ba, fu'ad kuwa murmushi yayi ya d'aga hannu har xaiyi magana suka had'a ido da yarima yayi saurin mai da hannun yana washe baki.

Matar har xata fita ta juya tana kallon mera, tace Dr waye yaron ka acikin su da nake jin labari,

Batare da ya nuna mata ko d'aya daga cikin su ba, yace duka ya'ya nane kuma jinina.

Cikin rashin fahimta tace su d'in twins ne, amma akace yaron ka d'aya ne dake Phoenix.

Cikin qaguwa da tambayar nata dan da ba dan ita bace baxai kula ta ba ya nuna mata fu'ad yace wannan ne firstborn nawa shi na fara gani kafin wannan, ya nuna mata sultan yace shi kuma yaron sister d'ina ce Rumaisa kinga duka jinina ne babu banbanci,

Hakane kam masha Allah, kyawawa dasu, Allah ya inganta rayuwar su.

Yace amin, suka fice.

Dad wane ciwo ne infection kuma yaji muryar fu'ad na jefo masa tambayar.

Daga sultan har mera kallon sa suke kafin yace meyasa kake tambaya.

Ba komai saboda mu kiyaye da ciwon ne muma kada mu kamu da cutar ko ba haka ba sultan ya fad'a yana kallonsa.

Sultan yayi saurin gyad'a kansa yana murmushin yaqe cike da haushin fu'ad.

Mera yace wannan ciwon mata sun fi kamuwa dashi kuma mafi akasarin ciwon rashin tsabta ne a gurin.

Gurin ina? Suka tambaya lokaci d'aya suna xaro idanun su cike da mamaki.

Kallon su yayi cike mamaki sai kuma yaja dogon tsaki yace ba wannan na kira ku ba, sultan nan da 2wks ka shirya xaka koma Phoenix lokacin resuming School d'in ka yayi beside ma an kira ni akwai wasar da xaku gudanar tare da yan Germany.

Wani tsalle sultan yayi cike da farin ciki kafin ya xagaya ya rungume mera, thank you dad, I so much love you, wannan qasar kamar akan qaya nake.

Murmushi kawai mera yayi kafin yace kuna iya tafiya ina da ayyuka a gabana yanxu.

Suna fitowa fu'ad ya dubi sultan yana fad'in man sai wani nishad'i kake ni fa yarinyar nan ta min kyau sosai amma abinda ban fahimta ba duk gayun nan nata ace bata da tsabta, wane guri ne a jikinta wanda bata kula dashi.

Mtsew sultan yaja tsaki yana fad'in ni fa saboda ya xama dole ne nake yawo da kai wlhy amma Sam baka da class, qaseem ma ya fika wlhy, you are not my type.

Kai fa sai ana maganar mutunci ka sako

3 / 26