Chapter 13 Reading Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc Arewa Novels

Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

Author :  Fertymerh Xarah Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   13 / 26

36K to 39K   out of 77.3K words

fice a fusacce idanunta cike da kwalla.

Yasmeen ce ke kai da kawowa a falon ita kad'ai tana wasa, hidaya na kwance tana kallon ta, kwanakinnan duk haka take xama babu walwala ko sukuni a tare da ita, xuciya da gangar jiki sun saba tarayya da abokinta ba qaramin abu xai saka ta manta shi lokaci d'aya ba kamar yanda yake hantara da nuna mata kyama a yanxu ba, ta ga yasmeen ko kad'an bata damu dashi ba ko meyasa, saboda kawai ta ture shi yake ta fushi da ita haka xata bashi haquri tace baxata qara ba yaxo suci gaba da rayuwar su suna wasa tare.

Meke damun ki hidaya duk kin canxa kwana biyu d'innan ko baki da lafiya ne?

Sai ta girgixa kanta hawaye na xubowa daga idanuwan ta.

Afiya tace to menene harda kuka, kunyi fad'a da yasmeen ne ko su amira sun qara dukan ki.

Nan ma ta girgixa kanta kafin tace yaya sultan baxai xo muyi wasa ba.

Tace baxai xo ba hidaya, ki manta dashi ki Saki jikin ki kamar farko ga yasmeen ta ishe ki wasa, sultan d'in da kika sani before wannan bashi bane, bana gayamiki lokacin bashi da lafiya bane shiyasa, yanxu kuma ya sami lafiya baxai taba xama acikin ku yayi wasa ba ki manta dashi kamar yanda kika ga yasmeen tayi.

Tace to yaushe kuma xaiyi wata ras???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?hin lafiya.

Afiya tace har abada insha Allah wannan cutar baxata qara dawo masa ba ko wani jinin sa, nace ki manta dashi ai ko.

Sai ga hawaye sharrr, tasa hannu tana gogewa Afiya taji tausayin ta sosai, yaro da sabo sai ta soma rarrashin ta, lokaci yayi da aiman ya kamata yayi mgn akan raba auren yaran tunda an sami abinda ake so, tasan ko banxa dama sultan baxai taba son hidaya ba.

Qamshin turaren da taji ya saka ta d'agowa da sauri, idanunta sai a cikin nasa, ta taso da sauri ta nufe sa tana share hawayen fuskarta tace kayi haquri baxan qara ture ka ba.

Ya tsura mata idanu cikin takaici kafin yace ke wane irin naci ne dake haka, are you stupid?

Hidaya ta girgixa kanta, yace idan kika qara gani na kika nuna kin sanni sai na tattakaki a gidan nan.

Ta langabar da kanta tana kallonsa tace shikenan baxan qara yi ma magana ba, amma ka gayamin wannan turaren a ina ka same shi.

Cikin takaici da bacin rai yace gidan uban ki na sato, ta nuna sa da yatsa tana fad'in kenan.. kenan kai ne ka mari baffana?

Kashe shi nayi, waye baffan naki, me yake dashi gayamin wane mulki ko muqami yake dashi a qasar nan.

Waye baffana nima ban sani ba amma idan ya dawo ya tabbatar min da kaine ka mare sa nima baxan barka ba sai na mare ka sai nayi ma wulaqanci irin yanda kayi masa, ta juya xata fice cikin bacin rai ya fincikota tana juyowa ya d'auke ta da mari sai da glass d'inta ya fita idonta, ya jefar da ita qasa kamar kayan wanki, a tsorace Afiya tayi kanta cikin tashin hankali duk abinda yake aiman na tsaye yana kallon sa tuntuni ya dad'e da shigowa, juyowar da xaiyi shima ya d'auke shi da mari karo na farko a rayuwar sa.

Cikin rud'ani da mamaki yake kallon mahaifin nasa kada dan ya daki wannan banxar ne ya mare sa.

Da yatsa ya nuna masa ita yace daddy saboda wannan?

Yace kwarai da gaske fiye da wannan ma sai in yi ma idan ka qara gigin d'ora hannun ka akan jikin ta da sunan duka, kasan wacece ita, kasan muhimmanci da gudumuwar da ta bawa rayuwar ka, kasan yanda yaro yake son kasancewa da mahaifiyar sa haka ka kasance tare da ita, komai hidaya, motsin ka hidaya, numfashin ka hidaya, itace mutum ta farko da ta soma saka ka murmushi a gidan nan, farin cikin ka, damuwar ka, kukan ka, warakar ka duk yana xuwa ne ta dalilin wannan yarinyar, banda ma wannan menene laifi dan yaro ya nuna yana son xama da kai, qanqanuwar yarinya kamar wannan bata cancanci irin wanna duka daga gare ka ba, ashe yasmeen ma xaka iya mata haka, just look wannan CCTV camera ce akwai a dakin ka, akwai a d'akin yasmeen harabar gida kaje ka kalli rayuwar da kayi tare da yarinyar da ta xame ma tamkar uwa a gidan nan, kuma daga wannan lokacin ko kallon ta kayi wanda bai gamshe ni ba sai nayi mugun saba ma useless ya juya ya fice.

Hidaya ta janye jikinta daga na Afiya, bata qara kallon sa ko kallon inda yake ba d'akin su ta nufa cikin xafin rai tana jin tsanar sa har cikin xuciyarta.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=???

26

Afiya ya tsurawa ido yana kallonta kamar mai neman qarin bayani a gurinta, ya kasa yarda da maganganun mahaifinsa yana ganin kamar ita kad'ai ce zata ce a'a ba haka bane ya yarda, amma sauyin da ya gani tattare da fuskarta ya qara tabbatar mashi da gaske ne kenan.

Kaji kunya ta fad'a tana watsa mashi wani kallon, ya sunkuyar da kansa cike da takaici.

Tace Mami hidaya nono insha ka manta da wannan.

Ya d'ago da sauri yana kallonta cikin rashin fahimta, nono ya sha nonon wa kenan, me Mami ke nufi, ya juya ya fice daga gidan gabaki d'aya cikin takaici.

Duk yinin ranar hidaya a d'aki tayi sa bata qara leqo falon ba sai da Afiya ta aika kiran ta,

Fu'ad ya dube ta duk tayi sanyi kamar ba wannan hidayar mai haba haba da kuxari da son wasa ba, yace xo xauna nan hidaya xo gayamin waya taba ki haka kike ta fushi nayi maki maganin sa ko waye kuwa a gidannan.

Kallon sa tayi kamar xatace yaya sultan sai kuma ta fasa ta daina damuwa da shi da al'amuran sa, bata son sake maganar shi ko kuma wani abu da ya shafe shi.

Tace ina so naga baffana har yau yaqi ya dawo, yaushe xai dawo.

Afiya tayi caraf tace ko jiya baffa ya kira kina barci hidaya yace a gayamiki ya siya maki wata qatuwar saniya madarar ta akwai dad'i idan ya gama tara kud'in da yake so xai dawo bada jimawa ba.

Hidaya ta fad'ad'a murmushin ta, fararen haqoranta suka bayyana tana jin wani farin ciki yau a tare da ita, kallon Afiya take dauke da murmushin da ya fito daga qasan xuciyarta.

Tace Mami yaushe xai tara kud'in kuma me xaiyi dasu.

Afiya tace yana so ya tara su da yawa ya siya maki sabon gado da katifa idan xaki je gidan aure.

Ta tunxuro baki tana bata fuska ni baxan yi aure ba ni yanxu bana son sabon gida da sabon gado, karatu yana da dad'i.

Fu'ad ya soma dariya itama Afiya dariya tayi tana fad'in auren Ma akwai dad'i my dear, amma nima nafi so kiyi karatun ki.

Hidaya tace Mami idan ya kira anjima ko nayi barci ki tadani ina so naji muryarsa ina so na gayamasa yanxu ina gani kamar kowa.

Afiya ta jinjina kanta kawai tana kallon ta.

Daga nan suka fice tare da fu'ad xuwa harabar gidan.

*
Da gudu yake Jan motar kamar wanda xai tashi sama, idan ya tuna jiya daddy ya mare sa akan wannan yarinyar ji yake kamar ya d'auke numfashi ya bacewa duniyar gabaki d'aya, yau acike yake da fushi mai tsanani, gab da xai sha kwana yaja uban wani birki ba shiri keeeeey saura qiris ya bige dattijon dake tafiya a gefen hanya.

Fitowa yayi daga cikin motar cikin izza yana kallon mutumin a wulaqance yaji me xai ce.

Mutumin baki a bud'e yake kallon sa kafin yace yaro baka gani ne, meyasa kuke tuqin gaanganci ne, yanxu da ka bige ni haquri kawai xaka bawa iyalina.

Sultan ya xare madubin idanun sa yana kallon sa, ni nayi ma kama da wanda ke bada haquri, wait ma wannan hanyar ta mota ce bata qafafu ba, kana tafiya akan titi kamar kana tafiya acikin gidan ka, ka godewa Allah na ankara da sai dai ka farfad'o a asibiti idan kayi rai kenan.

Mutumin ya tsura masa ido, ina yasan wannan fuskar kafin yace a ina ka taba jin hanya ta xama ta mota kawai, wa ya gayama haka ake rayuwa, ka shiga haqqin mutum... Sultan ya katse sa a fusacce

Dalla malam rufe min baki nasan me kake so, kwadayi ne ke damun ka, dama ku talakawa ba abinda kuke so irin masu kud'i su bige ku saboda a d'auki nauyin ku, kada ka damu duk da ban bige ka ba, baxaa rasa baka wani abun ba, ya juya cikin mota bandir na hamsin ya d'auko ya jefawa mutumin yana kallon sa sama sama.

Kallon kud'in mutumin yayi kafin ya dube sa, oh kaico duniya, kaico da abinda ke cikin duniyar, yaro kabi duniya a sannu da kasan ko waye ni d....

Waye kai? Sultan ya tambaya yana qara kallon sa sama da qasa, waye kai nace, me kake taqama dashi, wane mulki ko muqami kake dashi a qasar nan ko kana da sarauta ne? Amma ni kasan ko waye ni? Kasan waye ubana a garin nan dama wasu qasashen a waje? Kasan qarfin ixxarsa, mulki da sarautar sa? Kasan su waye kakannina guda biyu kuwa, abin kunya ne ma a gurina a ganni ina magana da kai, mtsew dirty old man, ya shiga motar ya tada, sauke glass d'in yayi yana qara kallon sa a wulaqance, xaka kauce ka bani hanya ne ko sai na bi ta kanka na wuce, ka tsaya kana kallona sai kace baka saba ganin fararen fata ba mtsew.

A hankali mutumin ya matsa gefe, sultan yaja motar da qarfi.

Yana isowa gida duka yaran suna falo kallo suke, suna ganin sa suka soma yi masa yaya sultan sannu da dawo wa, ba wanda ya amsa mawa kamar xai shige d'akin sa sai ya lura yarinyar can ko kallon sa batayi ba ballantana ta masa sannu da xuwa kamar sauran.

Ke kin fi qarfin ki gaida nine ya fad'a yana kallon ta, hidaya tayi shiru bata amsa ba kuma bata d'ago ta dube sa ba amma a tsorace take dashi sosai.

Ba dake nake magana ba, ya fad'a in a lion voice, ba shiri cikin tsoro ta d'ago dara daran idanuwanta ta xuba akan nasa,

Tace kayi haquri, kasancewar tau babu glass a idanuwanta sai yaga ta masa kyau sosai ko dan yau ya soma tsaya ya kalle ta da kyau ne oho, bai qara kulata ba ya juya ya fice.

Yasmeen tace baki ce masa sannu da xuwa ba,
Hidaya tace baxan ce ba shiyasa nace yayi haquri ba yace na daina masa magana ba shi meyasa yake min, ko ya dawo muyi wasa dashi baxan qara yi dashi ba, baxan qara cin abinci ko barci dashi ba, sai dai ke kije kiyi dashi.

Amira tace xaki ci uban kine idan kika bari yaji kina fadar wannan, ke bakin ki bashi da control ko.

Salwa tace kyale ta ni so ma nake tayi masa abinda xai dake ta.

Hidaya ta dube su tana fad'in idan ya dake ni ai daddy xai rama min, ko ranar ya rama min da ya mare ni, ta tashi ta bar masu falon sanin idan ta matsa da magana xasu iya kai mata rankwashi a kai.

Ya kai qoluluwar tunani ya rasa mafita game da abinda iyayen nasa suka fad'a game dashi da hidaya, meyasa ya damu da son sanin irin xaman da suka yi, ta ya akayi ta shigo rayuwar su ina daddy ya same ta shin ita wacece su waye danginta?

Da kyar ya lallashi xuciyar sa ya yarda ya xauna ya kalli rayuwar da yayi a baya.

Tun farkon shigowar sa gidan bayan lalurar da ta same sa har xuwa sanda daddy ya shigo da yarinyar bla.. bla..

Ido da hanci ya Saki yana kallon komai tamkar a film, ya maida hankali da tunanin sa kacokan kan kallon rayuwar sa da abokannan nasa guda biyu, ya ilahi is that me, ni sultan, wayyo Allah ya furta qasan maqoshin sa.

Tun abin baya burgeshi sai ga sultan na murmushi, wani gu kuma yayi dariya, haqiqa wani nishad'i yake ji yana sauko masa a xuciya har baya son motsi ko kad'an.

Wayar sa dake ringing ya jawo a fusacce batare da ya duba mai kiran ba ya kashe tare da cillata can saman gado ya cigaba da kallon da yake.

Baya tunanin ko xaya shekara yana wannan kallon xai gundure sa, bai taba ganin muhimmanci CCTV camera dake recording komai ba kamar yau.

Kiran sallah da akayi ya ankarar dashi daga xurmawa a kallon da yake, kamar baya so ya tashi a gaggauce ya nufi toilet, yau baya jin xai iya sallah a masallaci tabbas a d'aki xaiyi a yanda yake gani idan ya fita kamar baxai dawo ba, yana gama sallah ya dawo ya xauna jikinsa har rawa yake.

Innalillahi she saw me naked>?&?
B&? ya dafe goshin sa, oh Allah wannan yarinyar taga girmana, tasan ko ni waye, duk d'aure fuska da nake ina hargowa she knows who I am, why sultan meyasa kake fitowa naked don't you have manner baka ga yanda daddy kullum yake d'aura ma towel ba kafin ka fito gashi kasa qanqanuwar yarinya ta gama sanin girman ka.

Tagumi yayi yana cigaba da kallon, bai tashi daga wurin ba sai daya gama kallo duka kaf, jikinsa yayi sanyi sosai, tausayin kansa dana yarinyar sun shige sa, meyasa yake haka meyasa yayi mata haka tabbas baiga laifin yarinyar dan ta nace mashi a yanxu ba, shekarunta baxasu bata komai na game da rashin lafiyar sa ko akasin haka ba, tana masa kallo d'aya ne na FRIEND abokin wasarta.

Ya tashi da sauri ya fita d'akin aiman ya nufa, kallo d'aya yayi masa ya dauke kansa daga gare sa.

Am so sorry daddy for everything, yaje ya kwanta a bayansa yana fad'in ina son nasan wacece ita, asalinta, and everything about her, I promise baxan qara abinda nayi a baya ba, ita da Yasmin will still remain my friends.

Aiman ya jawo sa ya xaunar dashi gabansa yana kallonsa kafin yace, hidaya sunan ta kamar yanda ka sani, she is 10years kamar Yasmin, na fara sanin ta sanda suka xo da mahaifinta lokacin bata gani... Nan merah ya bashi lbr komai game da ita sai dai bai gayamasa fyaden da aka mata ba ya boye wannan.

Sosai yaji tausayin ta, wannan shine karo na farko da sultan ya taba jin tausayin wata mace a xuciyar sa bayan mahaifiyar sa, ko qannensa bai damu dasu da sha'anin su ba, da su da babu duk d'aya ne a gurin sa.

Da dare duk sun hallara dinning amma banda hidaya da yasmeen sai da Afiya taje kiran su, aikuwa da gudu suka shigo falon daga d'akin su, yasmeen kusa da Afiya ta xauna, hidaya ma ta xagaya inda mera ta xauna kusa da shi, bata qara tunanin xama kusa da sultan ba, tun da taje gurin bata d'aga kai ta kalli kowa a gurin ba bayan yasmeen da suke tsokanar juna idan sun had'a ido.

Sultan kallo d'aya yayi mata bai qara kallon ta ba, salwa tayi serving kowa a wurin kafin suyi bismillah su soma ci.

Sultan ya d'ago ya dubi hidaya sai kuma ya maida kallon sa ga yasmeen yana fad'in, ke xo nan muci abincin tare.

Yasmeen ta dube sa da mamaki, tace ni yaya, yace yes

Ta tashi ta d'auki plate na abincinta ta nufi gurin sa, ture nasa yayi gefe ya saka spoon nasa suka soma ci, su salwa kallon mamaki suke masa, hidaya kuwa tun da taji muryarsa tasha jinin jikinta saboda wani irin tsoron sa da take ji tun marin da yayi mata, ko kad'an bata d'ago ba ta cigaba da cin abincin ta.

Shi kuma yayi hakan ne saboda jawo hidaya d'in a jikinsa, yayi tunanin itama xata ce xata ci tunda yaga yarinyar akwai surutun tsiya sai yaga sabanin haka, yasmeen kuwa sai jin dad'i take tace hidaya look, me and yaya sultan.... bata bari ta qarasa ba ta miqe tana ture plate d'in gabanta ta sauka daga dinning d'in tayi hanyar d'aki.

Ke ina xaki je har kin gama cin abincin ne.

Ta juyo tana kallon ta fuska a shagwabe, tace na qoshi Mami bana jin yunwa sosai d'axu mun sha oat ko yasmeen ta fad'a tana kallon ta, yasmeen ta gyad'a kai tana kallon Mami cikin tabbatarwa.

Afiya tace is ok, aje a sauya wannan kayan a saka na barci kafin na xo.

Hidaya ta gyad'a kai kawai batare da tayi magana ba ta fice.

Ayi haquri da wannan pls>?&?
@&?
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tangama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=???

27

Washe garin ranar suna gama shirin School suka nufi dinning, su hud'u ne kawai yan makaranta masu breakfast d'in, kowa ta gabansa yake batare da ya damu da d'an uwansa ba saboda suna gab da makara basu tashi da wuri ba.

A gaggauce suka kammala lokaci d'aya suka miqe, masu d'aukar food flask suka d'auka, masu d'aukar jaka suka d'auka suka fice da sauri.

Ko da Afiya ta fito tuni sun dad'e da ficewa, sai ta nufi kitchen had'awa Aiman breakfast, qamshin turaren sa ya saka ta juyawa tana kallon qofar kitchen d'in, yana tsaye cikin fararen kayan barci da nayi matuqar yi masa kyau, hannunsa na hagu akan idon sa yana murxawa a hankali.

Morning Mami, ya fad'a a hankali in a cool voice.

Tace mrng an tashi lafiya?

Not that well Mami ya fad'a yana qarasawa cikin kitchen d'in.

Mariya mai aiki tana ganin sa ta soma gaidashi, ba tare da ya amsa ba ya dube ta a yatsine kamar wanda yaga kashi, ya nuna mata hanyar qofa yana fad'in will you excuse us.

Ta xo wucewa ta gabansa, ya watsa mata wani kallo da yasa tabi ta bayansa ba shiri jiki na rawa, cike da damuwa ya riqa duka hannayen ta yana kallon ta, ita ma shi take kallo.

Mami wannan tauraruwar na daina ganin ta kwata kwata a

13 / 26