Chapter 23 Reading Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc Arewa Novels

Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

Author :  Fertymerh Xarah Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   23 / 26

66K to 69K   out of 77.3K words

iyakar xaman kenan babu saura tund....tayi saurin katseta cikin tashin hankali.

Ke fa banxa ce wani sa'in baki san rarrashi ba sai baqar kafuwa, wai meyasa kike hakane tunanin ki yaya sultan baya gayamin duk wulaqanci da kike masa, tell me hidaya did my blood brother deserve duk wannan abin da kike masa.

Hidaya tayi shiru cikin dabircewa sanin halin yasmeen tace nidai kiyi haquri.

Tsaki yasmeen ta ja ta tashi xata fita daga d'akin tana fad'in babu ranar xuwa na kenan kuma baxaki qara ganin qafana a wannan qauyen naku ba nayi tunanin babu abinda xan nema a duniyar nan kiqi min shi.

Hidaya tayi saurin riqa hannun ta tana fad'in kiyi haquri shikenan naji please amma ni ba yanxu xan koma ba ta fad'a kawai saboda ganin yanda yasmeen d'in ta d'auki xafi.

Ko da yasmeen xata tafi da taxo rakata kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta, ya shiga motar cikin mamaki hali irin na hidaya ko bata mishi magana dan komai ba ai ta gaida shi a matsayin sa na mijin ta.

Wasa wasa tun daga lokacin kullum sai sultan yaxo gidan amma baffa yaqi bud'e masa ya hana shi ganin hidaya.

Yau ma kamar kullum yayi magiya yayi roqo amma fafur baffa yaqi bud'e masa qofar gidan, yana xaune kan motar sa ya xubawa gidan ido tunani yayi idan fa bai nuna wa wannan tsohon nima kafuwa ne dani ba kamar sa baxai bani matata ba, ya diro daga saman motar da qarfi ya buga qofar kusan sau hud'u sai gata ya ballata kamar wancan lokacin, hidaya tana ganin shigowar sa tayi cikin daki da gudu baffa kuwa kallon ikon Allah yake shi kam a rayuwa bai taba ganin ja'irin yaro ba kamar sultan.

Yace wannan karon sai ka biya kud'in wannan qofar da ka balla kuma xanyi qarar kane ga hukuma domin su yi min iyaka da kai.

Sultan ya xauna kusa dashi yana fad'in bama qofar ba ko gidan kake so a sake ma a yau xan saka a yi ma wanda yafi wannan balle mutum da gidan uban sa har ana masa iyaka da shigowa.

A fusace baffa yace waye uban naka da har kake maganar gidan uban kane.

Sultan yace kai mana ai ubana ne kai, uban matata ubana ne gidan matata gidan mu ne so kaga babu wani banbanci.

Baffa yace amma kai anyi marar kunya, dallah malam tashi ka barmin gida bana son ganin ka, kace matar ka sadaki aka karba ne.

Sultan yace ko baka karbi sadaki ba dai an d'aura kuma mutane da dama sun shaida hidaya matar sultan ce, ni kud'in sadakin ma kashe su xanyi kamar yanda ka kashe min kud'in waya sai ayi 1-1 kuma hidaya tana nan a matata kuma dole xaa bani ita.

Cikin fusata baffa yace baxaa baka ita ba, xan nuna ma nafika tantiran ci kai d'an iska da kai waye xai so had'a jini da kai marar tausayi kawai.

Sultan ya furxar da iska cikin bakin ciki xuciyar sa na sosuwa da irin kalaman baffa xuwa gare shi, yace naji dan iska ne abinda ake kirana dan iska domin shi yanxu nawa ne haqqina ne, ya tashi yana fad'in tuntuni ina batawa kaina lokacin wurin roqon ka ma sam na manta da ina da haqqi da gidan matata ina da ixinin shiga ko ina nake so a gidannan kuma na kebe da ita, baffan ta nima baffana ne ko yana so ko baya so, ai kai d'in ubana ne kuma gidan ubana naxo, kafin baffa yayi yunqurin tashi tuni sultan yayi wuf ya tsallaka shi ya shige d'akin tare da rufo qofar da qarfi ya saka mata sakata, juyowar da xaiyi ya ganta tsaye tana kallon sa jikinta na kyarma.

Murmushi yayi mai sauti yana shafa sumar kansa......

littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980 or? 08030811300*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*


*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*

42

Tun daga lokacin bai qara kula ta ko neman ta ba sai harkokin sa yake, duk da haka kullum yana hanyar xuwa wannan qauyen inda baffa.

Baffa ya dube sa yana fad'in nayi tsammanin tunda na baka hidaya kuma baxaka qara waiwaye na ba xaka manta da ni kuma.

Sultan ya cira kai yana kallon taurarin sama kafin yace kaine kaqi yarda da cewa wannan sultan d'in ba wanda ka sani bane a baya, xuciyata bata kyamar talaka ko yaya ne xan iya xama dashi, banga laifin ka ba Dan kaqi amincewa dani saboda ko daddy bai yarda na shiryu ba, sultan ya dube sa yana fad'in har yana min magana ma baxai bani hidaya naje da ita ba,

Baffa yayi dariya batare da yayi magana ba, sultan ya d'auke dubban sa gare sa yana fad'in da xaka yarda da ka bimu can ka xauna.

Baffa yace wai na xauna tare da kai da hidaya? Sultan ya girgixa kansa yana fad'in haba dai ai xaka takura mana da yawa ka dai xauna gidan ka daban, sultan ya juya yana kallon sa gaba ki d'aya kaga xan baka gida kuma na bud'e maka Company da xaka riqa sarrafa wad'annan shanun naka kana yin yoghurt.

Menene yugurt baffa ya tambaya yana kallon sa, sultan yace duk xaka sani kuma xan d'auki mutanen kirki na had'a ka da su da xasu yi ma jagora akan komai idan ma kana da wasu mutane da kake son d'auka duk xaka iya d'auka kana biyan su duk wata.

Baffa yayi shiru yana naxari sai kuma ya dubi gidan sa yana fad'in shi kuma wannan gidan fa sai na barshi ba kowa.

Sultan yace aa gyara shi xaa yi sosai xaka sha mamaki idan ka gani xan cire part nawa dana hidaya in case muna son xama qauyen sai kuma naka bangaren kai da amarya Dan dole xaka yi aure baffa xama haka baxai yi ba, ka tsufar da kanka alhali kai ba tsoho ba, cikin qanqanin lokaci xan saka a gyara ka xaka ga yanda xaka dawo wannan dogon hancin baxai je a banxa ba yam'mata xaka ga suna mutuwa akan ka.

Baffa ya kaiwa sultan duka yayi saurin gocewa yana dariya, yace baxan gaji da gayama ba,? baka da kunya sultan, ja'irin yaro dawo xauna ka gayamin wacece xata so ni a haka.

Batare da ya xauna ba ya d'an cira kai alamar tunani kafin ya dube sa yana fad'in ai baxaa rasa ba, xanje nayi ma sabbin d'inkuna, na kaika ayi ma gyaran kai da fuskar nan, kayi wanka ka wanke jikin nan da kyau hasken ka daya gushe xai dawo, sannan wannan kayan fulani na al'ada ka sauya su xuwa tsadaddiyar gezner na baka mota mai kyau babu inda xaka shiga baka sami mace ko wace iri kake so taqi amincewa da kai ba, at your age baffa matashi ne kai fa kamar daddy kaine kawai ka maida kanka haka.

Baffa ya d'auke kansa gefe tare da goge guntuwar kwallah batare da ya bari sultan d'in ya gani ba bai san kuma ya riga ya gani ba sai ya d'auke kansa gefe yana murmushi kawai batare da yayi magana ba.

*

To 10pm ya qarasa gidan, ba kowa falon sai aiman gaida sa yayi kafin ya nufi sashen Afiya ya sanar da ita dawowar sa, yana fitowa aiman ya kira sa.

Yace an saka lokacin bikin ku duka yaran gidan nan lokaci d'aya, bayan manya sun xauna sun tattauna duba da yaran sun nuna suna son auren, yaran xamani kenan har kamar yasmeen ke amincewa da aure yanxu.

Sultan yace daddy amma mamee ta amince da auren ne.

Yace meyasa baxata amince ba, fu'ad ne fa d'an yayan ta ai da wani ne a waje yaxo babu ta yanda xata yarda ayi auren kaima kasani, Salwa da Amira ma ya'yan I.G El'mustapha xasu aura ka sani.

Bayan auren salwa da amira xasu bi maxajen su can Egypt tun da dama acan suke karatu, yasmeen kuwa ta canxa makaranta xasu je da fu'ad Loughborough ita ma acan xata yi, hidaya ce kawai xaa bari anan idan ka koma Phoenix bayan biki.

Cikin tashin hankali sultan ke kallon sa yace meyasa daddy bayan kace tare xamu je kuma har ka nema mata admission acan.

Aiman ya tashi yana fad'in yanxu na fasa sab??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????oda naga har yanxu kanka yana rawa baka shiryu ba tukunna.

Sultan ya tashi yana fad'in Allah daddy ya daina rawa tuni na dad'e da shiryuwa kayi haquri please.

Aiman baiyi magana ba ya tattara kayan sa ya need bedroom nasa sultan xai bi sa ya dakatar dashi yana fad'in kwanciya xanyi bana son damuwa, gobe xamu yi magana yayi shigewar sa.

Sultan ya furxar da iska wahala bata qare masa ba kenan har yanxu ya gama da baffa ga daddy ya bullo da nashi bayan wulaqancin da yake fuskanta a wurin hidaya d'in, ta ya ma kowa xaa bashi matar shi yaje da ita suna more rayuwar sa sannan shi ace baxai je da tashi ba kenan babu amfanin xuwan nasa, sarki xai gayawa wannan maganar.

Ya juya kamar xai je d'akin sa sai kuma ya nufi nasu d'akin shigar sa yayi dai dai da fitowar ta wanka daga toilet, kallon ta yayi daga sama har qasa kasancewar bai taba ganin ta da towel kawai a jiki ba ya juya yana kallon saman gadon ba kowa, ya qara kallon ta yana fad'in ina yasmeen?

Kamar baxata amsa ba sai kuma da kyar tace sun je gidan mommy acan xasu kwana, ta fad'a tana qara lulluba wani towel akan jikin ta ganin yanda ya kafe cinyoyin ta da kallo.

Ya tabe bakin sa kamar bai gane me take nufi ba yace well kin so kanki da baki bi su kun je tare ba da komai dare sai kin dawo, karki kuskura fita gidannan batare da ixini na ba.

Ta yatsina fuska ta shiga cikin d'akin tana fad'in wannan damuwar ka ne ni dai ka daina shigomin d'aki batare da neman ixini ba dan baka san yanda xaka sami mutum ba.

Taku d'aya, biyu, uku yayi ya isa gare ta lokacin da take qoqarin janyo rigar barcin ta, ta saka

Sakin rigar tayi cikin tsoro ganin yanda ya matso daf da ita sosai kamar xai maida ta ciki, hannun sa yasa ya xagayo dashi ta qugunta tare da matsota sosai xuwa jikin sa,

jin sautin shi da yanayin jikinshi ya sauya yasa tayi qoqarin xamewa amma ta kasa, ya soma _kissing dinta passionately_ ,jitayi numfashinta yana sauyawa yanayin jikinta ma na sauyawa,numfashinta ya soma fita da sauri sauri cikin tsoro da rud'ewa ...xata janye

yace please hidaya...

jikinta yayi lagwab tana ji ya cigaba da abinda yake yi ganin suna shirin shiga wani limit ya janye jikinsa da qarfi ya jingina da sirf yana _regaining consciousness_ gaba daya a tsorace take qafafunta ma rawa suke yi ta zauna bakin gado tana cike da mamaki dan haqiqa ta tsorata da lamarin sultan ta dauka cinyeta xaiyi ynda yake binta da tsotsa da sumba kamar namijin xakin da yunwa ta koro sa,

sai da ya samu nutsuwa cikin muryarsa a sanyaye yace kixo muje ki kwana a d'aki na please hidaya.

Gaban ta taji yana fad'uwa, ta kasa d'aga idanu ta dube sa gabaki daya jikin ta a mace yake ga wani haushin sa da take qara ji sanin ya gama ganin jikin ta a yanxu.

Ya d'auki rigar ta dake qasa ya d'ora mata akan cinya batare da yayi magana ba ya juya ya bar d'akin cikin mutuwar jiki.

Qaramin tsaki taja bayan fitar sa daga d'akin, tasa hannu tana taba bakin ta dake mata xafi, xata masa magana ya daina taba mata qirji bata son iskanci dan taji ranar yasmeen na hira da qawayen ta idan ana taba qirjin mace girma suke qarawa kuma su xube, da kyar ta tashi ta saka kayan barcin tare da tunanin sultan ko a ina ya koyi wannan abubuwan?

Ranar da kyar barci ya d'auke ta ga tunanin halin sultan ga kawaicin yasmeen da bata gidan.

Washe gari suna kitchen tare da Afiya kamar ko yaushe, ta fito daga kitchen d'auke da kaya xata nufi dinning tajiyo qamshin turaren sa, muryar sa taji yana fad'in ki jira ni yanxu xan iso, ya tsinke wayar yana kallon hidaya itama shi take kallo kamar baxata gaida shi ba sai kuma ta gaida shi tana d'auke kanta, bai amsa ba yayi shigewar sa kitchen ta bisa da kallo tana fad'in a fili kamar na kwarai bayan baa san abinda yake aikatawa a boye ba, sarai ya ji ta kuma ya san dashi take sai ya juya ya d'an dube ta yana d'auke kansa bayan ya qarasa ciki,

Mami xan fita yanxu amira ta kirani mota ta tsaya masu a hanya xanje na duba na gani.

Tace shi fu'ad fa?
Yace kin manta baya gari yaje auren abokin sa Kaduna.
Tace haka ne amma ka tsaya kayi breakfast tukunna tunda an kammala, ya fito yana fad'in jirana take fa a hanya idan na dawo xanci tunda ba jimawa xan yi ba, yasa kai ya bar falon.

Wacece ke jiran sa a hanya ta tambayi kanta tana bin sa da kallo har ya bar falon, haka kawai taji sam xuciyar ta ba dad'i wanda ta rasa dalilin haka, falon ta bari taje tayi wanka idanun ta akan clock fiye da minti talatin bai dawo ba, wurin wacece yaje haka?

Fitar mera gidan bada jimawa ba ya dawo, suna falo xaune su biyu, ya xauna yana fad'in mami kin ganni sai yanxu duk na gaji Haneefa tace a gaida ki.

Tace ina kuma ka had'u da ita yaushe ta dawo qasar,

Ya tashi yana fad'in can na same ta tare da su amira,

Tace breakfast d'in fa?
Yace am ok naci a gurin mummy, yayi shigewar sa.

Sam ta kasa sukuni wacece hanifa ma da tun d'axu yake gurin ta sai yanxu yake dawowa.

Kamar daga sama Afiya taji tana tambayar mamee wacece hanifa?

Daughter wata friend d'ita ce kusan sa'annin juna kuke ma amma xata girme ku keda yasmeen kad'an ba anan suke xaune ba ita da iyayen ta suna Cameron,

Hidaya ta jinjina kai tana tabe baki Afiya kuwa kallon ta take ganin damuwa a fuskarta ko kishin sultan take, murmushi tayi tana qara kallon ta tana cewa ke hidaya haka kika ga anayi miji ya dawo baxaki masa sannu da xuwa ba kuma ki ta xama batare da kin bisa kin masa ya gajiya ba, haka kika ga ina yi da nawa mijin.

Hidaya tayi shiru kuma batada niyar tashi, Afiya ta tashi tana fad'in sai ki ta xama kina barin mijin ki cikin kadaice a hakan xai kyallo wata dake nuna masa kulawa ya fara son ta har kiji anan maganar aure Ma kina xaune sake da baki.

Haka kawai taji hankalin ta is tashi karfa mgnr ta xama gaske, ta turo baki tana barin falon kamar baxata je d'akin na sa ba saw kuma ta shiga da sallama ciki ciki kamar bata so.

Jin muryarta ya saka shi juyowa daga wayar da yake, yana kammalawa kallo d'aya yayi mata ya d'auke kansa daga gare ta, kamar bata so tace barka da dawowa, bai amsa ba amma ya kafe ta da idanunta, kamar baxai yi magana ba sai kuma ya matso daf da ita yana fad'in har yanxu xuciyata ta daina xargin cewa tun farko ba sona kike ba, ta d'ago tana kallon sa sai kuma ta juyar da kanta gefe tana yatsina fuska batare da tayi magana ba, shima tabe bakin sa yayi ya juya abinsa, ta fice da sauri.

Daren yau ma ya kasance su biyu kad'ai ne a gidan su yasmeen sun qi dawowa, ta gaji da xaman kadaici sai take jin gidan baya mata dad'i, da kyar ta tashi ta bar falon bayan tayi wa Afiya good night wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga iya gwiwa ta hau gadon bayan tayi addu'a ta kwanta tare da light off na d'akin.

Lumshe idanuwan ta tayi cike da tunanin ko wane hali baffa yake ciki yanxu da tana da waya da ta kira taji muryar sa, da ta nemi yasmeen sun yi hira duk da basu tare, sai taji tana son riqa waya a yanxu ko yaya ne saboda sanin muhimmancin ta, ta jima tana tunanin kafin barci mai nauyi yayi awon gaba da ita.

Can cikin barci taji kamar mutum cikin jikinta yana taba ta, a firgice ta tashi xata kurma ihu yayi saurin riqo ta yana fad'in,

Xaki min tonon asiri ne cikin wannan daren, cikin bacin rai tace amma me kake yi anan har kaxo ka kwanta a saman gado.

Ya tashi ya kunna makunnin fitilar d'akin yana fad'in sauko, kallon sa tayi fuskar sa babu alamar wasa, a sanyaye ta sauko daga saman gadon tana kallon sa, hanyar waje ya nuna mata yace muje d'aki na.

Ta langabar da kanta tana fad'in me xanje yi, nifa barci nake ji ka kyale ni.

Yace kika sake bud'e baki kika min magana sai kin gane kuren ki, kuma kada kixo ki gani ya fita daga d'akin, qaramin tsaki taja a hankali batare da ta bari ya ji ba tabi bayan sa tana qunquni kome xan masa a wannan daren da baxai bari har gobe ba.

Suna shiga d'akin kai tsaye toilet ya nufa ya barta gurin, ta gaji da tsayuwa ta xauna tana tunxure baki, jin motsin fitowar sa yasa ta juya tana kallon wurin, yana tsaye da d'aure da towel iya qugunsa ga qarami a hannunsa yana tsane gashin kansa, kallon shi take cikin mamaki komai nasa na manyan maza ne tun daga faffadan qirjinsa, ya qaraso cikin d'akin qofar ya rufe da key yana kallon ta, xo ki taimaka min na shirya.

Hankalin ta ya tashi, ta yamutsa fuska kamar xatayi kuka Dan Allah kayi haquri ka barni na tafi ni barci nake ji.

Yace ai anan ma barci xakiyi, daga yau har na

23 / 26