Author : Queen Mamie Category : New Hausa Novels 2026
sona ko? to kisa aranki se kin soni kuma sai na Aureki ba Sumy kike tsoroba karki damu."
D'agowa tayi "kayi hkr ni fa inada miji agarinmu" dukan gaban Motar yayi "shut up kin maidani sakarai, kin kwa san yanda matan Abuja ke sona kuwa? su sa suke ma Gig Girls."
Tace "ni ka k'yaleni wlh bana sonka" Dariya yayi yace "zan baki Mamaki ne ya shige motar sa yaja. itama driver yaja itakam ji take kamar tai tsuntsuwa ta ganta a Mangalu Sam tun lokacin abinda ya faru taji gidan yafita a ranta.
*Mangalu*
Baba ne a tsaye gefen dakin sa ga Gwamma na huci yace "dama duk abinda kaga wani D'an nayi wasu iyayen ne basi masu kyakkyawar tarbiya ba Ashe tun tafiyar Mudi Lagos suke sata shida Lawandi daya ke akwai Wanda suke kaiwa shine shi Mudi ya ce ya dai na kai musu fad'a ya kaure tsakanin su suka yayyen ke Shi kuma ak'ark'ashin Gada suke kwana a ikkon, Shi Lawandi ne bayan abin ya faru ya gudo dashi shine bayan Sun zo kano dama akwai yaransu anan suka kuma yimai duka suka Jimai Rauni shine kika Ganshi haka."
Dama tun tafiyarshi Jikina bai Aminta ba Amma Gwamma kika Nace ai ga irinta nan."
Jummai tayi Jimami tace "Allah ya kiyaye Gaba." Gwamma kuwa duk bata yardaba acewarta da sa hannun jummai.
Malam yace "dole fa Dije ta Dena tallan nan ta na zuwa Makaranta yanzu Jbi Hansai jiya taimin waya tayi Jarabawar gama Secondary."
Gwamma tace "ai dama ba san su kake ba! yace meye banyi ba ran nan Dije har kusan zagin Maalam na Allon su tayi, Allah yagani na basu Tarbiya kin bata,wlh Gwamma kawai kinci darajar wadan nan yaran ne Amma da tuni na sallameki."
Hakan Gwamma take jinyar Mudi duk ta kare ga Masifar bashin dake kanta kullm sai anzo an fada akan hakan ga ciwon hannun da take yi duk tayi wujiga- wujiga .
By
*queen Meemi*
*Queenmeemi.WordPress.com*
. .
. ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣31❣
*JAN 2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION
*_'YAN GROUP D'IN QASAITATTUN MATA ADAD'E ANAYI SAI GASKIYA. GODIYAR NAKU NE ALLAH YABAR ZUMUCI_*❤
***********
Tunda Dady ya Yanke Hukunci Zuby ta shiga Matsala saboda tsagwaran san datakewa Fawwz kullum suna Manne awaya abinda ya dada sadda da Rashin gamsuwar ta ga Mijin Da aka bata sabili da zuwan da yayi Sam sai taga kamar batai mai ba yana basarwa had'e da nuna isa.
Agabanta yayi waya da Budurwar sa wacce yakeso bai wani nuna naam da ita Zuby ba La akari da tai watakil shima dole akai mai tundaga nan Jikinta yayi sanyi kullum kuka inda taje ta Samu Hajiya kan Maganar tace sai de tayi hkr.
Bangaren Ruby kuwa ba yabo ba falllasa sun dai-daita kansu Mutumin nada 'ya'ya biyu ba wani Babba ,ne sosai da Alama yayi Mata ,itama tayi mai tunda yaganta d'agwas- d'agwa kaji abin Manya k'warya tabi k'warya .
Itakam Ruma nata Suga Dady ne Babba ne yana da manyan yara Baban d'an sa ya Girme mata,itama tayi Naaam don Biyayya inda Shi kuma gani yake ya samu dami akala sai b'arin Naira yake wan nan kenan.
Shirye- Shirye ake inda Manya aka saka Ranar 22 ga watan March 2017 inda shine d'aurin Auren.
Zuby sai kuka take tana zaune ta D'ora kan ta akan cinyar Mama tace "na shiga uku Mama nifa wulak'anci yake min da Alama ban masa ba, kuma nima bai mun ba ,ki taimakeni."
Mama tace "kiyi Biyayya ki hkr" ba yanda ta iya ko waya ya bugo Mata sai de yayi tsaki yace ykk ba yanda ta iya tace Lafiya ahakan har aka suke waya.
Yauda suke zaune anata tsara Bikin ita kam Zuby kanta ke ciwo Ga Soyayyar Fawwz dake nuk'urk'usar ta kullum damuwa Sede su had'u dashi a School.
Zaune take Adaki taci kuka, bakin ciki ne yayi Mata yawa ta fita wajen Garden tana kuka kiran wayarta ne ya motsa ta dauka daga can Dan Sanata yayi tsaki "idan bazaki Magana ba zan kashee."
Haushi ya isheta "ka kashe mana Waya damu da kai ,duk abinda kake tak'ama dashi nima hakan" yace "bana Sonki don haka ki Sanar da Parents naki" kit ya kashe.
Tunani ta fara Lokacin da wani kb ke sonta da sukaje Jigawa k'ark'ari ta Dinga cewa bata Sonsa har kuka yayi agabanta ,ta Buda kasa a idonta tace bata Sonsa face to face, sai yanzu taji Ciwon abin ashe haka kb yaji? duk da ita tasan bata san Dan Sanata Amma taji d'acin kalmar na Bai Sonta.hmm Abinda kai Shi za ama.
Komawa Gida tayi tace Hansai ta dafa Mata kunun Gyada saboda bata iya cin Abincin.
*Bayan Sati 2*
Zuby ciwon so ya kwantar da ita itace har Asibiti nan hankalin Mama da Dady ya tashi kai kowa ma na Gidan, direct bayan treatment dinta da Doctor yayi ya kira Dady inda yace "ranka ya Dade 'yarka hawan Jini ke neman kama ta saboda damuwa da yawan tunani ya kamata ta samawa kanta salama."
Dady yace "okay ba matsala" yau kwanan ta 3 a Hospital Su Dady shida Mama na zaune Dady "yace yanzu Zuby kan na Rabaku da Fawwz shine Sanadin Sa damuwarki har ta ke nema ki jawa kanki ciwo?
Mama tace "Aa yarinyar nan fa D'an D'anata baya Santa koni wani Zuwa da yayi na zo zan fita naji yana gargaya Mata Magana kullum kuma sai tace min ga abinda yace Mata to ga Wanda takeso an Rabasu haka kuma Shi Wanda ake son had'asun yana yimata hakan Dole damuwa tai Mata yawa."
Shiru Dady yayi "yace ba Matsala zami Magana da Sanata d'in kan Maganar .
Satin Zuby D'aya aka sallamota duk ta fige Dady kuwa sunyi Magana da Sanata ya sanar mai abinda yake faruwa Sanata yace "ay 'ya'yan zamani sai ahankali, yanzu tunda abin yazo da hakan mu Janye had'in kawai, Allah ya had'a kowa da Raban sa, Amma wani hanzari ba gudu ba Minister ya kamata ku dai-dai da Baban Fawwz domin koba komai Gaba ba kyau kodan ka ceci Rayuwar 'yarka ,Amma ni da kaina zanje har can wajen nasa insha Allahu." Dak'yar Dady ya hkr.
BAYAN Sati D'aya Da k'yar da sid'in Goshi Baban fawwz ya sakko duk da dama Dady ke Gabar dashi ,ba yanda zai yi haka ya hkr yace Ayi daman shima Fawwz din duk ya rikicemai wan.nan shine Silar shiryawarsu nan akai maganar Auren aka Maida kan Fawwz Nan shirin ya kuma kankama.
Zuby ba Wanda yakaita jin Dad'i Auren Masoyi akwai dad'i su Dady an Rikice sai barin Naira ake komai daga waje ya wayar ai order Su ,ya'ya sun Samu irin Mazan da yake so.
Sumy anci K'uzun Bikin nan, Mama kuwa Mutanenta kowa Nason zuwan sa haka Umma to Bikin 'ya'ya Uku wasa ne! hansai ba abarsu abaya ba wajen son Zuwan Bikin Wanda Jikinta ke bata tabbas wani Burinta zai cika agun Wanda yayi dai-dai da Saura Wata d'aya cir.
Bari na tsagaita Anan .
By
Queen meemi
Queenmeemi.wordpress.com
. . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣32❣
*JAN 2017*
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION_
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_
***********
Gida kowa shirin Biki yake kai hatta su Hansai ba abarsu abaya ba an musu kaya da yawa kowa ne event da za agabatar suma an musu nasu kalar anko da su head din su duk iri d'aya .
ABangaren su Sumy Da Dady kuwa ba a cewa komai domin kaya na gani na fada suka dinka duk na event .
Amare kuwa ba a cewa komai. Lokaci na tafiya Bikin na dada K'ara sowa Ankawo Lefen kowacce aciki set 24 tamkar had'in baki kaya turmus kamar abude kanti .
D'aki d'aya aka ware musu nan aka d'auko 'yar Maiduguri tana Getta su masha Allah kowacce sai kyau suke ,yau da akewa Zuby Sady ta shiga Tace "Anty Ruma ya Za'a ai preparation na frnds event d'inku sa frnds naku?"
Zuby tace "no wan nan ai akwai masu yi ki bari kawai" Sumy ta shigo "wow gaskiya dole ai mini nima don na Rikita Nazi." dariya Ruma tasa "tab! nikam keda nazin nan kuna ban Dariya."
Sady ta tashi tana waya tafita don karbo dinkin ta hatta gidan sai da aka getta su duk an canja wasu kayan yau ta kama saura sati d'aya Bikin Hajiya ta duro da sauran Dangin Dady ,haka Dangin Maama da Umma suma suka duro. Anty kuwa k'annen ta ne zasu zo Amma sai anfara Event.
Nan fa Dida ya kacame Dangi kota ina Dady sai barin Naira yake tunma ba A faraa Bikin ba ,ga Gift da yake karb'a gun Abokanan Siyasan sa.
Shi kanshi katin Rabo kala -kala zaka ganshi Amare kuwa ko Giftawa sukai sai kaji kamshi kai gashin kansu ma ba abarsa ba ya ba wan nan kenan.
Ranar Talata shine Ranar fara Biki inda za ayi Dinner da dare wajen k'arfe 7 dai- dai aka fara talle Amare cikin wata me makeup ce tazo ta yimasu kwalliya me kyau kamar dawisai haka suka fito A tsadaddun Amare, kowacce taci latest gwan inda wani shegen matrial ne me d'aukan ido da less ajiki abu na manya idonka Shi zai tantance maka yawan kudin sa, Golden ne da red akai adon sa kuma dukkan su iri d'aya suka saka, sai de Head d'in Ruma red ne ,nasu Zuby da Ruby Golden.
Angwayen ma haka suka saka D'anyar Shadda Golden ,Ana gamawa aka fara kwasar su Frnds Na Amare ,Su Sumy da Sady kuwa Su Suka kwashi nasu frnds d'in a motocin su, Shigar nasu yayi kyau kamar Ka sace su ka gudu sun Balain kyau sai iyayi suke kowacce da hadaddun frnds nata.
Hango Hansai nayi ita dasu Kande sun kafa head masha Allah sunyi kyau musammn Hansai kyanta ya fito kayan sun karbi jikinta hakan aka dunga daukansu Ana kaisu tafkeken hall din da za a Gabatar haduwar gun da fadar sa Sayya b'atan Lokaci.
Cool Music ke tashi ga k'amshi ma na tashi nan MC ya fara Aikin sa,ko ina ka kalla wal -wal wan nan na wane wan can haka aka ci aka sha aka taka rawa aka gama aka Raba Atampah Super Holland da Calender dake manne Pictures d'in Amare.
Washegari Ranar Laraba shine Mothers Day nan fa Su Mama karfe 3 Aka fara inda Mama da Umma da Anty sukayi Ankon kaya iri d'aya me makeup ta yi masu duk sunyi kyau sunkafa head Sai tarbar Manyan mata suk.
Amare kuwa shigar wani kwantaccen Less sukai mai Manyan flowers da Stone Pink ne da ratsin Green inda Ka nad'a musuu head Green me adon pink suka saka wani a kafad'ar su ,Buba ce da zani sunsa wani hil Shoes Green sun Balain kyau Lokacin da suka fito ai nan da nan Masu vedios da Masu Photo suka fara Aikin su, Flower Girls suka? rakasu wajen zama wajen ya k'ayatu Su Sady ma sunyi kyau Sai tar bar frnds suke.
Mawak'in Nan Audu Gwanja ke watso wakar sa yauma Hansai sunyi kyau kamar ba 'yan Aiki ba.
Wajen 4 Pm Wata Sumammiyar Mota ta faka a harabar hall d'in.
Wata Had'add'iyar Matashiyar Budurwa ce ta fito bayan ta kashe Motar ta kulle akalla zatai 21 yrs bugaggiyar wayar ta ta fiddo a Jakar me kyau,tayi shigar wani material Ash tayi balain kyau, dole ka kalleta ka Kara gani nan ta danna kiran Sady tace tana harabar Hall ta fitoo Su shiga.
Kamar 3mint saiga Sady ta fito duk sokeken shoe da ke k'afarta besa ta tawo aguje ba inda suka Rungume Juna da Budurwar "wow Suhaima kin ganki kuwa!" Suhaima tace "ke ni k'yaleni Ina Anty? Sady tace "ke Anty banganta ba tana cikin mutane , ban d'auka zaki zo Mana ba Lokacin da na fada miki ai kuna Landonn ,yaushe kuka dawo daga Landon din? Suhaima tace "ke ni kyaleno muje kawai."
Karo Sukayi da Hansai nan Jakar Suhaima ta fad'I ,Head d'in Hansai ya fad'i Sady ta wanka Mata Mari "bakida hankali ne bakya ganin ina tare da bak'uwa?
Hansai tace "kiyi hkr banganku ba."Dallah Matsa Fool Gal kawai,ki bata hkr kona kuma Mazge ki Saida Gaban Hansai ya Fad'i tace "kiyi hkr" tare da share Hawaye Suhaima da taji hansai ta birgeta kuma ta bata tausayi, tace "bakomi."
Da sauri Hansai tayi gaba Sady taja Hannun Suhaima sukayi Gaba.Biki yayi Biki Gwanja sai samun naira yake ya rikice sai watsowa Amare wak'a yake yan Mata kuwa sai cashewa suke k'arfe bakwai dai de aka gama.
Sady ta rako Suhaima nan sukai sallama da Sady ,