Author : Queen Mamie Category : New Hausa Novels 2026
daga kai sama idon nan yayi ja sosai.yadan mike dole nabi Shawarar Abokina na koma gun sumy mu shirya, Bazan so A dinga k'untatawa Hansai akaina ba, domin so mai sonka, son maso wani kuwa k'oshin wahala ne.
hakan kuwa akai ya nemi wayar Sumy Sam taki d'agawa.
Wajen Kwana 2 yana Try Amma bata d'auka da kyar da Sid'in goshi Abokinsa ya shirya su ta hak'ura suka koma Soyayyar su kamar da.
By
Queen meemi👑
Queenmeemi.WordPress.com.
.
[5:52pm, 23/02/2017] 👑MEEMI💋: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣37❣
*FEB,2017*
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION(NWA)
_Sadaukarwa ce Ga basheer Usman Family's_
***********
RANAR MURNA
Wajen K'arfe 12 na Rana Lami ta dira A abuja Hansai na Tsifar kai A kusa da Fulawowi Ta gano Lami nik'i da kaya ta shigo da sauri Hansai ta je ta Amshe ta tana Murnar Ganin ta. Lami tace "ja'ira to tafiya nazo nayi dake."
Tsalle ta daka "haba Wayyo Dadi" Nan suka shiga side din Anty itama tayi Mamakin Ganin Lami tace "Aa Lami kece haka da tsakar rana kinsha hanya" zama tayi Wallayi kuwa tafiyan Gaggawa ce ta same Ni Shi Baban Hansai da kansa yaje guna yace amaida ita za'ai Mata Aure wlh kuwa,shiisa kika ganni."
Jikin Hansai ne yayi sanyi hakama Anty.
Bayan taci ta huta tayi Sallah Anty tace "Amma inaga sai de Gobe zaku tafi kinga yau Alhaji be sani ba" Lami tace "bakomi yau da Goben Ai duk dayane."
Hansai kuwa suk'uk'u ta dawo Jin cewa za'ai Mata Aure Sam se taji bata san komawa bata san wa za'a Aura Mata ba Amma ta basar.
har ta gama karfe 5 dai -de Iya tayi mata kitso me kyau.
Washegari Misalin k'arfe Bakwai suka gama Shiri Anty ta fito da kayan tsaraba hili Atamph, Shadda su Takalim kaya de turmus da sarka k'aramar Akwati tayi Mata tace taci Biki dasu .
Kuka sosai Hansai take taje sukai sallama da Umma da Mama su ma suka bata Atampha kowacce, taje gun su Sumy da Sady ma sukai Sallama sabo akace turken wawa koda ba zaman Dadi suke da itaba sunji rashin tafiyar ta .
haka dai duk sukai Sallama Anty ta bada kudin Aiki 200k san nan ta bawa Lami Dubu Goma da kudin Mota su Mama suka bawa Hansai dubu Biyar,da kuka ta tafi .Anty suka tafi Driver ya tafi kai su tasha.
Shekara uku kenan da zuwan Hansai Abuja yau Gashi zata koma don Ai Mata aure ,to muje zuwa.
*Mangalu*
Sai wajen 2 suka Shiga Mangalu A gajiye taxi ta aje su a k'ofar Gidan Suka Firfito da kayan wasu yara suka daukar musu suka shiga ciki, tun A soro take Jin Maganar Jummai tana Maraba ganin yara na shiga da kaya da gudu Hansai ta Rungumeta har da kwalla.
Jummai tace Lami "kede sannu ya hanya?" nan Lami ta fito da 200k "ga kudinta Ni dama tun acan aka ban nawa, ta dauki wasu kayan tace na tafi domin so nake nake gida na huta."
Jummai tace to "angode Lami Allah ya saka da Alheri d'awainiyar da ki kai da Hansai" tace "Amin."
Bayan firar ta Jummai tace "naji Dadin ganinki fes Hansai kamar dama can A birnin kika rayu, sai k'amshi kike" Dariya tayi suka shiga daki .
Tayi sallah taci Abinci suna hira da D'an Jummai da ya dawo daga Boko Jummai ce ta shiga d'akin Lokacin Hansai nata fito da kaya.
Tace "inna wai ina Baba Gwamma ne? Nasan dai Baba ba yanzu zai shigo ba.wai Da gaske Aure Za aimin?"
Jummai tace Eh Haka dai naji Malam ya gayawa Lami Amma de Anjima maji Dalili."
Zaunawa tayi "Lalle Hansai na yarda Dan Adam ba abakin komai yake ba,duk iskancin Mutum to akwai ranar kin dillanci ,wato Ranar da hajjar Maigari ta cika,duk zalincin Mutum Karshensa bai da bai kyau."
Hansai tace "Gaskiyane Inna"
"Ai In gaya miki tun Lokacin da Larura ta samu Mudi na fadan da sukai da. Abokan sa, da suka yayyanka Shi, Gwamma ta tashi hankalin ta gani take kamar Ni nayi mai Asiri har abokan suka samu dama akan sa, akan hakan ta sai da Akuyar ta taje gun boka, wai ya bata Maganin da zata samun don na nakasa ,duk wan nan Abu da take bata san nasan Abinda take ciki ba, domin da kunne na naji tana Gayawa Mudi dake kwance yana jinya kan sai ta dau fansa akaina."
"Hakan tayi Abinci ta zuba min duk don naci nikam tana kawo wa na zubar , tun tana zuba ido ta ganni daram nan ta dada tsangwama ta nikai Addua naketa zubawa kan Allah ya kawon Dauki."
"Bayan kwana biyu Mudi ya warware ya koma gun shedanin A bokansa sati biyu tsakani fad'a ya kaure kan kud'i inda mudi Yace bazai bada na wajen sa ba,domin bai dena Halin nasa ba na bunsu sace-sace, nan suka tasar mai Yace kudin nagun Maman sa."
"Washegari sai gasu kuwa! Lokacin bakowa Gidan Dije ta tafi Tallah ,nima na fita Malam baya nan sai Gwamma kawai ,suka shiga Mudi ya kasa ta ya tsare Gwamma Daga d'aki ta dinga d'uro musu Ashar wai ba zata bada kud'in ba ta cinye in na karfi ne su kwata."
"Da yake su 'yan zamani n,e sukace idan ba zata bayar ba se Sun illata ta, mudi Yace ta bayar kawai ya hkr, domin yasan halin su, Gwamma har da buga tsalle tace ba zata bayar ba tana zagin su kan kace me! Sun zaro Adda da wuka nan suka hau fada da Mudi .Gwamma har da d'auko tab'arya ta kwad'awa wani akai, kan ya fashe Jin zafi ya Shammaci Gwamma ya Lafta Mata Adda a hannu da k'afa dayan ya yanki Mudi a hannu ganin Gwamma ta Fad'i k'as kamar mara yasa suka arce."
"Ba adade ba, aka kaiwa Malam Labari ya dawo aka kai ta Asibitin cikin gari."
"Satin ta d'aya suka dawo duk ta fita Hayyacinta mai hali baya fada halinsa, tana cikin ciwon ma bata daina Rashin kirki ba, hakan ta cigaba da yiwa Malam abinda ta ga seda tayi wata daya san nan ta warke ,nan ma ta kuma sai da akuyar ta wadda ita kadai ta rage mata ta tafi gurin boka."
"Adalilin zuwan ta gidan Boka ne, Mota ta Bigeta m wan war tayi atiti, badon ta da nisan kwana ba data shura,nan aka kaita Asibiti,gashi wanda ya buge tan ya gudu, ganin yanda k'afarta daya data dagargaje aka yanke taci kuka ganin tadawo Gurguwa."
"Satin ta Daya da fitowa A Asibitti ,Malam ya zaunar da ita yana Mata fad'a,kan tayi hankali ta dawo Matar kirki, tashin farko ta Lailayo Ashar ta danna mai tare da Ambato babarsa da ta Dade a kushewa ta zaga, Harkuka yayi shikam Yace inde Itace Autar Mata ya saketa bazai iya zama da ita ba."
Ta b'ata tarbiyar 'ya'yanta Dije duk kauyen nan ba Wanda take shayi ga fada da maza ko ita Gwamma din ce tai Mata magana zaginta take.Duk halin gwammar ta kwashe sarai.Malam so biyi yana sata makarnta tana cire akanta,Mudi kuwa yazama Abinda ya zama baya kwana agida ma,ba irin fadan da Malam be mai ba kan kin karatu da sana a yaki har kaishi gun bakanike yayi don Ya dinga koya yaki ,duk sa aninsa Sun san me suke wasu ma sunyi aure,To ta Riga ta bata musu Tarbiya."
Hansai taja Numfashi "Allahu akbar Wanda yadau Duniya da zafi haka zata zo mai."
Jummai tace "yo ai Duniya tafi bagaruwa iya jima. Wanda Yace tukunyar wani bazata tafasa ba to nasa ko dimi bazaki ba."
Hansai tace "to yanzu tana ina?"
"Jummai tace "tana Gidan iya sema kin ganta abin tausayi ga ba k'afa duk ta Rame, iya kam sai hantara ce ke shiga tsakanin su ,Dije kuwa ko kallon ta batai balle ta taimaka mata sai de yawo.wataran Haka zata zauna da yunwa,se Iya ta samu take bata."
Hansai tace "Allah y kyauta."
Adai-dai time din Baba ya dawo yayi Murnar ganin Hansai, don Hansai har da kuka Tayi saboda aganin sa.
Baba ya zauna Yace "Allahu k'adirun Ala man yasha 'u tabbas abinda Allah ya shirya babu makawa tsaiya faru.
ya kalli Jumaai jiya bangaya miki Dalilin dawo da Hansai ba ko? to Dama dalilin dawo da ite shine Anga iyayenta na Asali."
Jummai ta mik'e tsaye tare da dafe k'irji! "da gske Malam? kai Alhamdlh."
Ita kam Hansai suman zaune tayi.
By
Queen meemi👑
Queenmeemi.WordPress.com.
.
[10:38pm, 25/02/2017] 👑MEEMI💋: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
⚜
❣ ⚜ ⚜❣
⚜
*❣RABUWA CE SANADI❣*
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣38❣ *FEB,2017*
_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_
*Fans kunjini Shiru ko? whtsup nawa ya samu Matsala ne shiisa Amma yanzu Normal ,hope kuna fyn,thanks for support nd care,😘*
***********
Kusan mintuna ta d'auka san nan ta d'ago kai cike da Hawaye tace "Allahu Akbar" Baba Yace "ki godewa Allah."
Hansai kan cinyar Jummai ta dora kanta tana Matsar Hawaye.
Jummai tace "Malam to ya abin ya kasance? taya aka same su?"
Dariya yayi "aike dai Jummai bar ikon Allah,Shekaran Jiya Sarkin kasuwa Yazo mani da Maganar, ina Gona yaje can da yake kinsan Ni bana zuwa kasuwa.
To ya zo mani da Maganar wani bawan Allah da yazo dai+ dai Babban Titin nan me kud'i dashi yana kuka Acikin motar sa kuma motar baud'e, su dai Sun rasa dalili yasa sukaje suka same shi.sarkin kasuwa Yace Alhaji meya faru?
Juyowa yayi Yace bakomi bawan Allah kawai wani abu nake tunawa anan hanya, Malam ban mantawa da wan nan Hanya Domin shekara Aru- Aru hanya tace duk shekara sai naje wani kauye gaba nan Dan tai makon bayin Allah Marasa k'arfi."
Akwai wata shekara da Tsautsayi ya afka Bomb ya tashi da Tsautsayi nazo wucewa dani da Matata da yarana Biyu to anan ne muka rasa D'aya har ila yau da nake maka Magana bamu sake jin D'uriya ba shiisa koyaushe nazo wucewa sai na koka saboda tunowa da Gudan Jini na.
Jin hakan Sarkin kasuwa ya shiga tunani na tsawon Lokaci nan ya tuno da ita Hansai dake guna yace zai Gwada sa a ko Allah yasa adace ,shine fa Mutumin ya Gigice Yace akaishi gun Mutumin, haka muka gama Magana kan cewa nan da kwana 3 zasu zo don tantancewa.
Yanzu dai Shi muke jira watak'il Gobe ko Jibi."
Jummai tace "Allah kasa su zamanto cewar shine iyayen nata da nafi kowa jin Dadi Malam Yace "wlh nima haka."
Hansai kuwa kuka take mai tsuma rai kamar ranta zai fita "Baba Yace Hansai keda zaki godewa Allah kuma kike kuka."
Ta d'ago "baba kayi hk'r Ni kune iyayena bana son Rabuwa daku." dariya Jummai tayi ai mu dake mutu ka raba ,Amma hankalin mu zai fi kwanciya in muka gansu Hansai,yau kiyi ta Addua Allah ya tabbatar da Alheri."
*8pm*
Hansai da Jummai na zaune sai hira suke ga Baba agefe yana cin Tuwo Abdullahi yana bacci Hansai ta fito da kud'in hannun ta dama ita suka d'amkawa ta mik'awa Baba tace "Gashi Baba kayi Jari dasu."
Baba Yace "haba Hansai kije ki wahalar Aiki mu daci"
Dariya tayi "Aini ba abunda zan dasu" Jummai tace "naki ne fa! nan baba Yace to ba matsala Angode" Hansai tace "baba ka daina Godiya Saboda Ni na cancanta na Maida muku da Alkhairi da kukai mini domin kun Nunan duk-kan k'auna."
Baba Yace "Allah ya miki Albark" Hansai tace "Amin."
Kamar An wullo Dije ta shigo Baba ya daka Mata tsawa "me kike awaje yanzu?"
Turo baki tayi "banjin bacci" Baba Yace "Allah ya shirya" tashi tayi zata kuma komawa "baba Yace "ina kuma zaki?"
Tace "Innarmu."
Hansai tace "haba dije Baban Kike gayawa Haka? gashi kinga dare ne fa!
"Eh to ina ruwanki ,naji inna tace na koma me zan tunda ba uwata agidan."
Ta fita tana gatsina.
Malam ya aje kwanon cike da damuwa Yace "Gaskiya Gwamma ta cucueni, duk ta batan tarbiyar yara yanzu ace ina magana Dije bata ji?" Jummai tace "sai hkr fa da Addua."
Gidan iya Dije tayi ta shiga d'akin da Gwamma ke ciki k'afarta da aka guntile na ciwo tace "Dije zo ki rik'eni zan mik'e"?"
Tace "nifa Bazan ba karki takuran."
Gwamma tace "Ni kike gayawa haka?sai kace sa arki." ko magana bata kumai ba tayi zamanta.
Gwamma ta matse k'walla halin da take ciki kenan ba mai Kula da ita kowa ya gujeta hatta iya hantarar ta take gashi yayanta ma nayi mata saboda rashin Tarbiya.
Mudi ne ya shiga yana fito Gwamma tace "Yawwa mudi, kayiwa Dije fad'a kan abinda take min."
Ya juyo "Nifa Gwamma ba ruwana da harkanku abin Babana ya ishen."
Kuka ta saka da k'yar ta mik'e ta shiga Band'aki. iya ta fito "yanzu ke Dije uwar taki kikewa haka?"
Dije tace "nifa banyi komai ba."
Iya tace Aa kyace baki komai mana tunda baki da tarbiya."
Nan Gwamma ta fito "yawwa iya ki gayawa mata ko taji."
"Yo Gwamma ai dama duk uwar dabata bawa yaranta tarbiyya ba ,tace 'ya'yanta sukad'ai ne 'ya'ya to wallahi abin kanta zai dawo, kede Gwamma kin b'ata Rayuwarki data yaranki,uban yara ya sasu Makaranta ta Allo ma kin hana, ba abinda suka sani haba kin musu Tarbiyar banza, ai wlh kad'an ma kika gani kin d'auka ban san bin Bokayen da kikai ba,kika mallake Miji da kishiya ko,har 'yar ruk'on nan ma haka kikai ta zalintar ta, ke 'ya'yanki ne yara miji an maida Shi hotiho, to ai ga irin ta nan ki fara tuba ga Allah tunkan ki kaiga kushewa."
Gwamma cike da haushi tace "to naji."
Iya tace "ai baki horu ba.
Ke kuma Dije uwarki komai rashin kirkinta to ki bita domin Allah ne Yace abi iyaye."
Nan ta juya ta shige D'aki.
Gwamma ta zauna da Guntulalliyar k'afarta zuciyar ta na danasani Amma Girman kai bazai barta ta nuna ba.
Domin aganin ta ta fad'o (lalle Gwamma baki horu ba).
*Washegari.*
Tun safe su Malam ke Tsammanin zuwan baki Amma shiru duk Jikinsu yayi sanyi waya ya bugawa sarkin kasuwa ko Sun zo yace mai Aa.
Haka aka wuce Ranar