RABUWACE SANADI COMPELET HAUSA NOVELS BY QUEEN MEEMI.txt

Author :  Queen Mamie Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   38 / 53

111K to 114K   out of 158.2K words

Amma shiru ba Labari sai kuma Hansai Jikinta yayi sanyi sai kallon Hanya take har dare ba Labari,cikin sallar ta sai rokon Allah take Allah yasa burin ta ya cika.
Cike da Jimami ta kwanta.


*Washegari Da karfe goma Ranar Laraba.*

Hansai tayi wankanta tayi kwalliya tayi kyau kai kace zuwa k'auyen tayi ta Tambayi gun Jummai zata je ta D'an zaga gari.

Tafiya take Ahankali tana tuna irin Rayuwar da tayi baya ak'uyen Muntari ne ya fad'o Mata kawai sai tayi Hanyar bayan Dutse wurin nan kamar yanda yake sai sassak'e wasu dutsunan da akai.

Zama tayi tana ta tunani da Murmushi ga iska na kad'ata ,tayi kusan Awa d'aya a zaune yasa ta mik'e don ganin Dad'ewarta tayi Hanyar Gida.

Daga can nesa ta gano wasu shimfid'ad'dun Motors guda 2 ak'ofar Gidan su,Badon tayi zaman Abuja ba, da sai ta tsaya ta Lailaya su.

Gaban ta ne let dukan uku- uku har taje daf da Motar ta tsaya bakowa aciki yasa tayi hanyar shiga Gidan a sanyaye.

Tun shigar ta taga Mutane Birjik a Babbar tabarmar Baba dake zama Asoro.

Cak! ta tsaya tare da k'arewa Mutan gun kallo har tazo kan wata d'anyar D'aby wadda taga kamar ita.

Kuka taji an fasa "Wallahi ko ban ga shaida ba wan nan Baby Husy ce!" kallonta ta maida kan me Maganar taji wani irin Fad'uwar gaba.


BY
Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.


.
[11:19pm, 25/02/2017] 👑MEEMI💋: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣39❣ *FEB,2017*


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_


*************



Rungumeta tayi ta d'ago hab'ar Hansai tace "tabbas wan nan itace" dai de Lokacin kyakkyawar Budurwar ta shiga Gidan Dady yace "Daga d'auko Album kin zauna ko?"

"No Dady ke ne ban gani ba Amotar sai dana duba."

Juyawa Hansai tayi sukayi Ido hud'u da budurwar Suhaima tace "You!" nan ta yar da Album d'in data d'auko ta Rungume Hansai "Mum wlh itace wadda nake baki Labarin suna kama da Arif wadda na ganta a gidan Anty."

Jummai ce ta fito rik'e da wata leda ta tsugguna ta aje Gaban Malam da smSarkin kasuwa, nan ya d'auko ya bud'e hoto ne guda biyu Daya ajiki Hansai ce da Malam aka d'aukesu a Ranar da aka tsinceta sai D'ayan kuma ita kadai ce nan ya mik'awa Dady ya karba Yace Allahu Akbar."

Nan ya d'auki Album ya duba sak! itace ce ba makawa Hansai 'yar su ce .Domin shigar Jikinta an Musu hoto ita da Hassanar ta.

Malam ya d'ago wato 'yan biyu ne kenan!"
Baba yace "tabbas twins ne" .

Sarkin kasuwa yace "mun godewa Allah."

Nan Dady ya kalli Suhaima yace "wan nan itace first Born dita Suhaima, sai su Twins Hassana Da Hussaina,sai kanin su Arif gashi nan."

Hansai dake bunsu da ido tana sharce k'walla sabida Jin wani sonsu da take.

Mum (Fatima) shine sunan ta ,ta d'ago ta kalli Suhaima tace "Amma ace kije Gidan Anty ki kasa gano kamar da suke da Hassy haba Suhaima."

Suhaima tace "Mum wlh tunda Naganta naji ina kaunar ta Sam abin bai kawon ba,don naji Ance ta Mutu."
Dady yace Aikin san dama su basa kama da Junansu, sosai Hussaina tafi kama da Mahaifiyar ku, ita kuma hassana da ni shiisa."

Baba yace "Masha Allahu komai de Daga Allah ne."

Nan Hassy ta zo ta k'urawa Hansai Ido ta d'an tab'a Hancin Hansai ta Rungumeta tana Hawaye I Missd u dear ,I luv u my Twins sis."

Itama Hansai ta Tungumeta ta na Tsiyayyar Hawaye "Me too sis."

Nan aka zauna sai Maida zance ake Hansai sai kallonsu take A ranta tana yaba su dukkansu Masu kyau Ashe wan nan finest Baby din Yayata ce Arif kuwa D'an Lukuti sai satar kallonta yake ,Mum Ma sai satar kallon Hansai take Ganin kamar da suke da ita.

Dady yayi gyaran Murya "yanzu yaya Sunanta? Malam yayi dariya sunan mu na k'auye take karb'a."


Jummai tace "Hansai
sunanta" dariya Arif yasa
hassy ta zungureshi, Hansai tayi Murmushi ganin yanda suka Birgeta ashe itama haka take ta yan uwa Masu kyau had'ad'd'u.

Mum tace "dama ba acanja masu suna ba,Hassana da Usainar su ake ce masu Sai mu da muka tak'aita muke cewa Hassana Hassy."

Malam yace "itama 'yar tawa tunda ga sunanta Wato Husaina sai Ana cemata hakan."
Dariya suka saka dukkansu.

Dady sa bakinsa yak'i Rufuwa yace "ai Malam karkaji irin dad'in da nakeji da ya zamanto irin ruk'on da kukai mata kun zame yan uwa domin Husaina 'yar kuce."

Sarkin kasuwa yace "Masha Allah ai tun Lokacin b'atanta mukai ta bada cigiya shiru."

Dady yace "ai A lokacin Bama hayyacin mu, domin duk asume muke Direct kano aka wuce damu sai da Mukayi 3 weeks akwance Domin Hassana ma mun d'auka Mutuwa zatai itama domin mun Saddakar Husaina ta mutun, Amma duk da Hakan bayan warkewar mu sai da Mukazo munka bada cigiya sai aka cemana ai da dama yara Sun mutu dai Muka hkr.

Amma Mahaifiyar su kullum Maganarta ai na hussaina na raye da yake Munfi zama a Landon to duk Lokacin da Mukazo Nigeria sai na biyo hanyar nan domin ina tunawa da ita."

Malam yace "ikon Allah domin shike k'adarta k'addara Allah abin godia."

Nan sukayi sallar azahar se kuma suke shirin tafiya.

Malam yace Hansai ta had'a kaya ta bisu nan tasa kuka dum da farin cikin dake gareta,Jummai ma kuka take tace "Hansai kibi iyayenki ai bamu Rabu ba.

Mum tace "iyayenki ne suma ai" Dady yace "lalle me iyaye hudu" aka sa Dariya nan taje iban kayanta Mum tace ta bar su a bawa wadanda basu dashi.

Haka Suhaima da Hassy suka k'an-k'ame Hansai Arif na gefe yana binsu Mum da Dady suka tsaya ya fito da check ya Rubutawa Sarkin kasuwa 1million, Malam kuwa check na 2million ya mik'a mai duk suka k'i karb'a k'arowa yayi ya Rubutawa Jummai na 500hundredk haka sukace su bazasu karb'a ba domin Hansai 'yar su ce komai sunyi ne don Allah da k'yar da sid'in goshi suka karb'a."

Dady Yayiwa Wani Driver din sa Magana kan ya karb'i check din yaje ya ciro musu.

Shamsu yace "oga driving din fa?"
yace "no Madam ta tuk'a, ka tsaya koba yauba har zuwa Gobe in Sun shirya sai kuje tare kacire Musu."

Da k'yar aka B'anb'are Hansai daga Jikin Jummai tana kuka tana kiran Baba da Jummai dak'yar tayi ta saduda suka fita.

cin-cirindon Mutane ne cike a awajen Motocin kan al' ajabin cewa wad'an nan First class d'in sune Familyn Hansai haka Hansai Da suhaima da Hassy da yasir suka shiga mota d'aya Driver yaja.

Mum da Dady suna Mota d'aya itake tuk'a su Jummai da baba sukai ta D'aga musu hannun da Alk'awarin dawowawr Dady gun Baba kan wani Aiki da zai Sama mai.

Fuuu! Motocin suka fita daga k'auyen Mangalu suka mik'a kan Titin Bunkure suka santali Hanyar kano.

Note -Hansai yanzu ta koma Husaina Husy ,don haka zakuji Ana cemata Husy.

By
Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.

.


. [11:25pm, 26/02/2017] 👑Meemi💋: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣40❣


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_


*_Wan nan page din naki ne @Ngileruma Tnz for ur luv nd care❤_*


*********


Direct Gidan Maman kano sukaje wajen k'arfe Biyar Jikin Husy yayi sanyi game da Mamakin meya kawosu Gidan Maman Anty Rabia.


Tana zaune Ita da Dan Autanta suna hira Suka shiga Falon Maraba tayi Masu, tace kuce da Ibrhm d'in kuka Mum tace Eh wlh Mama,nan dukkan su sukabo lafiyar kujeru, tace Aa Arif Dan lukuti har yanzu kanacin kayan fulawar ne?"

Dariya yayi , Tsai ta tsaya da maganar tace "to Hansai yana ganku tare ikon Allah sai naga kin saje kuna kama dasu ,keda akace Aure za'aimiki kodai Gidan Aiki kika canja?"

ba Wanda yace kala sai da suka zauna suka huta.
Dady ya kallai Maman kano yace "ikon Allah Husaina ce yar wajena data b'ace da dad'ewa wadda akace ta mutu."

Tafi Mama ta dunga Amma naji kunya yarinyar nan so biyi tana zuwa gidan nan inde za a kaita Aiki abuja ko za a maidata kasan gun Rabia tayi aiki.
Ashe ni nan Jinina ce ban sani ba ,shiisa nake k'aunar ta mana,koda yake ai duk mun Sadak'ar ta mutu ne shiisa Sam ban kawo ba
ikon Allah hansai zo nan Naji d'iminki."

Arif yace "no Maman kano yanzu sunan ta Husy not Hansai." Dariya aka saka dukka nan ta kamo Hussaina tace "wlh se yanzu nake ganin kamarta da Arif ikon Allah Ashe ba baya ba kike da kyau kunya ce ta kama Husy."

Haka sukai ta Maganar anan ta d'au waya ta Sanarwa Anty Rabia har da kuka tace Mama wlh shiisa nake k'aunarta har Raina Ashe Jinin mu ce."nan mama ta bawa Husy (hansai) waya suna ta waya tana tambayarta su Mubarak.

Bayan sun gama wayar Mama tace ni din nan da kike ganina Husaina Mahaifinki K'anina ne Uwa da d'aya Uba daya.

Mu 'yan Asalin nan kano ne Fulanin Garko Amma iyayen mu duk anan cikin kwaryar kano muke.

Kinzo cikin Arxiki Domin dukka familyn mu kowa nada Hannu da Shuni.
Babanki ya rik'e muk'amai A Nigeria irin Lucky Man din nan ne tun yana yaro shiissa tashi d'aya yazamana Done ku kanku a Landon aka haifeku acan kuke da zama yanzu hakan Ambassador ne na Nigeria to London,kuma yana kasuwanci Akwai taimakon ma kasa dashi ,Allah yasa kuyi koyi da Halin sa na taimako.

Mahaifiyar ki kuma ita Asalinta 'yar Adamawa ce fulanin can ce iyayenta Malamai kuma suna da abin hannu kakanninki duk suna nan na gun uwa Amma na Dady kuma saura Kaka mace Mahaifiyarki nada kirki da son jama'a batta k'yamar talaka kinga an raba ke kike kama da ita Hassy da Dadyn ku."

Dariya suka saka Dady yace kai Maman kano duk wan nan bayani haka?"

Tace yo Meye aigwanda na sanar Mata tunda ya zama dole.
tace yanzu dai sai an kwana 2 kyaje ki ziyarci Dangi."


Dady ya mik'e to ni na tafi Masallaci,Bayan fitarsa dukkansu sukayi wanka Saboda gajiya wajen k'arfe 9 na Dare kowa yayi bacci Abinsa na gajiya in Banda Hansai dake ta Sallah tana kai Godiyar ta ga Allah.

Sai Suhaima dake waya da Saurayinta.

*Washegari*

Hassy da Hussy na zaune sai D'an hira suke,Hassy ta ce ki saki Jikinki Tweeny"

Suhaima dake gefe tana taje kai tace "nikan Husy kinyi School ko?"

Tace "eh mana nayi Junior Class sai natafi Aiki Amma acan Anty ta d'aukon me Lessn har seda nayi Waec."

Hassy tace "Weldone Amma banso kikai Aiki ba",Husy tace "sis Ai ba yanda Mutum zai kaucewa k'addarar sa"

Suhaima tace "tabbas" "Hassy plss ban phone naki zan duba wani abu"
hassy tace kai "Ya Suhaima chatin nake"

"Ok dama bakya gajiya ai"
Hassy tace "sorry sis take it"

Husy sai kallonsu take sun bata sha'awa .Mum ta shigo tace "Oya kowa ya shirya 9 zamu tafi" haka kowacce ta shirya Hassy ta d'auko wani Material me kyau da tsada me ratsin Pink ta bawa Husy itama ta dauko wani ta saka cif sukai Ma Husy da yake kusan Jikinsu iri d'aya ne Suhaima tayiwa Husy kwalliya Hassy tace "wow my twin sis kinyi kyau"


Murmushi tayi "thnks Sis"


Hassy tace " Oya zomi Selfie🤳🏻 nan Hansai ta tsaya Hassy ta saita Ipon dinta ta daukesu sunyi balain kyau sai kamar su ta fito Rad'au.
Direct ta dora su kan Instrgram tana she's my twin sis.

Sai Dariya suke Arfif ya shugo yace wow "kunyi kyau Amma ya Suhaima Ai Husy tafi Hassy kyau ko?"

Hassy tace Lallema Lil Bro nidin?"

"No Hassy ai gaskiyane kefa bakki da Wushirya" Gwalo yayi mata.

Hassy tace komai NO Mr No kawai"

Yace "Naji tadai fiki kyau"

"Ai sekayi tayi"

Suhaima tace "zancen Gaskiya husy tafi ki kyau."

Hassy tace "Wayyo koma dai me zakuje Tweeny Dina ce munfi kusa kano da
Jigawa."

Ita dai Husy Dariya kawai take yi sai kallonsu take. Nan duk suka fita sukayi Breakfast Dady ya kalli Husy yace ya kika kwana My Lovly douter?"

Tace "Alhamdlh Dady" Mum ta kamo ta zo nan my Twin" nan Husy ta agida ta.

Hassy tace "shikenan ta k'wacen fada" dariya Arif yasa dama Dan adawar tane yace "sede ki hkr."

Dady yace "haba keda ita ai duk d'aya ne nan suka gama suka d'au Damarar tafiya Mama ta Rungume Husy "Allah yayi maki Albarka" ta bata wani Leda nan suka tafi.

Direct Gidan Kakan nin su suka tafi nan ma Sai ganin Husy ake yar dangi kakarta kuwa harda kuka tamkar ta Maidata ciki sai wajen 12 suka dau Hanyar Birnin
Tarayyya,hansai ta kunshe kai tana kukan tuno su Malam da Inna Jummai.

Muje Zuwa Dai

By
Queen Meemi👑
Queenmeemi.WordPress.com.



.
[4:33pm, 28/02/2017] 👑Meemi💋: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣

38 / 53