RABUWACE SANADI COMPELET HAUSA NOVELS BY QUEEN MEEMI.txt

Author :  Queen Mamie Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   35 / 53

102K to 105K   out of 158.2K words

"Suhaima tace banga frnds namu na Secondry ba! ,Sady tace "nakai musu inaga ko sai na gobe" suhaima tace "okay nikam ina yarinyar dazu? Sady tace Wan nan Dirty Gal din 'yar Aikin Gidan mu ce fa!

Suhaima tace "yarinyar she's so beautiful kawai naji ina sonta", Sady tace "ke rabani da wan nan ai kema me kyan ce ,Zaki zo goben?"

Tace "eh kinsan fa Gidanmu duk suna Landon nima Hutu Nazo Saboda na samu Hutun School nima Ina Gwarinfa Gidan Kanwar Mami Aikinga kuwa dole nazo,yanzu ma inason zuwa Bakery ne kicewa Anty ina gaisheta Gobe zamu had'u,nan sukai sallama ta tafi.



By
Queen meemi
*Queenmeemi.wordpress.com* .


. . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣33❣ . *FEB,2017*


®NAGANTA WRITERS ASSOCIASION(NWA)


_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman Family's_


_Sak'on gaisuwarki ya iso gareni *MAMAN SAFYAN*nagode da kauna da kuma bibiyar book dina ,da duk masoya masu turon da sako NGD.❤_

*********

Washegari Alhamis shine ranar kamu inda wajen k'arfe Hud'u Atafkeken filin Gidan su akai Decoration na Gargajiya su kwarya ,tum-tum,su Ludaya ,Fai-fai da sauran kayan Gargajiyar yayi kyau don masu tsara irin gun aka d'auko ga Masu kid'an k'warya ne da yan Gad'ar su aka dauko nan suka zo, yau duk shigar Gargajiya sukayi inda Amare Suka sa Super Sharaton Babbar Aka d'aura musu Gwaggwaro(head)da Atampar rigar akai Buba suka dora zanin akan Rigar sunsha Makeup sunyi kyau kamar ka D'auke ka gudu Amma yau kowacce da kalar tata Sai d'aukansu Vedio ake idan DJ ya kada sai mai kid'an k'warya tabuga.

Su Sady Kamar kai ya tsinke ko ina ka kalla sai walwali yake Ga yan Gada sai yi suke su Mama sai liki suke wa Hajia dake tsakiyar fili da Sauran Dattijai sai rawa suke , ko ina wadace da kayan motsa baki kowanne tebur.

Dai de an fara Kamu Ana ta zuba Uban guda wayar Sumy ta buga nan ta d'auka Nazi ne yace yana kofarar Get ta fito zai bata sak'o,tafita sai yauk'i take kugun nan yasha Murjani ,tana zuwa ta tsaya "my Nazi How far?" yace "fine dear ya Biki?" tace "Alhmdlh."

Nan ya mik'o Mata Gift Ga "wan nan ki bawa Sisters namu Gudunmawa, Dad'i taji tace 'oh! dear Sun Gode" yace "they diserve more" Murmushi tayi "Jirani na dawo" Juyawa tayi tana Mirgina Ukwu binta yayi da Ido ,kamar ance ya Juya Hansai ta fito daga Mak'ota da wani Makeken flaks akai da sauri ya fito zuciyar sa kamar ta fad'o wani irin Bugawa datayi tayi fat! fat!, "Hansai" taji ankirata cak! ta tsaya juyawa tayi Ya kafa Hula yayi shigar Abuja Boys ,yace "ke ya Biki?" Jiki na rawa tace "Lafiya"

Dariya yayi yace "ke bakya sona ko? dara daran idanuwanta ta d'ago ta zuba mai "I can't love you"

Shafa gemu yayi "Lol Yarinya kinfara Jin Speak ashe ,Harara ta watsa mai ta tafi ,ya rik'o maya finta, dai de Lokacin Sumy Ta fito rik'e da flaks da kayan take Away.

"Tab jar Ubban can!" tsawa ta dakawa Hansai "me kike anan? Jiki na rawa tace bkmi Anty" harara ta kaiwa Nazi yace "Sorry Princess tambayarta nake."
Mari ta kaiwa Hansai har da bugu ta dumata Dundu abaya, Durk'ushewa tayi tasa fasa kuka Nazi ya had'e rai "wait Sumy ki daina dukanta."
idonta yayi ja saboda kishi tace "ya zaka zo kana nuna Mata so bayan kasan banso wallahi hansai sekin ganekuren ki, in banda son matanka me zakai da hansai ,Ai se Nuhu maigadi, ki sani wild duk randa Na kuma ganin ki dashi sai kin koma kauyen ku."

Wani kallon masifa Tayiwa Nazi karma kazo kana ban hkr domin bazan Saurareka ba.A fusace Nazi ya shige Mota da Gudu taje mai take away a gaban motar afusace ya ja nan ta dawo kan Hansai "tashi banza ko yaushe akanki nake samun matsala da Nazi rankwashin ta tayi mai zaiyi dake adauri kashi ko abata Igiya."

Motar Suhaima ce ta Danno kai ta yau ba irin ta jiya bace motar hon tayi ganin Gidan cike ba Space yasa ta Dan matsa gaban Gidan tai Parking Motar ta fito Yauma tayi kyau kana ganin ta kasan hutu ya ratsa yau kuma shigaright Purple tayi, tayi Masifar kyau.

Sumy ce ta ganota "Oyoyo Sis Suhaima Welcm" idanuwan Suhaima ne suka sauka kan Hansai tayi Murmushi "meya faru yau kuma?" Sumy tace "Rabani da wan nan banzar 'yar Aikin tunda Saurayina ya k'yalla ido ya ganta Raina ke b'aci Agabana yake nuna Mata so bazan iya d'aukan kowane irin Nonsense ba wallahi."

Tausayin Hansai ne ya kama Suhaima tace "Sorry Aiba Lefinta bane" Sumy tace ai sena renama Nazi hankali.

Kamo hannun Hansai Suhaima tayi Ta d'aga ta ta mik'e nan ta dau flsk din Ta kalli Suhaima "Nagd" Duk yayin da ta kalli Suhaima se gabanta ya fad'i nan suka shige Gidan .

Biki yayi Biki gud'a ko ta ina nan aka bawa Suhaima Mazauni Lemo kawai tasha Sady Tazo ta jata Gun Frnds nasu sai yau shegamo suke domin An dade ba ahadu ba, sai kiran wayar Anty take ta nan sukai waya ta tashi ta doshi cikin Gidan Direct side d'in Anty tashiga.

Anty yau bata fita ba sakamakon kanta dake ciwo Da dugu Suhaima ta Rungume Anty tace "I mssd u Anty" Dariya Antyn tayi "Saukar yaushe? dama kuna Nigeria? Suhaima tace "no Anty hutu Nazo" duk Family suna can Amma Suma zasu zo hutun."

"To Allah ya kawo su cewar Anty."

Suhaima tace "nikam Anty akwai wata 'yar Aiki tun jiya Naganta yauma Naganta." Anty tace "wake nan? Kin san suna da yawa."

Tace "Kinga wata 'yar fara haka yar Doguwa bacan ba mai Manyan Ido da dogon hanci ,tana da Gashin Gira Da yawa harda Wushirya."

Dariya Anty tasa "Tamkar kanki kike Suffan tamin ai"

"Aa walh Anty aikin ga ni Banda wushirya kawai de haka take."

"Kode Hansai kike Magana?" kamar da had'in Bakin Hansai ta shigo da Khalil A hannu yana kuka .

Suhaima tace "yawwa kin ganta" Anty tace Au Hansai ai 'yar Aikina ce"
Suhaima tace "tana Birgeni Ga hankali saide ko yaushe saina ci karo ko Sady da Sumy na dukanta."
tace "ai haka suke sai hkr" .

wurin Bikin suka koma Haka akayi akagama aka watse

Washegari ta Kama Friday inda Amare da frnds Nasu suka hada lunching Nan ma ba a magana Na chase Inda Nura m inuwa yayi barin Wak'okin Bakin.

*Washegari Ranar Daurin Aure*

Nan ma Washegari Ta kama Saturday aKa D'aura Auren *RUMASA'U DA ALHAJI MUSA*

*RUBAYYA DA MUSTAPHA*

*ZUBAIDA DA FAWWZ*

Aka shaida Akan Sadaki Lakadan ba ajalan ba Kowacce dubu Dari Biyu.
Lalle burin Dady ya cika domin garin Abuja sun san Ana Bikin, ko ta ina mutane.
Su Mama kuma Suka Zarce Da yini Nan ma Faty Niger ce Tazo ta wak'e Amare.Haka akai biki Lafiya aka Gama sai fatan Zaman Lafiya.

Washegari Ta kama Ranar Sunday Aka fara shirin Mik'a Amare Zuby Anan Abuja Gidan ta Yake Haka Ruma ,Ruby ce zaa Mika ta Lagos ita se Washegari.

Amare sunci kuka sunkoshi kowacce akai musu Nasiha aka mika ta Had'dden Gidan ta.

Litinn Da safe aka tafi kai Ruby,Sai de muce Allah ya bada Zaman lafiya.

kudakace ni Fans sai kuma gobe In kowa ya huta da gajiyan Biki.


By
Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com


. . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣34❣
*FEB,2017*


_®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASSION_


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_



**********

Gida an Gama Biki an watse sai su Hajia da sai tayi Sati 2 san nan zata tafi ,sai su Sady sai hutun gajiyar biki suke haka su hansai keta aiki ko ina agidan saboda harkar biki sai an bata gu,Hajiya da Umma da Mama ke break fast A babban Falo tace "ku yanzu bakuji Dadi ba! jin kamar kun sauke Wani nauyi da Allah ya D'ora muku,musamm idan.mace ta isa Aure kuyi Mata inde ta isa Dan Sauke Nauyin Da Allah ya D'ora maka."

Mama tace "Wlh kullum sai nayi wa Allah Godia Saboda min sauke wani nauyin ." Umma tace kedai Bari Allah dai ya bawa yan baya maza na gari."
Hajiya Tace "Ameen".


*Bayan wata D'aya*

B'angaren Amare kuwa sai san barka Musamm Zuby Soyayya suke kwasa da Fawwz Dan sun tafi Honeymoon Dubai,haka Ruma tana zaune Lafy da Alhaji Musa Saboda Gidan ta da ban kuma sun fahimci Juna, sai B'angaren Ruby ma hakan take.


Sady ce zaune ta kafawa waya I'do tace "Sumy wlh inada damuwa! kin san wan Handsome din nan Wanda muka had'u dashi a Bikin Futha 'yar Minister ,wlh na Kamu da Sonsa."
Sumy ta d'ago da gud'a "yirrrrr! Lol Amma nayi farin ciki yanzu duk Irin Mazan dake sonki duk basi maki ba se yanzu nikam Zanso Naga wan nan Guy."

Sady ta FarFara Ido "ai suma zakiyi Idan kuka had'a Ido, keni fa Numfashina har neman sark'ewa yake yayin da na kalle shi ki,ba abinda ke Birgeni dashi sai basarwa d'in nan."

Sumy ta tab'e baki "ayi dai Mugani."
Hansai ce ta shigo da Mopper ahannu zatai Guga Sumy ta Harareta "Get out" Juyowa tayi ta koma Sumy tace "ban san Yarinyar nan Cuz duk ta Birkitan Nazi."

Sady ta k'yalk'yale da Dariya "tab! Amma Sumy kin fad'o kina Big Gal, Amma ace tsami Hansai zata kasa ki koda yake tafa kile yanzu, ahakan ma bata son sa kenan."

Sumy tace "Barni kawai kin san Nazi yanzu se yayi me gaba d'aya!"
Sumy tace "to ni wai kinsan Sunan shi Saurayin da kike so? tace "Aa"

"Aa! kinada Wahala sai ki dage."

Sady tace "Futha zan tambaya kawai!"
tace "daya fi maki," wayar Sady tayi K'ara ta d'auka Ganin number waje yasa ta daga "Aa Suhaima!" tace "naam"
"kin koma ashe!" tace "eh hutun ya k'are ai se kuma nan da 3 Month zan kammala Degree zamu dawo da har su Dady". Sady tace "Allah ya kawo ku,"
"Ina Hansai kuwa? tsaki Sady tayi "ke kin Mak'alewa 'yar Aikin nan tana can tanayi"
Tace "Okey ki Gaida" ta nan sukayi Sallama.


*8:Pm*

Nazi ne a d'akin wani Abokin sa suna kallo "yace Khalid kasan Sumy?"
yace "eh man!
yace "to Gidan su akwai wata Yarinya wlh ban d'auka Sonta nake da Gaske ba, kwanakin nan duk ta dabaibbayeni,kuma matsalar batta sona."

khalid yace "haba naga Sumy ce Budurwarka! yace "eh Dan so ina son Sumy, Amma Soyayyar Yarinyar nake sosai."
Yace "tab! zaka had'a Jalala kasan ba yarda Sumy zatai ba"
yace "sosai so nake kaban Shawara," shuru Khalid yayi kawai ka hak'ura da d'aya"

"Nida Sumy zata hkr ai nafison hakan" yace "Haba kai ma kasan Dadyn ka bazai so had'a iri da 'ya'yan talakawa ba ,naji kace 'yar Aiki ce ma"
Nazi yace "ni ba ruwana da wan nan inde akwai so is okey" khlid yace "my Fnd kawai ka rik'e Sumyn ka so me sonka" yace "zan Gwada."



* After 2 Weeks @4pm*

Juyi Sady keyi adaki don kuwa duk ta tashi hankalinta Domin Sosai take son Dream Guy nata Ganin ba sarki sai Allah yasa ta watsa kiran Futha
Ta dauka "Amarya bkya Laifi" tace "ya San Ranki" D'an Jimm tayi "nikam Futha a Bikin ki ai Naga wani Handsome Guy duk Samarin gun sai de Subi bayan sa wajen haduwa"
Tab'e baki Futha tayi "Banda Mijina dai!" Sady ta sa Dariya "haba dai Futha ai ko Mijinki Al barka, Pls kin san Shi ?"
Tace "ke ni ta ina zan sanshi" nan tayi taimata kwatance bata gane ba tace "aidama bazakii gane ba" tace "eh naji" nan suka kashe.


Kande ce ta shiga D'akin tace "Anty Sady wai kin bak'o awaje" tab'e baki tayi "naji"

35 / 53