Chapter 10 Reading THE REGRET BOOK COMPLETE BY BUDDO.txt Arewa Novels

THE REGRET BOOK COMPLETE BY BUDDO.txt

Author :  Buddo Category :  Hausa Novels 001

Chapter   10 / 13

27K to 30K   out of 37K words

My Hafsy Dear.

Umty luv 🥀,, Sis Mansura. And so on.

This page is dedicated to you guys. I love you all 🤫🌚



The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!



Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂💔


Mallakar Pending Amarya ce_



NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl











🦚💎
LONG CHAPTER ✍️


_PENDING AMARYA _


Page 19





Ƙarasowa su ka yi su ka zauna ku sa da Neneh, cikin muryarta mai cike da manyantaka ta ce "Lale marhaban ya Rafiƙ." Murmushi ya yi tare da gyaɗa mata kai alamun ya na jinta......





Kallon Liyana ta yi sannan ta kalli Jiddah da ke zaune, ya gane abin da ta ke nufi dan haka cikin sanyin muryarsa ya ce "Ya Zahra." Ɗago da kanta ta yi because haka Jiddah ke kiranta, "Shiga ciki manya za su yi magana." Nodding kan ta ta yi tare da ɗaukan wayarta ta nufi ɗakinta ba tare da ta tankawa Nenehn ba.


Matsowa ta yi sosai tare da kamo hannunsa ta ce "Rafiƙ, khairatu ce ta same ni da wata maganar da ta faranta min rai sosai, ɗan wajenta Hydar dai namu da kuma Liyana ta ke son a haɗa aure, ai kaga ɗaurewar zuminci kenan." " Liyanar ta ce miki ba ta da manemi ne?." "Ta doshi wata a gidan nan wallahi ban taɓa ji ko da wasa ance ana sallama da Liyana ba." "Zan ji ta bakinta toh dan ba za'a mata dole ba." " Toh Rafiƙ Allah dai ya tabbatar da Alkhairi shi ne kawai."

Bayan shigar Liyana ɗaki kuwa waya su ka kuma yi da Sultan.


Bacci ta ƙara komawa, ta yi baccin sosai, sannan ta tashi arround 4 , ta yi wanka tare da brush.sai da ta tsane jikinta sosai sannan ta ta fara shiri because partyn ma anko su ka yi ita da Lilian.

Duk da ba wani tsada ne da kayan ba ta zaro su daga cloth set ɗinta da ke sheƙe da kaya saboda shopping ɗin da ta ke yi, carton colored palazzo trousers ne sai normal hand long sleeve shirt coffee color sannan ta ɗaura ɗankwalinta matar minister, gucci high heels masu kyau black color sai jaka shima gucci black, latest phone ɗinta wadda ake ya yi iphone 14normal ta ɗauka tare da cilla fresh mint chewing gum a baki sannan ta shafa lipstick a heart shaped full lip ɗinta, sai ya ƙara wa shigarta kyau da kuma tsari, ba za ka so ka mata kallo ɗaya ka ɗauke kai ba.
Wani ɗan siririn eye glass da ke kama da medical glasses ta sanya amma kuma is for passion masu kyaun gaske da ɗaukan ido, sai da ta ɗauki wayarta ta sakarwa Instagram reels sannan ta fito parlour da Neneh ke ta kallon AIT NIGERIA.


kallon Nenehn ta yi tare da ɗauke kai, ta nufi Jiddah da ya ke a zaune ya na kallonsu.
" Jiddah! Dan Allah car key za ka bani." ta faɗa tare da siddar da kanta ƙasa,"ki amsa a wurin driver, sannan ina za ki je ?." Ba za ta iya faɗan birthday za ta je ba Jiddah is very judgemental, zai iya hana ta zuwa idan ta ce masa birthday za ta je.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan cikin muryarta mai zaƙi ta ce "Jiddah akwai wani ɗan ƙaramin biki da aka haɗa mana a school. Ƴan ajinmu ne suka shirya mana tun jiya bayan mun gama last paper na level300, shine ake ɗan ƙaramin biki." "A ina za'a yi?." Ta ƙara tsintar muryar Jiddah a kunnenta.

" A can wani ɗan gidan abinci a nasarawa G. R. A." "Allah ya tsare, in kin dawo za mu yi magana okay?." "Okay grandpa." Ta faɗa tare da bashi side hug. Ba ta kai ga fita ba Neneh ta ce " yadda ki ke rawan jikin nan da ƙyar in gaskiya kika faɗa." "Bara inna dawo zan yi maganin ki young lady." Daga haka ta fice tare da shigewa cikin Lexus LX 600 mai numfashi da tun ɗazu ta amshi car key ɗin wurin drivern Jiddah Adnan.


Sai da ta ɗaura seatbelt sannan ta yi connecting waƙa cikin talent ɗinta na tuƙi ta cilla hancin motar kan titin da ke shinfiɗe a street ɗin.

Tana jin waƙar ta na gyaɗa kai a daidai kwanar da za ta sha ta ɗauki hanyar kabuga ta bige wani ɗan Lexus RX 350 da sam ba ta lura da shi ba.

Kuma parking ɗinsa aka yi ba tare da an lura cewa kan hanya bane ba.
Wani ɗan ƙaramin tsaki ta ja tare da parker motar ta fito ta na kallon motar Jiddah da babu abin da ya sameta, sai wannan Lexus RX 350 ɗin da fitilarsa na baya ya ɗan fashe.


She didn't bother tun da babu abin da ya sami motarta har ta buɗe driver sit ɗinta ta zauna tare da fara driving ɗinta.
Aliyu da ke cikin motar ya na jiran isasshen da ya buge mai mota ya zo ya basa haƙuri har ya ga an tayar da motar.

Bayan an bashi fruit ɗinsa bayan motar ya bi ba wani delay.
Gudu ta ke shararawa, shima binta ya ke bai cimmata ba har sai da suka ƙaraso Piccolo, sannan ya yi mata overtaking, wan da hakan ya sa taja birki ta tsaya.

A fusace ta fito tare da rufe ƙofar motar da ƙarfi, shima fitowa ya yi ya kalleta da kyau he was shocked to see her again, ya na ganinta ya ganeta just ɗan girman da ta ƙara da kuma minor things haka, cikin tafiyarsa da ke cike da izza da kamala ya tako ya tsaya a gabanta tare da nuna ta da ɗan yatsa tare da faɗin ''haba no wonder, daman nasan wannan aikin sai mata irinku marasa tarbiyya da kamun kai, waƴanda iyaye ba su isa da su ba, You hit my car and you can't even say sorry, that's pure arrogance, kuma kika kaɗa motarki like nothing happened, is that a manner?.''


Tass ta wanke sa da mari, ya ɗago fuskarsa ya kalle ta sosai, wani marin ta ƙara wanka masa sannan ta ce ''baka sanni ba ba ka san ko ni wace ba za ka zo kai ta gayamin maganar da basu dace ba idan kasan wata ba ka san wata ba, kuma na mareka sai na ga uban wanda ya tsaya maka, complementry card ɗin Abbhi ta wulla masa tare da address ɗin gidansu, ta ƙara faɗin '' ga shi idan za ka kai ƙarar nawa wurin waƴanda su ka bani tarbiyyar. Christmas goat.'' tare da jan tsaki ta shige motarta tare da yin reverse ta bar wurin gaba ɗaya ta koma gidan Neneh.
Hydar da ya yi mutuwar tsaye,ya ji tsanar yarinyar ta ɗirar mai a zuciya a lokaci ɗaya.
Ya shige motarsa tare da kama hanyar komawa gida, dan yanzu haka he couldn't control his self. Dukan mace ba halinsa bane ba da sai ya yi mata lilis kafin ta bar nan.
magana shi kaɗai '' amma yarinyar ta ci ni wasa ya tsani yarinya mara kunya a rayuwasa.'' so ya ke ya tuno a ina ta faɗar mai da waya amma ya kasa, je must teach her a lesson, Allah ya ƙara haɗani da ke.''
Allah ne kaɗai ya kai Liyana gida, dan kawai tuƙi ta ke bata ko ganin gabanta, ranta ya ɓace sosai,ka zageta da komai amma banda rashin tarbiyya tana cikin haka ta ji wayarta na ringing, ''Who's that idiot?." tare da ɗaga wayar a ƙufule.
Lily cikin muryarta ta ce '' Liya it's time already kuma ba ki shigo ba har yanzu.'' ''I'm not coming.'' tana faɗan hakan ta kashe wayar.
Wani kalar horn ta ja wanda ya sa mai gadi ta shi a guje ya buɗe gate ɗin a miliyan ta shigo gidan tare da parker motar ta shigo cikin gidan Neneh na zaune ita da Salimah suna taɓa hira.

''ni dai wallahi a wurinmu da safe ake wannan, ya mutum zai shigo ba sallama kamar jiƙar bob Marley, ayi mutum ba tsari Allah na tuba.''

''Neneh da na shigo gidannan ban miki magana ba ki bar ni da abin da na ke ji.''


''Ahaf ai sai haƙuri nima haka na yi ta fama da samari a zamanina wallahi, ai na ki mai sauƙi ne.''

Tsaki Liya ta ja tare da kulle ƙofar ɗakin da ƙarfin tsiya.
Cire kayanta ta yi tare da watsa ruwa ta shirya cikin kayan bacci mai tsantsi dan yau ana isha za ta kwanta.
Salima ce ta shigo tare da kawo mata strawberry hollandia ɗinta ta ajiye mata a bedsides.
''Aunty Liyana Jiddah na kiranki wai a ɗakinsa.'' ''I heard you.''
Tana faɗan haka ta ɗauki wayarta tare da ficewa daga ɗakin.

Kallonta Neneh ta yi ta ce '' masu magana da yawun Queen Elizabeth, an fito kenan.''
''Wallahi Neneh darajar Abbhina da Jiddah ki ke ci a gidan nan, na bar Rufaidhat a gida na zo na huta kuma ki tiso ni gaba, who does that huh.''
''Salimah maza ki je, can ƙarshen layi, gidan gonan Alhaji Kyari ki tsinko mata tsamagiyya ta mun duka hankalinta ya kwanta.''

Kallon Nenehn ta yi sannan ta buga ƙafarta ta hau saman stairs.

''Ni na rasa mai Khairatu ta gani jikin wannan ta kamawa Hydar, dan wannan ta fi ƙanjamau illa.''

''Amma ai Neneh ke kika fara yin maganar kafin Mamin.'' Salimah ta faɗa ta na kallon Nenehn.
''yi aikin ki banason shirmen banza.''




Ƙarasawa ta yi ɗakin Jiddah da ke magana akan companyn sa da ake rulling na man gyaɗa a can Lagos.

Zama ta yi kusa da shi ta ce '' Jiddah da ma ina son maka magana da daɗewa.''
As usual he just smiled, sannan ya bata attention, '' Jiddah Please ka taimaka ka yafewa Abbhina abin da ya maka, we are all humans, we make mistakes, we are not perfect, at times wallahi sharrin shaiɗan ne ba komai ba, forgive and forget, you are a muslim, let bygones be bygones, please grandpa.'' ta ƙarasa maganar da hawaye because ba ta ɗaukan abin mahaifinta da wasa.



'' Ya Zahra.'' a sanyaye ta ce ''Na'am.''

''ki ce mai ya zo ina neman sa gobe In shaa Allah, kuma kar ki ba ri Neneh taji am I clear.''
''Yeah grandpa, tomorrow is my birthday anything for me, kuma dama ya ce gobe zai kawo min birthday gift soo no need na gaya masa ai.''

''Idan kika aminta da ni i promised you kujerar Hajji this year In sha Allah, Allah ya miki albarka za ki ji saƙona ta wajen mahaifin na ki, and kina da manemi?.''

A rayuwar ta sai yau ta taɓa jin kunya '' Noo i only have friends.'' (Ashe Liya na da kunya 🤫🌚😂).
''alright.'' daga haka ya cigaba da aikinsa da ya ke kafin shigowarta.

Murmushin ta mai kyau ta yi tare da ɗaukan wayarta ta masa sai da safe sannan ya wuce ta koma ɗakinta.


Washegari da sassafe tasa Salimah ta haɗa ma ta snacks with cupcakes, da kuma wasu abubuwan munch it.

Sai kuma juice because yau ne za ta cika 20 years 15 December. Kuma yau Sultan da yayan shi za su zo gidan Neneh, kamar yadda ya tsara birthday gift ɗinta zai zama shigowan magabata cikin relationship ɗinsu.


Zoo road tasa driver ya kai ta ta amso ɗinkinta na corset gown ta dawo gidan tare da haɗa komai a cikin wani ɗan ƙaramin trolly because kwalliya zata je yau ɗin.

Wankan ta ta fesa arround 10 O'clock saboda partyn zai fara from magrib kuma Leena event center za su yi ita da ƙawayen Lilian dan ita ba gwanar tara friends ba ce ba berekete.

Mint chewing gum ta cilla a baki tare da ɗaukan wayarta ta sa slippers ɗinta ta yi sama ɗakin Neneh ta na waƙan Ayra star _Bloody Samaritan_ .

A hankali ta tsaya a bakin ƙofa tare da leƙo kanta ta ce '' Tsohuwar manya, na fita unguwa ki sa ka Salimah ta dafa min fried rice dan Allah.'' ''Fridge za ta dafa ba fried rice ba.''
''Kya ji da shi.''
Daga haka ta fita daga ɗakin tare da kiran Ily dan tare da su je makeup ɗin.

Mukullin motar Jiddah ta amsa a hannun Adnan tare da barin unguwar ba ki ɗaya.

Sai da ta biya ta ɗauki Ily sannan suka ɗau hanyar France Road, wajen TMUAH, makeover.


Sun ɗauki lokaci sannan Abbhi ya zo ya ɗauke su.
Wani kalar sinadarin kyau Liya ke fitarwa, ta yi kyau sosai. Sam ba za ka ce Liya ba ce duk da is not heavy make-up.

Sai videos ta ke ta na Posting a Instagram because she's not a fan of TikTok dan mahaukatai ne marasa class, a cewarta.


''Abbhina yau Jiddah ya ce zai yi magana da kai i hope all is well.''

'' kar ki damu kan ki okay.''

ILY dai ba ta yi magana ba she's busy chatting with her friends da ta ke inviting zuwa birth day ɗin.

Sai arround 5 su ka isa gidan, wan da a ɗan kiɗime ya ke dan bai san mai zai tarar ba ya san waye Jiddah, farin sani ya yi mai ba kaɗan ba.

A hankali ya yi parking motar, idanun Liyana na ta yawo akan wani mota ɗan ƙarami ƙirar Kia Picanto da ke parke a compound ɗin ga rubutu a jiki _HAPPY BIRTHDAY DAY MAKER_ da sauri ta rungume Abbhin da ke kusa da ita ta na mai addu'a sosai.

Sannan ta amshi wayarta a hannun Ily ta fara videos ''_I love my Dad, my rock, bla bla bla_.''
(Sai shegen iyayin tsiya🌚😂🥱).


Shi ya fara shiga cikin gidan Neneh na zaune ana mata tausa.

Ko da ya shigo ya tarar da Neneh da ta ɗago kanta ta gan shi, cikin muryarta na manya ta ce '' Fita, fita, fita, kar Mala'ikun rahama su ƙi shigo min gidan dallah.''
Ta na ganin Liyana cikin shigar purple material da white stones da ya bi shape ɗinta ya lafe ga nude make-up da ya saje da fatar ta, ta ce '' wai Nabil ka haifo min skeleton a gida fi sabilillahi du be su kamar zombies, ita kuma wannan wacece? Ko Rufaidhat ɗin ce wannan?."

Liyana ba ta kalleta ba haka ma Ily da ta ke ta kiciniyar tafiya da heels akan tiles (😅hegiya gayu 😂).

Jiddah ne ya sauko cikin shigarsa ta kullum da walking stick ɗinsa.
A hankali ya ƙaraso ya zauna tare da kiran sunan Abbhi ''Nabil." ''Naam Babana.''
Cikin muryarsa na manyantaka ya ce '' Liyana maza kije bidirin na ki zan sa Adnan ya ɗauko ki.''
'' Okay granny."

Daga haka su ka fita tare da kama hanyar zuwa Leena event center.


Kallon Nabil ya ƙara yi sannan ya ce '' Nayi wa Liyana miji.'' zunbur Abbhi ya miƙe..............




















Sorry da bana update kwana biyu yau da zafi na na taho 🥹💎





THANK YOU FOR READING 💜




To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.
Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.
See you in the next chapter of our journey.

With love,
Pending Amarya 🦋




> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋

> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.


Pending Amarya as usual 🦋 🫠


I really love you readers 💎

> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday
> Mondays to Fridays from 8am to 12am follow for more 🎊🫂📚> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇 🤫



https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V






*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪

:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

The Noble Writters ✊
Dedication is our strong

THE REGRET 🙆

when love meets temptation who survives?








The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!



Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂💔


Mallakar Pending Amarya ce_



NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl






THIS PAGE IS DEDICATED TO AUNTY KHAIRY AND MY LOVELY FANS, MY LOVE FOR YOU IS BIG, BIGGER, BIGGEST 🫵🫂



Am in love with you 🌚 I won't lie babies 🤗😂🌚




🦚💎
LONG CHAPTER ✍️


_PENDING AMARYA _
Page 20

Daga haka su ka fita tare da kama hanyar zuwa Leena event center.
Shima Jiddah da Abbhi su ka hau parlourn sama domin tattaunawa.

Kallon Nabil ya ƙara yi sannan ya ce '' Nayi wa Liyana miji.'' zunbur Abbhi ya miƙe, sannan a hankali ya koma tare da durƙusawa a gaban Jiddah ya na mai alamar roƙo da hannunsa, a hankali ya fara magana, '' Baba ni nasan mai laifi ne, na amshi laifina, amma Dan Allah Dan Annabi kar laifina ya shafi Liyana, ba yanzu na ke da burin aurar da ita ba na fi son idan ma auren zan mata ta kai irin 30-35 haka kafin nan ta mallaki hankalinta, idan na mata aure yanzu, zai iya zama child abuse, kuma law zai iya kamani please Ba........

Bai kai ga ƙarasawa ba Neneh da shigowar ta kenan ta ce " Da kai da law ɗin kun ci kaza - kazan ubanku."

Jiddah da ya ke ta kallon Nabil tun da yafara magana ya ce " Umarni na baka ba shawarar ka na ke nema ba, ta shi ka ɓace min a wuri na gama magana."


" Ai kai ka tsaya jin sa ka ɓata lokacin ka akansa, in dan ta ni ce ai sai dai ya ga invitation card and kawo masa, kawai dan a fita haƙƙinsa ne a matsayin uba shi ne kawai, amma ai yarinya na hannun mu yanzu sai yadda na yi da ita Nabil ɗin banza Allah na tuba.'' Neneh da shigowarta kenan ta faɗi hakan.



Shi dai Abbhi kansa na ƙasa ya na jin tausayin Liya na kamasa, yarinya ƙarama haka a kawo mata maganar aure duk da ace mijin ta ɓangarenta ya fito zai yarda.


Nenehn ta ƙara faɗin ''in ka je ka sanarwa Salamatun, ita kuma uwar daɗin miji, kar ta tashi tsaye, kuma ka aiko min ita nan gobe da sassafe, zan yi magana da ita, in kuma ka isa kaje ka hure

10 / 13