Chapter 8 Reading THE REGRET BOOK COMPLETE BY BUDDO.txt Arewa Novels

THE REGRET BOOK COMPLETE BY BUDDO.txt

Author :  Buddo Category :  Hausa Novels 001

Chapter   8 / 13

21K to 24K   out of 37K words

dai ubanta be buɗi baki ya ce amana ba ni nasan amana ce a wurina bara na je na rarrasheta ba kunya ne da ita ba tsaff za ta kwashe kayanta ta tafi gidan wancan koɗaɗɗen, ga shi ina fama da kaɗaici, kuma mansura ba aure kusa ba balle ta zo ta ɗauke ni na mata zaman ɗaki."


Haka dai taita ƙananan maganganu har su ka gama cin abincin su ka hau sama.


Liyana kam daga ƙarshe dariya maganar Neneh ta soma bata lokaci guda kuma mood ɗinta ya sauya saboda tino da Sultan da ta yi jiya ai lafiya lau suka rabu, buh ita dai ba ta damu ba, in dai Sultan ne da kansa zai sauko, dan ita kam ba ta san mey ta masa ba.

Komawa tai gado ta zauna tare da ɗaukan wayarta ta ƙara dailing numbersa, ringing biyu ya ɗauka, shashsheƙan kuka ta fara tare da turo baki ta ce " did I do anything wrong da za ka yi punishing ɗina da not talking to you for almost 24hrs?."
" Babe you did nothing, kawai I don't like it kina posting kan ki a status day in day out, I don't like it, ki daina bana so."
"Buh dear posting status is normal." "Sai ki cigaba tun da in an miki magana ba kya ɗauka." "Am sorry." "Zancan kenan ai, toh ya kike ya su Ammi?." "Suna lafiya ya su Abuh da Mami." Daga haka suka cigaba da hirar su ta soyayya.



Ko da suka gama wayar wanka tai ta ɗauro alwala tai sallah sannan ta kwanta bacci.



Da sassafiyar ranar ta gama shiryawa cikin wani black yard da ya yi mata kyau, ɗinkin palazzo trousers with bubu shirt sannan tayi ɗaurin matar minister ta ɗauki jakarta ƙirar Gucci white color sai flat shoe Lv (Louis Vuitton) shi ma white color, sannan ta ɗauki wayarta ta fito dan bata tunanin za ta saka mayafi yau.


Ko da ta fito babu kowa a parlourn masu aiki ta bawa ordern fruit salad sannan ta dawo parlourn ta ɗauki wayarta ta na game ɗin candy crush.


Neneh ke saukowa daga matattakalar benen dai-dai lokacin da mai aiki ta kawo mata fruit salad, ɗago kanta ta yi suka haɗa ido da Neneh, harara ta sakar mata sannan ta fara shan fruit salad ɗin.
"Li ilafi ƙuraysh aniyar ki ta bi ki ƴar nan."

Ko kallonta Liyana ba ta yi ba,ta cigaba da shan kayanta.

"LIYANA ina kwana". Neneh ta faɗa. " Lafiya lau kin tashi lafiya?." Sakin baki Neneh ta yi kawai ba tare da ta yi magana ba.

Bayan ta gama shanyewa kitchen ta shiga tare da ajiye ceremic bowl ɗin ta ɗauki wani lunch box ta zuba strawberry Hollandia yourghurt, da kuma milky donut a cikin wani fancy rubber wanda zai ishe ta ita da Lilian.

Ko da ta fito suna zaune akan dinning table suna cin abinci ɓangaren Jiddah kawai ta je ta gaida sa tare da tambayar lafiyar jikinsa sannan ta yi hanyar waje zata fita.

"Ashe Nabil dai sisi Legas ya haifa ban sani ba?." LIYANA juyowa ta yi ta ƙara dalla mata harara a karo na biyu sannan ta fice daga falon. Motar Jiddah ta sa driver ya kaita school da shi..........


THANK YOU FOR READING 💜

To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.
Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.
See you in the next chapter of our journey.

With love.
Pending Amarya 🦋




> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋

> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.


Pending Amarya as usual 🦋 🫠


I really love you readers 💎

> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday
> Mondays to Fridays from 8am to 12am 📚> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V

> THE REGRET COMMENTS SECTION ✅ 👇


https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=ac_t



*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪

:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

The Noble Writters ✊
Dedication is our strong

THE REGRET 🙆

when love meets temptation who survives?





The very first day we met, I told you how I felt, wallahi i dey melt my baby you're the best 🫵✅🤗





The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!



Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂💔


Mallakar Pending Amarya ce_



NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl




THIS PAGE IS DEDICATED TO MY DEAR SIBLINGS MY STRENGTH

Every page I write carries a piece of our laughter, our fights, and our unshakable bond
This story is not just mine it's ours 🤗🤝







CHAPTER SEVEN : Neneh 😂🫵💎

_PENDING AMARYA _


Page 16




"Ashe Nabil dai sisi Legas ya haifa ban sani ba?." LIYANA juyowa ta yi ta ƙara dalla mata harara sannan ta fice daga falon. Motar Jiddah ta sa driver ya kaita school da shi..........




Bayan sun fito daga lectures arround 2 O clock, motar Lilian da ta zo da ita wanda Lamin ya siya mata.

Da shi suka fice daga school ɗin zuwa domino's pizza.

Dai-dai wurin da guy ɗinnan ya tsaya few years back sai a lokacin ta tuna tai murmushi kawai tare da faɗin "Mahaukaci ." Dan kusan kullum in sun zo sai ta tuna sa.



Bayan sun amshi pizza ɗin hanyar motarsu su ka nufa sun ɗan yi yawo kaɗan sannan Lilian ta maida ta gidan Neneh.


Bayan ta shigo gidan direct ɗakinta ta shige tai wanka sannan ta saka wani white crop top da da purple pocket palazzo, da suka amshi jikinta ta yi kyau sosai kitchen ta nufa tare da ɗaukan milky donut da Hollandia strawberry da ke fridge wanda ta sa a ajiye mata.

Ɗakin Neneh ta shiga tare da zama akan gadon tana kallon Neneh da ke ta faman jan carbi alamu dai bata daɗe da idar da Sallah ba.

Ɗago kai Neneh ta yi ta dalla mata harara tare da ɗauke kai ta cigaba da lazimin ta.

''Neneh dan Allah cewa masu aikin ki su haɗa min gireba ko ke da kanki ki haɗa min, na biya AFSHKUR BITES a kulle shagon ya ke kuma bayansu ke kaɗai ke iya gireba mai daɗi kin ji my Neneh.''

Sai da ta Idar lazimin sannan ta ce ''Sannu maryamu uwata sannun ki yemu, wallahi abin na ki iskanci ne, wallahi iskanci ne, ni dai a wurinmu da safe ake wannan.'' bata ƙara bi ta kan Liyana ba.

Ita ma dai da ta ga ba ta tanka mata ba ta ɗauki wayarta tare da shigewa ɗakinta.

Ko da dare ya yi cikin shirin ta na kayan bacci ta fito purple color wanda ya amshi jikinta ga wani kalan glowing da fatarta ke yi, she looks soo take a way, ƙafarta sanye da slippers na bacci masu kyau da taushi.


Tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ne ke dinning wan da ya gaji da haɗuwa.



Ko da ta ƙaraso wurin kowa ya hallara ita kaɗai ake jira, bayan sun gama ci Neneh ke faɗin "Liyana kike ko Libiya, ma za ɗauko min mayafina muje gidan Alhaji kyari na mai barka da dawowa, duk da dai mutumina baya nan amma sai ki saba sosai da sirikan na ki."

"Jiddah ka shiga tsakanina da matarka?."
Tana faɗan haka ta cigaba da shan fruit salad ɗinta.

Murmushi kawai yayi tare da ɗaukan walking stick ɗinsa ya koma ɗakinsa.

Matsowa Neneh ta ƙara yi kusa da ita tare da yaficota ta ce " kin ga yaron nan da nake faɗa miki ƙaff Nigeria babu wanda ya ke da arziƙin kyari, ki ajiye kai wallahi ki ci arziƙi, kin ga, kuma fa wallahi ƴaƴansa ma kaff duk sun ci sun tada kai, barimma wan da na ke gaya miki.

Ga mahaifiyyarsu mai kirkin tsiya kusan kullum sai ta shigo nan ta gaida ni kuma har ta tafi gwiwarta a ƙasa kaman mai neman gafara, ai in gayamiki matar nan ta yi, amma fa mahaifiyyarta Yarabawa ce ita Khairat ɗin amma akwai sauƙin kai wallahi."

Earplugs ɗin ta ta jona da wayarta ta kunna waƙar _RUSH _ na _ayra star_ ta cigaba da bi tana nishaɗi tare da tashi da ga wurin Nenehn gaba ɗaya.

Neneh ta sa ki baki hangangan ta na kallon Liyana ta ƙara cewa " ai wannan iskanci ne, ni dai a wurinmu da safe ake wannan, abin da kike min Allah ya kawo ƴaƴanki su yi wa Ikimat., kiji in da daɗi.

Mai farar fuska shiyasa duk wan da ya ganki ba ya son auren ki saboda baƙin hali, ni da na ke son ma na kaiki gidan daula, shi ne kike min haka, kya tsofe a gida wallahi ba miji, ni dalla gafara min tun da ba falon mijinki bane ba."

Ta faɗa tare da zama a kusa da Liyanar a 2sitter.


"Neneh na tambaye ki mana za ki bani amsa?." "Mai zai hana." Ta faɗa tare da washe baki.

"Dan Allah bakin ki ba ya iya shiru da surutu mara jigo da asali?, kusan one hour da cin abinci amma tun ɗa zu sai ihu kike min for once lemme enjoy this moment mana, na tabbatar in ba ki je police station yafi sau goma lokacin da kike budurwa saboda surutun ki kan iya raba auren da ba soyayya . Mata sai surutu mara sababi, ni sai da safe."

"Wallahi Ikimat ce zata je police station ba ni Ajiddeh ba, kiyi ta rashin kunya, ƙila a haka kika kori mijinki bamu sani ba."
"Kya ji da shi, wallahi kika ƙara min maganar ɗan kyari sai an buɗe mana fili da ke a gidan nan."
Baki hangame Neneh ta ce"Ni dai a wurinmu da safe ake wannan wallahi."
"Ko da asuba ne za ki san shayi ruwa ne."
"Duka na za ki yi?."
"Za ki gani a aikace." Daga haka ta kulle ƙofarta har da da key......


After 2 Weeks

Liyana ke zaune a parlour ta na ta jiran Lilian ta kira ta za su fita siyayyan birthday ɗin ta.
Sai kusan ƙarfe biyu sannan Lily ta kirata, ta shiga ɗakin Neneh ta sanar da ita sannan ta nufi hanyar fita daga parlourn tare da faɗawa driver ɗin inda zai kai ta.

Bayan sun ɗauki Lily kam boutique suka nufa sukai siyayya sosai sannan suka nufi wurin pictures.
Sai yamma liƙis ta dawo gida shi ma ta na wanka kawai kwantawa bacci ta yi dan tana off day ɗin sallah, kuma ba ta son takurar baiwar Allahr nan.......✍️





Ku yi manage please Bacci nai sosai yau kuma bana son na bar ku babu update.



THANK YOU FOR READING 💜




To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.
Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.
See you in the next chapter of our journey.

With love,
Pending Amarya 🦋




> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋

> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.


Pending Amarya as usual 🦋 🫠


I really love you readers 💎

> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday
> Mondays to Fridays from 8am to 12pam follow for more 🎊🫂📚
> EDITED 🤍> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V


> MY YOUTUBE CHANNEL LINK👇


https://youtube.com/@pendingamaryasbookcorner?si=ua40w5qJhdjEpXRT



> THE REGRET COMMENTS SECTION ✅👇


https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=ac_t



> PENDING AMARYA'S PEN WORLD 💎📚👇

https://chat.whatsapp.com/BimAgGC0XKpAObEGTBJf3x?mode=ac_t









*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪

:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

The Noble Writters ✊
Dedication is our strong

THE REGRET 🙆

when love meets temptation who survives?





She just wanna think of me like a bee 🐝
Hmmm uthman bee, if we're meant to be we gonna be🤗
Hmm my melanin, ta buɗe zuciyarta na shiga soo she got my time sabida na isa tell me what's your name 💎
Ta ce min A'ishah let's have a ride na ce mu ɗan fitaa 🫵😅 ta so come make i run your overall 🤭🤫..........




The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!



Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂💔


Mallakar Pending Amarya ce_



NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl




THIS PAGE IS DEDICATED TO MY DEAR SIBLINGS MY STRENGTH

Every page I write carries a piece of our laughter, our fights, and our unshakable bond
This story is not just mine it's ours 🤗🤝







CHAPTER EIGHT : BEIJING 💎

_PENDING AMARYA _


Page 17





Sai yamma liƙis ta dawo gida shi ma ta na wanka kawai kwantawa bacci ta yi dan tana off day ɗin sallah, kuma ba ta son takurar baiwar Allahr nan.......✍️






ILY ta kira suka yi hira har da Ammi sannan ta kwanta bacci mai nauyi ya ɗauketa.
Ɓangaren su Ammi kuwa tun ranar da Abbhi ya dawo su ka rasa gane ta kansa, ga faɗan da ya kewa mutane na babu gaira babu dalili.

Ita a tunaninta ko dai gamo ya yi da aljanu dan wannan nutsuwar ta sa dukka ba rabi duk ya yi wani.

Ga Rufaidhat da ta tisa shi a gaba ko bacci ya ke sai ta tashe sa ya rasa gane meke damun Rufaidhat ta ke wannan hali.

Ɓangaren Ilham kam ta samu ta fara zuwa school dan itama rijiyar zaki ta ke son dawowa idan har komai ya kankama amma in tuna da Ammi sai ta ji duk ta fasa saboda barin Ammi gida ɗaya da sheɗaniyyar matar nan masifa ne.




China, Beijing, Shunyi district :

Kwance ya ke akan lallausan gadonsa da ke shinfiɗe da _ peacock Alley _ bedsheets na alfarma.
Jikinsa sanye da pyjamas white color, idanunsa sanye da sleep mask ma su kyau.

Duvet ɗin jikinsa ya yaye a hankali tare da diro da ƙafafunsa ya lalubi wayarsa da ke kan bedsides.
A hankali ya gama zare sleep mask ɗinsa ya kai dubansa ga wayarsa wanda time ke nuna masa 9:00 saura two hours jirginsa ya ɗaga zuwa Nigeria.

Da sauri ya ajiye wayar tare da shiga changing room ya sanya bathrobe ɗinsa white color.
Ya nufi toilet ɗin da marble tiles ke malale a ƙasa, komai na toilet ɗin is golden color, a gaggawce ya yi wanka haɗe da brush.



Ya fito sanye da bathrobe ɗinsa, sannan ya shirya cikin _ Tom Ford Suits _ black color da ya amshi jikinsa sosai, sannan ya zaro agogon _ Rolex Explorer ll _ daga valet tray ɗinsa ya manna a tsinsiyar hannunsa da ke da yalwar kwantaccen gashi da sai sheƙi ya ke. Shoe shelf ɗinsa da ya ke cike da manyan luxury shoes ya zaro ɗaya daga cikin _ John lobb_ shoes ɗinsa da ya ke sawa a kan suits, tare da feshe jikinsa da turaren _ Valentino haɗe da Giorgio Armani.




Ta ke wani kalar sihirtaccen ƙamshi ya mamaye ɗakin, kallon kansa ya sake yi a wall mirror ɗin da ke ɗakin tare da shafa gemunsa da ya gaji da shan gyara, wani kalar malalacin murmushi ya sakarwa kansa da ya ƙara mai kyau da kuma tsari.

LV trolly ɗinsa da ke shirye da kayansa na amfanin yau da kullum ya janyo a hankali cikin aura ɗinsa ya fara ta ko wa cike da izza, ya fito daga master room ɗin nasa ya nufi hanyar living room.


Ko da ya fi to daga Master room ɗin na sa ƴar aikinsa ce a tsaye ta na goge dinning table ɗin da ke dinning area, cikin muryarta mai sanyi ta ce "Xiānsheng, zǎoshang hǎo." (Good morning sir).
Amsawa ya yi a taƙaice sannan ya ce mata ta tabbatar kullum zata gyara mai gida sannan ba zai daɗe ba zai dawo.

Da toh ta amsa mai sannan ta cigaba da gyaran gidan nasa.

Ko da ya fito daga entrance ɗin gidan, parking lot kawai ya nufa, tare da shiga cikin motar da ke da kyau da tsari ya nufi hanyar office ɗinsa domin submitting some documents kafin ya bar ƙasar.

Ko da ya ƙarasa compayn, companyn na da kyau da girma, komai na ciki contains white color, ga ko ina wani kalar securities aka baza, ko wani uniforms nasu na tattare da logo na Company da kuma sunansa H&K Ventures.(Hydar&Kyari ventures) H is for Hydar, K is for Kyari, which is his father, saboda mahaifinsa na da share a cikin companyn.
Staffs and local staffs sai gaida sa su ke, sai dai ya kaɗa kansa ya cigaba da tafiya har ya ƙarasa cikin ƙantamemen luxury office ɗinsa da ke shaƙe da office equipment.
A natse ya zauna tare da danna bell ɗin da ake kiran secretary da clearners, ta ke wata ƴar matashiyyar budurwa wadda daga ganin ta ka san Chinese ce ta shigo, ta gaida sa tare da tsayawa agabansa, "Coffee." Shi ne abin da ya furta cikin muryarsa mai amo da taushi kamar algaita. Sannan ya ƙara da faɗin a kira masa manager da assistant manager (shi CEO ne akwai manager da kuma assistant manager, su ne masu kula da lamarin compayn idan baya nan).


Ba'a fi minti biyar ba su ka shigo. Bayan sun zauna aka kawo musu coffe gaba ɗaya sannan suka zauna can gefe da ya ke kama parlour acikin office ɗin CEO ɗin tare da CEO.
Cikin muryarsa mai cike da nutsuwa da izza ya ce " Yau zan yi tafiya, a kula da companyn nan sosai, kar a ɓatawa manyan dealers rai in na dawo na tarar da hakan You people will be fired, am I clear? ." "Yes sir."." Sannan manyan dealers na mu kamar su Adafar Ventures na Singapore, da sauran dealers ɗin a haɗa musu fita shakatawa da iyalansu, ga documents ɗin da za ku buƙata na bar ku lafiya.". Sai da su ka amsa masa, daga haka ya bar office ɗin gaba ɗaya tare da bawa driver car key ɗinsa ya kai sa Beijing Capital International Airport (PEK).
A motar ma babu wanda ya yi magana har ya ƙarasa drivern

8 / 13