Chapter 2 Reading THE REGRET BOOK COMPLETE BY BUDDO.txt Arewa Novels

THE REGRET BOOK COMPLETE BY BUDDO.txt

Author :  Buddo Category :  Hausa Novels 001

Chapter   2 / 13

3K to 6K   out of 37K words

ba ya zauna a driver sit zai tayar da motar, juyowa yayi da kyau ya kalleta da kyau sannan yace "Kinga in zaki ware jikin ki ki ware ki kulle min ƙofar mota ba akanki aka fara samun ciki ba, mata nawa ne suke naƙuda basuyi haka ba saike, C'mon kulle min ƙofar motana.

A hankali ta lallaɓo ta kulle ƙofar saboda ita kaɗai tasan wani hali take ciki. Lallai Ya Nabil ya cika maƙiyin ta wanda kake cikin wannan halin da bai tausaya maka ba ai bazaku taɓa jituwa ba.

Tayar da motar yayi sannan ya ɗauki hanyar Hospital ɗin Nassarawa, basu wani daɗe ba suka ƙarasa Hospital ɗin.
A kiɗime ya fito daga motar ya ɗauke ta a hannu kamar yar baby yana ta zabga uban sauri (Namiji hankaka 😏).


kallon fuskanta yayi tayi yana tafiya she looks pale.Mutanen wurin sai tausaya mishi suke, because kana ganin ta kasan son da yake mata bana wasa bane ba (Nabil ka ji tsoron Allah 😂)

Doctors ne suka duba ta, suka ga ba adai dai kan yaron cikin nata yake ba dole CS za'a mata idan kuma dole haifar sa za tayi za ta sha wahala ko kuma a rasa ta gaba ɗaya.

Ko da aka samu Nabil aka gayamasa ce wa yayi shi dai matarshi ta rayu (Ni pending Nabil zai min lahani 😂)



After 5 hours



..Cikin Ikon Allah aka ciro kyakkyawar yarta mai kama da ita.

Jijjiga ta farayi wanda da ƙyar likitoci suka tsayar da hakan.



Nabil aka kira ya kawo kayan baby a gurguje yaje bakin Hospital ɗin ya siyo kaya da
Kayan tea, da dai sauransu.

Bayan an shirya baby aka kawo masa ita Doctor ɗin tace "Here is your pink jet" , murmushi yayi ya ce "Tnx".
Kallon yarinyar yake wanda a ta ke ya ji wani matsanancin sonta ya ɗirar mai.
Duk da jaririya ce amma hakan bai hana bayyanar da kyawunta ba.


Sai motsi ta ke da bakin ta alamun yunwa ta keji.

Huɗuba yayi mata da sunan late sister ɗinshi FATIMA amma za'a ɗinga kiranta da LIYANA.


BAYAN FOUR DAYS 💫


Yau ne aka sallami su Nabil daga Hospital, kafin suje gida kam kusan rabin familynsu na gidan amma ba kowa yazo daga Maiduguri ba, duba da yanca Nabil ke da zumunci da son yan uwa.


Ko da suka dawo gida bai yarda ya bar kusa da ita ba Ƙanwar Ikimat tai ta mai mita ya ƙi fita baƙi su shigo shi mai mata.

Ita dai Ikimat ba abinda ta keyi sai murmushi wanda yafi kuka ciwo.

Dan fatan ta bai wuce ace za'a tattara ta a mayar da ita gidansu ko gidansu Nabil ba.



Bayan anyi suna anci ansha an hantse bata ji alamun za'a ce ta tafi gida ba.
Ashe Nabil ya zaga baya yace ita ta faɗa mai babu inda zata je ta bar gidanta..

Babu wanda ya nuna mata alamar komai bayan taji abinda aka faɗa mata, tayi kuka sosai sannan tayi wa Nabil Allah ya isa ba adadi, haka rayuwarta ta cigaba kullum cikin ƙunci amma takan samu sauƙi ta sanadiyyar Liyana.

Idan ya dawo daga kasuwa kam Liyana ya ke ɗauka ya tafi ɗakinsa da ita har sai in kuka take sannan zai dawo da ita, kuma in ya dawo da ita ɗin zai tsaya akanta ne har sai ta gama breast feeding ɗinta zai amshe ta ya koma ɗakinsa da ita.

Liyana kam ta fi shaƙuwa da mahaifinta, kyakkyawar yarinya Ma Shaa Allah, bata da hayaniya ko kaɗan.

After 7months

Liyana ke rarrfe a parlour dake ranar Sunday ne bai fita kasuwa ba, ita kuma Ikimat na kitchen tana haɗa breakfast, rarrafen ta take yi hankali kwance, tana gwarancinta irin na yara jarirai, can jikin socket kam heater ne ta jona ruwan zafin da zata dama kunu saboda yanayi na mai shayarwa sai da abu mai ruwa da zai kawo mata ruwan nono.

Sam ba ta ji lokacin da ya ajiye Liya a parlour ba, kawai ita dai taji ihun Liyana tunawa da ruwan zafin da tayi ta saka a socket, Bata san lokacin da ta yar da wuƙar hannunta ba ihu ta ke yi tana kuka haɗe da gwarancinta a haukace Ikimat ta ɗauke ta sai taga ashe bata kunna socket ɗinba.

Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta juyo taji an fisge Liyana a hannunta tare da wanka mata mari, dafe ƙuncinta tayi ta kalli Nabil da yake kallonta kamar zai ɗaga ta sama, cikin muryarsa mai Amo ya ce "Ba ki da hankali ba kiga na ajiyeta ba da ban kashe socket ɗinba lokacin da na ajiyeta ba da tuni pink jet ɗina ta ƙone".

Kallonsa ta ke babu ko ƙiftawa sannan hannunta bai bar ƴar kafaɗar Liyana ba alamu dai kamar baka isa ka ƙwace min ƴa ba.


"Ba za ki saketa ba?" Cikin muryarta mai sanyi da kuma nuna gajiyawa da halin Nabil ta ce "Kai ka haifa min ita? Ba za'a saketa ba ɗin kai duk abinda zakayi".

Kallonta ya shiga yi bako ƙyaftawa, sannan ya juya ya ajiye Liyana akan kujera ya bata abin wasa haɗe da cewa "Lemme deal with your mom little princess" ƙyalƙyacewa Liyana tayi da dariya kamar taji abinda ya faɗa sannan ta maida hankali kan wasanta data keyi.



Zare belt ɗin jikinsa yayi ya naɗa shi a hannunsa sannan ya fara dukanta dashi ta ko ina ya samu a jikinta lafta mata yake yi, tun da ya zula ma ta ɗaya ta ke yaya kayi haƙuri amma ina Nabil zaneta ya ke taki ina, tun tana kuka har ta gaji.

Tsaki ya ja tare da faɗin "mara kunyar banza". Sannan ya ɗauki Liyana yayi sama da ita.



Haka rayuwarta ta cigaba babu wani sabo tsakanin ta da ɗiyarta har Liyana tayi shekara uku a duniya .



Kuma acikin shekaru ukun nan sau biyu ta taɓa zuwa gidansu duk da babu wani nisa tsakanin bachirawa da hotoro.



Shi zai kaita school shi zai dawo da ita can wurin aiki ma tunda tayi wayo tare suke zuwa tsakanin ta da Liyana sai dai gaisuwa da shiryata ta tafi school shima ba kullum ta ke shirya ta ba.




Yau dai ta kasance Sunday tun safiyar ranar ya sanar da ita akwai taron family , a gurguje tayi ayyukanta sannan ta shirya cikin wani after dress Mai ɗan kyau tunda Nabil duk iskancinsa yana wadata ta da komai na more rayuwa, tayi kyau ba laifi sannan ta riƙe hannun Liyana dake tsaye kusa da Abbanta sai da ta kalli fuskar mahaifinta sannan ta koma wurin Umminta .

Murmushi ya mata mai nuni da alamun ki je wurinta sannan yayi gaba cikin shigarsa mai kyau.




Sabuwar motarsa kirar Peugeot ya hau 2009 brand new blue color sai ɗaukar Ido take yi.

A hanyarsu na zuwa gidan suna zuwa aka fara gabatar da taro Ikimat kam kamar bare a cikin dangi, Nabil kuma kamar zai maidata ciki tsabar nuna kulawa da soyayya, cousins ɗinta da ba suyi auren ba sai taɓe mata baki su keyi.
Bayan dawowarsu gida kam ko kallonta be yi ba ballantana ta sa ran yau Liyana zata ɗan kwana a wurin ta ta samu taji ɗumin ƴarta.

Ɗakinta ta shiga tayi wanka ta saka kayan bacci mai ɗan kawri saboda yanayin damina dake saukowa a yan kwanakin nan.

Sai da ta gama shiryawa ta nufi ɗakinsa tsayawa tayi a bakin ƙofar ɗakin tana wasa da yatsunta ɗagowa yayi sosai ya kalleta na ƴan sakwanni sannan ya kawda kan sa gefe, cikin inda inda ta ce "emm.. Ya .. Nab...il please zak.......... Kafin ta ƙarasa ya dakatar da ita da faɗin "I'm not in the mood of that nonsense".

"Ya Nabil that's not what you think, nace dan Allah Liyana zaka bani ta kwanta dani since Last week ko cikakken fuskarta ban gani b...a" ta ƙarasa faɗar maganar a yanke.

Tsaki ya ja ya cigaba da ordern atamfofin sa daga Ghana, ba tare da ko Kallonta ya sake yi ba.

A kwana a tashi ba wuya Ikimat nada wani cikin, lokcin Liyana shekarunta biyar amma tana da tsawon ƙafa Ma Shaa Allah.

Laulayin yazo mata da sauƙi amma sam bata iya aikin komai sai dai ta kira ƙannen ta suzo tunda yanzu ba laifi yana ɗan barinta ta fita amma ba sosai ba......


The Regret wants your Reactions and comments for the person to regret 😂😂
Kaji wani turanci 😂😂🦚
Omo ku biyu pending amarya dan jin yanca zata kaya ✍️ 🦋
Pending Amarya butterfly writter 🦋
Ɗawisu gidan ado marubuta masu muhimmanci
The Noble Writters Alhaji🥀🦚✍️



What's wrong with this guy readers?
Meke damun guy ɗinnan?

Ku dai ki biyo Pending Amarya dan jin yanca zata kaya✍️✍️
Ta tanada muku amsoshin ku
This is just the beginning.


We haven't started yet
This isn’t the end. It’s the beginning of who they must become.
Because the hardest trials... leave the richest scars.

The Noble Writters 🌕 🦋
🦋
Let's end the war together 💔🤝
Kuyimana share sannan
Reactions ɗinku Is All we need the Most 👑🦚

Try your possible best guys 😍💃

Let the world feel what we have written ✍️✍️✍️

Don't forget with Pending Amarya as usual 🦋 🫠https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=r_c




*NIGERIA*🇳🇬
MY FATHER'S LAND
The Noble Writters

Proudly Nigerian 🇳🇬🇳🇬🇳🇬



Dedication is our strong 🦚🦚🦚✊✊

NDA DUBDO THE REGRET FAMILY 💔😂🥹 🦋
Bana cikin THE REGRET ni kam 🌸🥀🦚
Let's dive into the work of fiction 🤝💫

THE REGRET
(Dana sani)🙆🥀💔🥹
When Love meets temptation 🦚 who survives?
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 🦚

What comes arround goes arround 🥀 💔
Abinda ka shuka shi zaka girba 🦚
Abinda kayi wa ƴar wani za'a yi wa naka 🌚
Duniyar kenan🌕🤌


Is not that easy with you here, buh I know I want you to stay.
See this could be us in a few years 🦋🥀


Chapter two: The past that never let go.
Page 4

:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Laulayin yazo mata da sauƙi amma sam bata iya aikin komai sai dai ta kira ƙannenta suzo tun da yanzu ba laifi yana ɗan barinta ta fita amma ba sosai ba.


Tun da yasan daɗin yara kam yanzu yakan kaita scanning ba kamar Liyana ba amma fa Liyana na kusa da shi Ikimat kuma ita rayuwarta a bayan mota ne.

Tasan wasu daga cikin maƙotanta sosai barimma Ummin Salim maƙociyyarta ta ƙwarai takan shigo gidan su yi hira tun da ba kullum Nabil ke barinta ta fita ba.

Yau ma kamar kullum tazo tare da kawowa Ikimat Ɗanwake tun da ita gwanar son Ɗanwake ce sosai.
Suna zaune suna hira wanda duk akan mazajen su ne, Ummin Salim ke tambayar Ikimat "Kince za ki faɗamin sanadiyyar da ya sa Nabil ke muzguna miki kuma har yanzu baki gayamin ba.

Ko har yanzu ba ki yarda da ni bane ba?". Cikin muryarta mai sanyi ta ce "Ko ɗaya wallahi Ummin Salim, amma bara na baki labari."


Tuna baya

Nabil ya kasance cousin brother agareni ata dalilin mahaifinsa da mahaifina ƴan uwa ne mamansu ɗaya babansu ɗaya.



Na kanje gidansu Ya Nabil sosai duk da mahaifinsa na da kuɗi sosai bana wasa ba, yawanci acan nakan cinye hutuna na makaranta tun da bodin school nayi.



Ni kuma Ummi Salim tun da na taso naga Ya Nabil nake jin soyayyarsa araina, wanda har yau duk muzgunawarsa bai taɓa fita daga raina ba. Lemme just get straight to the point Ummi Salim.

"Yaya Nabil na soyayya da da wata yarinya mai suna Rufaidhat a unguwarmu ta ke muna magana da ita sosai duk da ni bansan suna soyayya da ya Nabil ba, nikam kawai dan inga ya Nabil ma nakan je gidansu na cinye kwanakin hutuna, inna zo gidanmu baifi nayi kwana biyu ba na koma school.

Soyayyar Nabil da Rufaidhat kam sai ƙara linkaya ta ke yi saboda zuwa lokacin mutane da dama a dangin sun sani wanda ni bansan da hakan ba.


Kwatsam ina school lokacin ina js2 ƙanwarsa wadda ta ke ƙawata mai suna Mansura ta sanar dani halin da ake ciki.

Na sha kuka sosai wanda har na cire rai da aurensa saboda magana na ƙoƙarin zuwa wurin magabata, in anzo min visiting akan zo da shi amma sai visiting na ƙarshe da za'a min a js2 na tarar ba' a zo da shi ba.

A ta ke na shiga cikin mawuyacin hali sa bo da indai a class ɗinmu kake kowa yasan alaƙata da Ya Nabil na ƴan uwantaka da ma wanda nake cusa kaina a wurin shi duk da ƙanƙantar shekaruna.


Har akai jarabawa wanda zai kai mu ga js3, mu kai hutu a lokacin shekaruna 13 na dawo gida still gidansu ya Nabil na sauka, Ummin Salim bazan miki ƙarya ba da ace ni Nabil ke so da nayi dace a duniya, saboda lokacin da na ke babu aure a tsakaninmu komai ya samu nice duk abinda ya samu ni yake bawa duk ƙanƙantar abun.


Bayan dawowata da sati ɗaya gidansu a lokacin Ya Nabil na maganar kai kuɗi gidansu Rufaidhat yana ƙoƙarin sanarwa da Abbana sai shikuma ya sanarwa da Abbinsa.

Toh ranar ta kasance Lahadi kowa na gida muna ɗaki ni da Mansura muna tattaunawa akan yadda zan cire soyayyarsa pldaga cikin zuciyata, ashe lokacin kuma Ammin ya Nabil ta gama jin duk wani feelings ɗina a kansa.
Dan kawai tasa ni farinciki ta sayar da farincikin ɗanta dan ta cika min nawa muradin.


Sai a lokacin ta sanar da Abbinsu Ya Nabil yadda taji ina magana harda kuka.
Bai yi ƙasa a gwiwa ba ya kira Nabil ya sanar dashi ya na son ya aureni, babu kunya Nabil ya ce wa mahaifinsa bazai iya aurena ba saboda ni ƙanwarsa ce sannan shi mai ra'ayin mata ɗaya ne ballantana ya aure ni ina yiwa Rufaidhat wanke wanke.
A take mahaifinsa ya wanka masa mari wanda a take fushi ya ɗebesa ya zo har inda nake yayi min barazana akan inna yarda na aure sa.



Ban mai magana ba sannan ban nuna alamar sanin abinda Abbih ke shirin yi ba.

An fi sati ɗaya ana bawa ya Nabil haƙuri mahaifinsa har alƙawarin zai bashi dubu hamsin yayi duk abinda yake so nan ma ya Nabil yace babu abinda zaiyi da kuɗi, kuɗi bazai iya siyan soyayyar sa da Rufaidhat ba.

Abin ne ya harzuƙa Abbinsa ya ce mai indai har ya auri Rufaidhat ya tsine mai daka cikin ƴaƴansa sannan in ya auri Rufaidhat ya ajiye duk wani abu da yake da wani abin family ɗin madaki saboda shi Aliyu Ibrahim ba'a haifi ɗan da zai juya sa ba.


Wannan shine sanadiyyar duk wani muzguna min da yake yi da kuma cin fuskar da yake min".
Ajiyar zuciya Ummi Salim ta yi sannan ta ce "Gaskiya Ikimat kinyi ƙoƙarin da ba ko wacca macace zata yi ba, kuma har yanzu babu wanda ya sani a gidanku ko dangin ku?"..

"Ummu Salim kenan ai babu wata alama da ya bari, ke da kike kusa dani ga baki ga hanci da ban gayamiki ba za ki sani?".
Nodding Ummi Salim ta mata alamar a'a.



Sannan ta cigaba da faɗin, "Ko bayan auren Ummu Salim Nabil bai bar ni na cigaba da school ba, sai dai idan Abbinsa ya tambaye sa yace ai ina zuwa day ya mayar dani.

Ni dai innace ban yafe ba wallahi zai bi Nabil.

One week ka ɗai na san mai daɗin aure wanda har yau kalubalen dake cikin ta nake fuskanta.

Nabil ya taɓa bari na for good ten days ba tare da ya bani abinci ba.

Haƙurin da nayi da Nabil bana fata Liyana ta samu kalar wannan mijin, bana fata wannan kalmar na abinda kayi wa ɗan wani ya yi ta si ri akan ƴaƴana duk da bansan mai ke cikina da zan haifa ba.

Haka ta gama korowa Ummu Salim duk wani abin da ke damunta irin cin fuskan da Nabil ke nuna ma ta for good nine years da aurensu.


Ita dai Ummu Salim babu abinda ta keyi in banda hawayen da ke zuba a idanunta wanda nima kaina pending amarya sai da na zubar da hawayena akan al'amarin Ikimat.



"Innalillahi ƙarfe huɗu yayi banyi girki ba kuma Wallahi yanzu zai dawo tun da da Liyana suka fita". Ikimat tayi maganar saboda ta kashe zancan duk da ta na son faɗawa wani, amma ba ta son abinda zai tona asirin wanda duk duniya shi ta ke son ta ƙare rayuwarta da shi sannan kuma ko ba komai shi ɗin ya kasance uban ƴaƴanta ne.

Da haka ta ƙarasa shiga kitchen ɗin da ke shaƙe da kayan abinci......





Na yau ba yawa manage please 💔

Wacece Rufaidhat?
Wannan ne kaɗai dalilin Nabeel?
Who's the real star the Mom or the daughter?☺️
Who's the one regretting 🌟

Readers mun kusa dawowa labari faa muyi paka paka mu gama mu ɗaura beyond heart break because nayi missing kowa wallahi 😂✍️

This is just the beginning

We haven't started yet
This isn’t the end. It’s the beginning of who they must become.
Because the hardest trials... leave the richest scars.

The Noble Writters 🌕 🦋
Ɗawisu gidan ado 🦚🦚🦋
Let's end the war together 💔🤝
Kuyimana share sannan
Reactions ɗinku Is All we need the Most 👑🦚

Try your possible best guys 😍💃

Let the world feel what we have written ✍️✍️✍️

Don't forget with pending amarya as usual 🦋🥀🦚🦋 🫠



> THE REGRET ONLY ON PENDING AMARYA'S BOOK CORNER.

> THE REGRET (Dana sani)

> EXTRA ORDINARY EVERYDAY ONLY ON PENDING AMARYA'S BOOK CORNER 📜 📚 https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=r_c
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪

:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

The Noble Writters 🦚🦚✊
Dedication is our strong 🦚🦚✊

THE REGRET 🙆🥀🌸🇳🇬

when love meets temptation 🦚 who survives?

💔💫

NIGERIA 🇳🇬
For Pending Amarya ✍️✍️

NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl🦧😂



CHAPTER THREE : RUFAIDHAT 🦋🥀


Page 05


"Innalillahi ƙarfe huɗu yayi banyi girki ba kuma Wallahi yanzu zai dawo tun da da Liyana suka fita". Ikimat tayi maganar tare da tashi tsaye tana ƙoƙarin shiga kitchen.

"Ikimat ba dai abinci za ki dafa ba?". Ummu Salim ta tambayeta cikin nuna kulawarta a gareta, "Eh Wallahi Ummu Salim yana hanya kinsan jiya ma haka na shirice ƙarshenta ni na cinye abincin ma".
Dariya Ummu Salim ta yi tare da ce wa "Malama zo ki huta abincin da na dafa da ke nayi ai".
Godiya Ikimat ta mata tare da zama suka cigaba da hira amma ba wanda suka fara ba, har magrib yaya Nabil bai dawo ba. Sai sannan Ummu Salim ta mata sallama tare da tambayarta yaushe zata cigaba mata labarin, "Duk lokacin da kike da time ta ce mata".

2 / 13