Chapter 7 Reading THE REGRET BOOK COMPLETE BY BUDDO.txt Arewa Novels

THE REGRET BOOK COMPLETE BY BUDDO.txt

Author :  Buddo Category :  Hausa Novels 001

Chapter   7 / 13

18K to 21K   out of 37K words

Rufaidhat.

Ko da suka ƙaraso Liyana ce da kanta tayi serving ɗin Abbhi sannan tai wa kowa, da ta zo kan Rufaidhat ma bata ƙi zuba ma ta ba cikin muryarta mai kyau ta ce ''Mom are you okay with the jollof ko na ƙara miki da pepe soup??." Murmushi kawai Rufaidhat ta yi ta na jinjina kissa irin na wannan ƴar yarinyar.

Bata ce ƙala ba itama Liyana jawo bowl ɗin fruit salad ta yi ta fara sha, as usual ita ke kusa da Abbihnta bayan angama dinner ɗin Abbhine ya fara ta shi ita ma Liyana ta bi bayan shi Rufaidhat ma ta bi bayansu.
Abbhi na shiga ɗakin mac book ɗin sa ya ɗauka ya na duba wasu abubuwan, zama Liyana ta yi a kusa da shi sannan ta ce ''Abbhi ina son komawa rijiyar zaki gobe in Allah ya kaimu sai kuma Sultan ya ce ya na son turo magabatansa zuwa next month in Shaa Allah.'' ta faɗi haka ta re da ɗaukan ƙafar Abbhi ta ɗaura akan cinyarta ta na mai massage ahankali.

Lumshe idanunsa yayi sannan ya ce '' kije ki shirya kayanki gobe sai na kaiki tunda zaman kusa da ni ne bakya so.'' '' nifa Abbhi sai na je yaushe rabo da naga Neneh, bazaka hanani ba wallahi kama daina fushin nan.'' murmushin sa mai kyau ya sakar mata sannan ta ƙara gyara mai gadon nasa ta mai sai da safe da idon shi dai ya bita sannan ya gyaɗa kansa.


Bayan ta koma ɗakinsu ta janyo trolly ta zuba duk wani kayan buƙatar ta, ta na kallon Ilham da tai shiru kamar za ta yi kuka.

''Hey chill one month zan yi na dawo akwai wajen da zamu je da Lilian, in ina gidan Neneh zan fi jin daɗin fita karki damu zamu ɗinga video call kinji?? , sannan babu ruwanki da waccan matar kinji dai na faɗa miki.''

Daga haka ta shiga toilet ta yi wankanta ta fito ta sanya kayan baccin ta sannan ta shafa almiski wanda indai bacci za ta yi shi ta ke shafawa tun da ta girma.


Ajiyar zuciya ILY ta sauke sannan ta ce ''Liya dan Allah ki raba kanki da wannan yarinyar, wallahi tun da kika haɗu da ita na fara ganin changes a rayuwarki, ni dai nasan muna da yawon joints wan da mu da Abbhi ke zuwa, buh yanzu fa har parties ki na zuwa, please change!! .'' ta na faɗan hakan ta lulluɓa da bargo, tare da juya mata baya.
Tsaki Liya ta ja tare da ɗaukan ear plugs ɗinta tana jin waƙan Rema _charm_.








Washegari da sassafe ta ƙara shirya komai tare da shiga wurin Ammi ta faɗa mata Neneh ta ce ta zo wurin ta yau bayan Ammi ta mata nasiha ta ɗaura da faɗin '' ina wannan yaron da ke zuwa wurin ki?? .''
''Sultan.'' ''what ever'' ammi ta bata amsa sannan ta ce mata ta turo sa ya ga Abbihnta she's not getting young any longer.


Sidda kanta kawai ta yi sannan tai wa Ammi godiya ta shiga ɗakin Abbhinta sai da ta shigo sannan ya yi wanka kafin ya fito har ta zaɓa mai fararen kaftan masu kyaun gaske.


Bayan ya fito as usual ya yi kyau sosai.

Mukullin motarsa kawai ya ɗauka sannan ya yi hanyar parlourn bayan ta gaida sa, murmushi ya mata sannan ya riƙe hannunta zuwa dinning in da Rufaidhat ke Kai komo ta na ta jera abinci akan dinning, bayan ta kawo warme na ƙarshe sannan ta wuce ɗakinta.



Zama ta yi next to Abbhi, sannan suka soma cin abincinsu hankali kwance, because Ammi da Ily, sai 10 suke karyawa, kallon wayarta da ya ke ringing ta yi ta ga Lily ke kiranta hakan yasa ta ɗaga tare da bawa Abbhi ta na mai alamar ya ce ta tafi.


Bayan ya sauke wayar dariya kawai ya yi tare da faɗin ''who's she??.'' '' a friend Dad.'' ''yaushe kika fara friends?? Sannan a friend, ɗin ma ban tantace miki ba, rana tsaka kawai kice friend daughter?? .''

'' Nima da kake tare da matarka you didn't tell me ai.''

Kallon seconds ya mata sannan ya ɗauke kansa.

Daga haka ba su ƙara magana ba har suka gama cin abincin su ka kama hanyar rijiyar zaki.


Sheikh Ja'afar Road tun da aka shigo unguwar zuciyarta ke dukan uku uku, because since last week ba suyi waya da Sultan ba, sai dai chat kuma unguwar su ata nan hanyar ya ke amma ba ta san ina ne gidansu ba..........




> Shirin daga bakin mai ita a yau a Pending Amarya's Talk, zai zo muku ne daga The Regret Comments section ✅
..... Dafatan zaki kasance tare damu.



Ina fatan yau akwai REACTIONS da COMMENTS idan babu gobe babu update faƙat 🤗💔


Ina da buƙata.

> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋 follow for more pages ✅ 🤗> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V


> THE REGRET COMMENTS SECTION ✅ 👇


https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=ac_t



> THE NOBLE WRITTERS FANS GROUP 👇


> THIS IS OUR NEW COLABORATIVE NOVEL GOLD DIGGERS 💦 🫦 👇


https://chat.whatsapp.com/GH4CkwiizsJAoMCw4tCqe7?mode=ac_t


> JAJIRTATTU ASSOCIATION WRITERS FANS GROUP 👇

https://chat.whatsapp.com/GGai9xKF94cESqFXBnPJIo?mode=ac_t


> THE NOBLE WRITTERS FANS GROUP 👇

https://chat.whatsapp.com/EmU2s5SrfEXKbANsCMNvg0?mode=ac_t


*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪

:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

The Noble Writters ✊
Dedication is our strong

THE REGRET 🙆

when love meets temptation who survives?




💔
Lemme show you loveeee and don't pretend, stay by my side even when the world is giving in........🥹🫂


It's Friday again 🙌 ALLAH KA HAƊA MU DA ALKHAIRIN DA KE WANNAN RANA YA KORE MANA SHARRIN DA KE CIKIN TA 🤝🌸




The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!



Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂💔


Mallakar Pending Amarya ce_



NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl




THIS PAGE IS DEDICATED TO MY DEAR SIBLINGS MY STRENGTH

Every page I write carries a piece of our laughter, our fights, and our unshakable bond
This story is not just mine it's ours 🤗🤝







CHAPTER SEVEN : SHEIKH JA'AFAR ROAD SHUWA ARABI STREET 💎

_PENDING AMARYA _


Page 14


Daga haka ba su ƙara magana ba har suka gama cin abincin su ka kama hanyar rijiyar zaki.
Sheikh Ja'afar Road tun da aka shigo unguwar zuciyarta ke dukan uku uku, because since last week ba suyi waya da Sultan ba, sai dai chat kuma unguwar su ata nan hanyar ya ke amma ba ta san ina ne gidansu ba..........



Manyan gidaje ke unguwar ga wasu Duplex houses da ke jere reras kamar estate wasu paints ɗin milk and white wasu kuma navy blue wasu gidan nada ƙofar shiga na automatic,yayin da wasu kuma keda CCTV da intercom system.
A cikin ɗaya daga cikin gidajen da ke da CCTV ya danna hancin motar na shi wanda tunda suka shigo unguwar idonta ya ke ƙurr kan Abbhinta saboda yanayi da sauyi mai girma da unguwar ta samu.


Bayan gate man ya buɗe musu gate gidan ta ƙara bi da kallo, yanayin gidan ya ƙara bata mamaki kamar aljannar duniya, gidan ba shi da wani girma sosai bai kai na su girma ba amma gidan ya gama ta fiya da imaninta.
Wasu tulip flowers ta gani ajere masu kyau white and purple color wanda a ta ke ta ji bad mood ɗinta ya kaw.

Purple and white are her favorites, ta na matuƙar son colours hakan dan ita ko ta samu wurin pictures.


Wajen parking space kam motocine na alfarma Jiddah na son Lexus sosai ba kamar Abbhi da ya ke son Mercedes Benz ba.
Motarsa ya gama fakawa sannan su ka fito atare cikin shigarta na atamfa six pieces gown wanda ya fitar da shape ɗinta, ga shafaffen tummy ɗin ta da ya ƙara bayyanar da kyawun siffarta. LV trolly ɗinta Abbhi ya janyo ya biyo bayanta da shi.

Tafiya ta ke hankali kwance kamar ba za ta taka ƙasa ba.

Cikin parlourn kam wani italian marble tiles ne ke malale a ƙasa, falon ya gama tsaruwa ainun.
Fitilar chandelier mai sheƙi na fitar da golden color shinny lights daga sama wanda hakan ya ƙarawa living room ɗin kyau.

Daga can ɓangaren kam wata farar mata ce tass idanunta sanye da medical glasses, masu kyau zaune cikin lifaya Black and Golden wanda haka ya ƙara fitar da asalin hasken fatar ta.
Ga wani ƙamshi da ke tashi a ɗakin, innace zan ƙarasa gaya muku gidannan yadda ya ke zamu ɓata pages fiye da haka let's imagine anything luxury kawai.


Yar dattijuwar da ke zaune ta na karanta Alqur'ani mai girma, ta ɗago kai sanadiyyar jin turaren da bata saba ji a gidan ta ba wato _ Greatness _ ko da ta ɗago ta kai dubanta gare shi kanta ta ɗauke tare da cigaba da abin da ta ke yi.



Stairs ɗin da suke jin taku suka kai idanunsu wurin ita da Abbhinta, Jiddah ne ke saukowa cikin farar jallabiyya, wanda ya ƙara futowa da furfurarsa da kuma kyaun fatarsa, hannunsa tsaye da walking stick ya na ƙara kallon Nabil da ya sidda kansa.

''Get out'' shi ne abin da Jiddah ya ce mai, ya na tsaye ko gezau be yi ba ya na jiran hukuncin Jiddah akansa.


Tari Jiddah ya fara yi sosai Nabil da idanunsa su ka yi jaa ya tawo da sassarfa, zai zo wurin sa, cikin tarin ya ce '' in ka tako ka zo wurina zan tsine maka.''
A hanakali ya ja ya tsaya yana kallon Liya da ke ta wawwara ido.

Neneh ce ta ƙaraso wurin Liyana ta ce ''Fatima wuce ki shige ɗaki, kallon Jiddah ta ƙara yi na some seconds sannan ta juya ta yi hanyar ɗakin da ke ƙasa idanunta na zubar da ƙwallar tausayin Abbhinta.

Tari Jiddah ke yi ba ƙaƙautawa, Neneh da ke tsaye ta na kallon Nabil ta ce '' ka fita hakan zai fi maka, da ga haka ta ƙarasa wurin mijinta ta ɗago shi ta re da kai shi ɗakinsa da ya ke upstairs.

Abbhi wayarsa ya ɗauka tare da danna kiran Mansura ƙanwarsa, bayan sun gama gaisawa ya ke sanar mata ya na gida Abbhi ya hana sa shiga. Duk da shakkarsa da ta ke yi sai da ta gaya masa abin da ke cikin ranta sannan ta kashe wayar.


Bin wayar ya yi da ido, text message ne ya shigo wayarsa ya ga sunan Liyana da yayi saving da _Day Maker_ ta na faɗin "Abbhina go back home, in Sha Allah zan dai-daita komai da yardar Allah.

Murmushi kawai ya yi ta re da ɗaukan car key ɗinsa, dan yasan Liyana ba ta failing ɗinsa in ta ce zata yi toh za tayi, wannan halin ka ɗai na ta ya isa yayi proving cewa ita ƴar sa ce.

Motar ta sa ya mirza ta re da barin Shuwa street gaba ɗaya.



Ko da ta shiga ɗakin tsaf ya ke komai na ciki fari ne.

Dan haka wanka kawai ta yi ta re da kiran Lily su kai ta hira har azhar ta yi sannan ta yi Sallah, ta re da kwanciyarta dan ba ta tunanin zata iya fita wani yawo yau.



Arround 4 o clock ta ƙara ta shi tare da yin Sallah tai wanka, ta saka kaya marasa nauyi ta re da zira slippers ɗin ta compayn gucci.
Simple hula ta ɗaura tare da fitowa falon da ke nan tass kamar babu halittar dake rayuwa a cikin ta, kitchen ta nufa nan ta tarar da ƴan aiki na kai komo a kitchen ɗin, 2 door deep freezer da ta gani a kitchen ɗin ta nufa ta re da ɗaukan fruits ɗin data gani a ciki ta fara yankawa da niyar yin fruit salad, tare da sa milk mai kauri, ta ɗauki ceremic bowl ɗin ta nufi ɗakin da yake a matsayin nata a yanzu da shi.


Sai da ta sha tai nakk sannan ta hau online ta na kallon videos ɗin da Lily ta turo ma ta ta je wani wurin cin abinci mai kyau sosai, da ita da wani muslim boyfriend ɗinta Lamin.


Bayan ta gama kalla Ily ta kira suka sha hira inda har ta ke bata labarin Rufaidhat yau sai da suka kusan dambatuwa da Abbhi bayan ya koma gida.


Dariya su ke sosai, Liya ta ce ''kinsan Allah dana sanin zuwa na ke, ke kin ga gidan Neneh kamar na ƴammata?." Zaro ido ILY ta yi tare da faɗin ''Neneh an faso gari, hala ta na nan da yaɓawa mutum magana.?'' '' Bansani ba dan tun da nazo bamu zauna ba, kuma har magrib ya matso ku sa.

Ajiyar zuciya Ily ta sauke tare da faɗin '' Ni bama wannan ba Sultan ya kira ki?.'', ''A'a be kira ba mai ya faru?? .'' ''wai ya kira you're not picking his calls tun last week da ya zo.'' '' ki ƙyale shi rigima ya ke so kawai.'' daga haka suka kama wata hirar.


Bayan sun gama wayar sallar magrib ta yi sannan ta ɗauki waya ta kira Abbhi lokacin ma ya na ɗakin Rufaidhat.

Sun fi 2hrs suna hira da Abbhi wanda hakan sai da yasa Rufaidhat ta kusa haɗiyar zuciya, dan da wannan ɗiyar Allah ya haɗa kishi ba da gyatumarta ba.





THANK YOU FOR READING 💜

To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.
Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.
See you in the next chapter of our journey.

With love,
*Pending Amarya* 🦋




> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋

> Share for more pages idan sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.


Pending Amarya as usual 🦋 🫠


> MUN TAFI HUTU IN ALLAH YA KAIMU RANAR MONDAY ZAMU YI RESUME DA TYPING.............

> The Regret only on Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday Mondays to Fridays 💎> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V

> PENDING AMARYA'S PEN WORLD 💎📚👇

https://chat.whatsapp.com/BimAgGC0XKpAObEGTBJf3x?mode=ac_t

> THE REGRET COMMENTS SECTION ✅🤗

https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=ac_t


*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪

:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

The Noble Writters ✊
Dedication is our strong

*THE REGRET* 🙆
~(Dana sani)~



when love meets temptation who survives?





Allah is my best friend & creator, always guiding me through life's journey. He's the one who knows me best & loves me unconditionally. Alhamdulillah! 🤲❤️





The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!



Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂💔


Mallakar Pending Amarya ce_



NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl




THIS PAGE IS DEDICATED TO MY DEAR SIBLINGS MY STRENGTH

Every page I write carries a piece of our laughter, our fights, and our unshakable bond
This story is not just mine it's ours 🤗🤝







*CHAPTER EIGHT : NENEH* 😂🫵💎

*_PENDING AMARYA _*


*Page 15*




*Sun fi 2hrs suna hira da Abbhi wanda hakan sai da yasa Rufaidhat ta kusa haɗiyar zuciya, dan da wannan ɗiyar Allah ya haɗa kishi ba da gyatumarta ba.....*


Bayan sun gama wayar Sultan ta kuma kira amma he's not picking kawai sai ta tattara lamarinsa a gefe.

Arround 8 aka kirata dinner already daman jeens trouser da long sleeve shirt white ne jikin ta, Neneh da ke zaune akan dinning cikin muryarta mai sanyi kalar na tsofi ta ce '' Uwargida kin manta damu, kema kin biye ma Abbihnki ko?? .'' '' Allah ya ja zamanin ki Uwargida a gidan Aliyu Ibrahim Shuwa Arabi, ashe ba ki mutu ba?? '' ''tsuke baki Neneh ta yi tare da faɗin''Ikimat ce za ta mutu ba ni ba ja'ira kawai.'' , sauko wan da ake ne ya sanya su mayar da hankali kan wanda ke saukowa, wannan karan Ash color ɗin jallabiya ce jikin sa fuskar sa ɗauke da fara'a.

Kallonsa ta yi da kyau sannan ta ce "Jiddah!!."Cikin takunta na natsuwa da ya zame mata jiki ta ƙarasa wajensa tare da hugging ɗinsa, ta karɓi walking stick ɗinsa suka nufo dinning area ɗin tare.

Bayan sun zauna su ka fara cin abinci cikin kwanciyar hankali, ta re da ɗan hira a tsakaninsu , she really missed her Grannies.

For almost 3years ba ta zo ba kuma su na gari ɗaya .


"Jiddah i missed you guys wallahi, Neneh du bi gidanki kamar na Amare, ni ko na yi aure ai nan zan tare da mijina."

"Daman ina son mi ki magana, duk sa'anninki na Maiduguri babu wanda bai da ƴaƴa, amma kin tsaya bi ye wa ja'irin uban nan na ki, da ba shi da buri sai na kalar nasara, ni dai a wurin mu da safe ake wannan, ai wannan iskanci ne, ta matso kusa da Liyana da ta wani cunkushe fuska kamar takashin shaniya, wallahi akwai wa ni yaro ɗan gidan Alhaji Ahmed Qasim kyari, wallahi yaron nan ba dai nutsuwa ba. Ga girmama ni da ya ke yi, nace ko shi ai ze iya maneji da ke ai."


"Gaya miki aka yi an gaji da ni a gidanmu?, ke ma mace ce ki sa Jiddah ya sawwaka mi ki kya auri ɗan gidan kyarin ko kuma shi kansa kyarin, kin ga girman zai ƙaru, kin ga ni dalilin da ya sa ba na son zuwa gidanki kenan."

" Daɗina da ke ba'a miki wasa, daga wasa sai ki wani mai da shi gaske, ni dai a wurinmu da safe ake wannan, wannan ai iskanci ne." Jiddah da ke ta dariya kawai ya na kallonsu, abin na ƙara burgesa.

" Liyana da ta ta shi a fusace ta re da faɗin"can za ki ƙarata daga ke har ɗan gidan kyarin in ta kama ki auri kyari meye ruwan ƴar gidan Nabil."

" Rafiƙ ka ji min ƴa daga wasa ta ɗauka da zafi, da wani ƙafarta kamar kara. Ko kallonta Liyana ba ta yi ba (Rafiƙ sunan da Neneh ke kiran mijinta da shi kenan , means companion).



"Oh ni Ajiddeh, Ka ga Rafiƙ duk da

7 / 13