Author : Buddo Category : Hausa Novels 001
mata kunne.''
''wacece Salamatu kuma?." Nabil ya tambayi Nenehn, ''Matarka mana, sallamamiyya, sannan zuwa sati mai zuwa za'a sa ka rana.'' maza ta shi ka fice min.''
''sai da safe.'' ''mu kwana lafiya.''
Ɓangarensu Liyana waƙoƙin afrobeat ake ta saki a hall ɗin , ga komai is white and purple hatta color , ɗin wutan..
her favorite artist aka saka wan da hakan ya sa ta fara bin waƙan _O. B. O. Baddest, it's Davido_ camera man na mata video , komai na masu aji suke yi, ga shampaign, ga kayan ciye ciye, dan ita ta wani manta da wani Sultan, shagalinta kawai take yi.
An ci an sha sannan an yi pictures, daga haka ita da Ily su ka hau mota su ka koma gidan Neneh, gidan shiru ba kowa a ƙasa sai Tv da ke ta aiki.
Ɗakinta su ka nufa tasa Ily ta yi wanka sannan itama ta yi.
Ko da ta kwanta da niyyar bacci miss calls ɗin Sultan sun kai 100 , ga text messages berekete.
Ba ta bi ta kansa ba dan ta san ba ɗagawa zai yi ba.
Kasa bacci ta yi, saboda kalmar ''Mara tarbiyya da kamun kai da ke ringing a brain ɗinta, Dan sai da ta yi shagalinta hankalinta ya kwanta.
''Allah Nagode maka dana mari wannan jar fuskar .''
Daga haka ta hau online ta ɗan yi chat kaɗan tare da sauka ta ja blanket ta na ƙara jin mauryarsa a kunnenta.
Washegari da sassafe bayan an gama komai na gidan Liyana bacci ta koma , dan ta gaji sosai ga kanta da ke mata ciwo.
Ɓangaren gidansu Hydar kam tun da ya dawo mamaki da al' ajabi sun hana sa ta ɓuka komai, is he dreaming? Numfashi mai nauyi ya furzar tare da ɗaukan mack book ɗinsa ya gama abin da zai yi da dealers, sannan ya cigaba da zaman shi ya na daddanna waya, amma still ya ma kasa concentrating, saboda saukan marin da ya ke jin sa har yanzu a fuskarsa.
Washegarin ranar.
Sultana ce ta shigo tare da faɗin ''Yaya Hydar, Abuh na kiran ka.'' gyaɗa kai ya yi tare da saka slippers ɗinsa ya nufi ɗakin Abuh.
Bayan ya shigo da sallama, kallonsa Abuh da ke tare da Mami ya yi sannan ya sakar masa murmushi, shi ma murmushin ya yi tare da zama a ƙasan Turkish carpet ɗin parlourn.
Sai da ya kalli fuskan iyayen nasa, sannan a hankali ya buɗi bakinsa ya ce ''Good morning Maami, Good morning Abuh.'' ''Mornig son.'' iyayen na sa su ka haɗa baki wurin faɗa.
Sai da suka mai kallon some seconds, sannan a hankali, Abbuh ya ce ''Aliyu.'' a hankali ya ɗago kansa ya kalli Abbuhn dan ya san everything serious, directly name na shi ake kira, from that stage da aka kira sunan sa ya san everything is serious, kuma babu maganar ma kar ya yarda, dan last last, ran shi ne zai ɓaci.
''Tunanin mai ka ke haka Papa.'' Mami ta tambaye shi.
''Nothing much maami.''
''Okay Papa, daman is about your wedding preparations.''
''Buh Mami, ni ai ban fitar da kowa zan aura ba, kuma na ji kina wedding preparations.''
Ajiyar zuciya Abbuh ya sauke, sannan a hankali ya ce ''kar ka bani kunya mana zaki, mun zaɓa maka mata ne dan mun yarda da tarbiyyarta da nasabarta, jiƙar Neneh ai abin so ce a wurinka, don't do that son.''
Kallon Mami ya yi sosai, sannan ya ce ''Mami am not ready, wallahi, ta ya ma za'a ce ni zan yi aure imagine, it doesn't make sense at all."
" Son ba za ka iya share min hawayena ba kenan, we have already discussed this with her parents please don't do this to us son."
" Son our last alfarma please."
" Ni Mami stop saying this please Dan Allah."
" Then ka aminta da zaɓinmu."
"Mom."
"Son."
"I can't do that."
"You can son, just try."
Ɗauke kansa ya yi ya cigaba da danna wayarsa.
Muryar Mami ya ƙara ji "please son."
"Mami ga Sultan ku basa ita mana, why me."
" It's because ka fi Sultan hankali, and you're the elder, by this time ya kamata ace kana da aure Papa."
" Am not ready Mami."
"It's alright an yi ta lallami ba ka yarda ba, yanzu kuma ko kana so ka ba ka so sai ka aure ta."
A hankali ya ɗago kansa ya kalleta tare da kallon Abbuh.
"Yeah ko ka na so ko baka so it's a most tun da ba za ka mai da mu ƙananan mutane ba, it's impossible, get out of my site."
Abbuh ya faɗa ya na kai dubansa wurin Mami.
Sai da Aliyu ya furzar da wani numfashi mai zafi sannan ya ce " na yarda zan aureta, buh make sure that a tabbatar duk wani shagali count me out ba na ciki."
"Better." Mami ta faɗa sannan Abbuh ya ce " sai ka shirya ka je ka ganta dan next week or next month, za'a yi komai, leave my presence."
Wayarsa kawai ya ɗauka tare da shiga ɓangarensa. Wanka ya yi kawai tare da shiryawa cikin kaftan black color, with cover shoe, sai hula da ya saka, tare da feshe jikinsa da turarensa na Armani Georgia, haɗe da Valentino.
Car key ɗinsa ya zara daga wurin ajiyar mukulli da ke jikin wardrobe, sannan ya fice daga gidan ba tare da ya yi wa kowa magana ba.
Ɓangaren Abbhi kuwa, ya rasa ta ya zai sami Liyana da zancan, dan sun ce idan aka yi auren Liya da zaɓin su za su yafe masa. Amma ya rasa ta ya zai ma fara mata wannan bayanin, dan shi ya ma manta da ance ya kira Ammi ta je can gidan, tunanin Liyana kawai ke kansa.
Liyana ba ta tashi ba sai arround 12 thirty shi ma da ke unguwar izala ce kiran Sallah ne ya tashe ta.
Wanka ta yi haɗe da wankan tsarki, sannan ta saka palazzo trousers ɗinta da wani polo shirt coffee color.
Ta maka slippers ɗinta, ta zauna a parlour ta na jiran a kawo mata ƴar everyday ɗinta.
Tun da Salimah ta ga ba ta tashi ba ta haɗa mata milky donut ɗinta da kuma, strawberry hollandia yourghurt , ta sa mata a fridge, da ta ji sawun ƙafarta ta fito tare da ajiye mata komai yadda aka saba.''
Bayan Salimah ta kawo mata ta ke tambayar ta ina Ily, ''Ai Aunty Liyana da sassafe ta wuce.''
Gyaɗa kai kawai ta yi tare da cigaba da cin kayanta.
Ko da ta gama sama ta haye ɗakin Neneh, tare da kallon Nenehn da ke ta waya da Mansura.
''Ai idan ba haka aka yi masa ba ba zai gane akwai ragowan ƙafiya a kan Babanku ba, sai kinji yadda ya ke magana wai sai Liyana ta cika shekara arba'in zai aurar da ita kiji fa rashin lissafi irin na shi.''
''Wace Liyanar za'a aurar a 40s Neneh ki daina min fata mara asali wallahi.''
''jai'ra uwar jin sirri, ki daina shigo min ɗaki babu sallama tun da ba gidan ubanki bane ba.''
'' ai ke na kakannin ki ne.''
Katse wayar ta yi tare da faɗin ''Wallahi na jima da sarewa a kanki, gwara na miki auren nan na huta, ke ba aikin fari bare na baƙi, kullum rawa a yanar gizo, wallahi duk rashin ɗan idon fir'auna Asiya ya aura nutsatsiyya da ita wallahi.''
''Kin taɓa ganinta ai.''
''Fita, fita kar ki min saɓo anan.''
''kin ga ba wannan ne ya kawo ni ba, amma dole na tambaya, wace Liyanar za'a yi wa aure? Bayan ni ban kawo wa kowa saurayi da sunan xan auresa ba?."
''Jiddahnku ne ya ce ya miki miji, ɗan gidan Alhaji Kyari.''
''Hankalinki ya kwanta ai ko?.'' toh wallahi Neneh in na mutu ke zan kama, Abbhina ba zai taɓa bari a min haka ba ma nasani.'' ta faɗa tare da murkuɗa baki.
''Shi ya ce a sa sati biyu ai, yau ɗinnan za'a yi komai.''
''Hala nasan rikicin tsohon saurayinki ne ya tashi kike ta imagination yau ɗinnan, bara na yi abin da zai fishe ni daga haka ta fita daga ɗakin Neneh.
Ko da Hydar ya fita gidansu abokinsa Amir ya nufa can Lamiɗo crescent.
Ko da ya zo unguwar a ƙofar gidansu Amir ya parker motarsa, dan ba daɗewa zai yi ba.
A farfajiyar gidan ya tarar da Amir da ke ta zaune ya na jiransa, shi ma ɗan saurayi da shi kyakkyawa ne ba laifi.
Bayan sun gaisa ya zauna ya na shan ɗan fresh milk da ya ke glass cup ɗin a hankali.
''Wallahi Hydar da ma ni na samu damar nan ace an samar min mata, da na fi kowa murna wallahi, ka daina wannan shirmen kawai just focus, babu wani China da zaka koma bayan handling business da ka barwa managers, kuma komai da ake yi kana gani anan since camera ɗin is connected da laptop ɗinka, wallahi kawai ka yi sha'ani.''
''You're mad, kawai ka yarda you're mad Amir, ni fa bana sonta, ban ganta ba amma ba na sonta, ni wallahi har su gama bikin na su baza su ganni ba.''
''Thats your own good oo.''
Tsaki ya ja ya cigaba da kallon Camera ɗin da akai connecting da laptop ɗin na sa.
Ɓangaren Ammi kuwa business ɗinta ta ke yi sosai, babu kama hannun yaro, dan yau akwai kusan gidaje uku da ke son, Classic Abayas, da hijabies a Lamiɗo crescent, tun safe ta ke kiran delivery guy ɗinta amma ba ya picking hakan ya sa ta ɗauki mukullin motar ta tare da fita daga gidan gaba ɗaya.
Gidaje biyu ta kai wa Abayas da hijab ɗin, ta na tuƙinta hankali kwance motar ta kashe kanta ba tare da tasan dalili ba.
Sakkowa ta yi ga ranar da ake tsalawa, mai mugun zafi, duk ya yi mata yawa.
Wayarta ce ta fara ringing, dubawa ta yi ta ga Abbih ke kiranta cikin muryarta mai sanyi da kamala, ta ce '' tohh lafiya? , yau kuma.''
Cikin muryarsa mai amo ya ce ''Hello, kina ina?. ''Na ɗan ta fi delivering kayane.'' ''Where?."
''Lamido crescent.'' ''in kin kai kije rijiyar zaki ana neman ki.'' '' da fatan dai lafiya.'' ''in kin je kya gani.'' ƙit ya katse wayar.
'' murmushi kawai ta yi ta na ƙara jinjina al' amarin Nabil ɗin.
Titin tsit ya ke babu napep ɗin da ke gilmawa, ko ina shiru.
Hydar da ke tsaye tare da Amir da ya fito raka sa ya ga wata mata ta ɗan yi backing na su duk da abaya ce a jikinta.
''Amir ne ya ce is like that lady overthere is searching for help.'' ''ni fa na fita harkar mata a yanzu, za ka iya zuwa ka gane ma kan ka idan hakan ne.''
''Dude Dan Allah zo muje we won't be local a sanadin haka please, kalli bayan ta da kyau wallahi uwa ce ta haife mu.''
''OKAY.''
Daga haka su ka nufi Ammi dake tsaye ta na duba ko Allah zai sa ta samu number mechanic a wayarta.
''Assalamualaikum, good noon Maa.'' Amir ya faɗa, Juyowa ta yi tare da faɗin'' Noon My dear.''
Ɗago kansa ya yi shi ma ya gaidata.
Sannan su ka tambaye ta mai ya sami motar.
''Wallahi Son I don't Actually know, kawai motar ta tsaya, ban ma san ya zan yi da shi ba .''
''Hydar ɗan zo ka duba tun da kai ne ke hawa lexus.''
A hankali ya ta ko tare da buɗe gaban motar ya ɗan yi taɓe-taɓensa sannan ya ce ta shi ga ta kunna, a ta ke motar ta kunnu.
Murmushi ta yi tare da faɗin ''Thank you Son, What's your name?.'' ta faɗa tare da nuna Hydar, '' Am Aliyu buh ana kirana da Hydar.'' ya yi maganar ba tare da ya kalli fuskarta ba, dan haka kawai nauyinta ya ke ji.
'And you?." Ta nuna Amir. ''Am Umar Maa.'' '' Ku duka babana ne kenan motar ta ta buɗe tare da ɗaukan dubu goma, ta bawa Aliyu dubu biyar, shima Amir ɗin dubu biyar.
''toh ga shi ku sa yi chewing gum.'' ''murmushi Aliyu ya yi ban da Umar da ya fara dariya ya ce Maami no need, we are very grateful.'' ''chicken change right?, lemme add more.''
''Noo Mom wallahi, Alhamdulillah, kawai dai we are now men not boys, that's why.''
Da ƙyar ta samu su ka amshi kuɗin, sannan ta shige motarta ta ɗauki hanyar delivery ɗinta.
Shima Aliyu ya ɗauki hanyar gidansu five kee ɗinsa a hannunsa (za ta yi maka rana 🌚😂).
Bayan ta yi delivery ɗin gidan Neneh ta kama hanya amma, yanayin unguwar ya canza.
Ko da Aliyu ya koma bai fi minti talatin ba Mami ta aike sa siyan fruits, Dan sun ƙare a fridge.
A hanyarsa na fita da ga unguwar su ka yi clashing da wata mota zuge glass ɗin ya yi ahankali itama ta zuge nata. ''Murmushi Ammi ta yi tare da faɗin "You again son?, you live arround here?." ''Yes Maa, ina wuni." "An wuni lafiya." Su ka ɗan gaisa sannan kowa ya yi hanyar sa, dan shi rumfar Shehu zai je siyan fruits.
A hankali ta ke gangara motar na ta akan titin da ke malale da kwalta, saboda gidan Nenehn ya ɗan shige mata duhu.
A side ɗin right hand ɗinta ta ga Aliyu shuwa Arabi's mansion, hakan ya ba ta dama da dalilin karkatar da hancin motar ta ta danna horn a cikin gidan.
Mai gadi ne ya buɗe, tare da tambayarta wa ta zo gani, sai da ta ba shi amsa, sannan ya barta ta shiga cikin gidan.
A hankali ta yi parking tare da futowa cikin shigarta na Abaya, ta nufi in da ta fi tunanin entrance ne, shigarta kam ya yi dai-dai, da fitowar hajja daga kitchen dan yau Salimah ba lafiya,.kuma slay queen na bacci.
" Duniya kenan, ƴar ɗakina ta yadda ni, toh yanzu ke miye riba, wallahi kin bani kunya har wannan mai fuska kamar jan ƙosai ya samu raba ni da ke wallahi kin ji kunya, ki tsaya anan na kawo miki ruwa, ƴar daɗi miji, maganar da zan miki second ɗaya ma wallahi ta yi yawa, Allah na tuba an gaya mana miji, har ya gama dai ƙuruciyyar sa bai min kishiyya ba." Neneh ta faɗa ta na kama kujerar falon, ta zauna akansa.
Durƙusawa Ikimat ta yi har ƙasa ta gaida Nenehn, sai da ta amsa sannan ta shigo ta zauna a ƙasa.
"Bara na kawo miki ruwa ƴar albarka, mai shiga tsakaninmu sai Allah, ko Maimu ba ta iya ba."
" Neneh da kanki za ki kawo min ruwa? Ina Liya, ina ƴan aikin?."
Har ta tafi ta dawo ta zauna.
"Liyana ko masifa da kata'i, ai ƙarar ta zan ba ku daman, bata gaida ni, in ban da zagi, da cin mutuncina a gidan nan da ta iya.
Akwai ranar da ta sa aka tsinko mata tsamagiyya wai za ta zane ni fa in gayamiki, nikam nace,hoho hoho idan ƴaƴan Ikimat ba su ji kaina ba wa zai ji kaina."
"Ita Liyanar?."
"Zan miki ƙaryane?."
"A'a Neneh."
" Ta shi kije kiyi girkin ma na fasa."
Ta shi ta yi ta shiga, kitchen ɗin da ya ke a goge sai sanyin tiles ya ke fitar da ƙamshin kayan ƙamshi, dan Neneh na son su sosai.
Cikin minti talatin ta gama haɗa cous-cous da ya sha goat meat, sai ƙamshi ya ke.
Ba su jima da cin abincin ba, Neneh ta fara sanar da ita an yiwa Liyanar miji, da kuma abin da Abbhi ya ce.
"Toh Neneh Allah ya tabbatar da Alkhairi."
"Amin."
Har Ammi ta tafi Liyana ba ta ta shi ba itama kuma ba ta tambaye ta ɗin ba.
Sai da aka kusan kiran magriba sannan ta tashi ta nufi bathroom ta yi wanka tare da saka kayan bacci, sai da ta sha maganin mura sannan ta koma baccin ya ƙara ɗaukanta.
Washegari da safe ma ba ta wani kula Neneh ba dan ba ta jin daɗin jikin na ta tun jiya, ga shi Abbin ya na ta magana akan ta yi haƙuri ta rasa ma da uwar mai za ta haƙura.
A kwana a tashi asarar mai rai hausawa kan faɗa, yau aka sa ranar Liyana da Hydar wan da gaba ɗaya a gidan Nenehn aka saka nan da sati huɗu biki.
Kuma har yanzu ba'a sanar da Liyana bikin ba, kuma har yau sai dai su haɗu da Sultan a gidan Lily ko kuma joint tun da ba school.
Yau dai kam kamar kullum shigarta na palazzo trousers da long sleeve shirt ne a jikinta sai hula black color da slippers ɗinta baƙi, car key ɗin motarta ƙirar Kia Picanto ta ɗauka tare da ɗaukan Atm card ɗinta, ta cilla mint chewing gum ɗinta a baki, ko da ta fito ba ta tarar da Neneh ba, dan haka wucewa ta yi kitchen ta ɗan ɗauki bottle water ta sha rabi sannan ta nufi hanyar motarta, ta ajiye tare da tada motar, mai gadi ya buɗe mata ta cilla motar titi, tare da sakin waƙan _Asake, terminator._
Ta na bin waƙar ta na gyaɗa kai har ta ƙaraso kasuwar kwari, dai-dai wani ƙaton shopping plaza na atamfofi da abayoyi , mai suna _LIYANA PASSION CO._ ta tsayar da motar ta, tare da futowa ta nufi cikin wurin da zamu iya kiransa da kasuwa, dan babu abinda babu a ciki na kayan da mata ke sawa ajikinsu.
A hankali ta sauko tare da shiga cikin babban boutique ɗin, Abbhi da ke tsaye ya na magana da receptionist akan duk wanda ya zo nemansa in dai ba Liyana ba ce ace baya nan ya na companyn atamfarsa.
A hankali ta tako tare da rufe masa idanu.
Murmushi ya yi sosai sannan ya ce "Day maker."
A hankali ta sake masa ido sannan su ka ƙarasa office ɗin sa.
Zama ya yi a CEO chair ɗinsa mai juya mutane, tare da faɗin " Sweet heart, The reason why I called you here is that......"
Kasa ƙarasawa ya yi dan bai ma san ya ya zai fara ma ta bayani ba , kuma this is the only way out for him, Dan Jiddah ya rantse idan ba'a yi auren ba babu su babu shi, ita kuma Neneh ya biya ta nonon ta da ya sha.
He has no choice than ya yi hakan, shi ya rasa mai ya musu da suka ɗauki zafi hakan.
"Abbhi just say it, kar ka ji komai okay, you're my own father, na san ba ka son ɓacin raina buh just say it."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin