MASARAUTAR KAIZUR COMPLETE BY NUSY BEE.doc

Author :  Nusy Bee Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 11

1 to 3K   out of 31.5K words

??????>?? ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument????1
0Table????????
Data
????????????????????? P? tKSKS?1
??????????GGGG+?$?4G??
?
?
?
?
?
?
?
?
$
?? *?GG?
?
GGGG?
? ?+? ?
+?
? +?
?
G+ =?Q?=???? MASARAUTAR KAIZUR =?Q? =????




'?Al?alamin Nusaiba Ibraheem Rimi (Nusy bee)



d'? Young talented writers association YOTA d'?

(Under YOTA'S AMAZING PENS)


Marubuciyar =?G?


Matar khalees
Barrister Hibba
SiraWin u?uba
?addararmu ce ta zo a haka


And now; MASARAUTAR KAIZUR

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE


Littafin MASARAUTAR KAIZUR ?agaggen labari ne,komai da ke cikin littafin nan ?ir?ira ne,kama daga mutane,labari zuwa gari,ko da wani abu ya yi karo da rayuwar wani a zahiri,to a yi min afuwa,a rashin sani ne=?O?



GARGA?I!!!

Labarin MASARAUTAR KAIZUR mallakin Nusaiba Ibraheem Rimi (Nusy bee)ne,ban amince a canja labari ko a juya min ta wata fuskar ba sai da izinina

Ban amince a karanta min shi a YouTube channel ba sai da izinina



SADAUKARWA;

Na sadaukar da wannan littafin ga shugaba,?awa,kuma ?ar uwa Zainab Shehu Abdullahi (Zee kumurya) alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke bright pens >?p?


Da fatan mun yi Sallah lafiya >?p? Allah ya karSi ibadunmu, yasa muna daga cikin ?antattun bayi a wata mai alfarma =?O?


Daga jiya zuwa yau na samu mutane da yawa da suka yi min tuni,(Nusy bee gobe ne fa=??yau ne da=?
? I really appreciate it=?
?na ji daWi sosai da kulawarku a gare ni,kuma ina matu?ar godiya, Allah ya bar zumunci =?O?





CHAPTER ONE

*TSOKACI*


*DAULAR KAIZUR*



"Ya'a?ub! ya'a?ub ka tashi!! masarauta babu lafiya,muna cikin masifa da bala'i"da sauri wanda aka kira da ya'a?ub ya Wago yana kallon mai yi masa magana,a kiWime ya ce"me yake faruwa ne Zayyad?"

"Ba'a ga YARIMA SAHAL ba,ana kyautata zaton sace shi aka yi aka fitar da shi daga masarautar nan,sarki Mu'iz da sarauniya Amna tuntuni sun fito bakin fada,gaba Waya kowa hankalinshi a tashe yake"

Shiru Ya'a?ub ya yi yana bin Zayyad da kallo cikin kaWuwa,an sace Yarima Sahal!magajin masarautar Kaizur,wannan wanne kalar ibtila'i ne ya afka musu haka?don tabbas ya san ba'a ci banza ba,don sarki Mu'iz baya yafiya

Jiki a matu?ar mace Ya'a?ub ya dubi Zayyad ya ce"to ina su Umayr da Urwa da suke kula da shi?"

"Umayr ya tsere,amma an kama Urwa,sai dai yana ta rantsuwa daga shi har Umayr basu da laifi,ba su san yadda hakan ya kasance ba,sarki dai ya ce a wuce da shi da sauran yaranshi a bincike su "Ya'a?ub bai sake magana ba ya mi?e yana gyara zaman tufafinshi,ya nufi hanyar fita daga Wakin nasu, Zayyad ya biyo shi jiki yana tsuma

A bakin fada ya ga jama'a sun taru,a nutse ya ?arasa cikin mutane kanshi a ?asa, Kamar yadda ya san al'adar masarautar,idan har Sarki yana magana ba'a kallonshi

Bayanan Sarki sun firgita mutane matu?a,sarki Mu'iz ya juya ya koma cikin fadarshi ba tare da ya saurari uzurin kowa ba, gimbiya Amna da ke tare da shi ta rufa masa baya

Cikin saSulewar jiki kowa ya fara zarewa da WaiWai da WaiWai bisa umarnin babban hadimin Sarki,wanda shima a take ya juya ya bar wajen,mutane suka fara watsewa suna ?us?us,kowa yana mamakin dalilin da ya sa aka sace Wan Sarki Mu'iz, da hanyar da aka bi duk da tsauraran tsaro da ke masarautar

Shima Ya'a?ub wucewa sashen su ya yi zuciyarshi cike da fargaba kamar kowa,da tsananin mamakin wanda ya aikata wannan Wanyen aikin cikin wannan talatainin daren






=???


Da tsananin gudu dawakansu suke keta manyan dazukan masu cike da ababen tsoro da matsananciyar duhuwa,su uku ne, dukkansu sanye suke da ba?a?en kaya,hatta fuskarsu rufe take da ba?in fuske,Waya daga cikinsu ne yake ri?e da wani Wan ?aramin buhu wanda da alamu akwai abu mai Wan girma a ciki

Sai daf da asuba suka iso masarautar Jasus,na gabansu,wato wanda yake Wauke da buhun nan ne ya fara jan linzamin dokinshi don tsayawa,hakan ya sa sauran ma suka tsaya

Juyowa ya yi yana kallonsu,cikin dakakkiyar muryarshi irin ta gwarazan mazan fama ya fara magana

"Nan da kowanne lokaci daga yanzu asuba zata iya yi,hakan kuma yana nufin fitowar mutanen cikin garin JASUS don yin Sallah,kuma idan muka shiga da wannan kayan ina da tabbacin asirinmu zai iya tonuwa, kun san dai yadda MASARAUTAR KAIZUR take,to masarautar Jasus sun fi mu

Su bala'i,don haka za mu yar da shi a nan kawai,akwai muggan namun daji, cikin Wan lokaci ?alilan za su iya gamawa da shi,amma ya kuka ce?"

Na farkon ya ce"ah!hakan ya yi sosai,babu matsala,mu aiwatar da hakan"babu musu suka jefar da buhun,shugaban yana kallonshi yana murmushi ya ce"to Magaji!

Sai na ce sai haWuwa ta gaba?"ya kaWa linzamin dokinshi,sauran ma suka kaWa nasu,suka canja hanya





BAYAN SHEKARU ASHIRIN




*DAULAR TAYYAR*


Tun daga nesa dakarun da ke tsaron babbar ?ofar shiga al?aryar Tayyar suke jin kaWe-kaWe da bushe bushe,wanda hakan alamu ne na nasarar ya?in da suka fita zuwa gawurtacciyar daular matsafa,kuma azzalumai wato daular BARUDA,inda Sarkin wannan daula,kuma gagarumin matsafi wato SARKI AKAAL yake mulki

Tsawon shekaru goma sha Waya kenan suna ?o?arin ya?ar daular ta Baruda,amma hakan ya gagara, sakamakon tsananin ?arfi da izza irin ta maya?a da matsafa a ?asar,sun addabi manyan garuruwan da suke ma?wabtaka da su

Farin ciki mai yawa ya bayyana a fuskokin dakarun nan,shugabansu,wanda ya kasance mai shela a yayin da maya?an suka fita ya?i,a yayin da jama'ar gari suke dakon jin sautin busa cike da fargaba

A yau dai sautin ya bambanta da wanda aka saba ji a duk lokacin da aka fita zuwa gagarumin ya?i irin wannan, musamman da daular Baruda,a maimakon sautin kukan mikiya da ya saba tashi wanda yake nuni da ba'a yi nasara ba,yau sautin sarewa, wanda yake bayar da tabbacin nasara daga wannan gagarumin ya?i shine ya tashi

Cikin Wan lokaci ?an?ani garin ya kaure da sowa da farin ciki, kaWe-kaWe da bushe,tuni mata suka fara Wora girke -girke da harhaWa ababen sha na alfarma,hatta yara ?anana cike suke da farin ciki

Cikin lokaci ?alilan maya?an da suka dawo daga ya?in suka ?araso,an samu shahidai mutum ashirin da bakwai a cikin maya?a dubu uku da suka fita,sannan an samu ribar ya?i har mutum hamsin da uku,ciki har da gawurtaccen maya?i,kuma matsafin nan wato KAZUZI

Sanannen abu ne cewa duk wanda ya yi karo da shi sai dai ya amsa sunan gawa, saboda tsananin ?arfi da tsafi da yake da shi

Kazuzi shi kaWai ya tarwatsa runduna guda da suka tunkari Baruda da ya?i a lokaci Waya,a kowanne lokaci kazuzi a shirye yake don ya?i,duk girman runduna da ?arfin maya?a ba sa ba shi tsoro,an taSa ?arar da rundunar Baruda,amma shi Waya ya yi nasarar ya?in ya gama da rundunar abokan hamayya ya gurfanar da sarkinsu a gaban sarki Akaal

Kai tsaye aka gabato da dakarun ya?i guda hamsin da biyu da aka kama waWanda aka Waure su da wata doguwar igiya Waya a bayan Waya, jama'ar gari sai ihun murna suke yi,kiWa da busar da ake yi ta ?aru,karo na farko kenan a tarihi da aka taSa cin nasara akan daular Baruda a tsawon ?arnin, kasancewarta daula mai tsananin ?arfin jarumai da ?arfin tsafi

Kawunansu a ?asa suke wucewa, mutanen gari da suka jeru suna kallonsu kowa da abin da yake faWa cikin farin ciki, dakarun da suka shigar da su suka rufa musu baya,kai tsaye aka nufi ?ofar fadar masarautar Tayaar

Daga nan keken doki na alfarma shigo,wanda yake Wauke da mutane ashirin da bakwai da suka yi shahada a wannan ya?in,kalamai na nuna tsantsar alhini suka fara tashi daga bakunan mutane,wasu kuma suna ?arfafa gwiwa da kasancewar sun yi gagarumar nasarar da ba su taSa yi ba a kowanne ya?i, ballantana ya?i a Daular Baruda

?aton toron giwar da ya fara shigowa cikin ?asaita ne ya katse cecekucen mutane,wajen ya yi tsit tamkar ruwa ya cinye ilahirin dubban jama'ar da ke bakin fadar

A saman toron giwar an Waure wani madaidaicin keji,wanda ake iya ganin mutumin da yake cikin kejin,amma ba'a iya ganin fuskarshi, sakamakon dogon gashin shi da ya sauka har kafaWarshi,ya zubo ta gaban kanshi ya rufe fuskarshi, kasancewar ya sunkuyar da kanshi, hannayenshi da ?afafunshi Waure suke da wata ?atuwar sar?a, irin wadda aka yi amfani da ita aka Waure kejin da yake ciki

Babu wanda ya ?ara ?wa?w?waran motsi sai da toron giwar nan ya shige cikin daular Tayaar,daga nan mutane suka fara watsewa Waya bayan Waya,da yawansu a razane suke duk da tarin nasarar da suka yi, musamman waWanda suka yi karo da shi suka san wanene ainihin KAZUZI

Daga nan kuma kallo ya koma sama, maganganu suka rin?a tashi na mamakin yadda kazuzi ya yarda ya shigo hannu, inda wasu suke ganin kawai nasara ce daga Allah,wasu kuma suke ganin lamSo kawai ya yi, hakan wata dabarar ya?i ce don ya cimma nasara akan abokan gaba, saboda sanannen abu ne a wajen duk wanda ya san wanene kazuzi,baya taSa yarda a yi nasara akan shi

Cikin Wan ?ankanin lokaci mai shela ya fara yekuwar sanar da al'ummar garin kiran da Sarki yake yiwa ilahirin al'ummar garin bakin fada,don a sallaci shahidan da suka riga mu gidan gaskiya a ya?in nan,sannan kuma zai yi muhimmiyar sanarwa,da haka kowa ya wuce gida don shirya amsa kiran sarki





*DAULAR KAIZUR*


Kamar yadda aka saba Rabee'a ne ya ja sallar azahar da aka yi a farkon mukhtarinta,kamar yadda sarki Mu'iz ya ba da umarni,yau gaba Waya masarautar a firgice take saboda yadda yanayin da sarki Mu'iz ya tashi da shi, kaWan daga aikinshi ne ya huce ta hanyar raba wani da ranshi

Kai tsaye turakarshi ya wuce bayan an idar da sallar azahar,kallo Waya za'a yi masa a gano tsananin tashin hankalin da yake ciki saboda yadda fuskarshi ta kaWa ta yi jawur

Da sallama sarauniya Amna ta shiga turakar, ba tare da ya waigo ya kalle ta ba ya ce"da wani abu ne sarauniya?"

Cikin girmamawa ta ce"dama batun abinci ne ya shugabana!

An gama haWawa,a kawo ne?"ba tare da ya kalle ta ba ya ce "ba yanzu ba,za ki iya tafiya"ta sake rissinawa ta ce"ka huta lafiya ya shugaba na"ta mi?e don ficewa daga Wakin

"Ki cewa yarima Zaffar ya shigo,ina son magana da shi"ta tsinkayi muryarshi

Sake rissinawa ta yi ta ce"an gama ya shugaba na"sannan ta nufi ficewa daga cikin ?asaitacciyar turakar

A ?aton katafaren masaukin ba?in da ke cikin gidan ta tarar da Yarima Zaffar da Yarima Jamal a zaune suna jiran fitowarta,ita kam zuwa yanzu ta daina mamakin duk abin da sarki Mu'iz ya yi, yadda yake ganewa a duk lokacin da Yarima Zaffar yake kusa da shi saboda tsananin ?auna da soyayyar junansu

Kallonshi ta yi tana murmushi,ya rissina tana faWin "Barka da fitowa ya shugaba ta!"

"Zaffar!

Yanzu mai martaba kuwa ya ce na yi masa magana da kai,ashe dai kana kusa,wannan ?auna tsakanin ka da mai martaba dabam take"

Murmushi yarima Zaffar ya yi, cikin girmamawa ya sake kallonta ya ce"ranki ya daWe ai tasirin jini ne kawai, kin san an ce jini ya fi ruwa kauri"

Sarauniya Amna ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce"haka ne!

To yanzu dai ka amsa kira, don kamar ma baya cikin yanayi mai daWi"

"An gama ranki ya daWe,ki huta lafiya"ya faWa da girmamawa kamar koda yaushe,sannan ya mi?e ya nufi turakar Sarki Mu'iz

Yarima Jamal ya bi shi da kallo cikin takaici,a yayin da sarauniya Amna ta yi tafiyarta ta bar shi a wajen,ya mi?e tsaye cikin Sacin rai,a ranshi yana jin dole ma ya karSi kujerar daular kaizur bayan wucewar Sarki Mu'iz zuwa kushewa duk da kasancewar Yarima Zaffar ya girme shi,da wannan tunanin ya bar wajen zuciyarshi cike da ba?in ciki,da muradai kala-kala

Sarki Mu'iz ya yi masa iso daga inda yake kishingiWe a kwance akan ?awatacciyar kilishin da ke shimfiWe a tsakar Wakin, Yarima Zaffar ya ?araso ya rissina a gabanshi yana faWin"Barka da wannan lokaci ya shugaba na"

Kallonshi sarki Mu'iz ya yi, lokaci guda ya mi?e tsaye,ya dubi yarima Zaffar ya ce"mu je Yarima!"ba tare da musu ba Yarima Zaffar ya mi?e,kai tsaye suka nufi wata kusurwa a cikin turakar

Kamar ba a cikin dakin sarautar ba,wajen da duhu sosai,sarki Mu'iz ya saka hannu ya taSa wani abu da shi kanshi Yarima Zaffar Win bai san da shi ba,take wata ?ofar sirri ta buWe,sai ga wani madaidaicin Waki ya bayyana

Ba yau Yarima Zaffar ya saba ganin Wakin ba,shi yasa ya zama sanannen abu a wajenshi cewa duk lokacin da sarki Mu'iz yake cikin wani yanayi mara daWi to yana da ala?a da wannan Wakin

Cikin rauni da sarewa sarki Mu'iz ya dubi ?anin nashi Yarima Zaffar ya ce "Zaffar!

Ban san tsawon wanne lokaci zan Wauka ina kuka da fargabar inda Wana SAHAL yake ba

Kai shaida ne,tsawon shekaru ashirin kenan da Satan shi,amma ban ga wani canji daga taurarin shi ba,sai dai kewarshi da fargabar halin da kujerar kaizur zata shiga idan na bar duniya

A kullum ina ganin taurarin Sahal da haske tamkar wal?iya,amma a yau na ga abin da ya kaWa hanji na"

Yarima Zaffar ya kalle shi zuciyarshi cike da fargaba, saboda wannan bayanin da sarki Mu'iz ya Wauko akwai dalili, cikin fargaba ya ce"menene yake faruwa da Yarima ya shugaba na?"






*To jama'a ya kuka ji tafiyar MASARAUTAR KAIZUR?ba mu saba irin wannan tafiyar ba ko? tafiya ta musamman kenan,ku biyo ni kawai!!!*


#Nusy_bee
08125952284

=?Q?=???? MASARAUTAR KAIZUR =????=?Q?





'?Nusy bee
d'? Young talented writers association YOTA d'?



(Under YOTA'S AMAZING PENS)



Page 2




Cikin jimami sarki Mu'iz ya kaWa kanshi, lokaci guda kuma ya buWe wani Wan ?aramin abu mai kama da akwati,take wasu taurari guda uku suka bayyana ?an ?anana,sai dai sun yi jawur da su

Yarima Zaffar ya Wan bi taurarin da kallo cikin fargaba,idan ya fahimta hakan na nuni da cewa Yarima Sahal yana cikin tsaka mai wuya kenan,to a wanne hali yake ciki?kuma a ina?kuma me ya same shi?

A ta?aice ma dai a ina ya rayu tsawon waWannan shekarun amma suka kasa gano shi duk irin yawon da suka yi?

Kallon sarki Mu'iz ya yi wanda ya damuwa ta gama bayyanar masa a fuska, cikin sanyin murya ya ce"to yanzu shugaba na menene abin yi?

Ya zamu yi?"sarki Mu'iz ya girgiza kai ya ce"nima bana ce ba,bana son sarauniya ta san da wannan batun,don ban san yadda zata yi ba,kullum ina gaya mata cewa Wanta lafiya yake,amma a wannan karon ban san yadda zata Wauki wannan maganar ba"

Kai tsaye yarima Zaffar ya ce"kar ka gaya mata ya shugaba na,ina fatan in sha Allahu watan watarana Yarima zai dawo cikin masarauta,har ma ya karSi ragamar da take jiranshi tsawon shekaru"

Sarki Mu'iz ya dafa kafaWar ?anin nashi, cikin raunin murya ya ce"ina fata fatan haka Wan'uwa"

Jiki a saSule suka fito daga cikin Wakin,sarki Mu'iz ya sake kwanciya a turakar tashi,yayin da Yarima Zaffar ya fice daga turakar cike da jimamin wannan abu





*DAULAR TAYAAR*

lokaci ?alilan baya,?asa da sa'a guda da aka sallaci gawarwakin waWanda suka yi shahada a ya?in da suka fita da daular Baruda,an raka su zuwa gidajen su na gaskiya cikin aminci, zuciyoyin masoya da yan'uwa cike da alhini da jimami,daga nan an dawo fada,don sauraren kiran sarki da jawabin da zai gabatar

Ba'a Wauki lokaci ba sarki IYAAD ya bayyana cikin shigar ta alfarma,fadawanshi da suke tare da shi suka nunawa mutane wajen zama,mutane suka zauna,fada ta yi shiru suna jiran abin da sarki Iyaad zai faWa

Tsawon wasu da?i?u ya Wan yi shiru, kafin ya yi gyaran murya cike da salon izzar mulki,ya yi sallama cikin wani amo mai jan hankali,wanda yake tattare da mazantaka

Gana Waya fadar aka amsa,cikin nutsuwa da kamala ya fara bayani

"To alhamdulillahi!

Bayan tsawon lokaci Allah mai kowa mai komai ya cika mana burin mu

Kamar yadda muka sani Daular Baruda daula ce da ta Wauki tsawon lokaci tana rainon azzaluman maya?a, waWanda suke tarwatsa dukkan wani gari da suka gani da aminci

Daular Baruda bata tsaya iyaka nan ba,tana ya?i da Muslunci da musulmai, kusan na ce daula ce da aka yi amfani da zalunci da ?arfin tsafi aka gina ta don a rusa musulunci

To amma da yake Allah shine mai iko a bisa komai a yau ya ba mu iko mun dur?usa daular azzalumai ta Baruda"take ilahirin fadar ta ruWe da kabbara da muryoyi mabanbanta,wasu har da kukan farin ciki

Sarki Iyaad ya cigaba da bayani "bayan mun yi nasarar lalata wannan azzalumar daula,mun yi nasarar hallaka sarkinsu,da sarkin matsafan wannan daula,da duk wani badakare da ake amfani da shi ake cin nasara akan musulunci "take aka sake ruWewa da kabbara,da ?ananun ?an maganganu ?asa-?asa da ke cike da farin cikin faWar ra'ayi,sai da aka nutsa sarki Iyaad ya Wora da bayaninshi

"Nasararmu bata tsaya anan ba,har sai da muka kama babban badakaren da ya mayar da ya?i tamkar wasa,sadaukin da idan bai Wauki rai ba baya jin daWi,jarumin da kisa tamkar ma?on ruwa ne a wajenshi,wanda duk girman runduna bata ba shi tsoro,duk ?arfin runduna baya razana shi, duk shiri da tumbatsar runduna a Wan ?ankanin lokaci zai iya tarwatsa shi komai yawanshi,jarumin da ya?i da Waukar rai tamkar wasan yara ne a wajenshi,wato Sadauki KAZUZI!"

?if fadar ta yi, tamkar babu wani mai numfashi a cikinta ba don komai ba sai don ambaton sunan kazuzi da sarki Iyaad ya yi, sarki Iyaad bai damu ba ya cigaba da jawabi

"Don haka muna cike da murna da farin ciki na wannan Gagarumar nasarar, wadda muka tabbatar da cewa ba wayon mu ko ?arfin mu bane ya bamu,sai iko da buwayar Ubangijin talikai,muna mai mi?a godiya a gare shi"

Gaba Waya mutanen fadar suka ruWe da kabbara,har da waWanda suka firgita da wanzuwar Kazuzi a cikin Tayaar,sarki Iyaad bai damu ba,ya cigaba da jawabin farin ciki da suke ciki,a ?arshe ya ?ara da faWin"muna yi wa iyalan shahidanmu gaisuwa, musamman ma jarumi WALEED,wanda shine ya sau?a?a mana hanyar da muka samu nasara akan azzalumi Kazuzi,duk da cewar da kuskure a hakan

A ?arshe ina mai farin cikin sanar da ku cewa za'a yi babbar liyafa ta wannan nasarar da muka yi a bakin fada,zuwa gobe da hantsi,na sallami kowa"

Haka taron fada ya tashi,mafi akasarin mutane suna cikin matu?ar farin ciki,yayin da wasu daga cikinsu suke cikin fargaba saboda wanzuwar Kazuzi a cikin Tayaar,wanda sanannen abu ne a wajen jama'ar garin,ba ma su ba,har da ma?wabtansu na yadda yake da haWari





=???('


Sarki Iyaad ya dubi wazirinsa da yake zaune kusa da shi,ya ce"waziri!

Allah ya yi,mun yi nasara a ya?in nan da daular Baruda,har ma mun kawar da damuwar da ta addabi gaba Wayanmu, wato Kazuzi,yanzu ya kuke ganin za'a yi da shi?"

Waziri ya Wago kanshi a nutse, cikin girmamawa ya ce"ya shugaba na babu abin da ya rage sai a

1 / 11