MASARAUTAR KAIZUR COMPLETE BY NUSY BEE.doc

Author :  Nusy Bee Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 11

12K to 15K   out of 31.5K words

sosai, cikin Sacin rai ta fara masifa tana kai masa duka,amma ko gezau, sai kallonta kawai da yake yi, dakarun da suke tsaron lambun suka taho da gudu don jin ba'asi, idanunta a rufe ta ce"ku kira dakare Amjad!"babu musu wani badakare ya juya don kiran shugaban dakaru

Bayan sun iso ta dubi Amjad idanunta suna kaWawa ta ce"ku tafi da shi,ku azabtar da shi,har sai ya faWi dalilin da ya sa ya ?ura min idanu yana kallo na a yayin da nake wanka,kar a ba shi ruwa da abinci sai sau Waya a rana,a tabbatar an Wora shi a SIRA?IN U?UBA irin wanda bai taSa hawa ba tsawon rayuwarsa"shi Kazuzi sai yanzu ma ya ji laifinshi, Amjad ya rissina ya ce"an gama ya shugaba ta,sannan ya finciki Kazuzi, Kazuzi bai yi musu ba ya bi shi suka tafi

Duk da hukuncin da ta saka ayi wa Kazuzi hakan bai saka ta huce ba,cikin tsananin Sacin rai ta nufi sashenta, kamar yadda ta saba idan ranta yana Sace sai da ta kori kowa a sashen sannan ta kwanta akan gadonta tana sauke numfashi cikin Sacin rai

Ta rasa me zata yi wa wannan ?as?antaccen bawan ta ji sanyi a ranta,gaba Waya ya raina matsayinta,ba ita ba ma,ya raina dukkan wani mai matsayi a Tayaar,amma zata yi duk mai yiwuwa ta yi maganinshi




=???

Da gasken gaske su Amjad suke ganawa Kazuzi azaba iri-iri,kuma ko sau Waya bai taSa yun?urin kare kanshi ba,hakan ya bawa dakarun mamaki,kuma ya yi musu daWi, waWanda suke jin haushinshi suka samu damar rama duk abin da ya yi musu

A cikin kwanaki uku sun yi nasarar galabaitar da Kazuzi irin yadda suke so,sai dai babu alamun rissinawa ko tsoro a tare da shi,kuma sam babu alamun damuwa a kan fuskarsa

A wannan ranar ne gimbiya Hayat ta saka aka fito da shi,kai tsaye aka nufi lambunta da take zaune ita da amintattun kuyanginta kamar yadda suka saba,suna nan a zaune dakare Amjad ya shigo da Kazuzi da taimakon wasu dakarun,suna zuwa suka jefar da shi a gaban gimbiya

Murmushi mai kyau Hayat ta yi tana kallon Kazuzi, kafin ta ce"a kwance masa igiyar"babu musu aka kwance masa igiyar,ta dubi dakarun ta ce"za ku iya tafiya"suka rissina suka juya suka fice daga lambun

Cikin isa Hayat ta kalli Kazuzi ta ce"na san baka yi nadama ba yanzu ma,don da alamu kana da girman kai da Waukar kanka wani,bayan kai Win ba wata tsiya ba ce illa bawa ?as?antacce

Ko babu komai zuwa yanzu ka gane ni ba kalar matan da kake kalla bane lokacin da kana garinku na zalunci,ba zan ce ka daina ba,amma hukunci yanzu aka fara Wauka a kanka"

Gyara zama ya yi yana yin ?asa da kai,ya ce"ki gafarce ni ya shugaba ta,ban san me kike magana akai ba,amma a duk lokacin da kike shirin Waukar mataki akaina a shirye nake na amsa ya shugaba ta

Amma ina so ki sani cewa,babu wata mace a idanun Kazuzi sai MALLI!duk wata mace koma bayan Malli namiji ne a idanun Kazuzi!!!"

Da tsananin mamaki take kallonshi,da farko kasa magana ta yi, kafin ta ce "har ni?Nima kana nufin namiji ce?"

Kai tsaye ya ce"har ke,ki gafarce ni ya shugaba ta"ya Waga kai ya kalle ta ya ce"an sallame ni?zan iya tafiya?"



(Ga masu son VIP group ga number ta nan a ?asa)

#Nusy_bee
08125952284



=?Q?=???? MASARAUTAR KAIZUR =????=?Q?





'?Nusy bee
d'? Young talented writers association YOTA d'?

(Under YOTA'S AMAZING PENS)




Page 8



Hawaye ne suka zubowa gimbiya Hayat,wani irin kuka ya ?wace mata, tunda take a rayuwa ba'a taSa ci mata mutunci irin na yau ba, kallonta Kazuzi ya yi,a hankali ya ce "ki gafarce ni ya shugaba ta,ban faWi hakan don na Sata miki ba,na faWa ne don na wanke kaina ban yi tsammanin abin zai yi miki zafi ba

Abin da nake so na fahimtar da ke shine ni ba ma'abocin kula mata bane,mace Waya na so a rayuwa ta,kuma a kanta na Wora dukkan burina,da ban same ta ba shine na cire dukkan buri na akan wata mace,amma idan ba ki gamsu ba za ki iya Waukar mataki akaina"

"Tashi ka ba ni waje"ta faWa a tsawace

Mi?ewa ya yi ba tare da ya sake magana ba ya fice daga lambun, ta bi shi da kallo zuciyarta tana yi mata zafi

Ita da kanta ta sani tana cikin mata uku da suka fi kowacce mace kyau a kaf ilahirin ?asar Tayaar,sai dai sam maza ba sa gabanta,amma yau wani ?as?antaccen bawa, kafirin banza yana kiranta da namiji,ita kuwa zata so ta ga wannan Malli Win da yake cewa ita kaWai ce mace a idanunshi,don ta gani da me ta fi ta

Mi?ewa ta yi ranta a jagule ta nufi sashenta da yake jikin lambun,a ranta tana ?ara jin tsanar wannan ?as?antaccen dan wula?ancin,a cewarta






*DAULAR KAIZUR*


Cikin wata duhuwar dokar daji yake tafiya,mai cike da ababen tsoro da firgitar da bil adama, sanye yake da wasu ba?a?en kaya waWanda ba su bayyanar da komai nashi ba,sai ?wayar idanunshi da ta bayyana daidai wajen da aka shata a jikin yankin da ya yi amfani da shi ya rufe fuskarshi, tafiya yake nutsuwa da kwanciyar hankali babu alamun tsoro ko firgici a tare da shi

Sam halittu masu ban tsoro da kukan dabbobin da yake arba da su ba su ba shi tsoro ba, cikin nutsuwarshi ya cigaba da tafiya har ya isa wajen wani ?aton kogo a tsakiyar dajin

Tun daga bakin ?ofar kogon mutum zai gane wannan ba wajen zuwan mutane masu iymani bane, saboda tun daga bakin kogon ake fara cin karo da ?asusuwa dabam dabam na sassan jikin Wan adam, ba tare da tunanin komai ba ya danna kai cikin kogon

Halittu masu razanarwa da iface-iface kala-kala na wasu nau'in halittu masu tsananin ban tsoro,amma ko kallo biyu baya yiwa halittun ya mi?e ya cigaba da tafiya har ya kai ?uryar kogon

Gaban wani dattijo ya rissina kanshi a ?asa, cikin tsananin girmamawa ya furta "gaisuwa gare ka ya babban matsafi, ishashshen da babu kamarshi,sarkin aljanu da mutane,uban duk wani matsafi, raina fansa ke a gare ka sarkin bokaye lamzur dodo a cikin matsafa"

Tsohon, wanda ya kasance abin tsoro ga duk wanda ya fara arba da shi a kallon farko,idan mutum mai raguwar zuciya ne ganin wannan hatsabibin tsohon ya isa ya halakar da shi saboda tsananin munin siffar halittar shi

Dattijo ne sosai,don a ?alla zai iya kai wa shekaru Wari da ashirin,farin gemunshi an raba su gida biyu an kitse su gefe da gefe,an yi musu kwalliya da wasu jajayen duwatsu marasa kyan gani,kanshi ?wal babu gashi ko Waya,sai wasu zane zane da suka canjawa kan kamanni,daga goshinshi akwai wani tambari mai kama da tsayuwar wata,kunnuwanshi sanye suke da wasu ?an kunnaye marasa kyan gani

Gaban dattijon wuta ce take ci sosai, dattijon bai ba shi amsa ba sai da ya Wauki wata kaza mai rai a gefenshi ya jefa a cikin wutar,bayan wasu yan da?i?u ya Wago yana kallon shi

"Uban shaiWanu!ka saSa al?awari!

Ba haka muka yi da kai ba"kan uban shaiWanu a ?asa ya ce"ina neman afuwa ya shugaba na"

"Amma menene dalilin da ya sa tun da farko ba ka gaya mana ba sai yanzu?"

"Kuskure ne da Satan basira ya shugaba na,amma ina neman afuwa"

"Babu afuwa!

Za ka amshi hukuncin ka,ka je,kar ka sake dawowa Sai nan da watanni shida,don haka ka tafi!!"ya ?arashe da tsawa

Jiki na rawa uban shaiWanu ya mi?e, ba tare da ya sake magana ba ya fice daga cikin kogon, duk wannan wahalar da ya sha ya zo wajen ba ita ba ce ta dame shi, damuwarshi shine yadda zai samu cikar burin shi cikin sau?i

Bai ji ko War ba, asalima ba wannan ne karo na farko da ya fara karSar hukunci daga boka lamzur ba, hukuncin ya ?are a Wora daga inda aka tsaya






*DAULAR TAYAAR*


Izuwa yanzu kwata-kwata Hayat ta yi duk mai yiwuwa ta rabu da saka Kazuzi a idanunta saboda har yanzu tana jin zafin maganar da ya gaya mata,ko da a ce zata shiga lambunta Kamar yadda ta saba matukar ta hango shi zata aika masa cewa ya fito tana son shiga,bai taSa nuna damuwa ba,sai ya fito

Tsawon sati biyu aka Wauka a haka, kuma har lokacin abin da Kazuzi ya gayawa Hayat yana yi mata zafi,kuma har lokacin tunanin hanyar da zata Wauki mataki akanshi take yi,amma ta rasa hanyar hakan

Yau tana zaune a lambunta tana shan ?a?an itatuwan da wata kuyangarta ta haWa mata,tana sha tana kalle-kallen tsuntsayen da suke shawagi a cikin lambun tana murmushi

Babu zato babu tsammani tana Waga kai ta yi arba da shirgegen kumurcin maciji ya fasa kai yana kallonta, gigicewa ta yi,ta kurma wani uban ihu a firgice,macijin bai yi wata-wata ba ya yi tsalle ya nufi inda take,ta dun?ule a waje Waya tana jiran mai afkuwa ta afku,don ta tabbatar kafin dakarun da ke tsaron bakin lambun su kawo mata agaji komai ya faru,gashi yau bata shigo tare da kuyanginta ba,da yake wasu lokutan ta kan yi hakan

Amma sai ta ji shiru macijin bai ?araso inda take ba,a tsorace ta Wago da kanta tana kalle-kalle

Da tsananin mamaki take kallon Kazuzi wanda ya dam?i wuyan macijin da tsananin ?arfi,a kallo Waya da ta yiwa macijin ta ga alamun galabaita saboda sha?ar da Kazuzi ya yi masa,a firgice ta yi kanshi tana faWin "kar ya kashe ka!ka sake shi!!ba ka da hankali ne?maciji bai san da wani karfinka ba,mutuwa za kayi"

Duk SaSatun da Hayat take yi bai sa Kazuzi ya saki macijin ba,dakarun da suka shigo da gudu suka tsaya suna kallonshi, Amjad ya daka masa tsawa "saki macijin nan!

Ko ba ka ji abin da gimbiya ta ce bane?"

Ko kallonsu bai yi ba, sai kallon macijin da yake yi, cikin nutsatstiyar muryarshi ya ce"ya zama gargaWi na ?arshe,kar ka sake"yana kai wa nan ya murWa wuyan macijin da ?arfin tsiya,take ya raba kan macijin da gangar jikinshi

A fusace dakare Amjad ya yi kanshi yana masifa, Sarkin ya?i da ya ?araso wajen ya daka masa tsawa,a fusace ya dube shi ya ce "a maimakon yabo da zai samu na ceton ran gimbiya har sau biyu sai ya samu sakamako irin wannan daga gare ka?"

Rissinawa Amjad ya yi,ba don ya so ba ya ce"ka gafarce ni ya shugaba na"daga nan ya juya ya fice daga lambun,sauran dakarun suka bi bayanshi,shima Kazuzi ya Wauki jikin macijin nan ya bi bayansu

A sanyaye Hayat ta bi Kazuzi da kallo, yaushe ya iso wajen ma har ya ceci rayuwarta duk da wula?anci da cin mutunci da take yi masa?

Take idanunta suka kawo ?walla, Sarkin ya?i ya rissina ya ce"ki gafarce ni ya shugaba ta,zamanki a nan akwai haWari,zai kyautu ki koma sashenki saboda samun aminci"

Babu musu ta wuce ta fara tafiya jiki a sanyaye,dakarun da ke tsaron bakin ?ofar suka raka ta har zuwa sashenta





=???

"Menene matsalarka da macen da take wula?anta ka a kowanne lokaci? menene dalilin da ya sa lallai sai ka kare mata hari?

Hakan ya tabbatar min da mazantakar taka ta ?arya ce tunda ta lalace a wajen Waukar wula?ancin mace"

Kazuzi da ke zaune yana gyara dogon gashin kansa da hannunshi ko Wagowa bai yi ba ballantana ya dube shi,asalima hankalinshi yana wani wajen, tunaninshi yana wajen abar ?aunar ruhin shi Malli, wadda da suna tare da yanzu ita ce take yi masa gyaran gashin

"A don haka ina mai jan kunnenka da ka tsaya a iyakarka,babu ruwanka da shiga sabgar yarinyar nan idan ba abu ta saka ka ba,da kana da zuciya da ka daina shishshigi da shiga shirgin ta don ka tsira da mutuncin da ya yi maka saura,idan kuma baka ji ba,duk abin da ya same ka kai ka janyo wa kanka,kafirin banza kawai "

Duk wannan SaSatun da yake yi ko Wago kai Kazuzi bai yi ba ballantana ya kalle shi,ya cigaba da gyara gashinshi cikin nutsuwa tamkar ba da shi ake ba,sai da ya juya,yana daf da fita ya ji muryar Kazuzi

"Mafi alkhairi a gare ka kar ka sake farmakar ta!"

Dawowa ya yi da baya yana kallonshi,ya kasa gaskata maganar da ya ji daga bakinshi,da ?yar ya iya faWin

"Ban ji abin da ka ce ba,ka san girma ya taSa kunnen"

Ba tare da wata shakka ba Kazuzi ya sake faWin "ka fita daga harkarta,ya zama karo na ?arshe da za ka sake farmakar ta

Zuwa yanzu na san ka gane Kazuzi ba kanwar lasa bane, kasancewa ta a cikinku hakan ba yana nufin daidai nake da ku ba, muddin ina numfashi zan gani idan makircinka zai iya taSa ko da silin gashinta "

Da tsananin mamakin yadda kazuzi ya gano shi ya dube shi, cikin matu?ar tsana ya ce"akwai abin da za ka iya yi akai ne?ka fara zama mai ?ima a cikin masarautar nan tukuna, kafiri zindi?i kai har kana da zarrar da za ka gaya min wata magana na yarda?"

"Yarda ko rashin yarda wanna ra'ayinka ne

Amma shi Kazuzi baya maimaita magana,bana shakkar na kashe ka a bainar jama'ar ?asar Tayaar,bana shakkar a kashe ni,idan har kana son ka kuSuta daga u?ubar Kazuzi to ya kamata ka Wauke idanu daga kan yarinyar da bata ji ba bata gani ba

Idan kai namiji ne kamar yadda kake jin kanka fitowa za kayi ka gwabza da namiji kamar yadda kake jin kanka,amma idan ka laSe a bayan tsafi kana nufin cutar da mace hakan zai saka na zargi kai Win ba namiji bane,Wan daudu ne "Kazuzi yana kai wa nan a maganarshi ya mi?e ba tare da ya sake bi ta kanshi ba ya fice daga Wakin yana ?arasa Waure gashinshi da ya gama gyarawa

Bin shi ya yi da kallo cikin tsananin razani da mamakin wannan abu,bai taSa tsammanin akwai wani mahaluki da zai iya gano Wanyen aikinshi a cikin Tayaar ba, dole ya san yadda zai yi ya gama da Wannan hatsabibin mutumin, kafin ya cigaba da yun?urin kashe gimbiya Hayat, so yake Sarki Iyaad ya ji zafi kwatankwacin wanda ya ji a shekarun baya





=???

A tsawon rayuwar gimbiya Hayat bata taSa ganin mutumin da har zuciyarta ta yaba da tsananin jarumta da sadaukantakarshi ba irin ta sadauki Kazuzi, jikinta ya yi sanyi sosai,a ranta tana tunanin duk mutumin da zai ceci tsayuwarta irin haka bai dace ta yi masa kallon ma?iyi ba

Na farko ya cece ta daga damisa,na biyu kuma maciji,duk da irin wula?anci da cin mutuncin da ta yi masa hakan bai taSa sakawa ya kasa taimakonta ko girmama ta da bin umarnin ta ba

Tsawon kwanaki biyar da faruwar abin bata da sukuni sai tunanin wannan taimakon da Kazuzi ya yi mata,wata ?ima ta musamman take ganinsa da ita a yanzu

Yau tana zaune da amintacciyar baiwarta Huda,hira suke yi sosai, kafin ta bijiro masa tambaya

"Huda! menene ra'ayinki game da wannan sadaukin da ya ?i amsar Musulunci?"

Murmushi Huda ta yi, kafin ta ce"wai sadauki Kazuzi?

Jarumin jarumai kenan,ban taSa ganin jarumin namiji mai zuciyar maza da sadaukantaka irin nashi ba

Har yanzu ina iya tuna yadda ya yi dambe da damisa,kuma ya kashe ta,kwanakin baya kuma cikin wani irin zafin nama ya ?araso ya dam?i wuyan maciji,mu da muke bakin lambun ya riga mu shiga har ya kawo miki Wauki"

Hayat ta ce"duk na ji wannan, menene ra'ayinki game da halayensa?"

Kai tsaye Huda ta ce "mutumin kirki ne ya shugaba ta, yana da tausayi da sanin darajar Wan Adam,amma sam baya Waukar wula?anci,kuma hakan ya dace da duk wani Wan Adam mai daraja kanshi,ko da yake shi Kazuzi bawa ne"

Hayat ta girgiza kai ta ce"duk ba Wannan ba,kin san yadda yake faWar magana babu girmamawa,hakan ya dace yana a matsayin bawa?nagartaccen mutum zai iya haka kuwa?"

Girgiza kai Huda ta yi,ta ce"ya shugabata yana faWar gaskiya duk dacinta ni a gani na mai zai hana a duba maganarshi kafin a yanke masa hukunci?

Zuwa yanzu dai mun fara gane kyawawan halayensa "


(Ga masu son VIP group ga number ta nan a ?asa)


#Nusy_bee
08125952284


=????=?Q? MASARAUTAR KAIZUR =????=?Q?






'?Nusy bee
d'? Young talented writers association YOTA d'?

(Under YOTA'S AMAZING PENS)



Page 9




Wani murmushi ya kubcewa Hayat,ta ce"Huda kina yabonshi da yawa fa

Kar fa ki manta ba musulmi bane ballantana na ce za'a yi ?ar gida"

Huda ta ?yal?yale da dariya ta ce"ya shugaba ta ai ko da ace na so shi ya cancanci a so shi Win, kyakkyawa ne ajin ?arshe,sannan gwarzon jarumi ne,kuma shi namiji ba'a san shi da tsoro ba, sannan mafi girma kuma ya ceci ran shugaba ta har sau biyu,dole na girmama shi na mutunta shi"

Bata san menene dalilin ba,amma haka kawai ta ji gabanta ya faWi,kuma sam bata yi farin ciki da maganar Huda ba,amma sai ta dake tana ya?e,ta dubi Huda da take ta ?ara ta?ar?arewa tana faWar kyawawan halayen Kazuzi,ta ce"to yanzu ta ina kike ganin zan iya mayar da shi kamar ku?

Kar ki manta shine ya kashe min Wan'uwa,silar haka mahaifiya ta ma ta rasu,kuma babu alamar nadamar hakan a tattare da shi fa"

"Shine silar shahadar yarima,ya bar duniya mai cike da ruWani da ababen ?i ya shugaba ta,ya mutu akan hanyar daukaka kalmar Allah, wadda Allah ya sanar da mu a Alkur'ani cewa su rayyayu ne

Sarauniya kuma,ki gafarce ni ya shugaba ta, kowanne mai rai sai ya WanWani mutuwa,amma ta hanyoyi dabam-dabam,ko da ace Sadauki Kazuzi bai kashe Yarima ba, tunda kwanansu ya ?are za su koma ga mahaliccinsu

Maganar nadama kuma,ya shugaba ta ki gafarce ni,bai yi abin da zai yi nadama akai ba har yanzu,shi ba musulmi bane,da musulmai suka tunkare su da ya?i sai aka ba shi umarnin tunkararsu, kuma ko da ace musulmi ne don musulmi Wan'uwanshi ya ya?e shi babu laifi ya kare kanshi

Su ba su san kalmar Allah ba, ballantana su yi tunanin Waukaka ta,a duba magana ta ya shugaba,amma idan akwai wata matsala a magana ta a yi min aikin gafara "

Hayat da ta zuba mata idanu kawai tana kallonta ta ja ajiyar zuciya,sannan ta ce"na ji duka,kuma zan duba,amma har yanzu ina cike da jin haushin wula?ancin da ya yi min don yana kallo na ina wanka na yi masa magana

Ya ce wai ni ba mace ba ce, Malli ce kaWai mace a idanunshi "

Kallonta sosai Huda ta yi sannan ta ce"ya shugaba ta wannan ai ba abin damuwa bane,ba ya faWa bane don ya

5 / 11