MASARAUTAR KAIZUR COMPLETE BY NUSY BEE.doc

Author :  Nusy Bee Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 11

9K to 12K   out of 31.5K words

ana yinshi da dole har yanzu Kazuzi bai yi lalacewar da za'a saka shi yin abu da ?arfi ba

Amma ke menene shawararki?"

Kallonshi ta yi, cikin raunin murya ta ce "Abby ya nuna baya ra'ayi, meyasa ba za ku ?yale shi ba?"

Murmushi sarki Iyaad ya yi,sannan ya sake dubanta ya ce"kina da labarin Sarkin ya?i da ya rasu,wato Sadauki Ilyas?"

Take fuskarta ta washe da murmushi, idanunta akan shi ta ce"na sanshi, idan ban manta ba da ni da yaya na Yarima Nashwaar ya Wauke mu a matsayin jikokinsa,yana matu?ar kula da mu a wancan lokacin

Na sani shi ma mun rasa shi a wani ya?in da Tayaar ta gwabza da Baruda "ta ?arashe fuskarta tana nuna alhini

Sarki Iyaad ya ce"to shi wannan bawan Allan da kika sani mahaifina a ribar ya?i ya samo shi kamar yadda aka samo Kazuzi,babban maya?i ne,kuma fitaccen jarumi a daularsu kamar dai Kazuzi,amma da babana sarki Nufail ya yi duk mai yiyuwa sai gashi an samu abin da ba'a yi tunani ba,bayan kasancewarshi Musulmi mai ibada a kowanne lokaci ya kasance shine mai jagorantar ya?i,kin san menene ya janyo mana nasara a wancan lokacin?"ba tare da ta yi magana ta girgiza kai a hankali

Sarki Iyaad ya ce"to jimirin jira ne,don sai da Sarkin ya?i Ilyas ya shekara bakwai da mu yana bin addinin shi na bautar wuta,a wancan lokacin mahaifina ya fuskanci ?alubale da dama,ya jure maganganu daga wajen mutane,amma sai gashi rana tsaka burin shi ya cika,sadaukin ya karSi musulunci,har ma ya ja Sallah a masallaci,shin ni ba kya son na kafa wannan tarihin ne?"

Cikin sanyin jiki ta girgiza kai,sarki Iyaad ya ce"to ki Wauki Kazuzi a matsayin da kike Waukar kuyangin ki da dakarun da suke tsaron lafiyarki, yadda kika mayar da su aminanki,masoyanki,makusantanki haka nake so ki mayar da Kazuzi,in sha Allah lokaci yana zuwa da za mu samu nasarar canja masa ra'ayi kamar yadda muka chanjawa sadauki Ilyas"

Rissinawa ta yi tana faWin "fatan nasara mai Worewa Abby!"

Sarki Iyaad ya yi Wan murmushi yana faWin"fatan rayuwa mai albarka da ma'ana yata "daga nan ya juya da niyyar ficewa daga Wakin

Gimbiya Hayat ta bi shi da kallo,ta gamsu da maganarshi,amma tabbas sai ta hukunta Kazuzi ko yaya ne, musamman da ya janyo Abby Winta abin alfaharinta ya Waga hannu da niyyar marinta





*DAULAR KAIZUR*

"Ya shugaba ta!mai martaba ne ya ce a yi masa iso"

?aga kai gimbiya Amna ta yi tana kallon jakadiya da kanta yake a ?asa,ta ce"ki yi masa iso Nayyab"Nayyab ta sake rissinawa sannan ta mi?e ta fice daga turakar

Bayan ?an da?i?u sarki Mu'iz ya shigo da sallama, sarauniya Amna ta rissinar da kai ta amsa,ya ?araso ya zauna kusa da ita, cikin girmamawa ta ce"Barka da zuwa ya shugaba na"

"Barkanki da warhaka sarauniyar Kaizur!"

"Jakadiya ta ce ayi maka iso"

Sauke ajiyar zuciya mai nauyi ya yi cikin damuwa,ta Waga kai tana kallonshi,a hankali ya furta"na kasa jurewa ne,dole na taho mu yi magana"

"Kan batun yarima Sahal?"ta faWa a raunane tana kallonshi

Shiru ya yi kanshi a ?asa,ta yi Wan murmushi mai ciwo tana girgiza kai ta ce"tunda na ji a jikina a kwanannan,na yi mafarkai da yawa,ga yawan faWuwar gaba na san Wana ya faWa mugun hannu,zuwa yanzu na san na rasa Yarima na"zuwa lokacin sosai take kuka

Girgiza kai sarki Mu'iz ya yi da sauri,ya ce"wannan hasashe ne kawai sarauniya,ina cikin damuwa ne kawai saboda tsawon lokacin da muka Wauka muna neman shi amma har yanzu babu labari,na yi duk mai yiyuwa amma babu nasara

Yarima Sahal yana raye,shine kawai tabbacin da nake da shi,amma banda haka da tuni na ha?ura,komai na bawa mu?addari ne"

Sarauniya Amna ta jinjina kai ta ce"haka ne mai martaba

Amma idan da hali ina so mu gana da Munaya, wata?ila mu samu wani haske "

Sarki Mu'iz ya girgiza kai ya ce"babu Abin da ganawa da Munaya zata haifar sai damuwa,da alamu waWanda suka saka ta aikin sun shirya, shiyasa ita ma ta shirya,sam bata tsoron ko da mutuwa, shiyasa bana son abin da zai haWa ni da ita yanzu"

Girgiza kai sarauniya ta yi,ta ce"kar mu yi haka, abu ne na ribar mu,idan yarima Sahal ya salwanta mu ne muka shiga matsala,idan ya bayyana amfanin mu ne,mu je mu tattauna da ita,ina fatan zata yarda ta ba mu ?arin haske"

Girgiza kai sarki Mu'iz ya yi,ya ce"mu je,amma bana jin hakan gaskiya, amma ni na riga na yanke hukunci,ba zata ?ara shekara Waya a Waure ba,zata ba?unci inda su Umayr da Ya'a?ub suka je"bata yi magana ba sai jinjina kai,sarki Mu'iz ya mi?e tsaye, itama ta mi?e suka fice daga turakar





*DAULAR TAYAAR*

"Barka da warhaka ya shugaba ta"

Kallonshi ta yi sosai, kafin ta fara magana a dake"ribatattun ya?i da aka kamo daga Baruda,an raba musu wajen aiki ne?"

Dakare Amjad ya ce"tukunna dai ya shugaba ta,amma yau in sha Allah za'a raba musu"

Sauke ajiyar zuciya ta yi,kai tsaye ta ce"to wannan zindi?in badakaren,ina so a saka shi cikin jerin masu yi min hidima "

A firgice shugaban dakaru Amjad ya kalle ta,a Wan tsorace ya ce"ranki ya daWe babu kasada a cikin hakan?"

"Umarni na bayar,bana bu?atar a tambaye ni,saura kuma ka kai ni gaba,tashi ka fice,na sallame ka "babu musu shugaban dakaru ya rissina sannan ya mi?e ya fice daga lambun nata cikin zullumi da fargaba

Har yanzu sadauki Kazuzi abin tsoro ne, ba'a gama sanin wanene shi ba,ta yaya ita mace mai rauni ta ce wai a saka Kazuzi ya yi mata hidima?shi dai yana ganin da kuskure a hakan

Hakan ne ya saka ya yi fatali da umarninta,bai yi ?asa a gwiwa ba ya samu Sarkin ya?i da maganar

Murmushi sarkin ya?i ya yi,a ranshi yana fatan abin da yake gani ya tabbata, gimbiya Hayat ta sau?a?a musu hanyar jan ra'ayin Kazuzi,don haka ya ce"ka bi abin da ta ce, sauran kuma mu bar wa Allah, in sha Allahu babu wata matsala"dakare Amjad ya rissina sannan ya mi?e ya bar wajen

A ranar aka rabawa sababbin bayi wajen aikinsu,ciki har da Kazuzi,da aka tura shi tsaron lafiyar gimbiya Hayat

Ta ji daWi sosai da labari ya iske ta, tana zaune a ?awataccen lambunta,amintattun kuyanginta sun kewaye ta ta aika Waya daga cikin asalin dakarun da suke gadin lambunta cewa ya kira mata Kazuzi

Babu jumawa suka ?araso,a fizge ta kalle shi sannan ta mayar da kanta gefe ?irjinta yana bugawa,tsawon lokacin da ta Wauka tana yi masa tijara bata taSa ?are masa kallo ba sai yau

Cikakken namiji mai cikar zati,dogo ne sosai,mai ?irar jiki mai matu?ar kyau,duk da cewa sanye yake cikin kayan bayi amma sai taga sun yi masa kyau tamkar ba bawa ba,sosai ta ga ya yi mata kwarjini tamkar ba bawanta ba,dogon gashinsa da ya Waure a tsakiyar kanshi ya sake shi ya zuba gadon bayansa,iska sai kaWa shi take yi

A dalilin haka ta kasa yi masa rashin mutunci da Wiban albarka da ta shirya,yana zuwa gabanta bai yi wata-wata ba ya zube a ?asa, kanshi a ?asa ya ce "Barka da wannan lokaci ya shugaba ta!"

Shiru ta yi da farko tana bin shi da kallo, kafin ta yi juriya ta ce"ka iya ladabi kamar gaske,amma ka haWa ni faWa da mahaifi na!"

Bata yi tsammanin zai ba ta amsa ba,amma ta ji ya ce"ki gafarce ni ya shugaba ta"

Da mamaki take kallonshi kafin ta ce"na san zuwa yanzu ka yi nadamar abin da ka yiwa Wan'uwa na da mahaifiya ta ko?"

Ba tare da shakkar komai ba ya ce"Kazuzi baya aikin nadama ya shugaba ta"

Da mamaki take bin shi da kallo,su ma kuyangin nata kallonshi suke yi, kafin ta sake dakewa ta ce"anjuma za mu fita yawon sha?atawa zuwa dajin Lahur,sai ka kasance cikin shiri"

Ya sake rissinawa gami da amsawa da faWin "an gama ya shugaba ta"

Cikin ?osawa ta dube shi ta ce"na sallame ka, za ka iya tafiya"

Ya sake rissinawa ya ce"na barki lafiya ya shugaba ta"daga haka ya mi?e tsaye, cikin takunshi na dirarren namiji mai izza ya bar wajen

Da yamma ta shirya kamar yadda ta saba lokaci zuwa lokaci,ta yi ado mai kyau,suka shiga keken dokin da suke fita da shi ita da kuyanginta, Kazuzi da wasu dakaru su biyu suka bi bayansu a dawakai zuwa dajin Lahur

Hayat tana tsananin son ganin tana yawatawa yadda take so, amma mahaifinta sarki Iyaad bai cika son hakan ba, shiyasa yau da ya yarje mata take cike da farin ciki

Daga ita har kuyanginta da ta mayar da su tamkar ?an uwanta sai shawagi suke yi cikin kwanciyar hankali,sam ba su kula da wata damisa da take fakon gimbiya Hayat ba,sai gani aka yi ta daka tsalle cikin zafin nama ta yi kanta.....



(Damisa zata lamushe gimbiya >?y?>?z?)


Comments da likes suna qaranci sosai9&?ko na tafi Hutu ne =??




#Nusy_bee
08125952284

=?Q?=???? MASARAUTAR KAIZUR =????=?Q?


https://chat.whatsapp.com/Is0HqhjNITL3VZIagV42u7?mode=gi_t



'?Nusy bee
d'? Young talented writers association YOTA d'?

(Under YOTA'S AMAZING PENS)



Page 7




Wata firgitacciyar ?ara gimbiya Hayat ta yi a tsorace,kafin ta zame ta zube kasa sumammiya, tuni kuyanginta suka cika dajin da iface-iface, lokaci guda komai ya yi tsit tamkar babu wani mahaluki mai rai a cikin dajin

Ba komai bane ya faru face tsalle da Kazuzi ya yi, cikin wani irin tsananin zafin nama ya cafke damisar, ba tare da Sata lokaci ba ya yi jifa da ita

Mi?ewa damisar ya yi yana gurnani yana kallon Kazuzi, Kazuzi ma kallonshi yake yi fuskarsa babu yabo babu fallasa,damisar bai bi ta kan Kazuzi ba ya sake nufar inda Hayat take kwance,da wani irin ?arfi Kazuzi ya sake dam?arshi,ya ja shi da ?arfi, ba tare da Sata lokaci ba aka kaure da kokawa tsakanin Kazuzi da damisar, lokaci guda damisar ta farke Waurin da aka yiwa ciwon hannunshi na damtse,kuma a take jini ya Salle a hannun

Kallon hannun ya yi sannan ya sake kallon damisar,yana murmushi ya ce"yanzu hankalinka ya kwanta?

To ba abin da kake tunani bane,amma ina gargaWinka da babbar murya ka fita a harkarta,idan ba haka ba tabbas za kayi nadama"bai rufe bakinsa ba damisar ya sake nufar inda Hayat take kwance da tsananin zafin nama fiye da na baya,wannan karon Kazuzi bai yi wata wata ba,yana dam?ar wuyan damisar ya ma?ure ta, ba tare da bata lokaci ba ya murWe mata wuya,bai sake ta ba sai da ya tabbatar bata numfashi sannan ya yi jifa da ita

Sai a lokacin hankalin kuyangin da dakarun suka dawo jikunansu, ba tare da ya yiwa kowa magana ba ya wuce inda Hayat take kwance ko motsi bata yi, tamkar babu rai a jikinta,bai yi wata-wata ba ya dur?usa ya Waga ta ya saSa ta a kafaWa,kai tsaye ya mi?e ya nufi cikin masarauta,sauran jama'ar suka biyo bayansu cikin mamaki da Wimuwa,babu mai iya magana a cikinsu

Kai tsaye masarautar Tayaar suka koma,kafin su isa labari ya iske mutanen fada cewa damisa ta farmaki gimbiyar Tayaar,don haka kai tsaye sarkin dakaru Amjad ya yi musu umarnin su wuce zuwa fada inda sarki yake jiransu, ba tare da Sata lokaci ba suka nufi can

Gaba Waya ilahirin fadar kowa yana tsaye a matu?ar razane suna jiran isowarsu,fuskar sarki Iyaad Wauke da matsanancin tashin hankali da ruWani,kan Kazuzi a ?asa,yana zuwa ya kwantar da ita a gaban sarki, kanshi a ?asa ya ce"ta samu firgici ne shine ta suma,amma babu abin da ya same ta,a gafarce mu idan mun gaza a aikinmu ya shugaba na"yana kai wa nan ya mi?e a hankali ya fice daga fadar






*DAULAR KAIZUR*


"Amincin Allah ya tabbata a gare ki yake wannan baiwa mai tarin ji da kai"

?aga kai ta yi a nutse tana Wan murmushi,a hankali ta furta "amincin Allah ya tabbata a gare ku ruhin ?asar kaizur"

?an murmushi sarauniya Amna ta yi,sannan ta zauna kusa da Munaya tana kallonta,sarki Mu'iz kuwa bai ce kanzil ba,ya zauna a inda ya saba zama yana kallonsu

"Munaya!

Tsawon shekaru ashirin kenan kina karSar hukunci iri-iri, kina fuskantar ?as?anci da wula?anci, menene dalilin hakan?

Sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?boda Satan abin da tun farko kin san ba naki bane, menene dalilin da ya sa ba za ki bayyana shi ba? ke a daina azabtar da jikinki?mu ma zuciyoyinmu su huta da azabtuwa?"

Kan Munaya a ?asa, cikin rissinawa ta ce "gaisuwa gare ku ya shugabanni na,kuma ruhin gari mai albarka kaizur

Munaya baiwa ce mai amana,bata taSa cin amanar wani ba,ko da ace Sarkin kaizur ne

Munaya bata salwantar ba,bata da riba a hakan"

"Na sani,amma menene dalilin da ya sa kika amsa ke kika fitar da shi daga Wakinshi?"

"Saboda ni na aikata hakan ranki ya daWe!"

Shiru sarauniya Amna ta yi na Wan lokaci kafin ta ce"to menene dalilin da ya sa kika aikata hakan?"

"Saboda soyayya ranki ya daWe "

Sarauniya Amna ta ce"ba dai soyayya ba,an saka ki ne"

Shiru Munaya ta yi na Wan lokaci, kafin ta ce"ba saka ni aka yi ba, amfani aka yi da ni,na gane hakan"

Zaro idanu sarauniya Munaya ta yi cikin firgici ta ce"amfani da ke?

Wanene ya yi amfani da ke?"

Ba tare da bata lokaci ba ta ce"ina son a ba mu waje ranki ya daWe!"

Wani mugun kallo sarauniya ta yi mata ta ce"a cikinmu wa zai ba ki wajen?ni ko Mai martaba?"

Kan Munaya a ?asa ta ce"mai martaba ranki ya daWe,tunda maganar tamu ce ta mata"

A wani irin fusace sarauniya ta saukewa Munaya mari,sannan ta hau faWa tana faWin"kina matsayin baiwa ?as?antacciya wadda take ?ar?ashin hukunci ko a gaban dubban mutane ba sai an ba ki izini za kiyi magana ba?har kike cewa wai mai martaba ya ba ki waje?"

Mi?ewa mai martaba ya yi,ya dubi sarauniya ya ce"ku yi magana,dama nima na gaji da jin maganganun tsinanniya irin ta,na gaji da ganin fuskar da ta fi komai muni a idanu na"yana kai wa nan a maganarshi ya juya ya fice daga Wakin ba tare da ya sake kallon sashen da suke ba

Yana fita sarauniya Amna ta watsowa Munaya wani mugun kallo, Munaya ta yi Wan murmushi, sarauniya ta ce

"Ya tafi,me kike so ki ce?

Kar dai ki manta ko me kika faWa zai koma kunnenshi"

Munaya ta jinjina kai ta ce"haka ne!

Dama game da Satan Wanki yarima Sahal ne"ta Waga kai tana kallon sarauniya da ta ?agu ta ba ta amsa, kafin ta cigaba da magana sarauniya ta ce"me kika sani game da Satan nashi?"

Munaya ta sake duban sarauniya ta ce"Kamar yadda na gaya miki a baya cewa amfani aka yi da ni to haka ne, Urwa da Umayr da aka kashe akan wannan rigimar duka basu da laifi, ballantana Ya'a?ub da babu abin da ya sani a kai

Wasu manya ne a cikin masarautar nan suka sa aka sace Yarima Sahal,ban san niyyar su ta yin hakan ba,amma na fi tunanin saboda mulki ne"ta ?arashe magana idanunta ?yar akan sarauniya Amna

A wani irin gigice sarauniya Amna ta ri?e hannayen Munaya da suke Waure a cikin sar?a,muryarta tana rawa ta ce"manya a cikin masarautar nan?

Su wanene haka?kuma menene dalilin su na yin hakan?"

Munaya ta ce"Nima ban sani ba ranki ya daWe,amma Kamar yadda na faWa da farko wata?ila shirinsu ne akan kujerar kaizur"

Shiru sarauniya Amna ta yi tana kallon Munaya cikin tsananin tashin hankali da Wimuwa, kafin ta ce"wanene a cikin MASARAUTAR KAIZUR da yake jin zai iya samun mulki muddin ya ga bayan Wana Sahal?"

Shiru suka yi su duka biyun, kafin Amna ta ce"Yarima Zaffar ko Yarima Jamal?

Su kaWai ne masu gadon sarautar wannan birni idan babu sarki Mu'iz

Amma ta yaya za su iya cin amanar sarki? musamman ma Yarima Zaffar,ke ma kin san ?arya kike yi,hakan ba abu ne mai yiwuwa ba"

Munaya ta rissina ta ce"nima na san da hakan ya shugaba ta,ban tabbatar da su wanene ba,amma tabbas manya ne a masarautar nan,kuma su ma za su iya gadon masarautar "

Shiru sarauniya Amna ta yi tana jin tana sake shiga ruWani,a hankali ta ce"tabbas zan yi bincike,zan saka mai martaba ya yi bincike akan duk wani mahaluki da yake da alhakin gadon MASARAUTAR KAIZUR, muddin na samu mutum da hannun shi a ciki tabbas zan Wauki mataki mafi muni,ke kuma ki jirayi dawowa ta"tana kai wa nan ta mi?e da sassarfa ta fice daga Wakin, Munaya ta bi ta da kallo tana murmushi wanda ita kaWai ta san ma'anarshi





*DAULAR TAYAAR*


Yau kwana biyu kenan da faruwar tsautsayi ga gimbiyar Tayaar, wato Hayat, an samu ta farfaWo,kuma zuwa yanzu zabure-zaburen da take yi ma ta daina

Sai dai tun da aka gaya mata Kazuzi ne ya Wauko ta tun daga dajin Lahur zuwa gida take jin haushin shi sosai, kwata-kwata bata yaba masa ba na cetar rayuwarta da ya yi, don haka ma ta ?udurce a ranta sai ta yi masa gargaWi mai ?arfi

Kazuzi yana zaune a lambun gimbiya bayan ya kammala aikin da badakare Amjad ya saka shi na gyaran lambun, cikin nutsuwarshi yake ?arewa ko'ina na lambun kallo,a hankali wani abu da ya shuWe ya gifta a idanunshi



('

"Sadaukin sadaukai!tsoro mai ban tsoro!wanda mutuwa take tsoro,takawarka lafiya abin alfaharin Baruda,kai ne sarki ko da ba'a yarda ba"

?aga kai ya yi yana kallonta, murmushi take yi tana wasa da gashin kanta,ya gyara zama yana kallonta,ta ?araso ta zauna a kusa da shi tana kallonshi tana murmushi,ya ce"kin fi taurari haske a cikin Baruda,ina ro?on abin bauta mafi haske ya rufe idanun wasu mazan daga ganin wannan haske,sai ni kaWai,kar wani ya yi min shigar sauri"

Dariya ta yi da sautin muryarta mai daWi,ta kalle shi tana murmushi ta ce"a tunaninka a kaf ?asar Baruda birni da ?auye akwai wanda ya isa ya mallaki Malli?

Ai ko da ace mutuwa ce ta raba mu kowa ya san Malli matar Kazuzi ce abadan,babu wanda ya isa ya mallaki wannan Malli Win sai sadauki Kazuzi "

Janyo ta ya yi jikinshi yana murmushi sosai,ya ce"na san da haka nima

Ke ce ?warin gwiwa ta a cikin daular Baruda,duk wani farin ciki da walwala ke ce sila

Muddin akwai Malli a gefena bana damuwa, komai na duniya ba komai bane akan Malli

Ki zama ba kya kusa da ni bani da maraba da bawa"

Igiyar tunanin shi ta yanke a daidai nan saboda ruwan da ya ji an watsa masa,ya Wago da sauri yana kallon Hayat da take kallon shi ranta a tsananin Sace,cikin hargowa ta fara faWin

"ShaiWancin da ka saba a cikin garin naku za kayi min?"

Kallonta kawai yake yi ba tare da ya yi magana ba,ta ?ara fusata

4 / 11