MASARAUTAR KAIZUR COMPLETE BY NUSY BEE.doc

Author :  Nusy Bee Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 11

3K to 6K   out of 31.5K words

sake la?ana masa kalmar shahada,idan bai karSa ba kawai a kashe shi kamar yadda aka yi wa sauran yan'uwan shi"

Sarki Iyaad ya dubi sauran fadawan ya ce"to kun ji,ki me kuke gani?"Sarkin ya?i ya girgiza kai ya ce"wannan ba mafita ba ce ya shugaba na

Abu ne sananne a wajenmu cewa Kazuzi ba zai amshi addini a haka ba,kuma muna bu?atar mutane irin Kazuzi a wannan garin,ni da nake cewa mai zai hana mu ja shi a jiki,mu fahimtar da shi musulunci, idan ya so ba ma sai an yi masa dole ba zai shiga da kanshi?"

Sarki ya jinjina kai ya sake mayar da dubanshi ga waziri, kafin ya kai ga magana sarkin fada ya Waga hannu,sarki Iyaad ya ba shi damar magana,Sarkin fada ya gyara zama yana duban Sarki Iyaad, cikin girmamawa ya ce"ya shugaba na,da alamu su Sarkin ya?i sun manta wanene Kazuzi!

Sanannen abu ne tabbas ba zai karSi musulunci ba ko me za'a yi masa,amma kuma ina ganin da kuskure a jan shi a jiki da za'a yi, saboda mu shaida ne,babu abin da jinin Baruda suka tsana kamar musulunci,duk wani wanda ya sha ruwan daular Baruda zai tashi da tsanar Musulmai da burin son ganin bayanmu,mai zai hana a yanke masa hukuncin shi kawai,kar ya yi amfani da yardar da muka yi masa ya cutar da mu?"

Girgiza kai sarkin ya?i ya yi, cikin girmamawa ya ce"ya shugaba na,a dai duba magana ta,ban hana a sakawa kazuzi idanu ba,amma ya kamata a ba shi wata dama, tunda har muka iya kamo shi,abin da babu wata daula da ta taSa samun wannan kwatankwacin nasarar,idan har ya gwada wata halayya muka ji ba mu yarda ba za mu Wauki mataki akanshi kawai,amma a matsayin mu na musulmai,sannan manyan babbar masarauta bai kamata a ce mun razana saboda wani bawa da Allah ya ba mu nasara akan shi ba,amma ya kuka ce?"

Shiru fadar ta Wauka,kowa yana nazari,zuwa can waziri ya katse shirun da cewa"to shikenan,a gwada shawarar taku,amma ni ina ganin a saka masa idanu sosai,sannan kuma a tsare shi,a yi duk mai yiwuwa don ganin an karya ?arfinshi,yadda ba zai iya wani tasiri ba"

Sarki Iyaad ya ce"shiyasa muka bayar da umarnin a killace shi, kafin nan sai da muka tabbatar mun raba shi da duk kayan tsafi da surkullenshi"

Waziri ya sake rissinawa ya ce"ya shugaba na,an Wauki matakin da ya dace, ragowar kuma sai mu bar wa Allah "

Sarki Iyaad ya ce"hakan ya yi,muna fatan yadda Allah ya ba mu ikon yin wannan jihadin muka yi nasara akan waWannan azzalumai, Allah ya ba mu iko da nasara akan wannan babban shaiWanin"

Fadawa suka amsa da "Ameen!"daga nan sarki ya rufe taro da addu'a,faWa ta watse




=???('

A hankali toron giwar yake zaunawa akan ?afafunshi bisa umarnin dakarun da suke umartarshi,shugabansu ya kama ?atuwar sar?ar da aka Waure kejin ya fara ?o?arin kwancewa cikin dakiya,sauran dakarun suka fara ?o?arin taya shi

Bayan gama warware ?atuwar sar?ar tsayawa suka yi cirko-cirko suna kallon juna a Wan firgice,duk jarumta da taurin zuciyar badakare ya san wanene Kazuzi, yanzu haka ma kallonshi suke yi, wanda shi duk abin da ake yi ko Wago kai bai yi ba ballantana ya kalli wani,har yanzu kanshi a ?asa yake,tunda aka shigo da shi cikin birnin Tayaar har yanzu babu wanda ya ga fuskarshi ballantana ya shaida a wanne hali yake ciki

Wani badakare ne ya yi ?arfin halin fara ?o?arin saukar da kejin,sauran dakarun ma suka saka masa hannu,suna saukewa kuma shugaban nasu ya yi ?arfin halin buWe kejin

Yana buWewa suka ja baya a Wan tsorace,kafin Waya daga cikinsu ya yi ?arfin halin matsowa yana kallon Kazuzi,da sai yanzu suka kula ashe duk abin da yake faruwa ma idanunshi a lumshe yake,babban dakaren ya saka hannu da nufin fito da shi, sauran dakarun ma suka saka hannu don fito da Kazuzi,amma duk ?o?arin su tamkar suna yun?urin matsar da ?aton dutse,ko motsi baya yi

Shiru suka yi,suka tsaya cirko-cirko suna kallon juna,kafin babban badakaren ya yi ta maza ya dubi Kazuzi ya ce

"Sadauki Kazuzi!

Kafin yau kai Win jarumi ne, mai gata da dama,mai sharafinshi a wannan nahiya,wanda ya gagari kowa,amma a yau kai ba komai bane face bawa,don haka sarki Iyaad yana umartarka da ka fito daga kejin nan don a kai ka inda aka warewa bayi irinka"

Maganar babban badakaren ta razana ?ananan,don da alamu sun manta wanene Kazuzi,sai dai abin da ya yi tsananin ba su mamaki bai wuce ganin Kazuzi ya yun?ura ba,cikin Wan ?an?anin lokaci ya fito daga cikin kejin ya tsaya a gabansu,kuma har zuwa lokacin idanunshi a rufe suke

Da farko bin shi suka yi da kallo cikin tsananin mamaki da kaWuwa,amma daga baya babban badakaren ya dake ya kama shi,kai tsaye suka wuce Wakin da aka tanada don Kazuzi

Ba su kwance masa ko sar?a Waya ba,daga ta hannu har zuwa ta ?afa,suka tura shi zuwa Wakin mai tsananin duhu,suka mayar da ?ofar da ta kasance ta wani nau'in ?arfe mai nauyi suka rufe ta ruf

Kai tsaye wajen Sarkin ya?i suka nufa, cikin girmamawa suka sanar da shi cewa sun kai Kazuzi zuwa Wakin da aka tanada don shi,sarkin ya?i Ra'uf ya kalle su yana murmushi ya ce"sannunku da ?o?ari,yanzu sai a kai masa abinci"suka rissina, babban badakare ya ce"an gama ya shugaba na"






DAULAR KAIZUR

A hankali yake tafiya yana bin doguwar hanyar, dakaru uku da ke tsaron lafiyarshi suna take masa baya,yana zuwa daidai inda suke tsayawa suka tsaya ba tare da an umarce su ba, gami da juya baya,sarki Mu'iz ya cigaba da tafiya zuwa cikin duhuwar bayan ya Wauki karan a ci bal-bal guda Waya da suke bakin ?ofar

?ar doguwar tafiya ya yi a cikin kogon kafin ya ?arasa inda yake muradin zuwa, murmushi ya yi yana kallon dattijuwar matar da take dur?ushe a kan gwiwowinta, Waure take da sar?a mai matu?ar nauyi,tana sauke numfashi a wahale,kayan jikinta zuwa gashin kanta a hargitse

"MUNAYA!"ya ambata cikin wani irin amo mara daWin ji, Wagowa matar ta yi da kanta, cikin ?arfin hali ta furta "Barka da zuwa ya shugaba na!"

Bai amsa ba,sai zama da ya yi a wajen da ya saba zama yana kallonta cike da tsana,bata damu ba,ta saba ganin irin wannan kallon daga wajenshi,har zuwa mutanen garin da suke kallonta a duk lokacin da aka fitar da ita daga inda take a kulle

"Munaya!

Tsawon shekaru ashirin kenan kina azabtar da zuciyarmu,akan abin da kika sani ba naki bane tun kafin wanzuwar shi a duniya, menene dalilin da ya sa ba za ki daina azabtar da zuciyoyinmu haka ba? menene dalilin da ya sa ba za ki huta ba mu ma mu huta?

Ki yiwa kanki adalci ki yi mana,ki bayyana inda kika kai ajiyar nan,daga nan za mu sallame ki kema ki huta"

A hankali Munaya ta Wago kanta tana sauke numfashi, ba tare da ta kalle shi ba, cikin sanyin murya ta furta "a yi min afuwa ya shugaba na!

Amma abin da na saba faWa dai shi zan maimaita,bani da masaniyar inda yake"

Shiru sarki Mu'iz ya yi yana kallonta zuciyarshi tana tafasa,da sauti irin na fushi ya ce"amma kin yarda da cewa da saka hannunki a Satan kadara mafi daraja a kaizur?"

Kai tsaye ta amsa da faWin"tabbas haka ne ranka ya daWe,ni na fito da shi,amma daga nan ban san komai ba,kuma ba zan iya komai don dawowarshi ba"






#Nusy_bee
08125952284


=?Q?=???? MASARAUTAR KAIZUR =????=?Q?


https://chat.whatsapp.com/Is0HqhjNITL3VZIagV42u7?mode=gi_t


'?Nusy bee
d'? Young talented writers association YOTA d'?



(Under YOTA'S AMAZING PENS)




Page 3



Sarki Mu'iz ya daka mata tsawa da cewa"ba ki da bakin yi min wani jawabi Munaya!

Ke kika Satar min da Wa,ki yarda da hakan,amma ba ki da wasu kalamai da za ki kare kanki daga hakan,za ki cigaba da karSar hukunci har zuwa lokacin da za ki bayyana Wana,ko kuma ki bar duniyar,ke azzaluma ce tabbas,amma zaluncin zai rufto miki"ya mi?e a fusace ya fice daga wajen, Munaya ta bi shi da kallo ba tare da ta iya cewa komai ba

Masu tsaron lafiyarshi ba su yi mamakin ganinshi a haka ba saboda kusan duk lokacin da ya ziyarci Munaya hakan ce take kasancewa,suka rufa masa baya don komawa fada,kamar yadda suka saba har suka fice daga wajen babu wanda ya iya magana





*MASARAUTAR TAYAAR*


Da tsananin farin ciki take shiryawa,kuyanginta suna taya ta,a yau tana cike da tsananin farin ciki irin wanda bata taSa tsintar kanta a ciki ba,ba komai bane ya faranta mata sai kame azzalumi Kazuzi da aka yi,wanda a yau ya dawo bawa a masarautarsu

Zata iya cewa a duniya babu wata halitta da ta tsana,tsana mai muni irin Kazuzi,shine ya kashe Wan'uwanta Waya tilo da take tsananin so fiye da rayuwarta,wanda a dalilin rasuwar shi ne zuciyar mahaifiyarsu ta buga itama ta bar duniya,yanzu daga ita sai mahaifinta suka rage a raye,a dalilin Kazuzi Sarautar da suka gada zata bar gidansu suna ji suna gani

"Ya shugaba ta ga abin kama gashin"a cewar wata kuyangar ta,bata yi magana ba sai murmushin da ta yi,ta sanya hannu ta karSa,ta kama gashin,sannan ta mi?e ta shiga gaba,su kuma suka biyo ta a baya,suka fice daga sashen nata

Sai da suka hau ?awataccen keken doki wanda ya kai su har bakin Wakin da aka ajiye Kazuzi,babban Waki ne wanda aka gina shi da zallar dutse da jan ?arfe, Waki ne wanda ake kai duk wani ta?adarin gagararre a cikin Tayaar

Dakarun da suke gadin ?ofar suka bi su da kallon mamaki,saukowa ta yi daga keken dokin,kai tsaye ta tunkari ?ofar ba tare da ta yi magana ba,babban badakaren ya ?araso gabanta ya rissina yana faWin "Barka da wannan lokaci ya shugaba ta"

Kallonshi ta yi fuska a tamke,kafin ta yi magana cikin izza

"Ina so na yi magana da dakaren da aka kamo a ya?in Baruda"

Muryarshi har rawa take yi wajen furta "ranki ya daWe su hamsin da uku ne ai,kuma....."

"Ina nufin Kazuzi,babban badakare a Baruda"

Cirko-cirko dakarun suka yi suna kallonta a matu?ar tsorace,ganin haka ta fusata ta ce"ko ba zan samu damar bane?

Ban isa a buWe min shi ba?"

Murya na rawa badakaren ya ce cikin girmamawa "ranki ya daWe akwai haWari a cikin hakan ne,ki yi min aikin gafara shugaba ta"

Kai tsaye ta ce"ina son a buWe min shi idan har ina da ikon faWa a ji a cikin birnin Tayaar"

Ba tare da ya sake magana ba,ya mi?e cikin rawar jiki, suma sauran dakarun suka mi?e,aka buWe mata ?ofar, ba tare da ta sake kallon ko da sashen da suke ba ta sanya kai a cikin tangamemen Wakin, kuyanginta suka rufa mata baya,suma dakarun huWu daga cikinsu suka rufa mata baya,ya rage saura biyu a cikin guda shidan da suke gadinta

A can ?urya suka hango Kazuzi a zaune,tun daga yadda aka shigar da shi cikin wajen har zuwa yanzu yana nan a zaune kanshi a ?asa, idanunshi a rufe, abinci da ruwan da aka kai masa ma ko bi ta kansu bai yi ba

Har yanzu damtsenshi,inda marigayi sadauki Waleed ya sare shi yana Wan zubar da jini,duk da cewar an saka masa magani a raunin

Daga baya kuyangin da dakarun suka tsaya,ita kuma ta ?arasa gabanshi tana jefa masa wani kallon tsana,kafin ta bushe da wata iriyar dariya,tana dariyar ta ?arasa gabanshi, ta sanya hannu ta Wago fuskarshi,ta sanya hannu ta yaye gashinshi fuskarshi ta bayyana

Ya subhanallahi!samun kyakkyawan namiji kamar kazuzi abu ne mai wahala,komai na fuskarshi mai kyau ne da tsaruwa,tamkar wanda ya shiga gasar zana kanshi, gashinshi da ya sauka har gadon baya ya sake ?awata kyau da sura da Allah ya ba shi,gashi namiji ne mai cikar zati da mazantaka,muradin ?an mata a wancan lokacin

"KAZUZI!haka sunan yake ko?

Barka da zuwa daular Tayaar,a wasu shekaru baya sunan Kazuzi kaWai idan maya?a suka ji yana kaWa musu hanjin cikinsu, ballantana karo da shi a filin ya?i,sau da dama maya?a suna yi maka la?abi da ka fi dodo illa, saboda yadda kake ragargazar maza kana gamawa da su

A haka karambaninka ya kai ka ka kashe min Wan'uwa na Waya tilo da mahaifiyata ta haifa,wanda sanadin hakan ya sa ba?in ciki ya yi silar barinta duniya

A ta?aice dai,ina yi maka kallon makashin mutum biyu, Yarima Nashwaar,wato yayana,da sarauniya Shahida, wato mahaifiyata

Ba sai na cika ka da surutu ba, yadda ka zo masarautar nan a matsayin bawa,na yi maka al?awarin sai ka amsa hakan,sai na tabbatar maka da lokacin wannan ba lokacin da kake tashe bane,ka san shi tashe lokaci gare shi,kamar yadda naka ya zo kuma ya shuWe

Sai na tabbatar da ka yi rayuwar ?as?anci a cikin masarautar nan,sai na tabbatar da dabba ma ta fi ka ?anci da gata a cikin Tayaar

Da gimbiyar Tayaar wato HAYAAT kake magana!!!"tana kai wa nan ta saki fuskar tashi ta mi?e cikin takunta na isa da izza ta fice daga Wakin ranta fes, kuyanginta dakarun suka rufa mata baya

Har suka ?arasa ficewa daga Wakin kan Kazuzi yana ?asa kamar yadda suka zo suka same shi,a karo na farko,tunda ya rasa muradin ranshi ya ji ya kamata ya buWe idanunshi don sake ganin wannan duniyar da ta yi masa yankan baya a lokacin da bai yi zato ba

Shi dai jarumi,maya?i,kuma sadauki KAZUZI IBN MURAAD shine wai aka kawo shi a Waure a sar?a a matsayin bawa,bawan ma na wani birni da ya raina,ya raina jarumansa,duk menene sila?MALLI!

tuna sunan kawai sai da ya ji zuciyarshi ta girgiza,a hankali ya mayar da kanshi ya jinginar yana sauke numfashi da sauri da sauri, menene amfanin rayuwarshi da babu Malli a ciki? meyasa aka kashe masa Malli a gaban idanunshi?shin ta cancanci irin wannan kisan? Wanene silar mutuwar tata?shine

To indai haka ne bai ga amfanin rayuwarshi a matsayin wani mai galihu ba muddin babu Malli a duniya,ya gwammace ya mutu a matsayin ?as?antaccen bawa da ya rayu cikin farin ciki amma babu Malli a gefenshi,zai yi fatan waWannan mutanen su yanke masa hukuncin kisa mafi wuya,ko zai rage masa ciwo da raWaWin wannan gangancin da ya yi har ya rasa abun da ruhin shi yake marari a kowanne lokaci na rayuwarsa

Malli ita ce farin cikinshi, walwalar shi, ma'anar rayuwarshi,fitilar rayuwar shi,kuma mahaWin rayuwarshi,ji yake yi a rayuwarshi zai iya bayar da fansar ranshi akan Malli Winshi ta ji rauni duk kan?antarshi

A yanzu jin shi yake yi a duk duniya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? babu wanda ya kai shi ba?in ciki,babu wanda ya kai shi shiga tashin hankali,babu wanda ya kai shi asara a rayuwarshi

"Ruhi na!ruhi na kana ji?

Yaushe za mu je ka kamo min irin wannan barewar da ka taSa kama min kwanakin baya?ina son namanta,yana yi min daWi sosai, musamman ma idan kai ne ka gasa min da hannunka,sai na ji wani WanWano na musamman ya ?aru"

A hankali ya mayar da kanshi ya jinginar yana sake lumshe idanunshi, ire-iren shiriritar Malli kenan a duk lokacin da suke cikin nishaWi

"Ruhi na!

Menene dalilin da ya sa ba ka bar babana ya jagoranci tawagar ya?i ba?

Ba shine Sarkin ya?i ba?ko so kake yi wani abu ya samar min kai?"

Murmushi Kazuzi ya yi ya dube ta ya ce"au haka ne?

Wato shi matarshi bata san soyayya ba da zata bar shi ya fara afkawa ba ni ba?"

?an murmushi ta yi tana yatsina fuska,ta zauna a kusa da shi ta ce"ka ga Ni da kai mun kusa aure,ba zai kyautu a ce angon wani abu ya same shi ba,don dai na san ka fi ?arfin wata runduna wadda ta wanzu a duniya ma, ballantana a wannan nahiyar tamu"

?an murmushi ya yi ya dafa kafaWarta,ya ce"hakanan Sarkin ya?i shima,ya girmi dukkan wata runduna,kar ki manta rundunar Baruda shine ya ba mu horo,har zuwa yanzu an rasa wanda zai iya tunkarar mu ya farmake mu,kai ko da ya iya hakan ma ba zai sha ba"?ar dariya Malli ta yi ta kwanto da kanta gefen kafaWarshi,ta lumshe idanunta tana murmushi ta ce"Duniya ta,kaine komai na,kaine dukkan buri na da cikar burina,ina matu?ar alfahari da kai"Kazuzi ya yi murmushi ya ce"nima ke ce farin ciki na,abin alfahari na, duniya ta,dukkan wani buri na,hasken rayuwa ta,ke ce komai na,sannan alfahari na"?ar dariya ta yi ya mi?e tsaye tana karkaWe ?asar da ta taSa mata tufafinta,ya yi Wan murmushi yana taya ta kaWewa,ta kama hannunshi,ya mi?e suka wuce cikin gari

Doguwar ajiyar zuciya ya yi saboda tunawa da ya yi wadda yake yin wannan tunanin da ita yana murmushi babu ita a duniyar,a karo na farko tun bayan da ya rasa ta ya iya buWe baki ya yi magana

"Abin bauta!!!

Wanne laifi na yi da girma?me na aikata ka raba ni da rabin rayuwa ta? meyasa?shin na cancanci hakan ne? menene dalilin hakan?

Na zaSi zama a matsayin bawa ?as?antacce,ko nima a raba ni da numfashi na kamar yadda ka bari aka raba ni da ?awar zuciya ta"ya ?arashe maganar cikin wani irin rauni da bai taSa jin shi ba a tsawon rayuwarsa





=???

"Barka da shigowa ya shugabana!"da kai ya amsawa kuyangar sannan ya ba su iznin ficewa daga sashen da hannunshi,babu musu suka du?a da girmamawa sannan suka fice daga sashen,ya mayar da kallonshi ga Hayat da ke zaune a bakin gadonta tana bin shi da kallon mamaki ganin yadda ranshi ya yi matu?ar Saci

"Barka da shigowa abbana!"ta faWa tana rissinawa

"Me ya kai ki Wakin hukunci Hayat?"

A hankali ta Wago kai tana kallonshi,zata iya cewa rabon da ta ganshi a cikin Irin wannan Sacin ran ta manta, cikin sanyin murya ta sake rissinawa,ta ce"a yi min afuwa ya shugaba na,na yi wani al?awari ne,shine na je na cika"

"Amma kin san cewa Kazuzi ya fi haWari haWari?kin san cewa Kazuzi ya fi shaiWan?ya fi sharrin maya?an abokan hamayya dubu?

Kin san wanene Kazuzi da kika tunkari inda yake ke kaWai ba tare da tsoro ba?

Yanzu da ace wani abu ya same ki fa?ko kin yi tunanin ya rissina ne saboda an kamo shi an kawo shi nan a matsayin bawa kawai?"

Hayat ya sauke numfashi, cikin girmamawa ta ce"ina neman afuwa abbana!

Amma tabbas na daukar wa kaina al?awarin sai na ga ya dur?usa a gaba na,sai na bautar da shi na wula?anta rayuwarsa saboda a dalilin shi na rasa duniya ta, Wan'uwa na magajin Sarautar Tayaar da mahaifiya ta, kana ganin na bar shi ya tafi a banza kenan?

Abby idan na yi haka bana jin na kyautawa Wan'uwa na"ta ?arashe hawaye suna zubo mata

2 / 11