MASARAUTAR KAIZUR COMPLETE BY NUSY BEE.doc

Author :  Nusy Bee Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 11

15K to 18K   out of 31.5K words

wula?anta ki,da alamu ya faWa soyayya ne mai wuyar sha'ani,a duk lokacin da mutum ya faWa soyayya da wani ko wata,ba sa ganin kowa a rayuwa sai waWannan masoyan nasu,komai da kowa ba sa wani burge su,duk kyau da ?awatuwar su kuwa

Yanzu da ace za ki ga yarinyar da yake so Win ke gani za kiyi bata dace ba ma, saboda bata kai a kira ta mace ba ma,amma ita soyayya ba haka take ba,bata duba komai, sai wanda ake so Win"

Hayat ta jinjina kai ta ce"soyayya!to Allah ya sa mu dace,amma menene a soyayya ne da yake rufewa mutane idanu? menene abin burgewa a cikinta?"

Huda ta yi ?ar dariya ta ce"ya shugaba ta ai soyayya ta yi, ita ce mahaWin rayuwa,sam ba za ki gane me nake nufi ba har sai kin faWa soyayya "

?ar dariya Hayat tayi ta ce"to malamar soyayya,bar ni haka da wannan surutun naki, lokacin shiga ta cikin gida ya yi "ta mi?e tsaye,Huda ta rissina ta kwashe mata kilishin da suka shimfiWa mata,suka nufi cikin gidan





*DAULAR KAIZUR*


"A ina aka tsaya? Har yanzu ban ji amsa daga gare ka ba kamar yadda ka ce za kaje wajen boka lamzur,har yanzu ban ji bayani ba"

?aga kai ya yi daga inda yake zaune yana kallon uwar sharri da ke tsaye akanshi tana jiran amsarshi ,a hankali ya girgiza kai,ya ce"ban samu yadda nake so daga gare shi ba,asalima ya yi fushi da mu,ya ce kar na sake komawa sai nan da wata shida"

Shiru uwar sharri ta yi na Wan lokaci kafin ta samu waje ta zauna,a hankali ta ce"to yanzu ya za'a yi kenan?

Ka ga abubuwa ba sa tafiya yadda ake so"

Uban shaiWanu ya girgiza kai ya ce"kar mu yi gaggawa,muka yi jimirin shekaru ashirin ma,don dai wata shida sai ya gagara?aiki Waya ya rage,wanda daga shi ne ni da ke mun samu burinmu da biyan bu?atarmu"

Jinjina kai uwar sharri ta yi,sannan ta ce"Allah ya nuna mana, lokaci ya yi da za mu cimma burinmu,mu canja tsarin wannan zalunci irin na wannan mutumin"uban shaiWanu ya jinjina kai, kafin ya yi magana uwar sharri ta sake faWin "amma da sharaWi,kar ka yi tunanin za ka ci amanar uwar sharri, don tabbas za ka haWu da sharrin da ya girmi tunaninka "

?aga kai ya yi yana kallonta da mamaki ya ce"me ya kawo wannan maganar ne kuma uwar sharri?"

Murmushi kawai ta yi, sannan ta gyara rufin fuskarta, ba tare da ta yi magana ba ta bar wajen,ya bi ta da murmushi,a ranshi yana ayyana abubuwa da yawa





*DAULAR TAYAAR*


Kwana biyu kenan da tattaunawar gimbiya Hayat da kuyangarta,ta gamsu sosai Da maganar Huda,amma bata san yadda zata yi don ta yi masa magana ba,asalima tun daga ranar bata sake fitowa daga sashenta ba ballantana har ta saka shi a idanunta,asalima wata kunyar shi take ji saboda abubuwan da ta rin?a yi masa a baya

Tana zaune a Wakinta, kuyanginta guda biyu suna taya ta shiryawa bayan ta fito daga wanka sai ta ga abu ya gifta,da farko bata kawo komai ba, musamman da ta ga alamu cewa su Huda ba su ga komai ba,sun cigaba da yi mata hira yadda suka saba

Sake ganin giftawar abu ta yi,ta tsayar da su Huda, lokaci guda suka yi shiru suna saurare

Kamar an ce kalli can,ta hango wata ?atuwar kada a kwance a gefen gadonta ta buWe baki, ihu ta kurma tana nuna ta da yatsa,su Huda suka gigice, don da alamu ba sa ganin abin da take gani,nan da nan suka rikice, Waya kuyangar mai suna Humaida ta fice daga Wakin da gudu ta nufi inda su mai martaba suke don a nema mata iso ta sanar da abin da ya faru

Kafin sarki Iyaad ya zo inda Hayat take tuni ta suma,abin mamaki har yanzu babu wanda ya ga komai a Wakin,mai maganin masarautar aka kira don ya duba ta

Sai dai tsawon kwana goma tun daga wannan ranar gaba Waya gimbiya Hayat ta zama wata iriya,bata da aiki sai zabura da firgita,gashi kuma har yanzu lokacin ta kasa magana ballantana ta gayawa mutane abin da yake faruwa da ita,aikin kenan daga kuka sai zabura





=???

Duk abin da yake faruwa Kazuzi yana da masaniyar komai,sai dai bai taSa nuna ya sani Win ba ko da a fuska ne,amma abin da yake ji game da halin da gimbiya take ciki yana damunshi

Don haka a yau bayan ya fito daga lambun gimbiya da yake gyarawa kullum duk da bata fitowa yanzu,kai tsaye ya wuce wajen Wakunan dakarun gidan,yana zuwa bai yi wata wata ba ya faWa Wakin da yake bu?ata ba tare da wata shakka ko tsoro ba

Dakare Amjad da yake zaune tare da matarsa ya yi firgigit yana kallon Kazuzi da ko sashen da matarshi take bai kalla ba,ya ?ure shi da idanu, Amjad ya mi?e a firgice yana kallonshi, kafin ya ce"mahaukacin ina ne kai da za ka shigowa mutane Waki ba tare da neman izini ba?

Ko a addinin naka ba'a koya maka ladabin sanin dokar shiga waje sai an nemi izini ba? musamman idan mutum yana tare da matarsa?"

"A addini na an koya min ladabi da neman izini ne daga waWanda suka cancanci hakan kaWai,don haka yanzu magana nake so na yi da kai,za ka wuce ta lalama ne ko kuwa?"

Amjad ya jefe shi da kallon tsana, kafin ya yi magana matarshi ta fara magana cikin fushi

"Tsinuwa da la'nar Allah gami da azabarshi su tabbata ga zindi?i kafiri kuma azzalumi irinka,wanda bai san darajar rai ba ballantana ya san darajar wani, kuma ka gaggauta fice min daga Waki,ko na kai ka ?ara inda za'a ?arar da rayuwarka"

Kazuzi ya kalli yadda take faWa da tsananin Sacin rai,amma sai ya Wauke kai ya mayar da kanshi ga dakare Amjad da yake watsa masa nashi kallon tsanar,bai damu ba ya ce"ka wuce mu yi magana,idan kuma ba za ka fita ba babu laifi sai mu yi a gaban matar taka, duk da cewa ba abin mamaki bane idan ya zamana kai da ita abokan cin mushe ne"

Dakare Amjad ya ce"duk abin da za kayi kar ka fasa,amma kai ba ka isa ka saka na fito daga Wakin matata ba, fita na ce"

"Zan fita,amma sai ka warware abin da ka yi"

Kallonshi Amjad ya yi a Wan ruWe, Kazuzi bai damu ba ya ce"ka warware abin da ka yi mata tsawon kwanaki, saboda ita ba ?arka ko matarka ba ce shiyasa za ka cuce ta,idan har kai namiji ne ubanta za ka cewa ya Waura Wamara,kai ma ka Waura ku Wauki takubba a ba ku fili ku gwabza

Namijin gaske ba ya laSewa a bayan tuggu da makirci ko asiri ya yi cin amana"

Dakare Amjad cikin rashin damuwa ya ce"ba zan warware ba!

Idan har tsafi abin ?i ne kai bai kamata ka faWi hakan ba, saboda shine ya gina daularku ta zalunci Baruda,da shi aka raine ka ka zama mutum,kuma shine yake ba ka nasarar ya?i

Kuma da kake maganar namiji,idan Ni da na laSe a bayan asiri don ganin bayan yarinyar don Waukar fansa,to kai kuma menene makomarka?

Ba zaka iya Waukar fansar ba kenan?tsafin naka ya daina tasiri ne? shi yasa ka zaSi zama bawan da mace ta mayar tamkar karenta?

Kar ka Wauka ban san irin wahalalliyar rayuwar da ka yi a Baruda ba,amma ka zaSi ka zamar musu bawa don baka da galihu daga kai har wanda ya tsince ka,don sanannen abu ne kai Win baka da asali!idan ubanka Murad bai sanar da kai ba ni yanzu na sanar da kai,ya Waura maka ba?ar laya a damtsenka na hagu wadda take ba ka ?arfin da za ka iya karawa da rundunar da bata da iyaka,ni na bawa Waleed izinin ya tsinke ta, don yana daga cikin matakin nasara ta shine na fara karya ka,tabbas sai na Wauki fansa akan abin da ka yi min na kashe min yara na

Na samu nasarar farko ta hanyar ganin bayan budurwar ka Malli,zan yi nasara akan Sarkin Tayaar ta hanyar ganin bayan tilon ?arshi,kuma babu wanda ya isa ya ya dakatar da ni!!!"

Tabbas maganganun dakare Amjad sun yi tasiri a zuciyar Kazuzi, zuciyarshi ta yi rawa musamman ambatar Malli da Amjad ya yi,amma sai ya dake ya yi murmushi,sannan ya fara magana

"Ka yi gaskiya!

Tabbas da tsafi aka raini Kazuzi,amma idan ka yi tunanin tsafi shine ?arfin Kazuzi baka yiwa kanka adalci ba, kai ganau ne ba jiyau ba,ka ga asalin Wanene Kazuzi lokacin da ka tura damisa ta farmaki gimbiyar Tayaar

Maganar Malli kuma haka zancen ka yake,malli ita ce dukkan rayuwa ta,mutuwar ta daidai yake da rasa farin ciki na,ka yi nasara sosai da ka saka aka kashe min ita

Sai magana ta gaba,me ma ka ce? yadda ka ga bayan Malli sai ka ga bayan gimbiyar Tayaar ko?za mu gani idan za ka iya hakan,ban zo nan don bani da yadda zan yi ba,ko don ban san yadda zan yi da abin da ka yiwa ?arinyar da bata ji ba bata gani ba,sai don ka san cewa ina sane da abin da ka yi,kuma idan ka cigaba kamar yadda na faWa za kayi nadama mara amfani a rayuwarka

A ?arshe,da alfahari nake faWa cewa Ni Kazuzi ibn Murad tsintacce ne kamar yadda ka faWa, wula?antacce a Baruda kafin na zama maya?i,kuma a ?arshe bawan mace,ina alfahari da hakan tunda ban kasance maci amana ba a tsawon shekaru na rayuwa ta!

Ina yi maka jajen ranar da asirinku zai tonu ku ji kunya a bainar jama'ar da suka Wauki yarda suka ba ku,kuma ba ku cimma mugun ?udirinku akansu ba,don muddin Kazuzi yana cikin Tayaar har abada ba za ku cimma mugun ?udirinku ba"yana kai wa nan ya juya da takunshi na isa ya fice daga Wakin ba tare da ya sake saurarar abin da za su faWa ba




(Ga masu son VIP group ga number ta nan a ?asa)

#Nusy_bee
08125952284


=????=?Q? MASARAUTAR KAIZUR =????=?Q?






'?Nusy bee
d'? Young talented writers association YOTA d'?

(Under YOTA'S AMAZING PENS)



Page 10



Da kallo Amjad da matarshi suka bi Kazuzi da ya fice daga Wakin babu alamun damuwa a kan fuskarsa,matar Amjad ta fashe da kuka tana ri?e hannun mijinta, cikin kuka ta ce"yanzu menene abin yi abu Huzaifa?

Ina tsoron kar wannan kafirin yaron ya tona mana asiri,mu ba muyi hakan don wani abu ba sai don zaluncin da aka yi wanda ya zama silar mutuwar yaranmu uku,ka je ku yi magana da shi"

Kallonta Amjad ya yi, cikin taushin murya ya ce "kar ki damu Layla,babu abin da zai iya,barazana ce kawai"

Layla ta girgiza kai ta ce "to ka warware abin da ka yiwa gimbiyar Tayaar,a tsorace nake da abin da zai faru, sarki Iyaad zai iya yanke mana hukuncin kisa akan wannan abu da muka yi"

Girgiza kai ya yi, cikin taushin murya ya ce"na gaya miki babu abin da zai iya,yanzu ba sai anjuma ba zan tsaface shi,babu abin da zai iya akai,mantawa ma zai yi da abin da ya gani,ki kwantar da hankalin ki"

Hankalin Layla ya kasa kwanciya??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????,ta dubi Amjad ta ce"ko ka manta ne Abu Huzaifa?

Shima matsafi ne fa,babban matsafi kuma,ba ka tunanin zai iya Waukar matakin kare kanshi,kuma a karshe ya ce zai yi mana raddi?"

?ar dariya Amjad ya yi, cikin nishaWi ya ce"a dalilin haka ya sa na saka Waleed ya yanke layar da aka Waura masa a dantsensa na hagu,duk wani sihiri da tsafi da yake ji da shi na karya alkadarin "

Murmushi Layla ta yi zuciyarta na sakewa,ta jinjina kai ta ce"na gamsu abu Huzaifa,mu yi ?o?arin ganin bayan wannan azzalumin,ban taSa tsanar wata halitta ba Kamar yadda na tsane shi,yara na huWu ya kashe min uku ya bar min Waya "ta ?arasa magana cikin kuka sosai"

Zuciyar Amjad ta girgiza,ya dafa kafaWarta, cikin taushin murya ya ce"ki kwantar da hankalin ki Ummu Huzaifa,nasara akan wannan fajirin kamar mun samu mun gama ne in sha Allah"





=???

Yana barin Wakin shugaban dakaru Amjad kai tsaye ya wuce Wakinshi da aka ba shi bayan an fito da shi daga Wakin duhu, Wakin bashi da tazara da lambun gimbiya Hayat,a lokacin da aka ba shi Wakin akwai kayan more rayuwa fiye da lokacin da yake rayuwarsa a Baruda,amma sai da gimbiya Hayat ta saka aka fitar da komai,aka bar masa Wan mayafin da zai shimfiWa da wanda zai rufa

Yana zuwa ya zauna akan dandagaryar daSen da ke Wakin,ya haWe kanshi da gwiwa yana tunani,shi ba mutum bane mai yanke hukunci cikin fushi,amma tabbas ba don haka ba babu wanda zai kalli idanun shi da alfahari ya gaya masa shi ya kashe masa Malli amma ya rabu da shi,da sai ya Wauke kanshi da takobi idan ya so komai zai biyo ya biyo daga baya

Bai taSa jin zafin gorin rashin asali da aka yi masa a Baruda ba,amma bai san meyasa ba yau karo na farko sai ya ji zafin gorin da Amjad ya yi masa,ya sauke zazzafan numfashi, lokaci guda kuma ya mi?e zumbur kamar wanda aka tsikara ya fice daga Wakin

Kai tsaye sashen gimbiya Hayat ya nufa,tunda yake a tsawon rayuwarsa bai taSa shiga ba,ko da ya kasance a cikin masu yi mata hidima ba ya wuce aikace-aikace ko kuma kula da lafiyarta,amma yau kanshi tsaye ya nufi sashen

A bakin ?ofa ya gamu da Huda, fuskarshi babu walwala ya ce"ina son ganawa da gimbiya"

A Wan daburce ta ce"am.....um... Gimbiya?dama....."

Wani mugun kallo da ya watsa mata ne ya sa ta matsa masa ya wuce jikinta yana karkarwa,bai sake kallonta ba ya kutsa kai cikin Wakin gimbiya

A kwance ya ganta tamkar gawa,mai maganin gargajiya da aka kira yana ta ?o?arin gano abin da ya same ta,amma yadda a tsawon kwanakin nan bai samo komai ba yanzun ma hakan take,gefe kuma ga kuyanginta guda biyu Humaida da Bil?ees, Kazuzi ya dube su gaba Waya fuska babu rahama, cikin dakakkiyar muryarshi irin ta mazan fama ya ce"ina bu?atar ganin kowa ya fita"

Mai magani ne ya Wago ya kalle shi,dama su Humaida da Bil?ees tuni jikinsu ya fara kyarma,mai magani ya ce cikin kwantar da murya

"Haba yaro!

Me za ka iya yiwa gimbiya?menene dalilin da ya sa kake so kowa ya fita alhalin kai baligin namiji kana Wakin?menene dalilin....."

"Cewa na yi kowa ya fita,ba magana na tambaya ba"ya faWa cikin tsawa

Da gudu suka fara fita a tsorace,suna daf da fita ya ce "ke!"cikin tsawa

A tsorace Humaida da Bil?ees suka tsaya jikinsu yana kyarma,da yatsa ya nuna Humaida ya ce"ke!

Zo nan,ke kuma fice ki ba ni waje"a guje Bil?ees ta juya ta fice daga Wakin kamar zata kifa don tsoro

A razane Humaida ta ?araso wajen da Kazuzi yake, tana zuwa ta zube a gabanshi,tana shirin fara gaishe shi cikin tsawa ya ce"Wauko min abin da shugaban dakaru Amjad ya ba ki ki Soye a Wakin nan"

?ara firgita ta yi,tana shirin fara rantse-rantse ya daka mata tsawa,take ta fashe da kuka,tuni fitsari ya kubce mata,ya sake cewa cikin dakewa "fito min da abin da Amjad ya ba ki,kar ki bari na sake tambaya"

Cikin kuka Humaida ta ce"ka yi min aikin gafara,na rantse bai ba ni komai ba"

"?arya kike yi!

Tunda kika ji na faWi haka ya kamata ki san na san komai,don haka ba ni kawai"

Tana kuka ta ce"na gaya maka ban san komai ba akai,ka gafarce ni don...."dam?ar gashin kanta da ya yi da tsananin ?arfi,hakan ya sa ta yi ta ?wala uban ?ara, cikin kukan azaba ta ce"zan Wauko,ka yi min afuwa zan Wauko maka"

Sakinta ya yi yana kallonta,jiki na rawa ta mi?e ta nufi bayan ?ayataccen gadon gimbiya Hayat ta zaro wani ?ulli,ta ?araso ta dur?usa ta mi?a masa,bai amsa ba ya ce"kwance ?ullin "

Babu musu ta kwance jikinta yana rawa,wani dun?ulallen abu ne a cikin tsohon tsumman da aka ?ulle ya bata umarnin ta fasa shi,babu musu ta lalubo abin fasawa ta fasa,take gimbiya Hayat ta kama wata iriyar jijjiga, Kazuzi ya mayar da idanunshi kanta amma bai yi yun?urin zuwa inda take ba

Sake mayar da kallonshi ga Humaida ya yi, wadda take dur?ushe jikinta yana ta rawa, hawaye wani na korar wani,cikin kakkausar murya ya ce"wuce ki rufe ?ofar Wakin nan"

A gigice ta mi?e tana faWin "in tafi?"

Wani mugun kallo ya watsa mata,a gigice ta ce"ka yi min aikin gafara"sannan ta wuce bakin ?ofar ta rufe,ya mayar da kallonshi ga Hayat da ke kwance a ?asa, zuwa yanzu ta daina jijjigar,tana kwance ta yi shiru,a kausashe ya fara magana

"Daga yau bana bu?atar ?ara ganinki a duk wani abu da ya shafi gimbiya,ki san me za ki gaya wa mutane,amma na haramta miki zuwa inda take,idan kuma kika kuskura na ganki ko a kewayen Wakinta ne,kar dai ki manta nine KAZUZI IBN MURAAD,ina nan a yadda kika san ni ko na ce kike jin labari na, bambancin wajen zama kawai na samu,don haka tashi ki fice daga Wakin nan"

Babu musu ta mi?e jikinta yana kyarma ta nufi ?ofar Wakin,a kausashe ya ce"zo ki kwashe tarkacenki"babu musu ta dawo ta dur?usa ta kwashe abin da ta kwance, sannan ta koma bakin ?ofar ta buWe ta fice, Kazuzi ya mayar da kallonshi ga gimbiya da ke kwance

Bai yi mamakin ganin idanunta a buWe ba tana kallonshi,don ya san zuwa yanzu abin da aka yi mata ya sake ta,ya rissina a gabanta kanshi a ?asa kamar yadda ya saba, cikin taushin murya, Kamar ba shine ya gama daka tsawa yanzu ba ya ce"fatan tsawon rai mai albarka da lafiya mai amfani ga gimbiyar Tayaar "

"Kazuzi ibn Murad!ba ka san sunana ba?"ta faWa cikin sanyin murya tana Wan murmushi

Kallonta ya yi a ranshi yana mamakin murmushin da ya ga ta yi,kafin ya yi magana sai ga sarki Iyaad da Sarkin ya?i da dakare Amjad sun shigo a firgice, Amjad ya nuna Kazuzi da ke dur?ushe gaban Hayat yana faWin "ka gani ya shugaba na!

Wannan fajirin ya kori kuyangi da mai maganin gimbiya don ya samu damar aikata alfasha da ita,ya shugaba na wannan bawan yana da tsaurin idanu da yake tunanin zai iya aikata alfasha da gimbiya,ya kamata a ladabtar da shi ko hakan zai zama darasi ga ?an baya"

Cikin tsananin Sacin rai da ba?in ciki sarki ya dubi Sarkin ya?i ya ce"a kama shi "a take gimbiya Hayat da ke kwance ta yun?ura tana ?o?arin yin magana,a Wan tsawace Kazuzi

6 / 11