MASARAUTAR KAIZUR COMPLETE BY NUSY BEE.doc

Author :  Nusy Bee Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 11

18K to 21K   out of 31.5K words

ya ce"A'a ya shugaba ta!

Abu Waya nake so da ke, na san kin ji komai,zai yi kyau ki rufa asiri ko don sake bayar da dama, mutum zai iya dawowa kan hanya idan aka ba shi lokaci ba'a hukunta shi akan laifin da aka san ya aikata ba"yana kai wa nan dakarun da suke tare da Sarkin ya?i suka dam?e shi, ba tare da Sata lokaci ba suka yi waje da shi

Hayat da ke kwance ta bi su da kallo tana hawaye,sarki Iyaad ya ?araso kusa da ita hankali a tashe yana faWin"sannu ?ata!

Bai yi miki komai ba dai ko?"bata iya cewa komai ba,ya kama ta ya zaunar da ita,da idanu ya bawa bayi da sauran dakarun da suke Wakin umarni, suka rissina sannan suka fice daga Wakin

Ya yi farin ciki sosai saboda alamun sau?i da ya gani a tare da ?ar tashi,duk a tunaninsa aikin mai magani ne,ya kwantar da ita akan gadon sannan ya juya ya fice daga Wakin








*DAULAR KAIZUR*


"Na san kin san su wanene suka sace min Wa,ko na ce da haWin bakinki aka sace shi,har zuwa yanzu na kasa gane dalilin ki na aikata hakan, Munaya! gobe idan Allah ya nuna mana da rai da lafiya, za'a sake fitar da ke a yi miki rajamu Kamar yadda yake a ?a'ida duk shekara,idan na ga dama zan bari mutane su jefe ki har mutuwa,don haka tun wuri ki gaya min,ina Wana Sahal yake?

Kasancewar shi a raye ya tabbatar min da cewa kin san inda yake,amma a kwanakin nan na ga alamu yana cikin matsala, Munaya,ina Wana Sahal yake?"

"Allah ya ja da ran shugaban Daular kaizur,na yi magana tun a farko,ban san inda Sahal yake ba,Nima ba zan so ya nisance ni tsawon shekaru ba, a?alla ko gani na yi ya wuce zan ji sanyi a raina

Idan har baka gamsu da maganar da nake ta maimaitawa ba tsawon shekaru ashirin a yiwa mutane izinin su jefe ni har mutuwa"

"Munaya!"sarki Mu'iz ya daka mata tsawa, cikin Sacin rai ya cigaba

"Da alamu taurin kai da izza tana damunki,yanzu ba sai anjuma ba zan saka a yi min maganinki"ya mike a zafafe ya fita,jum kaWan ya dawo da wasu zaratan dakaru su uku,ya dube su fuskarshi a matu?ar haWe ya ce"ku yi mata hukunci,kar ku saurari kukanta,kar ku saurari magiyarta,kuma kar ku saurara mata,kar ku duba kasancewarta mace ko don shekarun girma"yana kai wa nan ya juya a fusace,su kuma suka kama Munaya don aiwatar da aikin su

Iya azaba sun ganawa Munaya amma ta dake,ko sau Waya bata nuna musu raki ba,sun dake ta,da suka ga dukan bai yi ba suka Waure ta kanta a ?asa suka rin?a nana mata ?arfen da ya yi ja a wuta,sai da suka kwashe fatar bayan nata duka, sannan suka lafta gishiri a wajen,bayan sun gama Wanyen aikin suka sake mayar da ita suka Waure ta sannan suka fice daga Wakin

Washegari da sassafe aka fito da ita bainar mutane,sarki Mu'iz da mu?arrabanshi suna zaune a inda suka saba zama, cikin su har da sarauniya Amna, Yarima Zaffar da Yarima Jamal,aka kai ta inda aka saba Waure ta,bayan komai ya natsa shugaban dakaru na ?asar kaizur,wato Dawud ya dube ta ya ce"Munaya!

Sarki ke umartarki ki sanar da mutane inda kika Soye yariman kaizur,don tabbas idan kika yi turjiya ba za ki kai wata shekarar ba"

Shiru ta yi tsawon wasu da?i?u, Dawud ya sake maimaita abin da ya gaya mata, kanta a ?asa ta ce

"A yi min afuwa ya shugaba na

Tabbas ni mai laifi ce a cikin MASARAUTAR KAIZUR,kuma na san laifi na ya wuce yadda za'a yi min afuwa

Amma ina ro?on wannan sarki mai adalci da ?aunar talakawan shi,da ya bincika jama'ar da ke cikin fada,tabbas a cikinsu aka samu wanda ya sa aka Wauke Yarima,ni amfani aka yi da ni,tun daga lokacin da aka kawo ni MASARAUTAR KAIZUR zuwa lokacin da aka sace Yarima,an cimma wani buri ne,kuma wannan burin da ake son cimmawa ba iyaka kan yariman kaizur ya tsaya ba,har da kai ya shugaba na

Idan na faWi wani abu wanda ba daidai ba ina ro?on tausayawa da rangwame daga wajen wannan sarki mai adalci






#Nusy_bee
08125952284


=????=?Q? MASARAUTAR KAIZUR =????=?Q?






'?Nusy bee
d'? Young talented writers association YOTA d'?

(Under YOTA'S AMAZING PENS)




Page 11



Shiru ilahirin wajen ga Wauka duk da yawan mutanen,jikin yarima Jamal yana rawa ya mi?e ya nuna ta a kiWime,ya ce"me kike nufi?

Annamimanci za kiyi mana? ?as?antacciyar baiwa irinki zata ?ulla makirci a cikin masarautar nan? wacece ke da kika isa ki raba abin da kika zo kika samu tsawon shekaru?"

Kallonshi ta yi kai tsaye ta ce"Allah ya taimake ka,a tsawon zamana a kaizur ba'a taSa kama ni da wani laifi mai kama da makirci ko tuggu ba, kuma ko yaudara da cin amana da ake zargi na da shi ina da tabbacin za'a gane gaskiya nan da Wan lokaci ?alilan

Kamar yadda na faWa da farko,ya shugaba na a jarraba,a gwada binciken"

Sarki Mu'iz ya dube ta a fusace ya ce"Munaya!

Zuwa yanzu ya kamata ki gane mu ba ?ananan yara bane!har tsawon wanne lokaci za ki Wauka kina raina mana hankali?"

"Ka gafarce ni ya shugaba na,ban kai na raina muku hankali ba,iya abin da na sani nake faWa "

Sarki Mu'iz zai sake magana sarauniya Amna ta dakatar da shi,da hawaye a idanunta ta dube shi ta ce"a jarraba bincikawar ranka ya daWe, ba'a ?in ta mutum "ta dubi dakarun da ke tsaye suna jiran umarni ta ce"a mayar da ita inda take kulle,a canja nau'in azabtarwa,a rin?a ba ta abinci sau Waya a rana,ruwa ma haka,kar a dake ta, a yi mata wannan horon na tsawon sati guda mu gani, sauran al'umma kuma za su iya tafiya,an sallami kowa"tana kai wa nan dakarun suka rissina,suka kama Munaya suka wuce da ita kurkuku, sauran mutanen suka fara watsewa suna tsinewa da yiwa Munaya Allah wadai






*DAULAR TAYAAR*

Tunda Kazuzi ya zo Tayaar ba'a taSa shayar da shi narkon azaba irin wanda ake yi masa yanzu ba, gaba Waya ya fice a hayyacinshi,banda aiki mai tsanani ga horon yunwa,ga wahalhalu kala-kala,haka ya kasance a cikin wannan halin tsawon kwanaki uku bisa jagorancin badakare Amjad wanda duk da wannan azabar da yake gana masa har yanzu nazari yake yi ta hanyar da zai ga bayanshi

Daga Sangaren gimbiya kuwa,tsawon Wadannan kwanakin tana ?arasa jinya ne,bata fita ko'ina,kuma idan sarki Tayaar ya shigo inda take baya taSa yarda ya ba ta dama ta yi masa magana akan Kazuzi,hakan yana matu?ar damunta

Sauran kuyangin nata abin ya yi musu daWi, saboda yawancinsu sun tsani Kazuzi saboda halayensa,don haka sun yi farin ciki sosai da halin da Kazuzi yake ciki,a cikin su Huda ce kawai bata cikin farin ciki, asalima tunda aka kama Kazuzi bata ?ara kwana guda cikakke ba da farin ciki,kuma hakan yana da ala?a da yadda ta ga uwar Wakin nata Hayat

Yau kam Hayat ta tashi da wata iriyar damuwa,ko abinci kasa ci ta yi,sai kuka kawai,har lokacin abu biyu yake damunta,cin amanar da dakare Amjad da kuyangarta Humaida suka yi mata,don tabbas ta ji komai,sai kuma kama wanda ya ceci rayuwarta har sau uku a matsayin mai laifi dalilin haka yau ta kasa cin abinci,ta kasa walwala yadda ya dace

Huda ce ta kai wa jakadiya Rubayya labarin abin da yake faruwa,babu Sata lokaci ita kuma ta nemi iso wajen sarki da yake zauren shi na hutawa yana mi?e ?afa, kuma ba tare da Sata lokaci ba ta sanar masa da abin da ya faru

Cikin damuwa ya ?araso zuwa Wakin gimbiya Hayat,da a yanzu iya Huda ce kawai baiwarta da ta yarda ta raSe ta,bayan sarki ya shigo da sallama Huda ta rissina ta gaida shi,ya amsa sannan ta fice daga Wakin

A gefen gadon da Hayat take zaune ya zauna, cikin rarrashi da nuna ?auna ya dafa kafaWarta,bata yi wata-wata ba ta faWa jikinshi tana kuka mai tsuma zuciya

?an bubbuga bayanta ya fara yi alamar rarrashi,a hankali kukan nata ya fara raguwa, cikin kwantar da murya ya dube ta ya ce"yanzu gaya min, Wanene ya taSa gimbiyar Tayaar ne?"

"Abby don Allah ka sa a sake shi, don Allah Abby"ta faWa cikin kuka

Da kallon mamaki ya bi ta,kafin ya ce "Wanene kike magana akai?"

"Kazuzi Abby

Ha?i?a Abby baka yin abu ka yi nadama saboda dogon nazari da kaifin tunani irin naka,a wannan karon ma ina ro?on ka yi amfani da wannan baiwar taka akan Kazuzi,kar ka yanke masa hukunci daga baya ka zo kana yin danasani"

A hankali Sarki Iyaad ya girgiza kai ya ce "laifin Kazuzi ya kai na hukunta shi ne gimbiya

Menene dalilin da ya sa kaf matan masarautar nan babu wadda ta yi masa sai ke?

A matsayin shi na bawa,kuma wanda bai amshi musulunci ba?

A ?a'idar Tayaar,ke ma kin sani da tuni ba ya raye,amma na saka aka Wage hukuncin don kawai na nuna masa ?auna,ya ji cewa duk da kasancewarsa wanda bai amshi addinin musulunci ba amma hakan bai saka na ?yamace shi ba,amma sai gashi na ganshi a Wakinki,ya kike tunanin zan ji?kuma me yake nufi da abin da ya faWa kafin dakaru su fitar da shi?"

A hankali tana girgiza kai hawaye suna zubo mata ta ce"ba abin da kake tunani bane Abby

Da za ka ji abin da ya yi godiya za kayi masa,ba ka sa a kama shi ba, Abby kar ka manta a baya na tsani Kazuzi,amma nagarta da halayensa ya sa yanzu ina ganin ?imarshi, Abby ko don darajar sayar da ran da yake yi a kaina duk da kasancewar sa bawa a wannan masarautar me zai hana a ba shi wata dama?

Maganar abin da ya gaya min kamar yadda ya ce zan ba wa masu laifin damar ?arshe don su gyara kurensu,idan ba su gyara ba kuma zan Wauki mataki,ko ma na gaya maka komai akansu"

Sarki Iyaad ya jinjina kai ya ce"to babu matsala

Na yarda da maganarki,zan saka a sake shi,amma zan saka a saka masa idanu"Hayat ta rungume sarki Iyaad tana murmushi da hawaye ta ce"na gode Abby

Amma ina ro?on alfarma daga gare ka"

Sarki Iyaad da yake cike da mamakin yadda ta damu da Kazuzi ya ce"ina jin ki ?ata"

Hayat ta gyara zama ta ce"waWanda za ka saka su su kula da shige da ficen Kazuzi ka haWa da sarkin ya?i Ra'uf, badakare Adnan da kuma shugaban dakaru Amjad "

Bai yi wani dogon tunani ba ya ce"to ?ata, idan na yi hakan ya yi Miki ko?"

Tana murmushi sosai ta ce"ya yi min Abby, Allah ya tsare ka daga dukkan sharri "ta sunbaci goshinshi sannan ta ce"Abby bari na je da kaina na fito da shi,dole na nuna masa ban manta sadaukar min da ranshi da ya yi ba har sau biyu"sarki Iyaad ya yi murmushi sosai,bai kawo komai ba a ranshi sai halayen mahaifiyarta da ta Wauko na tsananin tausayi da girmama Wan adam

A keken dokinta ta je har Wakin hukunci inda aka kulle Kazuzi ana yi masa azaba iri-iri,ba iyaka badakare Amjad ba,har wasu daga cikin masu azabtar da shi suna matu?ar jin haushinshi,don ma wani lokacin Ra'uf yana hana wasu abubuwan,shi dama banda dalilin doka ce daga sama da so ya yi ya ji hanzarin Kazuzi,duk da cewa shima Kazuzin wani lokacin murWaWWe ne ba lallai ya faWa ba

Tare suka tafi da amintacciyar baiwarta Huda,kanta tsaye ta shiga Wakin hukunci bayan dakaru sun buWe mata ?ofa,tana shiga ta bi Kazuzi da kallo gabanta yana faWuwa ganin yadda aka mayar da shi, muryarta na rawa ta ce"ku kwance shi"

Babu musu aka kwance shi,duk da halin da yake ciki sai da ya dur?usa a gabanta ya ce"Barka da wannan lokaci ya shugaba ta"

Bata iya amsa wa ba,sai zuba masa idanu da ta yi tana mamakin ?arfin halinsa,suna cikin wannan halin ne badakare Amjad ya shigo Wakin a gaggauce,labari ya same shi cewa gimbiya Hayat ta shiga Wakin duhu, cikin girmamawa duk da yadda ranshi ya Saci ya dube ta ya ce

"Ya shugaba ta wannan umarnin mai martaba ne,shi ya ce a hukunta shi saboda abin da ya aikata a gare ki,ya shugaba ta kin san hukuncin mazinaci a cikin Tayaar, ballantana kuma wanda ya yi nufin aikatawa da gimbiya,a gafarce ni idan na faWi abin da bai dace ba ranki ya daWe"

Kallonshi take yi zuciyarta cike da matsananciyar tsanarsa,bata manta abin da ta ji ba,sannan ta sake titsiye Humaida ta gaya mata gaskiyar abin da ya faru na shirin da ya yi ba tare da ita kanta Humaida Win ta san niyyar shi ba,ba tare da tunanin komai ba ta Waga hannu a fusace da niyyar Wauke shi da mari,amma ta ji an ri?e hannun

Da sauri kuma a fusace ta waiga, Kazuzi ne,ya sakar mata hannu sannan ya sake rissinawa ya ce"ina ro?on a yi masa afuwa ya shugaba ta,ina ro?ar masa alfarma a duba shekarunsa,komai ya yi a Waga masa ?afa "

?asa magana ta yi da farko, ?walla ta cika mata idanu ta dube shi ta ce"ai ka san komai, menene dalilin da zai saka ka yi tunanin zan iya girmama tsufansa?"

Kan Kazuzi a ?asa ya ce"wani lokacin ma?iyi shiru shine yake firgita shi, musamman idan ya gaza nasara akanmu,a jarraba hakan ya shugaba ta"goge ?wallar idanun nata ta yi ta ce"haka ne,to biyo ni,ina son mu yi magana da kai"daga haka ta juya ta fice daga Wakin,sauran dakarun suka bi ta da kallo,kansu a Waure saboda maganganun da suka yi da Kazuzi yanzu,wanda ke nuni da wata a ?asa tsakaninsu da badakare Amjad

Shi kuwa badakare Amjad ji ya yi kamar ya nutse saboda kunya da tashin hankali,a zuciyarsa tsanarsu ta ninku,amma sai ya dake,ya juya ya fice daga Wakin ba tare da ya kalli kowa ba

Kai tsaye Wakin Kazuzi suka nufa,yana shiga ya samu waje akan daSen Wakin ya zauna,a ranshi yana Soye mamakinsa ganin an sauya masa kayan kwanciya,ya nuna mata makwancin nashi ya ce"Barka da zuwa ya shugaba ta,ga waje ki zauna"

Girgiza kai ta yi ta ce"ba zama zan yi ba,kawai tambayarka zan yi,ya aka yi ka gane cewa dakare Amjad ne yake neman rayuwa ta?"

A hankali ya lumshe kyawawan idanunshi ya sake buWewa,ita dai Hayat ta shagala da kallon ikon Allah, saboda zata iya cewa a tarihin rayuwarta bata taSa ganin namijin da ya amsa sunan kyakykyawa mai cikar zati irin wannan sadaukin ba,a hankali ta ji muryarshi yana faWin

"Babu wani tsafi da za'a yi wanda Kazuzi bai san yadda yake ba,bai san makarinshi ba

A iya tsawon rayuwata ilmi uku na samu daga wajen babana, shine ilmin tsafi,ilmin ya?i da na farauta,na koyi ya?ar duk abin da ya saSa da tsarina,na koyi farautar dabbobi masu haWari tun ina Wan ?aramin yaro, kazalika na koyi ilmin tsafi don kariya,da kai farmaki

Babu wani kalar tsafi da za'a yi na kasa ganewa,da damisa da macijin da suka farmake ki duk ba na gaske bane, dukkansu tsafi ne,kuma da an bar su wajenki kawai za su zo ba za su cutar da kowa ba, tunda dama don ke aka turo su

Da ya ga na yi nasarar rusa shirinshi har sau biyu shine dalilin da ya sa ya sake shiri,ya yi amfani da kuyangarki Humaida ya ba ta ajiya ta ajiye a Wakinki,a ?arshe kuma da na yi masa magana don ya warware aikin ya ?i har ya shirya min makirci

Ya so ya yi nasarar ya?a ta da tsafi,sai dai shi a ilimin tsafin babu abin da ya sani,don a bayyane yake babu tsafi a musulunci,ba kamar namu addinin ba da ya zama tamkar ibada,shi bai san haka ba, shiyasa ya yi tunanin ya tsaface ni,amma ha?anshi bai cimma ruwa ba"yana kai wa nan ya lumshe idanunshi kawai ba tare da ya sake magana ba

Shiru ya biyo baya na Wan lokaci,tuni gimbiya Hayat ta samu waje ta zauna tana kallonshi, kafin ta katse shirun da cewa "to yanzu ta yaya kake ganin za'a hukunta shi?"

BuWe idanu ya yi,kanshi a ?asa ya ce"lokaci ne zai hukunta shi ya shugaba ta,ina ganin a ba shi dama ko zai gane ya dawo hanya

Babu abin da hukunci cikin fushi yake haifarwa sai nadama da danasani,da ace zan yi masa hukunci cikin fushi da yanzu ba ya duniyar "

Girgiza kai ta yi a sanyaye ta ce"ba laifinsa bane kama ka da azabtar da kai,abbana ne,ka yi masa aikin gafara ya yi ne a rashin sani da son yin kishin tilon ?arshi,daga gare ka kam na tabbatar Amjad ba zai iya yin nasara ba"

A hankali Kazuzi ya girgiza kai ya ce"azabtar da Kazuzi ba shi da bambanci da sanya ?arfe a wuta,duk juyin da zai yi sai dai ya canja na Wan lokaci ?an?ani,amma ba za'a kassara shi ba

Sai dai tuni Kazuzi a kassare yake,kuma ba kowa bane ya kassara shi sai Amjad "ya yi Wan shiru yana sauke numfashi cikin damuwa,kafin ya sake faWin"ya kashe Malli!

Ita ce farin cikin Kazuzi,amma a yau babu ita, tabbas rayuwar Kazuzi bata da amfani,bata da al?ibla muddin babu Malli a cikinta"





#Nusy_bee
08125952284

https://chat.whatsapp.com/Is0HqhjNITL3VZIagV42u7?mode=gi_t



=????=?Q? MASARAUTAR KAIZUR =????=?Q?





'?Nusy bee
d'? Young talented writers association YOTA d'?

(Under YOTA'S AMAZING PENS)





Page 12




Shiru ya sake yi yana jan numfashi a hankali,har yanzu idanunshi suna ?asa,ita kuwa Hayat ?amewa ta yi a inda take zaune tana kallonshi cike da tsananin mamaki da tausayin da suka daskarar da ita a inda take zaune, Malli Win da yake faWa,yake bege a koda yaushe, wadda ta zama muradin ranshi bata raye dama?

Tunaninta ya yanke a lokacin da ta ji yana faWin "da ace Ni mai yanke hukunci cikin fushi ne babu abin da zai saka Amjad ya kwana a duniya ranar da ya kalli idanuna da alfahari yana gaya min shi ya sa aka kashe min Malli,kashe ta bashi da bambanci da kashe dukkan farin ciki da burin rayuwa ta kamar yadda na gaya miki,kafin shigowar Malli rayuwa ta bata da wata ma'ana,zuwan Malli cikinta shine ya sa na fara yiwa kaina kallon mutum"

A hankali gimbiya Hayat ta ja numfashi mai nauyi ta ce"kenan kana nufin Malli bata raye?

Na kasa yarda da wannan maganar"

Kallonta ya yi, kamar a mafarki sai ta ga ya yi murmushi,duk da cewa murmushin mai ciwo ne sai ta ga ya ?ara ?awata kyakkyawar fuskarsa, musamman da ya kasance bata taSa ganin murmushin shi ba,a

7 / 11