MASARAUTAR KAIZUR COMPLETE BY NUSY BEE.doc

Author :  Nusy Bee Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 11

24K to 27K   out of 31.5K words

Tayaar a matsayin musulmi ya shugaba ta"yana kai wa nan ya wuce da sassarfa inda dakaru suke jiranshi

Gimbiya Hayat ta bi shi da kallo, hawayen farin ciki suka zubo a kan fuskarta,a bayyane ta fara faWin"alhamdulillah! alhamdulillah ya Allah!

Allah ga bawanka! Allah ka tsamo shi daga Sata ya hayyu ya ?ayyum "





=???

Kallon farko da yawancin dakarun suka yiwa Kazuzi sai da zuciyarsu ta kaWa saboda tsorata,don ya fito a asalin Kazuzi Winshi da suka sani a filin ya?i, yana zuwa ya rissinawa sarki Iyaad,sannan ya kama ingarman dokinshi ya hau,babu Sata lokaci suka fara tafiya don barin cikin masarautar

Saboda yadda kazuzi yake kaWa dokinsa da azama ya sa ya yi gaba sosai, shugaban dakaru Amjad ya dube shi cikin tsananin tsana ya ce"ka ga!

Dakata mana!a tsarin tunkarar ya?i na musulmai sai an fara tsayawa daga baya an faWi kalmar shahada, idan sun maimaita shikenan sai a janye ya?in,idan ba su faWa ba kuma sai afka,kai yanzu idan ka yi gaba me za ka faWa su maimaita?ko an gaya maka ya?in musulmai haka ake afkawa kamar faWan dabbobi?"

Maganar ta zafafi Kazuzi,amma ya dake,ya ja linzamin dokinshi ya yi baya batare da ya yi magana ba,wasu daga cikin dakarun ba su ji daWin abin da Amjad ya yiwa Kazuzi ba,har suka yi masa magana akan hakan,wasu kuma musamman waWanda suke jin haushinshi suka ce ai gwara a gaya masa,tunda gaskiya aka gaya masa

Shi dai Kazuzi bai ce komai ba,suka cigaba da keta dajin suna nufar inda maya?an Haura suka yada zango suna jiran su

Ba su yi wata doguwar tafiya ba suka isa,daga nesa suka hango tarin dakarun da sarki Al'as ibnu mugaar ya fito da su,sai suka ga dakarun nasu sun koma tamkar wani zomo a gaban Giwa, don da yawa daga cikin su ma har sun fara karaya

Suna tunkarar ya?i,amma ba su taSa tunkarar dakaru masu tsananin yawa irin haka ba, Sarkin ya?i ne ya fara jan linzamin dokinshi ya tsaya yana kallon sarki Iyaad

Sarki Iyaad ya dube shi ya ce"Ra'uf ya dai?"

Ra'uf ya girgiza kai ya ce "ka gafarce ni ya shugaba na,amma wannan karon abu ne mai wahala mu haye makircin wannan fajirin"

Sarki Iyaad ya yi murmushi ya ce"nasarar Allah a kowanne lokaci a kusa take, Allan da ya bawa musulmai nasarar Waukaka kalmar Allah a ya?in badar shine zai ba mu nasara a wannan ya?in

Da ikonsa da izininsa nasara ta mu ce....."dukkan su shiru suka yi suna bin Kazuzi da kallo da suka ga ya tunkari rundunar kafiran nan a guje, ba tare da Sata lokaci ba su ma suka kaWa linzamin dawakansu suka bi shi

Sai da ya je daf da su ya ja linzamin dokinshi ya tsaya yana kallon su ba tare da wani tsoro ba akan fuskarshi,su ma su sarki Iyaad suka ?araso suna mamakin Kazuzi,duk da cewa sun san wanene shi tun ba yanzu ba

Sarki Al'as ya kalli sarki Iyaad yana murmushi ya ce"gaskiya na daWe ban ga mara kunyar sarki mai ji da isa a inda bai isa ba irinka Iyaad,ba sai na gaya maka ba,ka sani,an fi ?arfin ka da rundunarka,mai zai hana ka yiwa kanka karatun ta nutsu ka zubar da makamai?"

Sarki Iyaad ya yi murmushi,ya buWe baki da zummar bayar da amsa Muryar sadauki Kazuzi ta katse su

"Taron yuyuyu ba shi bane nasarar ya?i ko ?arfin maya?i,ka sa a ranka ya kai wannan raunataccen sarki,duk yawan Seraye kyanwa Waya ta isa ta tarwatsa su,ka Wauki rundunarka a matsayin Serayen"

Gaba Waya dakarun suka waiwaya inda kazuzi ya ja tunga yana kallon sarki Al'as cikin idanu yana mayar masa da magana fuskarsa babu annuri,sarki Al'as ya ce"ku gama da shi,ku kawo min kanshi nan"

Kafin ya rufe baki dakarun sun afkawa Kazuzi sun rufe shi ruf,bayan yan da?i?u sai ga su sun ?are tas,don tamkar mai wasa da takobi haka Kazuzi yake kashe su,hakan ne ya fusata sarki Al'as ya ce dakarun su afkawa rundunar Tayaar,kafin ?iftawa da bismillah wajen ya rincaSe da ?azamin ya?i

Ga duk wanda bai san wanene ainihin KAZUZI IBN MURAAD ba idan ya ga yadda yake ya?i a wajen sai ya Wauka ba mutum bane,idan ya Waga takobi ya sauke sai dai a ga kawuna suna zuba kawai

Cikin Wan lokaci ?alilan kazuzi ya yiwa rundunar Haura illa irin wadda ba su taSa tunanin wani mahaluki zai yi musu ba, sarki Al'as ya bayar da umarnin a kama masa Kazuzi, Kazuzi ya kalli dakarun da suka taho da zummar kama shi, cikin Wan ?an?anin lokaci ya ?arar da su ya koma ya cigaba da abin da yake yi

Daga yamma da suka fara ya?in kafin ketowar alfijir Kazuzi ya yiwa dakarun Haura illa ta ban mamaki,yana gab da samun nasarar ?arar da su wani dakare ya daka tsalle ya kai masa sara a wuya, cikin tsananin zafin nama ya goce, takobin ta yanke shi a gefen wuyanshi zuwa kafaWa,take jini ya wanke masa kafaWa

?aga kai ya yi ya ?arewa mai wannan Wanyen aikin kallo ba tare da ya yi magana ba,ya Wauke kanshi ya cigaba da kai farmaki har sai da ya ?arar da kaso mafi yawa daga dakarun Haura,sauran babu shiri suka gudu,ganin Sarkin nasu ma yana shirin guduwa sai ya hau dokinshi ya take masa baya,suka kasa tsere, Kazuzi ya shammace shi ya jefo shi daga kan dokin

Daga nan ?azamin faWa ya sar?e tsakanin Kazuzi da sarki Al'as,sarki Al'as yana cikin lokacin faWanshi ne kasancewar ko sau Waya bai yi ya?i ba,yayin da jini ya fara Wibar Kazuzi,ga gajiya kuma na tsawon lokacin da ya Wauka yana faWa,amma saboda tsananin jarumta da naci ya kasa ha?ura

Fuskantar wahalar da ya yi ne ya sa sarki Al'as ya cigaba da wahalar da shi,sai da ya tabbatar ?arfin halin nashi yana daf da ?arewa sannan ya shammace shi ya jefar da shi a cikin ?asa,kafin ya yun?ura ya tashi sarki Al'as ya Wora masa takobi a ma?ogwaro





#Nusy_bee
08125952284


=????=?Q? MASARAUTAR KAIZUR =????=?Q?






'?Nusy bee
d'? Young talented writers association YOTA d'?

(Under YOTA'S AMAZING PENS)



Page 14



Iya tsananin tashin hankali da firgici Sarki Iyaad ya shige shi lokacin da yake daf da ?arasawa inda suke,don a bayyane yake cewa Kazuzi ya fara gazawa, murmushi sarki Al'as ya yi cikin ?asaita yana kallon Kazuzi da shima yake kallonsa, cikin isa da gadara yake faWin "gwara kawai ka saukar da kai yaro,don nasara kuwa mun gama yin ta a kanku,idan...."

Ba sarki Al'as ba,hatta sarki Iyaad da sauran dakarun shi da suka shiga tashin hankali sai da suka zabura ganin wani irin zafin nama da dabarar ya?i irin ta Kazuzi, tuni ya saka takobin shi da babu wanda ya kula da lokacin da ya Wago ta,ya daki ta sarki Al'as da ?arfin tsiya,har sai da tartsatsin wuta ya tashi,sarki Al'as ya yi baya taga-taga kamar zai faWi saboda tsananin ?arfin dukan,kamar kuma wanda yake aiki da aljanu zumbur sai gashi a tsaye cikin tsananin zafin nama kamar ba shine wanda jikinsa ya fara gazawa ba

Da mahaukacin gudu sarki Al'as ya taho don ya Wauke masa kai da takobi,amma Kazuzi ya sare hannun,a wajen ya faWi yana malelekuwar azaba yana kallon hannunsa da ya faWi can gefe cikin tsananin mamakin wannan Sadauki,bai gama dawowa hayyacinsa ba Kazuzi ya sare masa kai a fusace,hatta da rundunar Tayaar sai da suka razana,ya Wauko kan sarki Al'as ya ya taho zuwa gaban sarki Iyaad ya rissina ya ajiye yana faWin "fatan nasara da cigaba mara yankewa ya shugaba na!"

"Sannunka da ?o?ari gwarzo kuma jajirtaccen maya?i sadaukin sadaukai!"a cewar sarki Iyaad cikin tsananin farin ciki da mamaki,bai yi magana ba, sai su Sarkin ya?i Ra'uf ke ta maimaita kabbara

Babu jumawa suka gabatar da sallar asuba da ake cikin lokacinta,duk da kasancewar akwai waWanda suka raunata nasarar ya?i bata ba su damar jimami ba

Shugaban dakaru Amjad ne ya jagoranci sallar,kafin ya tayar da sallar sai da ya aikawa Kazuzi wani kallo,shi kam Kazuzi abin ma dariya ya so ba shi,ya matsa kusa da ?aton kogin da yake kusa da filin da suka yi ya?in ya fara wanke duk inda jini ya Sata a jikinshi

Bayan an idar da sallar Liman ya mi?e ya yi jawabai sosai,na nuna tsantsar farin ciki da godiya ga Allah da wannan nasara da ta samu fiye da yadda suke tsammani a rayuwa,da godiya da yabo da jinjina ta musamman ga sadaukin sadaukai Kazuzi wanda ya bayar da kaso mai yawa don samun nasarar ta su,ba shi kaWai ba,da yawan dakarun ma sun nuna jinjina da yabo ga Kazuzi da yake gefe kaWan da su, kanshi a ?asa ba tare da ya kalli kowa ba

A nan ne liman ya sanar da mutane Kamar yadda aka saba bayan Wagawar rana za'a nufi komawa cikin Tayaar,amma kafin nan za'a duba maya?an da suka ji ciwo a yi musu magani

Hakan kuwa aka yi,a cikin maya?an da aka yi wa magani har da Kazuzi, wanda aka yanke shi a gefen kafaWarshi,mai maganin ya tsorata sosai, saboda ya ga alamun akwai dafi a jikin takobin da ta yi wannan Wanyen aikin,amma saboda jarumta da juriya ba lallai a gane hakan daga yanayin Kazuzi ba

Yana zaune yana ?arasa cin abincin da aka kawo masa, kamar wanda aka ce Waga kai,ya hango dakare Amjad yana isowa inda yake,Wauke kai ya yi kamar bai ganshi ba,ya cigaba da cin abincinshi,dakare Amjad ya ?araso wajen ya zauna,amma kafin ya ce komai ya ji muryar Kazuzi yana magana

"To yanzu yaya ka ji?wacce nasara kake samu idan ka kai min hari?

Menene ribarka idan ka yi makirci ka kashe Kazuzi?"

Duk da Amjad ya girgiza da yadda ya gane shine ya yanke shi,don ya canja kaya lokacin,kuma ya rufe fuskarshi,amma ya dake ya ce"har yanzu kana jin za ka cigaba da zama a cikin garin Tayaar tare da mu?

Har yanzu kana nufin shishshigin da kake yi kana samun mummunan sakamako bai ishe ka ba?

To ka cigaba,na yi maka al?awarin watarana sai ka samu mutuwa muddin ina raye"

"Kasancewar ka a raye ra'ayin Kazuzi ne,ba na shakkar kashe ka a bainar jama'ar da ka saka fuskar mutanen kirki kana yaudarar su suna yi maka kallon na gari, saboda ni ba munafuki bane, irinka"

Amjad ya ce"kai ba munafuki bane,sai kafirci ko?

Kai yanzu don Allah ba ka ji kunya ba muna sallah kana gefe kana kallon mu?"

"Da me sallah ta zata ?are ka dattijo?"ya faWa yana kallonsa,don tun Wazu maganar da yake yi ko sashen shi bai kalla ba

Irin yadda ya tsare Amjad da idanu ya sa hantar cikin Amjad Win ta kaWa,wani kwarjini da kamala ta musamman ya ga ya ?ara,hakan ya sa bai sake magana ba,shima dama Kazuzi tuni ya watsar da lamarin shi ya cigaba da abin da yake gabanshi

Da Wagawar hantsi suka bar wajen,bayan sun kwashe shahidansu sama da ashirin da rundunar Haura ta ?arar musu






*DAULAR KAIZUR*


Tunda aka rufe kuyanga Munaya tsawon kwanaki uku kenan ana yi mata sabon horo,don abu Waya ake bu?atar ta faWa,amma hakan bai yiwu ba,shine inda Yarima Sahal yake,amma har yanzu babu amsa

A Sangaren yarima Jamal ma za mu iya cewa babu sau?i, saboda duk yadda su sarki Mu'iz suka so jin wani abu daga gare shi hakan ya ci tura,sai nanata musu yake yi cewa da MASARAUTAR KAIZUR da duk abin da ya shafe ta baya gabansa,ba shi da lokacin Satawa akan neman mulkin kaizur,wanda a bayyane yake,babu adalci da bin dokar addini yadda ya kamata a masarautar

Yau ma Yarima Zaffar ya ziyarce shi,sai dai yau ziyarar a fusace yake ba kamar farko ba, cikin Sacin rai ya dube shi ya ce"Jamal!

Baka da hanyar kuSucewa kamar yadda kake tunani

Wacce mace ce wadda kuke haWuwa lokaci zuwa lokaci kuna tattaunawa da wani zaurance wanda ba'a ganewa?ko kana tunani babu mai ganinka a ?atuwar masarauta irin kaizur?

FaWar gaskiya shine yiwa kanka da iyalanka adalci,akasin haka kuma kamar jefa kanka cikin masifa kake yi kawai,da ?ara bar wa ahalinka abin faWa a kaizur, yanzu gaya min, menene shirin ka na gaba?me ka shirya a baya? wacece wadda kuke keSewa da ita kuna magana?"

Kwarai da gaske yarima Jamal ya shiga tashin hankali fiye da tunani saboda bai taSa tsammanin wani zai iya gano wani shirinsa har haka ba,amma hakan bai saka ya rissina ba,ya ce"kai ka san kana da wannan hujjar kuma ka zo nan ka turke ni?a maimakon a ganni a wajen rataya?"

Yarima Zaffar ya dube shi ya ce"ba zuwa na yi nan don ka yi min izgilanci ba,Wan yayana da ka saka aka sace,ina aka kai shi?"

Yarima Jamal ya girgiza kai ya ce"ba za ka samu amsa ba, saboda nima kaina ban san abin da ya samu yarimanku ba,a ta?aice ma dai ba ni na saka a sace shi ba,ku cigaba da bincike ko ku Wauki mataki akaina,ba wannan ne karo na farko da kaizur ta yanke hukunci cikin fushi da son rai ba,kuma ba sai ka maimaita min ba,na san Sarkin ku ba ya nadama"

Kalmar ta yiwa yarima Zaffar zafi,amma bai iya yin magana ba sai kallo da ya bi da Jamal da shi, Yarima Jamal bai damu ba,ya sake duban Yarima Zaffar cikin tsananin tsana ya ce"amma tabbas akwai ranar ?in dillanci Zaffar, musamman akan baiwar da kuka kulle tsawon shekaru ashirin kuna gana mata azaba,don matsayi da iko yana hannunku,idan ba ka da abin faWa za ka iya tafiya "

Bai yi musu ba ya mi?e yana kallon Jamal da rinannun idanunsa, Jamal ma ?yar yake kallonsa,a fusace ya ce"za mu haWu nan gaba,zan dawo"daga haka ya juya ya fice daga Wakin fuuuu, Yarima Jamal ya bi shi da mugun kallo cikin tsana







*DAULAR TAYAAR*


Kamar yadda aka saba na al'ada idan aka yi nasarar ya?i kaWe-kaWe da masu tsaron ?ofa suke ji daga nesa ne yake alamta musu nasarar ya?in da suka yi,hakan ya sa yau ma da zafi-zafinsu suka busa ?arar sarewa, cikin ?an?anin lokaci gari ya hargitse da tsananin farin ciki,duk da cewa bai kai na nasara akan Baruda ba,mutane da yawa suka gabato don taryar maya?ansu gwaraza

Da yawan mutane sai suka koma kallon Kazuzi da mamaki, musamman da wasu suka fara ?yan?yaso shine ?arfin nasarar ya?in ba tare da an wahala ba sosai,an yi masa magani a gefen kafaWarshi an rufe ciwon,kanshi a ?asa kamar yadda ya saba,kusan shine a gaba-gaba bayan sarki Iyaad,Sarkin ya?i Ra'uf,da badakare Amjad, shi kuma yana daga bayansu ,ya Waure gashinsa ya sake shi bayanshi

Da yawan mutane musamman yan matan da suka fito da kallo suka bi Kazuzi da ya wuce bai kalli sashen da kowa yake ba,sauran dakaru suka bi bayanshi, dama haka yake? kyakykyawa ne,ga cikar zati da kamala,kuma dama sun ji labarin ko da ya kasance bawa har yanzu bai yarda ya rissinawa wani an wula?anta shi ba,dama a bayyane yake Kazuzi baya tsoron mutuwa

Ana sauka kai tsaye Kazuzi Wakinsa ya wuce ransa yana Saci,ya yiwa gimbiya al?awarin karSar musulunci kafin ya dawo daga ya?in nan,amma sanadiyyar Amjad ya fasa,bai taSa zama ya yi tunanin Waukar wani mataki akan wani ba sai Amjad

Bayan ya yi wanka ya sauya kaya yana jin ana ta nemanshi a fada amma ya yi banza,har zuwa lokacin da abokinsa khidr ya shigo yana nemansa,amma sai ya yi kamar barci yake yi,dole khidr ya juya ya koma, saboda masarautar Tayaar masarauta ce da take da tsananin bawa wanda yake ?ar?ashinta ha??insa

Yana nan kwance ya lumshe idanu ?amshin gimbiya Hayat ya ziyarce shi,da sauri ya buWe idanu ya zauna,idan ya ce bai yi kewarta ba ya yi ?arya,kai tsaye zai iya cewa tana Waya daga cikin waWanda suka shiga rayuwarsa wadda ba zai taSa mantawa da ita ba, tunaninsa ya yanke a lokacin da ta shigo Wakin da sallama

?aga kai ya yi yana kallonta, fuskarta ?awace da murmushi, sai dai jikinta ya yi sanyi ganin ciwo a jikinsa,ta ?araso ta zauna tana kallonsa, kafin ta ce"an ce kai ne gwarzon wannan ya?in,kai ne ka jagoranci wannan tafiyar, saboda kai ne ?arfin ya?in,na yi farin ciki sosai,amma kuma na ji babu daWi da na ganka da ciwo"

?an murmushi ya yi,ya ce"Barka da zuwa ya shugaba ta!

Ina fatan mun same ku lafiya

A yi min aikin gafara ya shugaba ta, ban samu nasarar sauke al?awarin da na Wauka ba"

Shiru ta yi tana bin shi da kallo, kafin ta ce "ko dai wani abu ya sake faruwa tsakanin ka da dakare Amjad?"

Kanshi a ?asa ya jinjina kai a hankali

Gimbiya Hayat ta harzu?a,a fusace ta ce"menene dalilin da ya sa ba za ka Wauki mataki akan shi bane?

Ko ?arfinka ya fi ne?

To tunda kai ba za ka Wauki mataki akanshi ba zan sanar da Abby komai,idan ya so shi sai ya Wauki matakin da ya dace"

?an murmushi Kazuzi ya yi,ya Wago yana kallonta tana ?o?arin tashi tsaye,ya ce"

Ya shugaba ta yaushe kika shirya jin labarin soyayyar Kazuzi da Malli ne?

Ni kaina na ?osa na ba ki tarihin"

Komawa ta yi ta zauna ta ce"ko a yanzu ma a shirye nake,amma na ga a gajiye kake,ga ciwo,zan bari sai gobe da safe,ya yi?"

Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, gimbiya Hayat ta cigaba da magana "bari na saka a kawo maka abinci"Kazuzi ya rissina kai ya ce"godiya nake ya shugaba ta"

Har ta kai bakin ?ofa sai kuma ta juyo tana kallonsa ta ce"wai ka san suna na ma kuwa?"bai amsa ba ya yi murmushi kawai, ita ma murmushi ta yi ta fice daga Wakin,ya bi ta da kallo yana lumshe kyawawan idanunshi

Washe gari da wuri ta tashi,bata san menene dalili ba amma ta ?agu ta ji labarin Kazuzi,ko da yake ta san dalilin ba zai wuce yadda ta fuskanci irin ?uncin da ya shiga a rayuwa ba,da kuma irin yadda ya rasa Malli Winshi da yake ganinta a matsayin komai nashi

Bayan ta kammala karyawa da ?afa ta taka har cikin lambunta, kuyangarta Huda tana biye da ita,bayan ta isa zuwa rumfar da take zama take hutawa Huda ta shimfiWa mata kilishin da take zama,ta zauna sannan ta kalli Huda ta ce"ki yiwa dakare Waya magana a cikin waWanda suke gadin lambun nan ya kira min Kazuzi,ke kuma ki je na sallame ki"Huda ta rissina ta ce"an gama ya shugaba ta, Allah ya ?ara miki iymani d tausayi"daga haka ta mi?e

9 / 11