Author : Lipton Girl Category : Romantic Hausa Novels
Ita kuma ta fito
"Hassina Bare na kawo maki ruwa ko"
Ae kuwa .kamar mai jira ta meki tsaye "Aa Umaa akwai wani aiki ne na taya ki???
"Ki barshi kwai yanzu nan zan kara aiki"
Da saure ta nufi inda taki
"Haba Umaa Ina zauni zan barki kiye aiki, Dan Allah kije ki huta ni zan girka abince"
"Aa ki ye zaman ki hakan ma nagode"
"Dan Allah Umaa ki dai na wanna zance inda Mahaifi ya tace ae bazan barta taye aiki ba
kima matsayin mahaifiya ta kiki Dan Allah ki barshi naye"
"Tau Allah yayi maki Albarka"
Umaa ta gwada mata abunda zataye aiki da shi Ae kuwa Hassina ta fara aiki
Bangaren Abba kuwa ya fito wanka Inda Umaa ki bashi lbr Hassina tana kitchen tana girki
"Haki ka Mubarak yana wasa da wanna Matar da Allah ya bashi gata da kirki "
"Hmm Alhj.kinan ae yanzu idan yazo sai kaye magana da shi"
"Ae kam haka Za'aye "
Hassina kuwa sai saure ta Kai ta gama girki kafen Abba ya shigo tana gama wa ta saka
a food flask
Dakin baki ta shiga taye alwala taye sallah Abba da Umaa basu shuko ba sai da sukaye
Sallah ...ko da suka sauko Hassina Har ta gama abince zauna wa sukaye suka fara ce
"Kai gaskiya Wanna yarinya ta iya girki sosai"
Mummy ta kalle shi "Allah kasa dai bata fine ba"
Dariya Abba yayi "Haba taya Wata zata fi matata jya girki"
Hasina kuwa ta gama sallah sai tunane taki ye meyasa Abba ya ki son magna da Mubarak
Allah kasa dai Lafiya
Mubarak ni ya shigo da sallam lokacin Hassina ta fito daga daki ganin Abban sa ya saka
ya washe Baki
"Abba saukan yaushi Barka da zuwa"
Ko kallon sa baiye ba shikuwa ya San dai ba abunda yayi ma abban sa
Abubakar ya tashi ya zauna busan kujera dakin falon
"Naji dadin ganin ka don ina son magana da kai"
Fuska sa ba walwala
Hassina ta zauna kasa Haka ma Mubarak
Gyaran murya Yayi
"Waton Mubarak a gaskiya abunda ka aikata banje dadin sa ba Sam kuma ka bani kunya
sosai ban taba tunanen Dana Wanda na Haifa Zai iya aikata hakan ba"
"Abba meya ki faruwa ne ban fahimce ka ba???.....
"Dukan abun da ka aikata ina Sani da shi Abunda kaye ma Hassina Sam baka dace ba
taya zaka Saki ta don ta tai maka ma makawce Yar ta ka kuwa San irin hakin da mutum yaki
da ga makwabcin sa ,kama ta yayi Kaye alfahare da ita ba wai kasa ka mata da saki ba
Sam bai dace ba kuma bare kaji da nece iyayen Hassina bazan bare ka dawo da ita ba"Duk
maganar da Abba kiye kansa na kasa waton shiyasa tace ya kawota don ta kai karasa ga
Abba ..ba kome ae zasu koma gida
"Da kuma abunda kayi mata jiya,...Ki.Hasina kinye kuskure bai kamata ace a matsayin ki
na matar aure ba ki tsaya da wani har kina ye masa Dariya ki Sani cewa mu maza muna da
kishin abunda muki so ...ama ba irin kishin Mubarak ba domin shi Mubarak Kishin sa na
Hauka ni " .dago kansa Yayi ya kalle Abba
Hassina kuwa ko kadan bata ji dadi ba meyasa Zai zo ya gaya ma Abba abunda ya faru
jiya
Kuna jina ko
"Eh Abba Muna saura ranka "
"Hassina abun da zan Ce maki shine ki kara Hankuri domin shi zaman aure zaman hankuri
ni"
"Insha Allah Abba nagode sosai da nasihar da Kaye man"
"Yauwa,kai kuma Mubarak ka guje furta maganan saki nan kuma ka kara hankuri zama
da Matar ka sa'an ba kome a ki zuwa ana fada ma iyaye ba kamar jiya daka zo ka gaya ma
mahaifiyar ka shi aure sirri ne don haka ka reki sirrin auren ka da kuma tarbiyar gidan ka
.....don haka zaku iya tafiya na sallameku
Tashi sukaye Suna ye ma Abba godiya suka fita Gidan.........
*muje zuwa Mubarak yana tunanin Hassina ta kawo karan shi ,ita kuma bata je dadin da
ya gaya ma mahaifiyar sa ba Tau ko me zai faru keep flowing me*
*Lipton girl*
♠ *KISHI*
♠ *Ko Hauka*
```STORY AND WRITING BY```✍
*KHADIJA UMAR S. DOGARAI(Lipton Girl)*♠
*Marubuceyar*
1. ~Auren Bazata~
2. ~Dr. jameesha~
3. ~Rayyana~
4. ~Bani na kashe su ba~
5. ~Nuriyya~
~And Now~
~KISHI KO HAUKA~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*Jeeda Ina yin ki over*
*kuyi hankali da me Wan nan number 0810 770 7692,yana amfani da wata dama nasai da
books d'in yen Golden pen macuci ne book dinmu free ne except raggon namiji 2 so Plss be
careful*
*A short story*♠
°°°°°°°°°°°°°°
~page~ 2⃣0⃣>2⃣1⃣
Tunda suka shiga mota ba Wanda yace ma Wani kala a hakan suka shiga cikin gida Mubarak
ya tsaya falo ita kuwa Hasina ta shiga daki ranta a bacci.... Zauna wa tayi kan gado Tana ta
kaicen irin wanna halin na mijin na ta ace mutum Duk abunda ya faru Sai ya gaya ma iyayin sa
yanzu Allah ka dai ya san irin kallon da sukiye man... Ni kam naye mamaki su Abba suna ta
tambaya na yah mijina ashe ga abunda ya aikata Dan karamen tsaki taja ta kwanta kan gado
don marata tana ye. Mata ciwo
Shi kuwa kan sa ya aza kan kujera ya lumshe ido "Meyasa Hasina zata kai karan sa gurin
Abba Tunda yaki da Abba bai taba ganin fushin sa ba irin na yau"
Tashi yayi ya nufi upstairs da karfe ya ban kado kofa Sai da Hassina taje tsoro ta tashi da
karfe
"Hubby lafiya??
"Ye man shiru Munafuka banza Idan kika zaunar dani kika gaya man cewa abunda naye maki
baki je dadi ba Ae Sai na baki hankuri shine kika je ki ka gaya ma Abba ko, Tau sanun ki Abba
yayi man fada hankalin ki ya kwanta ko..... Nikam naye mamakin kince Na kai ki inda Umaa Har
da cewa kinye missing inta ashe duk na muna fuce ne ki kam kinje kunya"
Kallon sa taye da idanun ta wadan da suka ye ja sosai
"Yanzu Hubby ne ka ki cema Munafuka??????
"Ance maki din mi zakiye ne?? Ae gaskiya na fada kuma kin bani kunya sosai Ba zaki iya reki
abunda da naye maki ba Har sai kinje inda Su Abba kin gaya masu"
Girgiza kan ta taye don taje ya fara Mata ciwo Ga zuciyan ta sai bugawa ya kiye da saure
saure
Lumshe idanun ta taye tana ta kai ce irin wanna halin na mijin na ta
"Ita Meyasa bata ye masa magana ba yaje ya gaya ma Umaa abunda ya faru jiya sai ita da
bata ma san taye Abu ba yana kiran ta da Munafuka wanna wane irin Abu ne"
"Auw Ni ki ka mai da Dan iska kika kyalene Ina zuba Haukata ko .. Zaki gani kuren ki"ya fita
daga dakin gurin motar sa ya nufa ya shiga ya bar gidan
Hasina kuwa a ranta tace "Allah kasa ba Umaa zai je ya gaya ma ba kuma"
Blanket ta jawo ta lulube jikin ta don Har sanyi taki je
Tafe 40mnt tana cikin Blanket jikin ta sai rawa ya kiye da gudu ta tashi ta shiga toilet tana
kwara Amai mai yawa taye.. Ni kai na sai da na tausaya Mata Gashi tana ganin jire da kyar ta
samu ta kai kan Bed inta ta rufe jikin ta da Blanket Ji kinta sai rawa yaki ye musan ma Idan ta
tuna da abunda Mubarak yace dazu
Ta ye kussan 1hour tana kwance da kyar ta iya tashi ta shiga kitchen Ta fara dafa ma Mubarak
abince tana ta fiya tana dafe kan ta a hakan ta samu ta gama masa abince tana gama wa ta
shiga dakin ta ta rufe jikin ta
Mubarak kuwa Har ankaye magrib bai dawo ba Gashi bai sa ba kai dare bai dawo ba.. Wayan
ta taye Mata nissa tana son ta Kira shi taje lafiya
Har akaye isha bai dawo ba a hakan ta daure ta dauko Wayan ta. ta Kira shi ama bai daga ba
saki kiran sa taye still bai daga ba na ukkun da ta Kira taje Wayan a kashe
Hankalin ta kuwa ba karamen tashi yaye ba kar dai ace Wani Abu ya same shi??
Messg ta shiga rubuta masa "My Hubby pls am sorry pick my call "
Ta tura masa ajiye Wayan taye kusa garita ta lumshe idon ta bacci yayi awon gaba da ita
Mubarak kuwa bai dawo gida ba sai kusan 10 na dare abince da ya gani kan Dinner ya shiga
fara duba wa ko ba'a gaya masa ba ya san Hasina bata ce abince ba ama don misikilan ci na
shi ya deba ya fara ce yana gama wa ya kai plate kitchen Bai ma shiga dakin ta ba ya wuce da
kin sa ya saka Lock koda ta zo taje shi a rufe ta wuce da kan ta
Hasina kuwa sai sharan baccin ta ta kiye bata falka ba sai karfe 5:00am Reki kan ta taye don
Har yanzu yana ye Mata ciwo duba gefi taye bata ga mijin na ta ba
"Hubby bai dawo gida ne ba ko kuma bai shigo daki na ne ba??
Wayan ta ta dauko ta kirasa ama a kashe ajiye Wayan taye da ta tuna da bataye sallah jiya ba
ta shiga ranka wa taye asuba ta karanta alkur'ani tana gama wa ta shiga kitchen ta fara daura
masa break don taga yace abince
"Hmm Hubby kinan kasan bance abince ba ama ba ka damu ba Gashi ko daki na baka shiga
ba balan tana kaga bani da lafiya"
Wasu Hawaye ne suka zuba a idon ta goge wa tayi ta cigaba da aiki bayan ta gama ta haura
zuwa dakin sa murda kofa taye ama taje ta a rufe knowing ta fara ye "Hubby pls open the door
am really sorry "
Shi kuwa lokacin ya fito daga wanka. Yana jinta ya kyaleta
Ae jiya daki ka ga ban dawo ba, baki Kira ni ba sai ynz zaki zo kiye man magana banza
Wayan sa ya duba ya ganta a kashe ganin bashi da charge ya saka cikin pocket in sa Idan yaje
office sai yasa charge
Kasa ta zauna don ta gaje da tsayen
"Hubby na san kana jina Dan Allah kayi Hankuri hakan ba zai saki faruwa ba"
Shiru bai ce Mata kome ba Har sai da taye 10mnt a gurin tashi taye ta koma nata dakin shi
kuwa ya fito bai ma tsaya cen abince ba ya wuce war sa kwai
Hasina kuwa tana shiga daki ta Kama Kuka "Meyasa zaka ye fushi dani Hubby Kasan irin
sonda nakiye maka kuwa saboda irin son da nakiye maka ne wata rana ko Kaye man laifi naki
kyaleka why kaki ye man haka? Baka ma damu da ka gani ba Har zaka wuce gurin aiki ba tare
da ka ga fuska na ba baka san irin halin da naki ciki ba"
Kuka taye sosai Ita ka dai ba mai lalashin ta da kyar ta tashi ta hau kan gado
Sai Kuka ta kiye
Ta jima tana Kuka Har kusan 10 ganin kukan da ta kiye bashi da amfane ya sa ta tashi ta
watsa ruwa ta sauka Kasa ta kuna TV kallo ta kiye ama bata fahimtar kome tafi 2hours TV
yana aiki ama Sam Hankalin ta Baya nan Wayan ta dauka ta Kira Hubby ama a kashi tashi
taye ta fara girka masu shinkafa da miya shinkafa ta fara daura wa sa'an ta daura tafashin
nama Gurin mai (oil) ta nufa ta dauko cikin Wani Bowl ta fara tafiya ama bata san inda taki
saka kafan ta ba faduwa yayi ya fashi da saure ta ja Baya ta kashe Gas duka wa taye ta fara
cire glass ta saka a dustbin jin Kara Wayan ta ya sa ta dago kanta sai murmushi ta kiye may be
Hubby ne ya ki ra ta Hankalin ta yana kan Waya bata san lokacin da ta saka kafan ta ciki mai
(oil) ba Ae kuwa sai gata Kasa
Rufe idon ta taye don Wani irin zafi da taki je ganin jini yana zuba a kafan ta ya bata mamaki
sosai ta dai san ba period taki ye ba to jinin mene?? da rarafe ta nufe gurin wayata ganin ba
Hubby ne ba taje Wani irin ta kai ce kiran sa tayi Ta kuwa ye sa'a ya shiga sai dai bai daga ba
sai a karo na biyu ya daga wayan "Hello Hubby"
"I am busy Ina gurin Meeting "
Bai tsaya ya jira me zata ce ba ya kashi wayan wane irin ta kai ce ta jiya ta jifar da Waya sai
da ta fashe....
Ta rasa me zata ye ga jine a jikin ta ga duhu duhu da taki gani.........
*Muje zuwa*
*Lipton girl*
♠ *KISHI*
♠ *Ko Hauka*
```STORY AND WRITING BY```✍
*KHADIJA UMAR S. DOGARAI(Lipton Girl)*♠
*Marubuceyar*
1. ~Auren Bazata~
2. ~Dr. jameesha~
3. ~Rayyana~
4. ~Bani na kashe su ba~
5. ~Nuriyya~
~And Now~
~KISHI KO HAUKA~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*kuyi hankali da me Wan nan number 0810 770 7692,yana amfani da wata dama nasai da
books d'in yen Golden pen macuci ne book dinmu free ne except raggon namiji 2 so Plss be
careful*
*A short story*♠
°°°°°°°°°°°°°°
~page~ 2⃣1⃣_2⃣2⃣
Ta rasa ya zata yi ga shi tana ganin jini yana zuba a jikin ta ga duhun da take gani kuma baza ta
iya tashi ba dafe cikin ta tayi don Wani irin zafi taki ji
"Inallilahi wa'ina illahi Raji'un ya Allah ka fidda ni cikin wanna halin ya Allah ka kawo wanda zai
tai maka min!"
Abun takaici ko mai gadi bata da balan ta nata Kirashi ya kai ta Asbt
Tana cikin Wanna Hali sai ga Muktar ya shigo cikin gidan yana sallama!
Hassina na jin murya sa taji Wani sanyi
"Muktar pls come and Help me "
Dube-Dube yake yi ko zai ganta can ya hango ta kasa kwance ya karasa kusa da ita
"Subuhalilah yaya me yake damun ki ganin jini a jikin ta ya sa ya kauda Kansa"
Ina zuwa Aunty bari na Kira Amina da gudu ya fita waje
"Ke Dan Allah kiyi sauri ki shigo cikin gida kin tsaya kina wani yanga Aunty bata da lafiya"