Author : Lipton Girl Category : Romantic Hausa Novels
"Oyah ka ce abince don nasan Tunda ka rabu da Hasina kome baka ce ba"
Shiru yayi bai ce kome ba har tsawom 15mnt
Mubarak "lafiyan ka klau kuwa ka saka abince sai tunanen karya ka kiye"
Dago kan sa yayi Umaa Tunanen karya fa kika ce??
"Eh manah to in ba tunanen karya ba na dai san ba zai wuce Hasina kaki tunane ba kuma
baza ta dawo ba domin auren ka da ita ya riga da ya kare sai dai wata kuma ba dai Hasina ba"
Kallon ta yayi da idanun sa wadan suka ye jaa sosai
"Umaa idan aka mutu a na dawo wa??
"Wanan wace irin tambaya ce ae ka fi kowa sanin idan an mutum ba'a dawo wa"
"Ji naki tamkar na mutum domin an raba ne da ruhi na"
"Ae kuwa sai a kai ka gidan ka na gaskiya"
"Umaa meki ki nufi da hakan? Kina nufin yanzu na rabu da Hasina"
"Ba ina nufi ba hakanan abun yaki auren kai da Hasina sai dai lahira ko kuma I kon Allah "
"Haba Umaa ki dai na Wanan magana manah aure na da Hasina ae ba za'a rasa yanda
za'aye ta dawo dakin ta"
"Tabas Mubarak na tabata yau baka da Hankali domin mai Hankali ba zai ye Wanan magana
ba... Don haka ka tashi ka bani guri "
Haka ya tashi ya fita sai yawo ya kiye cikin mota.. Wani gida naga ya shiga da sallama ya
shiga....
Zaune yaki kan tabar ma yana karanta da Mutane da ka gan shi Kasan mallame ne.... Ganin
Mubarak ne ya bashi mamaki
"Kujera ni zan ye magana da bako"
Tashi sukaye Mubarak ya zauna ..
"Allah ya gafar ta mallam na same ka lafiya"
"Lafiya qlw.. Mubarak yau kai ne a gidan namu.. Kuma Meya same ka duk ka rame
haka????
Nan fa ya shiga bashi labaren abun da ya faru
Shiru yayi
"Haki ka yanzu ka rabu da matar ka domin Kaye mata saki daya har ukku... Don haka ba
maganar aure a saka nin ku...!! Shiyasa aki cewa kafin ka furta saki to Kaye tunane mai zurfi
Ana son idan zaka saki mata ka saki ta idan ta aikata Babban kuskure, ama ga Dukan bayanen
ka ba wani Babban dalile ne ba kwai kana furta saki a lokacin da ka ga dama........
Shiyasa da za'a bada saki aka ba Namiji, domin Namiji yana da Hankali yana da tunane sosai,
don da za'a ba mace saki to da zata iya ye maka saki ya kai goma ama kai abunda kayi kamar
mace don haka yanzu babu aure tsakanin ka da Matar ka"
"Allah ya gafar ta Mallam babu wani abu da za'aye Wanda zai sa na koma ga matata domin
Ina matukar son ta ita ma din tana sona sosai"
"Duk son da kuki ye ma juna ba zata dawo gari ka ba har sai in taye aure ta fito sa'an fitowar da
zataye ba Wai don son ranta ba, ina nufin auren kashi wuta nasan Kasan ko me naki nufi"
"Dan Allah mallam ya isa Hakan... Ae na san da Wanan Nazo gari ka ina ye maka magana
ka gaya man idan akwai wata hanya na mai da matata shine kaki kawo man wani zance ta ye
aure ne bani da Hankali ne da zan bata taye aure har wani ya sadu da ita... "
Meki wa yayi tsaye Mtswwww
"Nabarka lafiya"
Ya fita daga gidan fuuuuu
Mallam kuwa yana mamakin irin Wanan hali na mubarak
*pls share*
*lipton girl*
♠ *KISHI*
♠ *Ko Hauka*
```STORY AND WRITTEN BY```✍
*KHADIJA UMAR S. DOGARAI(Lipton Girl)*♠
*Marubuceyar*
1. ~Auren Bazata~
2. ~Dr. jameesha~
3. ~Rayyana~
4. ~Bani na kashe su ba~
5. ~Nuriyya~
~And Now~
~KISHI KO HAUKA~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*Sadaukar wa ga*
*Khadeeja z*
*Sumayya dugumaje*
*Ummu Haneef*
*Hauwa'u Haliru*
*Safiya Muhammad*
*Nafisat*
*Da dai sauran su duk ina jin dadin comment in ku* *love you wujega wujega*
*kuyi hankali da me Wan nan number 0810 770 7692,yana amfani da wata dama nasai da
books d'in yen Golden pen macuci ne book dinmu free ne except raggon namiji 2 so Plss be
careful*
*A short story*♠
°°°°°°°°°°°°°°
~page~ 3⃣6⃣_3⃣7⃣
Mubarak kuwa ya koma kamar wani mahaukaci kullum yana zuwa wajen malamai yana
tambayar su amma duk amsar su da suke bashi ka daure mishk kai kansa ya daura kan sitiyari
domin zuciyar sa tana yi masa wani irin ciwo wanda shi kan sa ba zai iya missalta wa ba
"Na cuce kai na da kai na, na rabu da mata ta saboda saunanci irin nawa... Yanzu ya zanyi ba
zan iya rayuwa ba sai da Hasina gashi Ana son a raba ni da ita...!! Gaskiya ba zan yar da ba
domin kuwa ina son Hasina sosai "
Tada mota yayi bai tsaya ko ina ba sai gidan su Hasina
Zaune suke kan Dinner suna cin abinci duk da Hassina ba wani cin abincin take yi ba..
Hakalin ta yana ga Hubby ko yaci abinci???
Tana cikin Wanan tunanin sai ga shi ya fado bako sallama
Dad ne ya tashi tsaye
"Mubarak kana da Hankali kuwa Meya kawo ka gida na??? Ka shigo mini gida bako sallama "
"Ayi hakuri Dan Allah a bani mata ta wlh ina son ta"
"Kai ban son iskan ci kana jina ko bana son iskanci Wannan kalmar matar ka ta fita daga
bakin ka domin yanzu ba matar ka bace ka riga da ka tsinke igiyar auren ku don haka ka fita ka
bani guri kafin nasa a bata maka rai"
Da sauri ya karasa kusa da shi ya rike masa kafa"
"Na yarda duk abunda zaka yi mini zaka iya yi... Amma dan Allah kada ka raba ni da mata ta "
Yaya salim dake zaune ya tashi ya riko masa Riga
"Ina jin yanzu nan Dad yace kada ka sake cewa matar ka ko??? Wai kai Meyasa baka da
Hankali sakaran banza... Naushi ya kai masa ga Baki
Hasina dake tsaye tayi saurin karasowa.
"Haba Yaya Me yasa zaka naushe shi jifa yanda jini ke fita a jikin shi"
Tana kokarin goge masa
Riko ta yayi "ke bana son iskanci ai nan naga kina cikin ciwo ya Kara miki wanin saki har kike
tausaya masa"
"Yaya Tun ina karama kake ce mini Duk abunda akayi mini kada na saka shi a rai na na
barwa Allah komai shi zai magance mini matsala yanzu kuma Meya same ka pls ka kyaleshi...!
Ta juyo kan shi
"Pls Hubby ka koma gida"
"In koma gida fa kika ce?? Taya zan koma gida ba tare da ke ba??
"Hubby dole ka koyi zama kai kadai domin yanzu mun riga da mun rabu "
Tana magana tana kuka
Rike Hanunta yayi "pls ki daina fadin mun rabu.. Ba zamu rabu ba ni dake mutu ka raba... Ba
wanda ya isa ya raba mu "
Kallon sa tayi
"Amma ai ka riga da ka raba mu, zama na da kai ya zo karshe shawara da zan baka pls kada
ka sake zuwa gidan nan domin yanzu ba muda wani Alaka da kai... Kayi auren ka fatan da
zanyi maka Allah ya baka mata mai hankuri wanda zata jure kishin ka"
Hawaye ne suka zuba a idon sa
"Dan Allah ki dai na Wannan maganar aure ba wacce zan aura kece mata ta ke kadai dan
Allah ki dawo dakin ki"
Salim kuwa ganin idan ya kyalesu haka zasu dame su da surutu ya saka ya ja hanunsa ya
kai sa waje "kada ma Kayi tunanin cewa nan zaka kwana kamar yanda Kayi kwanakin baya
domin yanzu duk abinda zaka yi ba zata koma ba ko da kashe kan ka zaka yi sai dai Kayi
amma ba inda zata je wawa kawai" Ya rufe get da karfi sai da mubarak ya razana Shiga yayi cikin motar sa ya bar harabar
unguwar domin ya san Wannan Karon salim ba zai bar shi ya mai da matar sa ba.......
*pls share*
*lipton girl*
♠ *KISHI*
♠ *Ko Hauka*
```STORY AND WRITTEN BY```✍
*KHADIJA UMAR S. DOGARAI(Lipton Girl)*♠
*Marubuceyar*
1. ~Auren Bazata~
2. ~Dr. jameesha~
3. ~Rayyana~
4. ~Bani na kashe su ba~
5. ~Nuriyya~
~And Now~
~KISHI KO HAUKA~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615
*Rayuwar Duniya sai da Hakuri.. Idan baka saka Hankuri ba kai kan ka baza ka je dadin Duniya
ba*.
*kuyi hankali da me Wan nan number 0810 770 7692,yana amfani da wata dama nasai da
books d'in yen Golden pen macuci ne book dinmu free ne except raggon namiji 2 so Plss be
careful*
*A short story*♠
°°°°°°°°°°°°°°
~page~ 3⃣7⃣_3⃣8⃣
Mubarak kuwa kallo daya zaka ye masa ka fahimci yana cikin damuwa sosai domin ya rame ya
lalace ya dawo kamar wani Mahaukaci ya dai na cin abinci.... Ga gida duk ya haukace kamar
ba mutum a ciki.....
°°°°°°°°°°
Hasina kuwa yau kwana biyu da cika Idda. Ita ma kallo daya zakaye mata zaka fahimci tana
cikin damuwa domin Dukan su... Suna son junan su
Zaune taki tana karatun Alkur'ani Yaya salim ni ya shigo da sallama bata amsa ba sai da ta
idar da karatun ta sa'an ta amsa masa Gaida shi taye
Ya amsa cikin sakin fuska
Bakin gado ya kara sa ya zauna "Am Hasina ina son ki bani Aron hankalin ki... Kina jina
ko???
"Eh Yaya ina jin ka Allah kasa Alakaire ni"
Washe baki yayi kamar sabon ango
"Daman zanyi maki magana ne akan Abdul Tunda kin gama idda yana son aye maganar
auren ku"
Da karfe ta jeyo tana kallon yayan na ta "Yaya salim kana nufin aure???
"Sosai kuwa... To me zaki tsaya jira.. Kin san dai yanzu babu aure tsakanin ki da mubarak
ko, kuma na riga da naye magana da Mom da Dad kuma sun Amince da hakan don haka ki
shirya anjima zai zo ku gaisa naye masa bayane akan komi da ya faru daki kuma ya yarda zai
aure ki a hakan yaron yana da Hankali da natsawu ba irin tsohom mijin ki ba mubarak"
Hawayen da suka gangaro a idanun ta, ta share su "Gaskiya Yaya banji ina iya yen aure ba
yanzu ba duka duka yaushi na rabu da Mubarak da har zan kara wani aure????
"Wanan bai dame ne ba Tunda har Allah bai hana ba.. Banga abun matsala a ciki ba , idan
ba aure kika ye ba Allah ka dai ya san abunda Wancan Mahaukaci zai ye "
Yana gama magana ya fita ya bar ta cikin daki sai kuka takiye........
"Haba Yaya taya zaka zo man da maganar aure duka yaushi na rabu da Mubarak har za'aye
man maganar aure "
Kuka taye sosai kamar yau ne Mubarak ya saki ta............
Hasina na zaune ta buga Uban tagume Don Tunda Yayan nata yace mata Abdul zai zo
gaban ta ki faduwa... Tana cikin Wanan Tunanen sai ga Yaya salim ya shigo cikin daki
Zauna wa yayi kusa da ita
"Hasina Abdul yazo yana jiran ki a falon baki don haka ki tashi ki tafe... Kuma kina jina kada ki
sha masa toka domin auren ki da shi kamar an daura ne "
Bata rai taye "Haba Yaya Meyasa ba za ku bani lokaci ba.. na manta da Mubarak kafin
naye wani aure???
"Ae bazaki iya manta wa da mubarak ba don nasan har yau har gobe kina son shi kuma
idan aka bar ki ba zaki saki yen aure ba, Ba Wai duk maza halin su daya ba.... Shi din mubarak
Rayuwar sa da ban ta ki na taba ta Abdul zai reki ki amana kuma zakuye zaman fahimtar juna
ba irin zaman da kiki ye da Mubarak ba......! Don haka ki tashi ki tafe" Fita yayi daga dakin.... Ita kuwa sai da taye kuka daga bisane ta tashi ta wanki fuskan ta
Dauko Hijab ta saka Kitchen ta shiga ta dauko kayan mar are ta saka a plate da sallama ta
shiga cikin falon.... Abdul kuwa yana jin muryar ta ya dago kan sa... Idanun sa ne suka sauka
akan kyakyawan fuskan ta... Ga sura da Allah ya bata a ransa kuwa yace ina ma ace tun farko
ni na aure ki.......
Kara sowa taye ta ajeye Plate a dan karamen teble da ki cikin Falon Har kasa ta Gaida shi
"Sanu da zuwa Yaya Abdul"
Kallon ta yayi
"Yauwa, na sameki lafiya??
"Lafiya qlw"
Kan ta yana kasa
"Haba ki tashi mana ki zauna"
Ba musu ta tashi ta zauna ama duk da hakan kan ta yana kasa don bata son hada ido da shi
Gyaran muryar yayi
"Kiye hakuri nasan na ta kura ki na saka ki fitowa"
"Ba kome Yaya Abdul "
Yaya Abdul kuma???
"Eh manah Abokin Yaya salim ae Yaya na ni"
Murmushi yayi "Mijin ki kuma fa????
Dago wa taye ta kalle shi a karo na farko da saure ta mai da kan ta kasa
"Baki bani amsa ba??
Dan karamen Murmushi taye wanda ya kara fitar da kyawun ta
"Ba Yaya bani..... To mene
"Yaya Abdul a dai na Wanan magana"
" Aa ba za'a dai na ba sai kin gaya man"
Gyara zaman ta tayi
"Ina son in gaya maka abunda ya faru dani kwana kin baya domin idan akace maganar aure
za'aye to ba'a son a boye kome"Tana magana ta na wasa da fingers inta
"Ohk ina jinki"
"Nasan ba zaka rasa sani abun da ya faru dani ba.. Ama hausawa suka ce waka ga mai ita
tafi dadi "
"Hakane"
"Sunan tsohon mijina Mubarak kuma yana sona sosai nima din ina son shi"
Dago wa yayi ya kalle ta suka hada ido..... Duk da bai ye magana ba tasan abun da yaki
nufi......
"Ama yanzu mun rabu da shi babu wata igiyar aure data rage a saka nin mu"
"Hakane Salim yayi man bayanin kome Kuma naje dadi da kika sanar dani da bakin ki.... Ina
fatar babu matsala akan auren mu ko?????
Shiru taye don ta san idan tace bazata yarda ba Yaya salim zai yanka ta
Kasa tayi da kan ta
"Allah ya kai mu lokacin"
Ya Amsa da Ameen
Nan suka dan taba Hira Yayi mata sallama ya wuce ita kuwa daki ta shiga tana rai ra kuka.......
"Eh Allah ya amshe Adu'an mu kuma idan so samu ne wani sati za'a daura maku aure Tunda
kinga ba Budurwa kiki ba ba wani biki