INUWAR KADDARA BOOK COMPELET BY MAIMOON

Author :  Maimoon Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 14

27K to 30K   out of 40K words

lokacin visiting ya kare, babu yadda zasuyi haka suka fito suka bar kawu lawal don yai jinyar abby dake bacci har ynx. Ko da suka fita ta ringa ware idanu ko zata gansa ammah shiru har suka tsayar da adaidaita suka bar bakin asibitin&

Suna isa gida kuma se ga en jaje sun fara shigowa don yi masu jaje, ita dai yasmin na shiga gidan daki ta wuce direct ta dauki wayar ta data bari cikin drawer din ta ta shiga dialing number din sa da har yau batai saving din sa ba, ko da ta kira ba ai picking ba hakan ya sanya ta aje wayar tana hade rai ta fita tsakar gida tai alwala ta tada sallah, idarwar ta ke da wuya taji wayar tata na ringing, da sauri ta nufi wayar tata ta dauka tana kallon numbern nasa at same time kuma juciyar ta na bugawa da sauri, picking tai ta kai wayar kunnan ta bakin ta dauke da sallama, nan daddadar murayar ta ta sauka cikin kunnan sa wanda hakan ya sanya shi lumshe ido yana me jingian a jikin motar sa  ya jikin babah? Hakeem ya tambaya cike da kulawa,  da sauki ta bashi amsa a takaice, daga haka kuma tai shiru don bata san ta ina zata ma fara yi masa godiya ba, can dai tace  na gode sosai Allah ya kara budi, Allah ya bada lada, Allah kuma ya saka da alkhairi har tana iya jiyo sautin murmushin sa kafin daga bisani yace  stop thanking me yasmin, just focus on dua Allah ya bama baba lfy ta amsa da ameen kafin tai masa sallama don jiyo muryar amma datai tana kwala mata kira don ta dora kalacan dare. Tana girkin abubuwa daban na mata yawo a xuciya, na farko yadda kaddara ta kara hada ta da hakeem, na biyu kirki da kuma tausayi irin nasa, na uku kuma yadda take kasa daina tunanin sa 24/7 koda tayi kokarin yin hakan, tabbas tana jin wani abu na daban a kansa, wani abu da bata taba ji akan kowa ba se shi... ko da ta kai ma su innah abinci sosai taji ba dadi tunawa da tai abby baya nan, nan da nan kuma xuciyar ta da tunanin ta suka koma gun sa,  ko yanxu ya farka? ta tambayi kanta, muryar maman saddiqa da ita saddiqar ce ya katse mata tunanin ta, cikin xuciyar ta tai hamdalah don tun daxu take son ta koma daki ammah innah ta hana ta wai ta zauna cikin mutane ba wai zama cikin daki mara haske ba kamar wata bokanya , saddiqa na yima innah da ammah jaje wanda da kyar ammah ta amsa don sam basa ga maciji da ita tun wani fada daya hada su akan dukan da taiwa yasmin ita kuma taje har gida tai mata rashin kunya wanda hakan yasa ko a hanya basa ma kallon juna don fadan har maman su saddiqar se da ya shafa ammah taje har gida itama tai mata diban albarka yanxu ma don ance inna ta xo ne da kuma albarkacin yasmin kuma mahaifin nata bana banza bane amma da duk su biyan ba abunda xe saka su taka cikin gidan. Yasmin ce ta ja saddiqa dakin su don tun wancan ranar da ta je office din wancan watsatstsen take ta so tambaye ta abu ammah bata samu sun hadu ba,  ya jikin abby yasmin? Saddiqa ta tambaya cikin kulawa,  Alhmdllh da sauki da muka baro shi ma yana bacci ne  Ohk toh Allah ya basa lfy yasmin ta amsa da ameen kafin kuma ta gyara zaman ta tace  ummm saddiqa wai wancan ranar da kika ce naje na kai wallet din da wani kalan response aka ce neh? Jimm saddiqa tai kafin tace waii gaskiya na manta don ni sanda ma aka turo sakon bacci ne a ido na, ammah na taho da wayar ay se ki duba ta fada tana me mika mata wayar, ko da tai arangama da email din sosai ranta ya baci ammah sam bata bari hakan ya nuna a kan face din ta ba don yana wuya ta nuna bacin rai akan face din ta duk da dai a ranta takan ji zafi wanda hakan ba karamun punishment bane wanda ta sabarwa kan ta dashi tun tana karama. Maidawa saddiqa wayar tai, saddiqa tace  lfy da wani abun ne? Ta fada tana kallon cikin wayar tata, gwalo ido waje tai kafin tace  kambuu wannan wani kalan mutum ne mara da ah? Kai amma ban so ma ace kin mayar ba da wallahi se mun gama masa azaba kan mu bashi tun da shi bashi da tarbiyar magana, ay maka magana jaka amman ko godiya babu? saddiqa ta kare maganar tana huci, murmshi yasmin tai aran ta tace  se kun ma hadu da shi sannan zaki tabbatar da hakan mikewa tai ta shiga laluban kudin da hakeem ya bata, sosai kirjin ta ya buga ganin ba kudin ba kuma alamun su, ita bawai batar kudin ba, questions din da zata amsa take gudu, sosai hankalin ta ya tashi ta shiga fiddo da kayan nata daya bayan daya, duk abinda take saddiqa dai kallon ta take kawai da mamaki. Wani hamdalah ta saki bayan ta jiyo tudun kudin cikin aljihun wata rigarta, da sauri ta ciro kudin tana kallo, ware idanu saddiqa tai tana kallon kawar tata da kuma abun da ke hannun ta, seda ta mayar da kayan da duka xubo kasa kafin ta koma mazaunin ta na daxu ta damkawa saddiqa kudin, with shock saddiqa tace  a ina kika samu duk wan.. da hannu yasmin tai mata alamar tai kasa kasa  zan miki bayanin yadda aka samu kudin daga baya Ammah dai kudin treatment din abby ne and I want you keep it with you the money is not safe in this house ta fada a hankali pleadingly, Shiru saddiqa tai tana nazarin abin da kawar tata ta ce mata kafin tai ajiyar xuciya tace  toh yasmin nasan ba zakiyi abin da ba shikenan ba I trusted u amma gaskiya ajiya kudi me yawa haka a agurina babban risky ne coz if akai finding out a gida na banu and bazan iya mentioning name din ki ba kin sani ta fada a raunane, shiru ne ya dan wakana na kusan 10 seconds kafin  yasmin din ta ce hakane kuma nima bazan so na saki cikin damuwa ba, don t worry xan aje a guri na ta kare maganar tana dan murmushi. Hararar ta saddiqa tai kafin tace  toh kinji nace bazan amsa bane ba? Ita dai yasmin bata ce komai ba se kallon saddiqa da take kawai da mamaki  ayy ina da banki na OPay se na kaima me pos ya saka kudin ammah fa bana anguwar nan ba daman gobe in muka je kasuwa ni umman mu zamu wuce sheshe gidan aunty murja se a saka mun acan daman akwai wani me pos da ya taba cewa yana sona toh nasan ma ba lallai ya amshi chargis ba ta fadi hakan tana tura kudin cikin kugun ta, ita dai yasmin se kallon saddiqa take don wayon ta is extraordinary dan bata bari sam kanta ya kulle zata samar da mafita, ana haka maman saddiqa ta shiga kwalla mata kira akan su xo su tafi, haka nan duka fito daga dakin duk su biyun, yasmin ta raka su har kofar gida tana masu godiya, ganin idon innah ne ya sanya ammah yin shiru ammah da se tai mata kacha kacha akan gayyatar mata saddiqa da tai cikin daki. Se gurin 2 sannan yasmin ta kwanta bayan ta raba dare tana yima mahaifin ta adduar samun lfy da kuma hakeem da ya taimake su, a cikin adduar ko har samun kanta tai tana fadin  ya Allah in alkhairi ne bawan nan naka Allah ka tabbatar da alkhairi a wannan lamari, in ko ba alkhairi bane Allah ka raba ta rufe adduar tata da adduar isthikara&


Still on free pages& ..



INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY)


By moon

Chapter 8: A Proposal She Wasn t Ready For& .


Washe gari friday ta tashi da safe kamar kullum tai duk gyaran gidan da dumamen abinci, yau sam ba tada niyar xuwa ayki don so take taje ta kula da mahaifin ta. Tana cikin juya ruwan zafi a cikin wani ribabben plass se ga ammah ta fito daga daki tana hamma kamar zata hadiyi babu, direct inda yasmin din take ta nufa fuskar nan tata da taci uban bleaching a hade  uban me kike har yanxu baki wuce ayki ba? Murya na rawa yasmin tace  daman-daman ina so in ce ko zaki fadawa mami abby ba lfy bazan samu damar xuwa ba se ya.. Marin data zabga mata ne ya sanya ta hadiye zancen nata tana yarfe hannaye, ammah na huci tace  dan ubanki so kike a kore ki a aykin koh me? Toh Wallahi ko mutuwa yai se kin je, dan haka xo ki wuce ko na kara miki wani kin san hali na, daman tun jiya ina ciki dake ta karashe maganar tana huci. Duk abinda ke faruwa innah bata sani ba har yasmin din ta bar gidan don Allah yayi ta da dan banzan nauyin bacci don tsaf se a sace ta bata sani ba. Tana isa bakin titi taga ba motar gidan mami a inda habu ya saba yin parking, wayarta ta zaro tana kallon lokaci taga 7:48 still da sauran lokaci, tana taye agun can se ga motar ta karaso hakan ya sanya ta yin ajiyar xuciya don ta dauka ya gaji da jira ne ya sanyashi ya tafi.  A gafarce ni yau na makara wlh kin san garin akwai sanyi sosai kuma abun mamaki duk da safiya ce yau amman na tarda go slow ya fadi hakan yana me figar motar da gudu.

ko da suka isa gidan a parlor ta tadda nazli da mami, har kasa ta durkusa ta gaishe su jiki ba kwari don har yanxu bata gama recovering daga marin da ammah tai mata ba, mami ta dube ta cikin kulawa tace  morning jasmine how s your night  Alhmdllh ta fada takaice, mami tace taje kitchen akwai breakfast dinki acan, godiya tai ta tashi tana jan kafa ta bar gun, mami ta maida duban ta kan nazli dake pressing phone din ta tace  je ki ki duba omair tun da ya dawo jiya be fito daga room din sa ba haka nazli ta mike tana turo baki don jiya se da ya kusan mammake ta akan ta batai masa knocking ba. Tana shiga parlon sa taga baya nan, don haka tai yunkurin nufa dakin da tasan definitely yana can, daidai ta taba handle din kofar se gashi nan ya bude kofar, sanye yake da wani hoodie white color wanda sosai yai kyau fatar sa me kyau da sheki ta kara bayyna wanda hakan ya sanya nazli furta  woow brother kaga yanda kai kyau kuwa? Ta fada tana kara admiring brothern na ta. Cikin dacin rai omair yace  what?  Ba komai u just look good ne as always ta fada tana turo baki, juya kyawawan idanun sa yai gamida sakin wani karamin tsaki kafin yace  what brought you here?  Ohh mami ce, she said I should call you tana downstai.. be jira ta karasa maganar ba yai banging kofar tasa wanda saura kadan ya hada da nata face din, ayko ta koma gun mami tana hade rai kamar wanda aka daka. Cikin natsuwa yake taka stairs din idanun sa na kan smartphone din dake hannun sa, fuskar nan tasa a hade but looking handsome as always. Zama yai a kasa kusa da kafar mami ya gaida ta cikin harshen Turkish despite ya gaishe ta daxu da subh, amsa masa tai cikin natsuwa tace  are you not hungry? Na san jiya ma tun Fettuccine Alfredo din da kaci baka kara saka komai a bakin ka ba se coffe without looking in to her eyes yace  I wasn t hungry yesterday shisa, but I will make tea right away yana fadin haka ya mike ya nufi haryar kitchen. isowar sa bakin kitchen din yai daidai da fitowar yasmin wacce ke rike da jug of pineapple juice a hannun ta, duk cikin su ba wanda ya lura da wani coz duk idanunsu da kuma tunanin su basa a tattare da su, wanda hakan ya sanya su yin kicibis da juna, ayko nan take drink din dake cikin jug din ya xube jikin white hoodie din nasa  Subhanallah, Im so sorry I didn t mean to, I didn t see you.. I yasmin ta fada cikin tashin hanakli. Uffan be ce da ita ba se ma stepping back da yai slightly gami da kurawa stain din dake jikin rigar tasa ido wanda ya kara saka ta feeling so guilty coz expression din face din sa was unreasonable yet distant cold. Ana haka se ga mami ta karaso, bayan fuskantar abun da ya faru ya sanya ta maida kallon ta kan yasmin kafin tace  jasmin, are you okay badai ki ji ciwo ba ko? Ta fada very gently,  ehh mami, Im sorry ban kula bane ba shine na.. Shiru tai da maganar ganin Omair ya bar gun without a single word, tai kasa da kanta tana Jin ba dadin abun da tai masa, muryar mami ce ta tsinkaya tana fadin  karki damu kanki kinji, don t bother your self kinji? Coz it was an accident, ba wanda ya wuce yin haka jiki a sanyaye tai nodding head din ta kafin tace  toh mami, bari ma gyara gun tana gama fadin hakan ta bar gun ita kuma mami ta koma gun zaman ta fuskarta dauke da murmushi. Se da lokacin sallar juma ah tai sannan ya fito don xuwa masallaci, don tea din nasa da breakfast din sa ita da kanta gai masa don tasan tunda ya koma baxe kara fitowa ba se abu me amfani sosai, mami ta dube sa kafin ta ce da shi  har ka shirya kenan? A takaice ya bata amsa da  ehh daga haka yai mata sallama ya nufi downstairs a ranta tana ta faman jujjuya maganganun da hajja da aunty fiddou suka kira ta suka gaya mata yau da safe. Duk da yasmin na son komawa gida ammah haka ta daure ta jira har habu ya dawo daga masallacin jumaah sannan mami ta barta ta tafi, ko da ta isa parking lot wata mota ta gani a parke very close da wacce habu ya saba daukar ta da shi, motar se faman kyalli take, daidai ta nufi motar da zata maida ta gida don habu ya ce ta shiga ta dan jira shi yana xuwa se kawai taga an bude wannan motar da batai zaton akwai mutum a ciki ba, saurin yin baya tai don ta tsorata sosai, kallo daya yai mata ya dauke kai gamida barin gurin, da sauri ta shige cikin motar tana maida numfashi don ta tsorata sosai& .

ko da ta isa gida ta tadda innah ce ita kadai a gidan se su hafsa da suka dawo daga makaranta tuntuni, ammah ta tafi tun safiya kaima su abby abincin kalace, itama innah yasmin din take jira ta dawo ta rakata can asibitin, ba yadda innah batai da ita ba akan da ta zauna ta ci abinci ammah se tace mata she s Ohk ta ci a can inda take ayki, dan haka ko 10mins basu kara a gidan ba suka wuce asibitin. Da mamaki shimfide kan fuskar yasmin take kallon tilin kayan fruits, ruwa, drinks da duk wani abu da marar lafiya ke bukata a space din da abbyn yake, tambaya fall a bakin ta mah kuma ta kasa don bata fiya son yin dogon magana ba more especially da waenda suka girme mata. Jikin abbby yayi sauki sosai, ita dai da ido take ta bin gurin hoping ko zata ga hakeem ammah shiru, tanata zauna agun tana ta faman tunane tunanen da ita kanta bata san dalilin yun su ba. Muryar inna ce ta dawo da ita daga tunanin da take don ta tambayi question din dake makale a ran yasmin din tun daxu  lawal wa ya kawo duk waennan kayan alaton nan gun iye? Ko dai na waencan bayin Allahn ne suka baki ajiya? Ta tambaya tana satarwa kallon gadon wani tsoho da familyn sa suka kusan cika dakin. Kawu lawal ya kara gyara zaman sa kafin yace  wannan dai likita dan albarka wanda ya biya kudin magani shine jiya bayan kun tafi ya jido duk kayan nan, Wallahi yaron na da matukar kirki sosai don badan shi ba da jiya yunwa ta kashe ni, se guraren 10 sanna ya bar nan gun, Ashe shima likita ne, wallahi sosai yaron ya kwanta mun a rai sosai, dabadan mariya saura wata 2 bikin ta ba ay da na nema ma mata auran sa da kaina in xe yarda kenan ya karashe zancan yana washe hakoran sa da goro yai wa lahani.  tirr ammah dai lawal akwai ka da son xuciya wanna yarinyar taka me gutsurarren hanci zaka hada shi da ita? ina lefin ma yasaamin er kyakyawa da ita son kowa kin wanda ya rasa hade rai ammah da kawuawal sukai Jin abin da innah ke kafa, ci gaba da magana inna tai  duk ma ba wannna ba amma gsky wannan yaro dan aljannah ne in sha allahu, jifa kaya kala kala, ya kyauta sosai Allah dai ya biya sa duk suka amsa da ameen banda yasmin da haka kawai taji xuciyar

10 / 14