INUWAR KADDARA BOOK COMPELET BY MAIMOON

Author :  Maimoon Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 14

24K to 27K   out of 40K words

tace  toh shikenan Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi, se kasan me zaka ce ma su hajja da daddy also ka samo wacce zaka aura nan kusa tunda ka ki er uwar ka tana gama fadin haka ta mike ta fice daga dakin& .

NOTE: (duk yawanci maganar da mami take yi da omair da Turkish language ne saboda shi ne yaren da suka taso suna yi duk da kuma suna jin hausa, english, Arabic da kuma sauran foreign languages ammah zamu ringa yi da hausa don saukin fahimta daman kuma ni bajin Turkish language din nake ba lol)& .



INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY)&

By moon


Chapter 7: The Day Poverty Almost Won..

Ko abincin ma ta kasa ci gabadaya komai ya fice mata a rai, bata san me sa take crossing part da wannan mutumin ba sam, gashi duk haduwar tasu ba ta dadi ba, ita kan yau da ace ita ke da kanta da gai quitting aykin nan ta nemi wani abun coz ta san in dai ta cigaba da zama toh tabbas zaa samu damuwa. Guraren karfe 1 ta shirya komawa gida don sun gama aykace aykacen da zasuyi, gabadaya walwalar ta ta dauke diff, tunda suka fara tafiya take tunane tunane don har suka iso bama ta sani ba se da habu yai mata magana sannan ta farga, tun daga bakin kofar gidan su ta fara jiyo muryar elder sistern abby, da sauri ta karasa cikin dakin gamida saurin daga yagaggen labulen dakin mahaifin ta, nan tai ido hudu da mahaifin nata da ake durawa wani ruwa kamar na magani ganin hakanne ya sanya ta karasawa ciki da mugun sauri tana fadin  abby! Abby! Me ya same shi tsawan da wan mahaifin ta ya daka mata ne ya sanya ta jan bakin ta tai shiru, masifa ya ciga da yi yana fadin  iskancin banza iskancin hofi, sanda aka ce ku maidosa nan kauye ai masa maganin gargajiya ay duk ki kukai, ita kishiyar uwar taki har kusan zagi na tai ke kuma kika barewa mutane baki kina wani kukan banza, wallahi Wallahi da badan innah tace mu taho ba da Wallahi ba uwar da xe saka ni kara takowa cikin gidan nan, duk ba da maganin gargajiyar muka rayu ba? Da zaku wani ce se anyi na asibiti? Toh wai kun tara wata uwar da zaku kaishi asibitin ne ma? Ina nan aka koro ku daga asibitin? Shine se da kika ga babu sarki se Allah ya xo gangara shine zaki wani kira mutane se kusan yadda zakuyi dashi nidai daga wannan taimakon ba abin da zan kara ya karashe maganr yana huci kamar xe rufe Ammah da duka don sosai yakejin haushin ta duk da kasancewar su en uwa na kusa sosai. Se da innah ta gama tofe kanin nata da adduah sannan ta juyo ta kalleshi tace  kaga lawal akan yasamin zan iya tsine maka albarka wallah, in zakai masifar ka kayi da zulai ammah ba da yasaamin ba, Allah na tuba yarinya karama da ita me ta sani da zaka sata a gaba kana mata tsawa ehh? Ta fada tana kankance idanu alamun ranta ya baci sosai, daga haka dakin yai shiru ba abin da ke tashi se Sheshekar kukan yasmin,  ke kuma ki rufewa mutane baki cewa akai ya mutu ne wai? Inna ta fada tana janyo yasmin din jikin ta, haka suka wuni a cikin gidan ba tare da sun iya tabuka komai ba, don yau shekara 3 kenan tunda abby ya samu matsarla sakamakon ginin da ya fado masa time din suna gina wani katafren gida, wanda tun daga wannan lokacin komai na rayuwa ya canza masu don sosai rashin lafiyar tasa tai contributing gun duk wani abu da take fuskanta gun ammah don ta san ko me zatai mata abby be isa ya hana ba tun da a yanxu ya nakasa sosai don sanadiyar hakan stroke ya kama sa ga hawan jini me karfi daya damkeshi saboda damuwar abun da ke faruwa a cikin gidan sa gashi ba shida iko ko damar daukar mataki akan hakan. baze iya sakin ammah ba don ita ce rufin asirin sa a yanxu, don ita ke kula da su tun daga ciyar wa da sauran su dan shi danginsa tsaffi ne kuma a kauye suke shine ya dan samu ya fito brini, in ya saki ammah ita kanta yasmin din ba tada yadda zatai don se dai ta koma gun innah a kauye ita kuma inna bata da karfin rike ta yayyin sa kuma aurar da ita zasuyi ko tana so ko bata so, duk da mafarkin ta na rayuwa ya gama rugujewa wannan karan ko ba xe so ya kara ruguza mata mafarkin ta ba, hakan yasa har yanxu be dauki mataki akan ammah ba se ma bawa yasmin din hakuri da yake yawan yi& ..

Can yamma ganin dai kamar jikin nasa kara gaba yake ba baya ba ya sanya ammah kallon Yasmin ba annuri a face din ta tace  jeki chemist ki cewa ayuba ya taimaka ya xo ya duba jikin sa mikewa tai don yin abin da amman ta sata yi, hade girar sama da kasa inna tai tana fadin,  taya zaki ayke ta bayan ga umar a gida ba inda ya je tun da ya dawo daga makarantar boko? Har ammah ta bude baki zatai magana se kuma tai shiru don tasan halin innah dede take da kugun sa wandon ta don bata wuce tak mata tatas ba agaban yaran nata don haka ta ayka umar wajan ayuba me chemist. Ko da ayuba ya duba jinin nasa yaga ya mugun hawa fiya da ko yaushe se ya dube su yace  gaskiya da damuwa don jinin sa ya ninka na da hawa sosai, kamar ma treatment din sa na da yayi failing, da so samu ne kawai a kaishi asibiti suyi masa check up me kyau ya fada yana hada kan kayan aykin nasa, kawu lawal ne cikin fushi yace  karyar banza karyar hofi kullum haka dai daga ace wannan se wannan in banda kame kame ba abin da kuka iya, ni dai sisi bazan bada wlh se dai in ku ku san yanda zakuyi dashi shidai ayuba be kula sa ba don ya kula kamar kawu lawal bashi da seti kuma ba tun yau ya saba yin haka ba kullum ya xo gidan duba mahaifin yasmin se kawu lawal ya suke shi ammah don ganin mutuncin yasmin da na mahaifin ta da yake yi ne ya sanya shi yake daga masa kafa duk da yayi alkawarin cewa wataran se ya gwada masa danyan kai irin na gen Z& ..

wunin ranar haka ta wuni se zubda hawaye take, she cant afford to lose her dad don ganin sa a raye na matukar bata courage a rayuwar ta, guraren karfe 4:30 jikin abby ya tashi sosai don se da ya suma sau 2, ko da ya farfado ma in banda sambatu ba abin da yake, dole kawu lawal da umar suka samo adaidaita sahu don kaishi asibitin malam aminu kano don acan tun farko aka fara masa treatment kafin su watso shi saboda rashin clearing bills din su da basu yi ba. Kuka sosai yasmin take ganin halin da mahaifin ta ke ciki, ganin ta damu sosai ne ya sanya inna cewa ta shigo su tafi tare in ya so kawu lawal ya makale a gefe tunda ita yasmin din ba wani kaurin kirki ke gare ta ba. Suna isa asibitin suka karasa ward din maza suka amso weelchair aka daura shi akai aka shigar da shi cikin ward din, nan litoci suka shiga bashi temakon agaji, xuciyarsa ce tai weak har ta sanya bata iya pumping blood yadda ya kamata ga kuma wani ciwon kai da ke damun sa sosai, tashin farko aka rubuta masu magani allurai da kuma tests iriri wanda kudin yakai 10000, ko da aka mika masu paper din Yasmin ce ta amsa don ita ce ta iya karatu kaff cikin su, duk suka xuba mata ido suna kallon ta duk jira suke suji me zata ce masu, hawayen da suka gani na bin fuskarta ne ya sanya hankalin su kara tashi a haukace ammah tace  dallah malama ki fada mana me suka ce kin xo kin samu gaba kina kuka ko an gaya miki kin fimu sansa ne? saurin share hawayen nata tai kafin tace  wai kudin magani da tests din da za ai masa dubu dari, da karfi innah tace  dubu dari? Mun shiga ukun mu yanxu ina muka san zamu samu dubu dari ni halima? Ta fada tana daura hannu a kanta ammah da ta kafe yasmin da idanu tace  na shiga uku nah ni zulai, hanxu ina zamu samu kudi masu yawan gaske haka? Ta karashe zancen tana fashewa da mugun kuka, sun shafe kusan 20mins suna nan zaune agun sunyi jungun jungun har se da wata nurse ta dube su tace  auu kuna nan har yanxu baku sayo maganin ba? ana fa bukatar maganin nan da sauran abubuwa da gaggawa in kuma kun shirya fita da gawa ne toh kuyi ta zama ay ammah bata san sanda ta mike tai kan wannan figaggiyar nurse din ba tana zagin ta ta uwa ta uba harda kokarin kai mata hannu, wasu majinyata ne suka samu suka ririke ammah dake ta faman yi masu tirjiya, ita dai yasmin na can gefe ta rakube kamar wata kaza tana ta faman tunanin yadda za ai a ceto ran mahaifin ta don ko kaffara bazatai ba innah da kawu lawal ba suda hanyar samun wannan kudin don suma a kauyen ba abin da suka aje se wasu ramammun akuyoyi guda uku wanda su duka ukun ko saida su za ai basu fi 70k ba don ko nama ba suda shi ajikin su, xumbur ta mike tunawa tai da kudin da hakeem ya bata wanda if she s not mistaking toh tabbass 10000 thousand naira ne daidai saboda boundle ne guda na kudi. Sadaf sadaf tai ta fice daga ward din da sauri hannun ta rike da takardar maganin, ita dai ta san a cikin aljihun rigarta akwai kudin da xe isheta ta je gida ammah banda na dawowa don saidai ta amsa agun kawar saddiqa, tafiya take cikin sauri kanta a kasa, karo tai da mutum, da sauri ta ja baya gamida durkusawa ta dauki papper din da ya fadi, se dai kafin tai hakan mutumin yai saurin kai hannu ya daukar mata, mika mata yai cikin sanyi tace  yakuri bawan All.. maganar ne ya makale mata a makoshi sakamakon wani bugu da xuciyar ta tai da karfi yayin da tai arba da kaykkawar fuskar sa, wani iko na Allah sam ta kasa janye idanun ta daga kan nasa duk da kasancewar ta yarinya me kunya, shima kuma kallon ta yake with confusion, duk da wancan ranar bata samu ta mai kallon natsuwa ba ammah tabbas ta gane shi tass  yasmin? ya fada fuskar sa dauke da farinciki da kuma mamaki, saurin sauke kanta tai kasa, kafin tace  good evening be amsa gaisuwar tata ba ganin kamar tana cikin damuwa don haka yace  what happened my dear? Me kike yi anan wani ne ba shida lfy? Or kinxo dubiya ne? Ya jero mata tambayoyin gamida kafe ta da ido dan jiran amsar ta yake, bata san sa addah ta saki wani kuka ba kamar yarinya karama agun har wasu mutane na bin ta da kallo, sosai hanaklin sa ya tashi ganin tana kuka sosai, da sauri yace  ya salam yasmin talk to me, rasuwa akai muku? ganin kamar hankalin mutane na yi kan su ne ya sanya sa fadin  relax muje ki zauna a can se ki fadan koma mene but pls relax and stop crying fuskar sa dauke da damuwa ya fadi maganar yana me nuna mata wani seat dake nan gaba da su, samun kanta tai da takawa towards the seat, se da ta zauna sannan ya zauna a kujerar dake facing din tata ya ciro wani hanky me dan banzan kamshi ya mika mata, hannu ta saka ta amsa ta share ragowar hawayen fuskar tata, seda ya tabbatar da ta daina kukan sannan ya kara maimaita mata tambayoyin da yai mata da farko, murya na rawa tace  abby ne ciwon sa ya tashi ta fada tana share kwallar dake xubo mata,  Subhanallah, meke damun sa? Ya tambaya, shiru tai ba tare da ta basa amsa ba, doguwar ajiyar xuciya Hakeem ya sauke kafin yace  look yasmin, ki taimaka ki fadan damuwar ki, I promised you in sha Allah i will help you, kuma ma karki manta matsalar ki tawa ce, your dad is my dad too amma if kikai shiru ba yanda zanyi na san me ke damun sa ya fada cikin sigar lallashi, sosai tai nazarin maganar daya fada a brain din ta after a while tai deciding fada masa duk abin da ke faruwa amman bata mentioning cewa basu da kudin ba. Ko da ta fada masa halin da abby yake ciki sosai yai kwantar mata da hankali sannan ya ce da ita  rakani ward din da aka kaisa ba musu ta mike suka jera tare har suka shiga cikin ward din, tun shigar sa nurses din gun suka shiga gaida sa cike da ladabi harda ma doctors din, sosai mamaki ya cika yasmin don be ce mata yana ayki a wanann hospital din ba, haka har suka karasa gun da abby yake wanda ba me bin ta kansa don ba su kawo kayan da za ai masa treatment din da shi ba ganin ba wani taimakon kirki da abbyn yai receiving duk da condition din nasa is worst ya sanya shi calling attention din wata nurse dake duba wani mutun a cikin room din, da ladabi ta nufo sa tana kara gaida shi despite sun gaisa tun shigowar sa, on a serious note ya ce da ita  how on earth ba a bashi treatment me kyau ba duk da condition din da yake ciki da sauri nurse din tace  sir an basu takardar magani da sauran abubuwa ammah sunce basu da halin biya daya daga ciki ma ta nemi ta tayar mana da husuma shisa doctor sambo yace a kyale su da halin su ta karashe maganar tana hararar ammah don har yakushin ta se da ammah tai duk da dai ita er rabo ce bama da ita akai fadan ba. Girgiza kai yai kafin ya ce da nurse din  we are talking about someone s life here amma zaku a barshi haka? What s wrong with you people? ya fada rai a bace da sauri nurse din tace  sorry sir maida kallon sa kan Yasmin da tai shiru tana sauraron tattaunawar ta su yai,  yasmin ya fada da wata murya bata iya ce masa komai ba se kara yin kasa da kanta da tai, duk wannan abu da ake su ammah bama su san anayi ba don sun dauka random doctor ne ya xo yake tamabayar ba asi, hannu ya mika mata alamun ta bashi takardar maganin, a hanakli ta mika masa ya sanya hannu ya amsa daga haka ya bar gun ba tare da yace mata komai ba, sauke ajiyar xuciya tai tana sake sake kala kala a ranta, after a while se gashi nan ya taho hannun sa rike da ledan magani, gefansa kuma doctor sambo ne yana masa magana, tana ganin sun karaso tai kasa da kanta gamida basu guri don aywatar da aykin su, su ammah na ganin doctor ya yi kan abby suka tashi daga zaman bihim din da suke suka nufo sa suna gwale idanu, ba jimawa doctor yai masa gwaje gwajen da zeyi kafin daga bisa ni yace, toh yanxu saura tests wanda in ruwan da aka saka masa ya kare se aje ay masa a nan lab, ya fada yana niyar barin gun, da sauri ammah tace  ammah likita ba ance wai se mun biya kudi kimanin dubu dari ba sannan za a duba shi ba? Kodai tallafi muka samu ne? Ta fada tana zazzare idanu, innah ce tai saurin fadin  ke dallah yi mana shiru yanxu inma mantuwa sukai suka duba sa se ki ja su fasa ayy ta fada tana hararar ammah, ita dai yasmin ji take kamar kasa ta bude ta shige cikin ta, murmushi doctor sambo yai kafin yace  a a innah ba kuskure bane ba wani kallo hakeem ya watsa ma doctor sambo don tun farko se da ya rokeshi akan kada yai mentioning name din sa kawai yace wani me hali ne ya taimaka masu ammah se gashi yana shirin bata masa shirin sa, dauke ido dr sabo yai daga kan na hakeem sanan yace  wanan bawan Allahn ne ya biya komai da komai and he s willing to pay every single naira da za a bukata a nan gaba nan fa su hajja suka maida kallon su kan hakeem that was trying to leave the place coz this is not his plan at all ammah dr sambo ya bata masa shiri& .. nan fa suka shiga xuba masa godiya harda kawu lawal me bakin hali, shidai uffan ya kasa ce masu se da yaga dai da gaske godiyar tasu ba me kare wa bace ba sannan ya furta  Allah shine abun godiya kawu, ku kara gode masa, Allah ya bama baba lfy yana fadin haka yai saurin barin gun, da ido yasmin ta bishi har ya fice daga ward din, sosai taji ba dadi da ya tafi don ko godiaya batai masa ba gashi bata ma fito da wayar ta ba balle ta kira sa, ana cikin haka se ga wani gansamemen mutum ya shigo yana korar visitors alamun

9 / 14