INUWAR KADDARA BOOK COMPELET BY MAIMOON

Author :  Maimoon Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 14

3K to 6K   out of 40K words

ringa girki ba coz there s my maid da zata zo from Turkey sunan ta BAHAR duk abun da ya shafi girki ita zatai, kedai se dai ki taya ta da kananan ayki ta kare maganar tana kallon ta, ganin duk Yasmine din a takure ne ya sanya tace  ki saki jikin ki fa yamla& ? Hakane sunanan? girgiza kai yasmine taI cikin girmamawa tace  a a yasmine ne jinjina kai mami tayi tace  masha Allah jasmine Ashe flower ce me tsada a cikin gidan namu yau ita dai yasmine bata ce komai ba se dan murmushin karfin hali da take yi don haka Allah yai ta da rashin sabo wanda hakan ya samo asali daga kiwar datai tun tana yarinya.  shekarun ki 20 right? Kuma kinyi secondary school koh? Nan ma ta gyada mata Kai kamar wata lizard, a jiyar numfashi tai kafin tace toh  masha Allah haka ake so muje na nuna maki part din da zaki ringa zama in bakida ayki .



**INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY.) BY moon

Chapter 2: The mansion of unfamiliar kindness


Ta wata kofa dake ta cikin parlon kasa suka bi se ga wasu rooms guda biyu sun bayyana, na biyun ta shiga da ita wanda ba abunda babu a ciki, dakin yayi mugun haduwa she couldn t believe that wai nan ne dakin hutu, nan ta shiga tambayar kanta toh ya sauran rooms din en gidan ze kasance?  you will be staying here more especially if ba aykin da zakiyi, there s a telephone if yayi ringing to u should pick coz tanan zamu ringa communicating if wani abun ya taso, dakin kusa da wannan da kika gani na bahar ne wanda nan da anjima jirgin su ze iso nigeria. in Banda nodding head din ta ba abunda take yi, a haka ta ringa binta a baya har ta gama nuna mata abubuwan da suka dace.
suna komawa parlor suka ci karo da wannan matashiyar da ta bude mata kofa dazu se faman frowning face din ta take, mami ta kalle ta tace  nazli I told you that I despise these attitudes de kike displaying lately, haka kawai ki ta hade rai kamar an dake ki? I had you shouting at the driver and Im very sure he did nothing wrong ammah kin sa Shi a gaba kina fada kamar danmi, what s dis please?? Mami ta fadi hakan a kufule don ta tsani kalan attitude dinnan and ta kula tun ranar suka dawo nigeria take haka. Zama tai kan cushion sannan ta ma yasmine alamun ita ma ta zauna, can gefen kujera ta zauna, mami dake kallon nazli tace  ina jinki se da nazli tai raurau da eyes din ta kafin tace  anne ba big brother bane ba ya.. mami tai saurin tamabayar ta kan cewa me yai mata don tasan baya wasa da ita balle har yai mata wani abun Sedai in ita ta tabo sa. Se da nazli ta zauna sannan ta cigaba da fadin  bakiga abunda yai ma layla ba, yanxu muka gama video call da ita, she was crying about what he did to her, jiya ita da course mates dinta sunje shopping ta hadu dashi she talked to him buh ya nuna kamar he doesn t know her and in front of her friends, har kokarin tuna masa inda ya santa tayi coz she thought ko ya manta tane Ammah he ended up shouting at her in front of lots of people, he even called her an attention seeker fa bakiga yadda yai embarrassing din ta ba, yanxu duk yadda muke da layla yace be santa ba?, da kansa fa yake kaini gidan su and ita ma she used to come over ammah ji abunda yai mata Ta karasa maganar kamar zatai kuka. Duk abunda suke yasmine na zaune kasan lallausan carpet din da ke shinfide a tsakiyar tsararren parlon ta kurawa gu daya idanu tana sake sake daban daban, se da mami tai ajiyar numfashi kafin tace  ni da kike fadama so kike na dake shi ko me? Kin fi kowa sanin halin sa and am very sure ita ma laylan ko bata San halin sa a zahiri ba ta sani a labari, en uwan sa ma na jiki ya ya kare da su talk less of a friend of yours? Nima kaina so nake ya canza wannan halin nasa, Buh ki bata hakuri shi ma kuma ayy next xe dawo i will talk to him not just because of your friend harda sauran abun da yakeyi don nan his family members duk suna nan so baze yu ya ringa treating din su that way ba. Murmushi nazli tai kafin tace  much better mami, that s why I love you ta fada tana me barin parlon bayan tayi pecking cheeks din mamin. Murmushi mami tai ta bita da ido har ta haye upstairs kafin ta maida idunan ta kan yasmin da ta luluka duniyar tunani.  jasmine? Se da mami ta fada sau biyu kafin ta dago a dan firgice, tace  na am hajiya Murmushi mami tai kafin tace baki saba da sunan ba koh? Murmushi Yasmine tai gamida sunkuyar da kanta kasa, mami ta cigaba da fadin  nafi Saba wa da sunan jasmine akan Yasmine though duk meaning dayane so I will be calling you jasmine not Yasmine hope you like it? Seda ta fadi hakanne sannan ta tuna cewa since se turanci take yi and bata sani ba ko ita Yasmine din najin turancin, Ammah bisa da mamakin ta se taji ta bata amsa da  it sounds good i like it seda mami ta danyi kamar me son tuna wani abun don cousin din ta dake nan kano ta fada mata cewa me aykin da aka samo mata tayi secondary ammah kuma batayi tunanin tana Jin turancin har haka ba dadin dadawa ba accent take amfani da Shi ba na Nigerian bane ba shisa she was a bit surprised. Tana so ta tambayi Yasmine din abubuwa da dama ammah se ta bari nan gaba ta tambaya. Kallon wrist watch din ta tai kafin tace  yau ba aykin da zakiyi buh akwai list da zan baki zakuje supermarket ke da driver ku sayo groceries amsa kawai ta bata sa  toh hajiya girgiza Kai mami tai tace  next time around akwai punishment akan wannan sunan da kika kakabamun da sauri yasmin tace  yi hakuri hajiya in sha Allah zan se kuma tai sauri ta toshe bakin ta wanda hakan da tai ba karamin dariya ya bana ammin ba& ..

********
wannnan karan ma tunda suka dau hanya xuwa Supermarket habu ke ta faman yi mata zan ce harda tamabayar ta wai ko tana da saurayi, uffan bata ce da shi ba don Sam bata son magan ko a cikin en uwanta mata talk less of shi da yake na miji. Gabadaya tunanin kalar aykin da zata jibga take if ta koma gida, har suka karaso bata sani ba seda yai mata magana sannan ta dawo daga duniyar tunanin da take, ko da suka shiga cikin dankareren supermarket din habu ne ke fada mata me za ta dauka tana saka masa a basket don list din na cikin wayar sa, seda suka shafe tsawan minti 20 suna abu daya don sosai suka cika cart manya manya har guda 3, daga bisani kuma suka nufi gun biyan kudi.
tsaye take jikin mota su habu da wani ma aikacin supermarket din suna shigar da kaya cikin boot din motar, ita kanta bata San me ke damu ta ba en kwanakin nan, fada, duka da aykin wahala duk ta Saba da shi ammah bata taba Jin she s frustrated Akan duk abunda ammah ke mata ba kamar these few days, ji take kamar ta gudu ta koma gidan innna tabarau amma tasan ba hali don ko rami zata shige se ammah ta biyo ta ta zakulota, balle wani gidan inna tabarau da ba bakon ammahn bane ba ba. Tana cikin sake saken ne taga wata tsadaddiyar mota ta xo tayi parking dab da ita, kurawa motar ido tai har after some seconds me shi ya fito daga ciki, haka kawai ta samu kanta da kallon mutumin even though bata iya hango fuskar sa don ya juya mata baya, sanya yake da off white trouser and brown top se kuma boyfriend jacket da ya daura kan top din shi ma off white, tunda take a rayuwarta bata taba Jin kamshi kalar wannan kamshin ba, har wani lumshe idanu tai don a take taji wani natsuwa da kwanciyar hankali wanda ta dade bata ji kalar sa ba ya xo mata, har yanxu she haven t seen his face, but ta dai San foreigner ne don ba abunda ya suffanta sa da nigerian kama daga kyakkaywan skin din sa wanda yake misalin a xubawa coffe madarar ruwa har ixuwa kan gashin kansa dake kwance baki wuluk, wanda hakan ya kara mata son ganin face din nasa. Yana kokarin rufe murfin motar tasa wayar sa ta fara ringing, hannu ya kai cikin pocket dinsa ya dauko wayar sa kirar samsung ya kara a kunnan sa, duk wani motsi da yake a kan idonta yake don sosai ta maida duk attention din ta kansa, bata san da cewa ana iya samun natsuwa da kallon wani dan adam ba se yau, ko sallma beyi ba taji ya shiga magana da wani language wanda take ji kamar ta taba jin kalar sa, duk da ba aga murya yake ba ammah hakan be hanata gane cewa fada yake ba don se faman xura long finger din sa yake cikin bakin gashin kansa, can kuma ya daki jikin motar kafin ya zare wayar daga kunnan sa yana fadin  fuck you nazir yana gama fadin haka ya shige cikin motar ya rufo kofar da karfi sannan ya tayar da motar ya bar cikin supermarket din da mugun gudu, bin motar tasa tai da kallo kafin ta sauke idanun ta kasa,  me yake damu na ne wai? Ta fada a fili tana dan dukan forehead din ta, karaf idon ta ya sauka akan wani wallet dake yashe a dadai inda mutumin ya tsaya, kurama gun ido tai kamar me son gano wani abun, tabbas tasan cewa daxu ba wallet a gun kafin ya xo amma yanxu kuma se ga wallet does that mean cewa nashi ne??  Amma garin ya banyi noticing sanda ya fadi ba? Ta tambayi kanta,  kina can kin shagalta da kallon sa ta ina zaki gani wani bangare na zuciyar ta ya bata amsa, a hanakli ta taka ta nufi inda wallet din yake, har ta sunkuya zata dauka se kuma ta fasa tana me tantama  kodai trick aka hada min na dauka na bace daman ance foreigners suna amfani da naman mutane gun hada sausage ta fada a ranta, (lol da alamu dai yasmine karshe ce gun tsoro). kawar da tunanin tai sannan tai bismillah ta dauka ta mike tana kallon unique wallet din. Ganin habu ya dunfaro inda take ne ya sanya ta bude murfin motar ta zauna tana jiran karaso warsa, a hankali ta bude wallet din, tabbas wannan dollers ne, ta fada cikin ranta don ta tuna sanda tai wining wani competition da sukai 3year ago har wani bature ya bata kyautar 20 dollars amma tunda ammah tai ido hudu da kudin ta amsa bata kara ganin kyallinsu ba,  good old days ta fada a fili tana murmushi, ko banza a wannna ranar tayi farin ciki sosai ta sanadin hakanne ma ta samu damar yin NECO exams, awards da kuma scholarship wanda ammah ta tsaya tsayin daka ta hanata zuwa makarantar gaba da secondary. har habu ya shigo bata sani ba don har se da taji yace  sorry pretty na barki kina ta jira koh?? Wallahi mami ce ta kira wai a kawai abunda ta manta bata saka a list ba shine fa seda na je na memo sa, cimarsu ce ta can en kasar turkiyaa, kin san rayuwar su gabadaya a can take, se su shafe shekaru kusan 5 basu xo ba, toh se yanxu allah yai suka dawo nan gabadaya, ayy wato in gaya miki ni ayy tun filazal ina ayki a gidan cousin sister din ta dake nan itama GRA amman fa ba girman nan bane ba don gabadaya haihuwar su da girman su a can turkiyan akai amma mamanta er Egypt ce Shi kuma&   da sauri yasmine tace  muje dan Allah ta fada kamar zatai kuka don kanta har ya fara mata wani iri saboda surutun sa, ga motion sickness daya dameta tun daxu da ta hau motar. Maida hankalin ta tai kan wallet din dake hannunta, wani tsarsren complementary card ta gani Wanda aka kawata shi da black and golden color, rubutun jiki da italics aka kawata shi,  DOMINION AUTO ta karan ta a fili, kome ta karanta se ta maimaita sau biyu a haka harta karance gaban card din tass wanda ya hada da location harda kuma email address and the rest, har ta xo mayar da complementary card din se ta lura akwai wani rubutun a bayan card din wanda ya kunshi suna da ceo and chairman s info, sunan ceo din ta kurawa ido kafin daga bisani ta maida card din cikin wallet din, can ta hango membership card da debit card Wanda su ba wani bi ta kansu tai ba,  tabbas wannan wallet din me amfani ne sosai definitely nasan dole me wallet din will look for it lumshe idanun ta tai ta jingina kanta jikin window din  adon gari lfy kuwa? kodai zazzabi kike ne?? Habu ya fada yana me leken ta ta mirro, a takaice tace masa  lfy yace  toh Allah ya sa daga nan kuma ya maida hankalin sa kan tukin da yake.

Ko da suka isa gida shike shiga da kayan cikin gidan yayin da ita kuma mami ke nuna mata inda zata aje cikin katoton refrigerator wanda ko a tv bata taba ganin kalarsa ba har wani smart screen ne dashi a ciki harda camera wanda mutum xe iya gano abunda yake ciki ba tare da ya bude ba, kofar ma kanta French door style ce, a haka ta ringa xuba wa har ta gama.  sannu jasmine, nasan kin gaji koh? Murmushi tai kawai ba tare da ta ce komai ba don wannan ko 0.5 na kalar wahalar da take sha be kai ba, cigaba da magana mami tai  ko zaki zauna ki huta xuwa anjima se habu ya maida ki gida? dan jimm tai kafin  tace toh mami Murmushi mami tai tace  Yauwaaa jasmine se kije can room ki zauna ki huta xuwa anjiman se ki wuce, ammah bara ina xuwa ta fada tana mikewa tsaye, ita dai yasmin tunda ta sunkuyar da kai bata dago ba, haka kawai taji matar ta shiga ranta gashi as same time take Jin wani mugun kunyarta. After few mins se ga mamin nan ta dawo da wasu daga cikin abubuwan da sukai shopping na ciye ciye ta aje a gabanta  ga wannan kije ki aje a room dinki if there s something you need, just give me a call Ohk? she was lost in words kawai ta tai Shiru can dai tace  na gode mami ammah dis is&  da sauri mami tace  shhh, dis should be the last tym da inna baki abu zakiyi trying rejecting din sa, just because you are working under me that doesn t mean I won t treat you good so don t do that again kinji?  To mami na gode in sha Allah bazan kara ba ajiyar xuciya mami tayi kafin tace  good, zaki gane room din??  Ehhh zan gane tana gama fadin haka ta kwashi tulin kayan ta bar gun.

Koda ta shiga dakin a kan empty dressing mirror din dake room din ta daura kayan sannan ta zauna akan carpet ta jingina kan ta da jikin gadon, ji take nan din kamar wani safe place din ta ne, gurin da ba hayaniya ba tsawa and the rest, she doesn t know for how long mami zatai cigaba da treating din ta dis good, Buh she doesn t care at all, coz she appreciates the care and the real love data nuna mata for dan zaman nan da tai, yeah real love wanda yana daya daga cikin abunda tai lacking a rayuwar ta, ta hadu da mutane da dama a rayuwar ta wanda is either su sota dan kyawun ta ko kuma su kita don tana da kyau, Buh as for mami s case bata ga alamun hakan ba. seda ta shafe minti 20 tana tunani sannan ta tuna da wallet din da ta sanya cikin pocket din rigarta, cirota tai a fili tace  dama security guard na bama ajiya da duk ba haka ba yanxu ya zanyi da wannan hakkin? ta fada kamar zatai kuka, wani da bara ne ya fado mata don haka ta matar da ita cikin pocket din din nata ta zaro er keypad din ta ta shiga laluban numbar kawarta saddiqa don akwai dan Ragowar bonus a cikin sim din nata. kiran na shiga ta dauka, sallama tai mata ta amsa sannan tace  saddiqa dan Allah wani alfarma zaki mun daga daya bangaren saddiqa tace  to kawalli ina jinki  dan Allah anjima da rana zan xo ki aran wayarki in saka data in tura sako ta email in ba damuwa? Tana jiyo dariyar saddiqa kafin saddiqar tace  Allah ya shiryaki yasmin shine harda wani yin kasa kasa da murya, kin

2 / 14