INUWAR KADDARA BOOK COMPELET BY MAIMOON

Author :  Maimoon Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 14

18K to 21K   out of 40K words

da kyawawan idanun sa, ciro wayar tata tai yai mata alamu da ta kara a kunnan ta, a karo na biyu tai murmushi don she founds his actions very funny, ba musu ta kara a kunne bayan tayi picking  hello dis is your feature husband s number ya fada yana sakar mata murmushi, sauke idanun ta tai kasa tana me blushing, a na cikin haka se ga wani me nappep nan ya nufo inda suke, ya san ba zata shiga motar sa ba shima kuma baze yi insisting hakan ba don ya kula tana da tsoro da kuma kamala. Tsayawa yai yana kallon nappep din wondering me xe ce masa ya tsaya, kafin yai wani yunkuri ta tsayar da nappep din ta fada masa in da xe kaita, sannan ta shige, ganin me nappep din xe wuce ne ya sanya sa saurin ciro kudi masu yawan gaske ya aje a gefen ta sannan yai saurin barin gun ba tare da ya jira ta cewar ta ba duk da yana son ya tambayi sunan ta ammah kuma gudun kada ta dawo da kudaden da ya bata ne ya sanya sa kin tsayawan..  Bawan Allah dan Allah ko zaka iya juyawa gun wancan mutumin? Ta fada tana dan dardar,  anya kuwa hajiya? Gaskiya yamma tayi se dai ki sauka ki samu wani don ni yanxu sauri nake zani gida lokacin tashi na yayi, kawai ki dafe kudaden ki ko kimun sadaqa in yawa yai miki tuna wahalar da ta sha kafin ta samu nappep dinne ya sanya ta cema ma me nappep din su je kawai. Ji tai duk ta manta da bakin cikin da wancan watsatsen mutumin a dasa mata , duk da dai ta ji dacin abun da yai mata ammah se Allah ya kawo wannan bawan nasa da maganganun sa suka mantar da ita wancan bacin ran.

*****
5pm daidai ta isa gida wanda tun kan ta karasa shigar da kafafun ta ciki taji xuciyar ta ta kara jagule wa sosai, bakin ta dauke da sallama ta karasa cikin tsakar gidan da ba kowa a cikin ta, wanda hakan ya tabbatar mata da cewa su hafsa na makaran ta, dakin da Abby ke ciki ta nufa, ta gaida shi ya amsa mata ya tambaye ta ya aykin ta bashi amsa da Lfy kalau Abby, daga haka ta mike ta bar dakin ta nufi na ammah tai mata sannu da gida, ciki ciki ta amsa mata kafin daga baya tace  ga abinci can ki dauka ta fada tana nuna mata wata er karamar cooler,  toh na gode sam bata jin yunwa ko kadan ammah gudin kartai musu a hanata na dare ya sanya ta daukar coolern ta fice, babu kowa dakin don su hafsa na Islamiyyah harda su twins, hijab dinta ta rataya jikin kofar dakin sannan ta fiddo da kudin daya bata daga aljihu tana kallo, haka kawai taji ta tuna da rude man dinnan, tsaki tajaa sosai which is not her habit, mayar da kudin tai cikin pocket din ta, tana son ta kawo wa siblings din ta chop chop din da mami ta bata ammah tana tsoro kar ammah ta sata a gaba ta ga kamar wata duniyar ake bata a gidan mamin. Tana zaune har kusan 20mins bata ji ammah ta sata ayki ba which is unusual don haka ta janyo quranin ta ta shiga yin bita har se da ta ji kannen ta sun dawo sannan ta rufe don baza su barta tai karatun ba. Bayan ta idar da sallan magrib ta karasa kofar ammah tai sallama sannan ta tambaye ta me za a a dafa,  taliya da manja da yaji, kije gidan auntyn haske ki amso mun murjin taliyar saura kuma ki tsaya gun gantalallar me awarar nan don wlh kika dade se na daka ki a gindan nan.

Tafiya take cikin duhun daren nan, don ko hasken fitila babu wayarta ma ta dauke don battery din ta ya fara samun matsala shisa take saurin sauka, ita kadai ce a layin se wasu maza da take jin maganar su a bayan ta, gabadaya ta tsorata da lamarin mazan duba da kalar hirar da suke ga muryar su kana ji kaji na original smokers, kiris ya rage bata saa gudu ba bayan ta jiyo muryar daya daga cikin su daf da kunnuwan ta, da sauri ta matsa gefe tana ambaton sunan Allah gamida kankame jikin ta, kan kace me mazan da zasu kai su 5 suka zagaye ta suna bin ta da kallo kamar sunga nama,  kai kaga wata baturiya kamar ka lashe? wani me xubin mayunwata daga cikin su ne ya fadi maganar yana me tande baki kamar maye,  jar uba ashe dai bani kadai nake gani ba da fari na dauka abar ce ke sani nake gani ba daidai ba ashe ashe rayality ne haka suka sata a gaba suna ta faman sambatu gashi daga tayi runkurin guduwa se su maza su tare mata hanya, haka suka dinga wahalar da rayuwar ta kamar mage ya samu bera, wani dan zalama ne daga cikin su yai yunkurin kai hannun sa jikin ta ayko ta daddage ta kwalla wata siririya kara wacce ta janyo hankalin wasu samari da suka xo wucewa, ganin hakanne ya sanya su tarwatse wa don kar ta san kar ne tsakanin su, xubewa tai bisa knees dinta tana sakin wani kukan bakin ciki, ta rasa me taiwa mutane da wasu sam basa son ganin ta tana rayuwa kamar sauran mutane, if she could remember correctly dis is the 4th time da akai attempting molesting din ta, na farko malamun islamiyyar su, na biyu kuma a school na uku kuma wani cousin din ta a kauye ga kuma na yau don Allah ne kadai yasan me waennan bayin nasa zasuyi mata da Allah be kawo waenan samarin ba, sosai take kuka har numfashin ta na daukewa,  Sannu baiwar Allah, ina fatan dai basu miki komai ba koh? Matasan suka tambaya, da kyar ta samu ta gyada masu kai,  tashi mu rakaki gidan ku, kada kuma mu barki ke kadai wani abun ya kara faruwa ba fata ake ba jin abunda suka fada ne ya sanyata mikewa xumbur kamar an tsikara mata allura, se a time din mazan suka lura da fuskar ta da sauri dayan yace  Auuu Ashe ma yasmin ce, me ya fito dake haka da duhunnan bayan ga umar a gida kallon rashin sani take masa don haka tai gum da bakin ta aranta tana mamakin a ina ya santa bayan ita ko me kama da shi bata taba gani ba. Ganin she s confused ne ya sanya shi cewa  muje mu kaiki gida a hankali tace  na gode Allah ya saka da alkhairi, ammah ba gida zani ba  ba komai, ina zaki toh?  nan baya ne ba nisa..

Haka matasan nan suka tasa keyar ta gaba suka kaita har gidan antyn haske, shiga tai ta gaida auntyn hasken sannan ta fada mata sakon ammah, mikewa tai ta dauko mata robar da taliyar ke ciki sannan tace  ayy tun da rana na gama ita nake jira ma ta xo ta amsa, da har zan tura yara su kai mata ammah se na tuna tace bata son kowa ya kawo mata zata ayko me amsar ita dai yasmin bata ce komai ba se amsar robar da tai tai mata se da safe, daidai ta juya se ga sallamar wannan matashin cikin gidan, kallon sa take tana mamakin me ya shigo da shi cikin gidan matan aure ko dai bashida kai ne, muryar auntyn haske ne ya katse mata tunanin da take,  dan albarka ka dawo kenan? Yau ma ay na dauka gun abokan naka zaka kwana, ace mutum yai ta gudun gidan su? Baban ka tun yana fadan harya gaji yayi shiru, ya kamata kaima kanka fada haske tunda ka dawo baka zauna ba se fice fice da kake ba ma kada lokacin mu.  toh aunty a yakuri za a gyara sim sim yasmin tai zata fice se ta jiyo muryar auntyn haske tana cewa  yasmin kun ko gaisa da dana haske kuwa? nasan ba lallai ma ki tina sa ba don sanda ya tafi kudu neman kudi ba kida wani wayo sosai, haske ka gane ta kuwa? er marigayiya ce fa me kukan nan sosai ta fada tana dariya, a sanyaye yasmin tace  ina wuni tana fadin haka tai saurin ficewa daga gidan, luckily kuma abokin nasa baya wajan dn haka tai saurin barin gun, haka kawai taji kuma bata bukatar temakon nasa wanda ma yai mata a farko Allah ya sa masa albarka. Tana isa gida ta kunna wuta ta dora taliyar, tako ci sa a ammah bata nan ta shiga gidan makociyar su maman daddy, ko da ta dawo ma batai mata fada ba don ta ta dan jima a gidan maman dadyn, sam batai gigin fadin abin da ya faru ba, toh wa ma zata fadawa? Wa ma wanda xe saurare ta. Tun da ta dawo se faman firgita take don ko motsi taji se ta firgita, haka nan dai ta gama girkin ta debar wa ammah nata shima abby haka sannan ta xuba wa en uwanta a wani tray, bata debar wa kanta ba don bata jin zata iya cin abinci yau dinan duk da dai akwai shinkafar ta ta daxu da bata ci ba. Tafi minti 10 tana kallon missed calls din da akai mata wanda take da 100% sure cewa na wannan mutumin ne na daxu, a tsakanin fitar da tai da kuma girkin da ta tsaya yi se da ta tadda missed calls goma sha biyar, aje wayar tai can gefe sannan ta janyo cooler din abincin ta shiga ci a hankali. Se da tai wanke wanke ta wanke ma su hafsa uniform sannan ta kwanta. the next morning kamar kullum ta tashi da wuri tai gyaran gida ta daura ruwan wanka ma su hafsa sannan ita tai dana sanyi, shiryawa tai cikin army green hijab din tsohuwar islamiyyah su sannan ta fita xuwa dakin ammah, bakin ta dauke da sallama ta shiga cikin dakin,  ammah zan tafi ta fada kan ta a kasa,  xo nan kirjin ta ne ya wani buga jin abun da tace mata, kamar me tsoron taka kasa haka ta shiga ta kowa, ganin kamar zata bata mata time ne ya sanya ta damko ta, daman abun ka da jikin fulani se gata ta fado dukan ta kan amman, tunkuda tai kafin ta ce  tashin mun a jiki wawiya kawai ayko da sauri ta mike tsaye xunbur jikin ta na rawa, hijabin jikin ta ta dage mata da sauri yasmin ta rike hijab din gami da sauke shi, marin da ammah ta gaura mata ne ya sanya ta sake hijab din a gigice, Allah ya xuba ma ammah zafin hannu don marin da tai mata yanxu se da ganin ta ya dauke ya dawo,  uwar me zan gani a jikin naki ehh, dan kaniyar ki? Nace me zan gani a jikin naki ta fada tana kara kai mata mari, da sauri ta sanya hannu ta kare fuskar ta da shi,  ayyooo ta nan kuma kika bullo? Nice zan dake ki kisa hannu ki kare, wato ban isa ba kenan, toh ko zaki doke ni ne ehh marar kunya? Koda yake ma koma me kikai lefi na ne dana dauke ki na kai ki gidan daulaa yin ayki shine har kika koyo sabon sallon lalata in banda kuka da girgiza kai ba abinda yasmin din take, har yanxu bata daina jin radadin marin da tai mata ba, laluban aljihun rigar ta ta shiga yi ayko taci karo da 1000 ragowar kudin da mami ta bata,  gidan uban wa kika samu kudi ehh?? Wato mu muna nan muna fama da kan mu ammah ke kina nan kina more rayuwar ki koh? Waye ya baki? ta daka mata tsawan da nan take jikin ta ya dau kerma hawaye kuma suka shiga yin ambaliya akan kyakkyawar fuskar ta& & .


Ya jama a yasmine tayi goshi=؃?=؃?

And finally yau dai Allah yayi ta hadu da omair suraj shugaban marasa M=??



INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY)

BY moon


chapter 6:  The Man Who Healed, The Man Who Hurt


*****



Bata san sanda tace  mami ce ta bani na sayo mata kanwa kallon irin kin rena mun sense din nan ammah ke bin ta da shi kafin tace  ni zaki renawa hankali? Kanwa a cikin wannan dankareran gidan? an gaya miki ni yarinya ce da zan yarda da karyar ki? Ko kuma an gaya miki ni sha sha ce? Girgiza kai yasmin tai kafin tace  da gaske nake miki ammah kin san bazan miki karya ba, sirikar ta ce zata xo yau shine tace tana son cin danwake, ta tambaye ni nasan inda ake saidawa nace mata ehh shine ta bani kudin ta ce na sayo mata, in ma baki yarda ba ki kira ta ki tambaya ta fada a tsorace don sam bata saba karya ba wannan karan ma bata san ya akai ba taji tana zuba zance haka don bata da jurar yin magana me yawa balle ma har tai karya ko musu da mutum, Shiru ammah tai tana studying face din ta kafin ta cilla mata kudin tace  duk ran da ta baki kudi karki sake ki taba ko sisi ki kawo mun su nan, in ko ba haka ba na kama ki da su wallahi se kin yi dana sanin haifar ki da akai, fice ki ban guri da sauri ta dau kudin ta fice daga dakin jiki na rawa, ba wai ba zata iya bata kudin bane ba, kawai ta san da ta bata shikenan ta kara bude ma kanta kofar ta kura a cikin gida. Ko abba batai ma sallama ba ta fice daga gidan&

Tana xuwa titi ta hango motar na jiran ta, shiga tai bakin ta dauke da sallama, amsa mata habu yai yace  sannu da fitowa preety yau an makara looking at another direction tace  ya kuri, kuma sunana yasmin murmushi habu yai yace  kaji wani suna irin na larabawan misra, Daman ni ina ganin ki na san cewa ke fa ba pure er nageria bace ba, ammah jin sunan ki yau ya kara tabbatar mun da haka. Banza tai masa ya cigaba da surutun sa shi kadai. Kamar wacce aka tsikara haka kawai taji harsh words din guy din jiya na dawo mata, ita tun da take wani na miji be taba mata haka ba saboda ita bata shiga harkar kowa balle ma a zageta har haka, daman dai ammah zagin ta ya zama mata abinci da sha don haka baya daga mata hankali but surprisingly wannan se crossing mind dinta yake. Vibration din wayar ta ce ya dawo da ita daga duniyar tunanin da take, tsirawa number din ido tai na tsawon lokaci kafin daga bisani tai picking ta kara a kunnan ta, Shiru tai bata ce komai ba, daga daya bangaren taji an ce,  Alhmdllh!! Alhmdllh!! Allah na gode maka, I thought I lost you na dauka you won t pick up my call, ammah na gode sosai am over the moon, thank you so much thank so so much for picking my call shiru tai don sosai ya bata mamaki jin yadda yake magana with full of excitement kamar wanda akaima Albishir da gidan aljanna all in the name of tayi picking call din sa, cikin sanyin murya tace  Assalamu alaika  wa alaiki Salam ya yana me Jin natsuwa a cikin ransa.  kiyi hakuri ina ta damun ki da kira and early in the morning naxo ina cika miki kunne, Im so sorry kin ji? Ya fada a hankali, jin tayi Shiru ne ya sanya sa cewa  hello? don ya zata ta katse wayar ne,  hello ta bashi amsa,  Hi& I hope I m not disturbing.  It s me, hakeem the man from yesterday ta kula duk ya daburce ya ma rasa ta ina xe fara, ganin hakanne ya sanya ta fadin  na tuna, ina kwana  lfy kalau Alhmdllh  masha Allah daga haka tai shiru, shi yai breaking salience din da fadin  i noticed that you don t talk that much you preferred listening that talking right? Shiru yasmin tai tana wasa da dogayen nails din ta, kafin tace  Eh daga daya bangaren yace  That s fine Some people talk less but mean more. I like that about you daga haka kuma shiru ya dan wakana kafin cikin natsuwa sosai yace  in kin ban dama ina son inyi introducing kaina, that s in kin ban dama cikin natsuwa tace  ba damuwa cikin muryar sa me dadin saurara ya fara magana kamar haka  My name is Hakeem Suleiman moddibo. Ni likita ne psychotherapist. Ina aiki a Hayat Specialist Hospital, am 29yrs kuma ni asthmatic ne, I live with my parents a nasarawa, I think that s all about me, ohh na tuna, I help people deal with emotional pain and mental stress& amma tun ranar da na ganki, it s like my own heart found peace. A hankali ta sauke numfashi, ta ma rasa abun fadi, ganin kamar in tai shiru bata ce komai ba yayi sounding rude ne ya sanya ta fadin cewa  ohh masha Allah daga haka tai shiru, she didn t mean to sound rude or something like that kawai dai bata saba bane ba this is her first time da meeting someone like him.  Now you know me a little. Tell me about you, ko sunan ki

7 / 14