INUWAR KADDARA BOOK COMPELET BY MAIMOON

Author :  Maimoon Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 14

12K to 15K   out of 40K words

tai miki haka da fuska? Ta fada tana sauke idonta kan fararen hannun ta sukai tabon duka sakamakon using dinsa da tai as a shield, wani ashar saddiqa tai kafin tace  kina uban me kike yi tai miki kalar dukan nan baki gudu ba ehh? Saboda ke gaki damo sarkin hakuri koh? Toh Wallahi ki jirani a nan in dauko hijabi na akwai abokin masoyi dan hisba ne Wallahi gunsa zamuje mu shigar da report ay zalincin yayi yawa kuma fisabilillahi da sauri yasmin tace  dan Allah ki bari kinsan banson tashin hankali, lefina na ne ni nai mata lefi dan Allah a bar maganar nan kin ji saddiqa? na barta da Allah kawai baki bude saddiqa ke kallon yasmin kafin tace  kin fi son ki zauna ta kasheki koh? Toh in ta kashe ki kema kina da xunubi don baki temaki kanki ba, kuma ni wallahi bazan zauna in xuba ido ana aykata barna ban hana ba tana fadin haka ta juya ta koma cikin gida, ita dai yasmin ta bita da kallo daga karshe ta cigaba da tafiya a hanakali don har yanxu jiri take gani sosai.

Daidai inda yai parking jiya ta hango motar, da sauri ta karasa ta bude motar ta shiga, a hankali tace  ina kwana? Na barka kana jira koh da sauri yace  Lfy kalau emmata, a a wlh ba komai yanxu ma na karaso ya fada yana tada motar. Tunda suka fara tafiya take Jin kamar ana rugurguza kashin ta da guduma, hakanan tai lamo jikin kujeran gamida dan rufe fuskarta da hijab dinta, se da taji ya kashe motar sannan ta bude idon ta a hankali jiki kuma a sanyaye ta fice ba tare da tace dashi komai ba. Ko da ta isa bakin kofar shiga parlorn hannu ta kai ta danna bell din jikin kofar, ba jimawa akazo aka bude, wata mata ce wacce a shekaru zatai 40 years fara sal da ita kuma er chubby chubby da ita, kallon juna kawai suka tsaya yi kafin daga bisani ta matsa ma yasmin din ta shigo ciki, a hankali yasmin tace da ita  good morning da sauri matar tace  morning yasmin ta fada tana dan Murmushi, da mamaki yasmin ta kalle ta Jin ta kira sunan ta, a karo na biyu matar tace  nice bahar and I believe that kinji magana ta agun mami sosai mamaki ya kashe yasmin Jin yaddatai hausar kamar bahaushiya, watsar da wannan tunanin tai kafin tace  ehh ta fada mun barka da isowa daga haka ta shige ciki tabi bayan bahar data danyi gaba,  I have cleaned up everywhere, yanxu abunda zamuyi shine girki, mami tayi list din abubuwan da za a dafa ma bakin yau and i believe that you will help me make them with respect yasmin tace  sure daga haka ta karasa cikin katafaren kitchen din tanajin kamar zata kife kasa don ba karamin jiri take ji ba.

Koda suka shiga kitchen din bahar ta mika mata wata piece of paper tace  these are the list of the dishes we are to make  a hankali ta sa hannu ta amsa,  zobo, dambu, fried rice with roasted chicken, kunun aya, se wasu sunayen abincin da bata ma taba Jin sunana su a duniya ba, mika ma bahar tai kafin tace  toh da wanne za a fara? Dan jimm bahar tai kafin daga bisani ta ce,  let s start with dambu and roasting the chicken, though I have already marinated the chicken and also zobon ma anyi boiling dinsa tiger nut drink kuma was made since in the subh ta fada tana me fito mata da vegetables, haka nan suka shiga yin girkin ba ji ba gani don she was told by bahar that guest din will arrive by 12pm don haka suke ta ayki ba tsayawa, bahar se hira take mata gamida mata tambayoyi don she was impressed by the girl s cooking skills, haka dai sukai ta aykin se 11 suka gama, wani iko na Allah se kuma taji duk zazzabin ya barta kawai dai ciwon kai ne ke dan damunta, tunda ta xo bata hadu da mami ba se da bahar tai using telephone din kitchen din ta kira na gurin ta se gata after few minutes ta shigo kitchen din da shigar alfarma, da ladabi yasmin ta gaishe ta ta amsa mata cikin sakin fuska, harta wuce ta dawo looking at her face kamar me son gano wani abu, ganin kallon da take mata ne ya sanya yasmin din yin kasa da kanta  what happened to you Jasmin? Your face wasn t like dis yesterday, meya faru? Dan Shiru yasmin tai tana tunanin me zata ce mata, can tace  faduwa nai ta fada a takaice, jimm mami tai kafin tace  sannu akwai ointment a room zan dauko miki anjima  ngd ta fada slightly, mami bata ce mata komai ba se bude tsadaddun warmer din da ta shiga yi daya bayan daya, nan take aroma ya cika ko Ina da ko ina na kitchen din.  Mami ina kika samu great cook haka? She s so good ni kaina se kallonta nake kawai don sosai ta birge ni bahar ta fada tana kallon yasmin da ta sunkuyar da kanta kasa, murmushi tai kafin tace  se dai na gode Allah don da alamu nayi sa a kam, yanxu kuje ku huta don ba abunda ya rage kume se in sun xo ne za ai serving dinsu mami ta fada tana me kai glass of hibiscus drink din bakin ta, ba musu suka nufi hanyar fita daga kitchen din bayan bahar ta daukar masu nasu breakfast din don basu samu Daman yi ba saboda ayki.  tsaya yasmin Chak ta tsaya ita kuma bahar tai gaba daya breakfast din nasu, mami ce ta karaso kusa da ita kafin tace  meya samu fuskar ki? Nayi noticing ba iya face dinki bane ba and it clearly looks like kamar dukan ki akai, fadamun gaskiya a gida ne aka dake ki haka? Ta kare maganar a sanyaye, se da tattaro natuwarta sannan ta fara magana don ba abinda xe sa ta fada mata gaskiyar abunda ya faru  a a ba a gida bane ba a islamiyyah ne aka zane duk en ajin mu Shiru mami tai tana nazarin abunda ta fada kafin daga baya tace  ammah kuma kuna mata suke maku kalar wannan dukan? Dis is not fear at all look at you face for goodness sake, ya kamata a samu ay ma masu makarantar magana don be kamata ba, zan turo nazli ta baki ointment ki saka taga haka mami ta fice daga kitchen din. Tana shiga dakin taga bahar takai mata abincin nata don haka ta zauna nan kasan carpet tana sauke ajiyar xuciya don yanxu kuma zafi take ji da yunwa don haka hannu a hankali ta shiga cin lafiyayyen breakfast din da bata taba cin wani abu me dadi kalarsa ba don yaji spicies da sauran Kayan girki da ita bata taba ganin irin su ba.

Guraren karfe 12:5 taji ana knocking door din da take ciki, a hanakli ta mike ta bude taga bahar ce, Murmushi ta dan sakar mata, itama bahar tace  mami tace the guest are here a hankali ta furta  ohh tana me fito wa daga dakin, gabadaya she s feeling so awkward kasancewar tana ayki tare da bahar dan a haife bahar ta haife ta shisa ma bata iya kiran sunan ta ko abu take son ta tambaye ta sedai kawai tai mata magana. Tun kan su karasa parlon sama take jin kamshin perfume kala kala iri iri, kanta a kasa take tafiya harta nufi inda dining table din yake ta aje warmer din dake hannun ta, jin bahar na gaida bakin ne ya sanya ta matsa wa kadan ta durkusa har kasa ta gaida su ba tare da ta kalle su ba, su 5 ne a dakin, mata 4 da namiji 1, cikin su kadan ne suka amsa don duk ragowar hankalin su na kan smartphones din su, ganin hakanne ya sanyata mikewa a hanakali ta tashi ta bar gun, muryar wata tsohuwa ta jiyo tana cewa  ke kuma Amina ina kika samo wannan yarinyar ko itama tsintar ta kikai a turkiyan? Tsohuwar da suke ma lakani sa suna hajja ta tambaya tana me kai fruit din da ke gabanta baki gamida bin yasmin da ido kamar zata cinye ta, Can kuma facalar mami wacce take auran kanin daddyn su nazli me suna aunty fiddou tace  Kinga mami garin kwashe kwashen nan naki wataran se kin tsinto aljanu don ita kanta wannan ni ina da ayar tambaya a kanta Jibe ta fah? Se a lokacin matashiyar macan da zatai sa ar nazli da brother dinta wanda xeyi 28 years haka suka dago kai suka dubi yasmin da ta juya baya zata bar gun, can kan cushion daban wata mata ce ta sha shigar alfarma, a shekaru zata kai mami, suna kiran ta da hajiya karama don sunan ta daya da hajja wato safiyyah, wacce tunda ta xo take ta fama pressing phone din ta don ko cikakken gaisuwa basuyi da mamin ba, daman ita waya shine abokin hirarta don takan iya shafa hours tana danna waya ba tareda da tace wa kowa uffan ba, jin maganr da su hajja ke ne ya sanya ta dago kai gamida yamitse fuska tace  wai wata yarinya ake magana akai ne? Aunty fiddou ta bata amsa da fadin  maid din mami ce na ganta kamar ba mutum ba " a karo na biyu hajiya karama ta yamitse fuska tace  as in? Tai maganar a takaice tana kallon bayan yasmin dake sauka daga stairs din, still aunty fiddou ce ta kara bata amsa da fadin  the girl is hella beautiful bata kara cewa komai ba se maida idon ta kan mami da tai wacce was busy helping bahar gun arranging dining table din don suyi sauri, se da ta ga mamin zata juyo se ta dauke kai ta maida kan wayar ta da take dannawa,  the dining is ready mami ta fada tana jama hajja kujerar da zata zauna. Gaba daya se yaba abincin suke ta yi banda hajiya karama dat was just playing with her spoon, ba kuma don abincin be mata dadi bane ba, kawai dai halin nata ne ya matso though she s always moody. Seda sukai nisa gun cin abincin sannan er aunty fiddou me suna yusra fadin  mami where s nazli? Ko ba tare kuka dawo bane ba charaf aunty fiddou ta amshe da fadin  ayy ba zata fito ba jira take muje har daki mu gaida ta mami dai bata tanka ba don tun dazu taje room din taji ta a toilet wai wanka take where as ita da sassafe take wanka duk don kada ta hadu da familyn baban nata shine take using din shiga wanka as an excuse, daidai hajja ta bude baki zatai magana se ga nazli nan ta shigo parlorn kana ganin yadda take frowning face din ta kasan she s not happy to see them at all, seda ta xo dap da su sannan tace  Good afternoon everyone, sannun ku da xuwa ta fada tana zama kan dining chair, cousin brother din ta wanda shine da daya agun hajja karama me suna hateem se binta da kallo kasa kasa yake kamar xe cinyata don rabon da su ganta anyi kusan 6years don yanxu ma se da hajja tai magana sannan suka dawo nigeria don sam in akwai inda basu son xuwa toh nigeria ne, suna hada ido da hateem ta galla masa harara don sam bata manta bakin halin sa ba da rashin M din sa don ko yaxo gidan su ma turkey bata ma shiga harkar sa saboda girman kansa da halin shariya irin na mahaifiyar sa hajiya karama daya kwaso.  kaniyarki naazli, nace kaniyarki, mu zaki gaishar a gantale kamar wasu en iska? Halan bakisan matsayin mu a gunki ba ko? Toh Wallahi ki kama kanki in ba haka ba zamu saka kafar buje daya dake cikin nigeria ta fada tana kankance ce idanu, turo baki nazli tai kafin tace  granny daga xuwa na harkin fara mun fada daga gaisheki ta fada kamar zatai kuka, mami ce ta daka matsa tsawa gamida hade rai tace  will you keep quiet ko se na baki dirty slap? Hajjar sa ar kice? Mami ta fada kamar zata doke ta,  hmmm daga baya kenan aunty fiddou ta fada tana kai spoon din ta baki daga haka kuma ba wanda ya kara cewa komai a gun se da suka gama tasss sannan yasmin ta shigo do min dauke kwanukan, cikin natsuwa take xuba su cikin wani medium sized luxury basket, gabadaya ta kagu tai abin da ya kawota ta bar gun, dan gabadaya a takure take a gun, tunda ta fara kwashewa bata yarda ta dago idanun ta ba har ta gama ta bar gun, tana isa kitchen din ta sauke ajiyar xuciya, ta juye plates din cikin sink ta shiga washing dishes din& .


*******

Zaune yake kan kujera ta alfarama yana going through wasu sabon motoci cikin mackbook din sa babu wani walwala kan fuskar sa, can gefen sa kuma wani mutum ne ke kwance kan wata tsarariyar cushion 3 seater yana wasa da yo-yo hankalin sa kwance kamar wani karamun yaro, rintse idanu omair yai don gabdaya karar yo-yo din takura masa yake kuma nazir din ya san be so hasalima intentionally yake don ya saka sa magana,  would you stop that already? Ya fada sounding so pissed up, Jin abinda ya fada ne ya sanya nazir din yin murmushi don abunda yake nema ya samu don haka ya mike zaune, daidai ya bude baki zeyi magana kawai akai knocking door da sauri nazir yace  come in wani kallo omair ya bishi da shi Jin abun da yace, PA din sa ne ya shigo yace  good afternoon sir be amsa gaisuwar ba se fadin  proceed da yai hakan ya sanya PA din fadin  your schedules for today is as follows& 1:00 PM Lunch meeting with potential investors regarding Dominion Auto s expansion, 2:00 PM Inspection of newly arrived vehicle models in the showroom. 4:00 PM Strategy meeting with senior management, 5:00 PM Preparation and briefing for tomorrow s court appearance and 6:00 PM Review and approval of pending reports and emails, that will be all for today, sir. can kuma se yace  also& sir regarding the girl that.. daga masa hannun da omair din yai ne ya sanya shi yin shiru da bakin sa yana me jiran Jin abinda xe ce masa  Cancel the 1 PM meeting, Push the 4 PM to tomorrow and make sure I m not interrupted dan Shiru PA yai kafin yace  ohk sir.. ya nufi hanyar fita daga office din kamar daga sama yaji yace  call the receptionist nan ma ya amsa masa da Ohk sir. Duk wannan abun da ake Nasir na zaune ya saki baki da hanci yana kallon ikon Allah . After a while se ga knocking din receptionist din nan, can kasa kasan makoshi ya furta  come in nervously take tafiya dan yaune karonta na farko da ta taba shiga office din sa kuma gashi ta san ba alkhairi bane kiran da yai matan ba, after kusan 2mins da shigowar ta ya sauke medicated glasses din sa ba tare da ya dago ba ya fara magana  who came here yesterday? Ya jefa mata tambayar, Jin ta yi Shiru ne ya sanya shi dago kyawawan idon sa yai mata wani sharp kallo daya sanya xuciyar ta buga wa, kusan a fusace a kuma gadarance yace  I asked you a question. Murya ba rawa tace  S-sir& a girl came. She said she found your wallet but  But? yai interrupting dinta coldly, ta hadiye wani abu daya tsaya mata a makoshi sannan ta cigaba da fadin She didn t have an appointment, so I told her you were unavailable.  She came all the way here& to return something that belongs to me amma you sent her away? nan ta shiga defending kanta da fadin  sir, it s protocol. No one sees you without Protocol? ya tambaya sharply kafin ya kara da cewa let me make something clear, If someone walks into my company with honesty you don t send them away like they re nothing.  I m sorry, sir.. ta fada kamar zatai kuka Lura da nazir yai ba daina mitar abun xeyi ba ya sanya shi fadin  Kinga dismissed we will handle the situation shi dai be kara cewa komai ba se maida hankalin sa da yai can smartphone din sa, da kamar kar ta tafi ammah da ta tuna yadda take Jin labarin kusancin nazir din da shi se ta fice don tasan tunda nazir yasa baki toh an yafe mata har gaban abada&

 Nazir get out of my office banza nazir yai masa kamar beji me yace ba, ajiyar xuciya yai ya dauke idon sa daga kallon nazir din, gabadaya friend din nasa sai testing patience din sa yake more especially wanna dawowar da yai Nigeria don he s just finding any possible excuses da xe yi amfani da shi don ganin yayi getting on his nerves, don dai shi ba biye masa yake ba amma da tuni sunyi hannun riga, shiru ne ya wanxu na kusan 5mins

5 / 14