INUWAR KADDARA BOOK COMPELET BY MAIMOON

Author :  Maimoon Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 14

15K to 18K   out of 40K words

can dai nazir ya maida kallon sa kan abokin nasa yace  look omair saboda wallet zaka ringa acting haka? A zafafe ya juya ya kalli inda nazir ke zaune yace  keep your damn mouth quiet karka karasa batan rai pls, my concern is that my contact card, membership card and my driving license are all inside the wallet and kaima kasan how important those items are ya fada looking so disturbed and annoyed, er dariya nazir yai kafin yace  toh dai ka yakuri, kama gode ma Allah yarinyar me gaskiya ce coz da ba haka ba da ba abinda xema saka ta taxo nan talk less of emailing you  look it doesn t matter ya fada yana me kallon wani direction din daban  bara zanma KB magana se a bashi address din ta yaje ya amsa, is that Ohk for you? A takaice yace  no dafe kai nazir yai yace  Wallahi omair kafi yaro dan karami damuwa, kai ba a taba birge ka koh? Toh shikenan do what suits you yana fadin haka ya dau belongings din sa ya fice daga office din, don daman yana nan patient suna jiran sa. Tsaki omair yaja yana jin ransa na mugun baci, saboda batan wallet dinnan nasa jiya se kwana yai a apartment din nazir gashi harta logage dinsa a cikin hotel room dinsa yake don kayan da xe sa ma da wasu kayan amfanin sa se da suka tsaya suka siya a wani supermarket even though nazir yayi insisting da yai using nasa outfits din ammah yace shi sam baze saka kayan nazir din ba duk da ko kayan sabbi ne fill a ledar su. Wayarsa ce tai kara alamun shirowar message, a hankali ya bude kyawawan idanun sa ya daura a kan screen din wayar tasa, tsaki yaja bayan ganin message din nata, daman ya san message din ta ne don tunda ya kunna wayar tasa ita da en MTN suke rige rigen masa message, batai worthing time din sa ba don haka bema bude ya karanta message din nata ba, after a while ya kara tunawa da wallet din sa that s with a stranger hakan ya sanya ransa kara baci don haka ya kai hannu ya dau wayar direct cikin email din sa ya shiga wanda tun jiya yaga email dinda tai masa amman ya ki yin reply saboda he doesn t feel like doing so, after a while yai replying da  Ohk, bring it yourself  yana tura email din ya dire wayar a gefe gami da mikewa tsaye ya nufi kan full body massage chair din dake office din ya zauna yana me adjusting necktie din da ke wuyan sa, sam jiya be samu damar bacci a apartment din nazir ba even though daman tun can shi he s a night owl ga kuma surutun nazir ya cika shi da shi wanda se da akai sallar asuba sannan nazir din ya kwanta, shikuma 8 ya taho gun aykin ba tare da ya bi ta kan nazir dake ta sharar bacci ba, shine kuma by 11 ya biyo sa nan office din nasa ya cigaba da takura masa& & ..


Dan Allah wa xe raka ni muje muyi ma Yasmine duka ne? yarinyar sam bata da karsa shi=??

Toh dai ga me wallet ya bayyana Amman fa kamar bakin haki gare sa=??

Gaskiya naso ace saddiqa ta kira en hisba sunyi gaba da ita=??


Su hajja anxo an kwashi girki Harda takeaway amman still ana taba bakin hali& ..




INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY..)


By moon


Chapter 5: One Saw a Liar. The Other Saw a Future.



YASMINE& ..


Gama wanke dishes din keda wuya wayarta dake cikin aljihun rigar ta ta fara ringing, da sallama bakin ta ta kai wayar kunne, daga daya bangaren saddiqa tace  ynx email ya shigo, wai yace ki kai masa can din dan jimm yasmin tai kafin tace  toh shikenan na gode daga haka sukai sallama, kamar daga sama taga nazli ta shigo cikin kitchen din, ointment din da mami tace ta bata tun dazu ta mika mata ba tare da tace mata komai ba, amsa yasmin tai tai mata godiya, instead of nazli din ta fita daga kitchen din se ta haye kan chair din dake kitchen din ta zauna ta cigaba da danna wayar ta a nan gun, ita dai yasmin ta cigaba da goge gogen ta, after some minutes se ga mami nan ta shigo, turus tai tana kallon nazli that was busy pressing her phone bama ta san da shigowar mahaifiyar tata ba, bata ankara ba taji an fizge wayar tata daga hanun ta, da sauri ta dago kai, hada ido tai da mami dake kallon ta rai a bace tace  get out ba musu nazli ta mike daga kan kujeran kanta a kasa ta bar kitchen din, mami ta bita da ido har ta fice kafin daga bisani ta maida kallon nata kan yasmin da ta maida hankalin ta kan abun da ke gabanta tace  bahar zata kawo takeaway a xuba ma hajja abinci a ciki tana fadin haka ta fice ta bar kitchen din ba tare da ta jira amsar yasmin din ba. Se guraren karfe 4 sannan su hajja suka tafi bayan an masu packaging takeaways din a cikin basket, suna tafiya ita da bahar suka kara tsaftace gidan yadda ya kamata suka saka turaren wuta a ko wani lungu da sako na cikin gidan, bayan tayi sallah ta ninke prayer mat din ta aje shi kan bedside drawer, dakin da bahar take ciki tai knocking a hankali sannan ta dan ja gefe ta tsaya, bude kofar bahar tai da alamu itama bata dade da idar da sallar ba don ta hango prayer mat a floor din dakin,  ummm aunty na idar, daman na xo nai miki sallama ne ta fada tana me wasa da gefen hijab din nata, daman bahar din ita ta sanar mata da sakon mami na cewa if ta gama aykin taje habu ya maida ta gida, murmushi bahar tai tace  toh Allah ya kaimu gobe da safe journey my dear daga haka sukai sallama ta fice, gabadaya se taji wani iri da taga mami bata wani kulata ba se take ji kamar tayi mata lefi ne, tana fita ta tadda habu nata faman goge daya daga cikin motar gidan, a hankali take takawa kamar bata son yin tafiyan don tana tuna cewa gida zata koma se mood dinta ya kara baci, ko da ta shiga motar se tunanin yanda zata cema habu ya aje ta a hanyar wannan car company din take don so taje ta bayar sannan ta wuce gidan, bata Jin zata iya fada masa cewa ya sauke ta a wani gun don haka tai shiru bata ce masa komai ba. Ko da yai dropping dinta se da ta tabbatar ya yi nisa sosai sannan ta tsari adaidaita ta kwatanta masa gun da ze kaita don akwai kudin da mami ta bata a pocket din ta& .

Ta tsaya a gaban Dominion Auto karo na biyu, amma wannan karon xuciyarta tana bugawa da sauri fiye da jiya. Yau batare da kauyanci ba kai tsaye ta nufi gun receptionist Win jiya wanda ta gane ta nan take. Tun kafin yasmine tai magana tace  good evening ma, thank you so much for your honesty Please, have a seat ta fada cikin mutuntawa. Yayin da receptionist din ke making call idonta yasmin ya sauka zuwa wani babban showroom, wanda wasu motoci masu tsada suke kyalli a ?ar?ashin wani haske, bata san sanda ta mi?e a hankali ba kamar ana janta ta taka cikin nutsuwa idonta ya kasa daina kallon motocin. Subhanallah&  ta furta a hankali tana me taSa Waya daga cikin motocin a hankali kamar ba gaskiya ba, nan fa gilashin ya nuna hoton ta kamar wata ?aramar yarinya a cikin babban duniya. Muryar receptionist ya dawo da ita daga duniyar da ta tafi da sauri ta nufe ta  let s go ma am nan ta shiga bin ta a baya kamar wata jela har suka shige elevator wanda xe kai su 4th floor wanda nan ne office din his excellency omair suraj yake=??& &

ko da suka fito daga elevator sosai take bin ko ina da kallo don gun ya burge ta saboda tsari da haduwar sa se mutum ya rantse yace ba a kasar yake ba duba da tsarin gun. A haka har suka isa bakin kofar office wanda kamar hadin baki duk su biyun suka ja suka tsaya, bayan tattaro jarumta receptionist din ta fara knocking door din kamar tana tausayin kofar, sau biyu tai knocking daga haka bata kara ba, seda sukai kusan one minute sannan sukaji ance  come in sauke ajiyar xuciya tai sannan ta kalli yasmin that look so pale tace  a nan zan barik ki karasa ciki  wato matar nan na Jin hausa shine tai ta saka ta turanci kamar a america . Ta fada cikin ranta a zahiri kuma tai saurin fadin  but-i bata jira jin maganar yasmin din ba tai saurin barin gurin, ajiyar xuciya yasmin tai tana me kara seseta natsuwar ta don haka kawai ta samu kanta da jin tsoran shiga cikin office din, after a while kawai tai bisimillah ta murda handle din kofar ta shiga cikin office din a hankali. Sosai ta shagalta da kallon haddaden office din nasa, the air was cool, perfumed faintly with something expensive, duk da yaji an shigo amma he didn t look up immediately, he was leaning back on his chair, one hand resting on the desk, the other holding a pen writing something in that sharp, precise way that matched his personality. Bakin ta dauke da sallama ta karasa shigowa, ba tare da ya dago kai ba ya amsa ciki ciki using his deep voice, kasa karasowa tai ta tsaya daga can nesa, a hankali ya dago kan sa yana me aje pen din hannun sa gefe guda, Just as she had imagined, his face carried the same cold perfection sharp, unreadable, impossibly elegant and heartbreakingly handsome, se da ta shafe kusan 1min be ce ba bata ce ba, can dai tai breaking silence din da fadin  ina wuni, Im the.. Strictly ya katse ta da fadin  who are you and who let you in? When he finally spoke, his voice was low and deep, it wasn t loud, but every word sound like an order. Chak ta chake don batai expecting hakan ba though tayi noticing kamar ba wani ishashen kirki gare sa ba duba da yadda ya barta nan tsaye kamar wata statue, bata ce masa komai ba ta saka hannun ta cikin hijab dinta ta zaro wallet din that was inside her pocket ta nufi inda table din nasa yake tai dropping din sa kafin nervously tace  dis is what brought me here  Where did you get my wallet? Ya jefa mata tambayar, shiruu ta danyi kafin tace  na faWa jiya& I found it on the road  And you expect me to believe that? Nan take hawaye ya cika idonta muryarta na rawa tace  Wallahi ban dauki komai ba duk wannan abun da ake bema dago ya kalle ta ba  you think you can walk into my company and lie to me? Yafada gami da kai hannu ya dau wallet din ya shiga cire, driving license, ID card, black card, contact card, da membership card din sa da kuma wasu cards din da bata san na me ba, Jin ta yi Shiru bata bashi amsa bane ba ya sanya shi dago idanun sa masu cike da kwarjini ya daura a kan nata da hawaye suka cika shi famm, ita tai saurin daukewa tana Jin kirjin ta na bugun dubu dubu, mamaki ne ya cika shi sedai be bari hakan ya nuna a kan fuskar sa ba  here for your honesty ya fada yana tura mata wallet din gaban ta ba tare da ya cire dollars din dake ciki ba, a sanyaye tace  I didn t do it for money  everyone does something for money ya fada looking at another direction daban, kamar daga sama muryarta me sanyin dadi ya sauka kan kunnan sa tana fadin  not everyone sir and that includes me tana fadin haka ta juya, sosai yaji zafini amsar data bashi don ji yai kamar ta kunduma mashi zagi, he s unused to being challenged don haka da sauri ya dago idanun sa ya daura a kan yasmin wacce take daff da fita daga kofar,  you are either arrogant or stupid&  kamar wacce aka xuba ma ruwan zafi a jiki haka ta ji dan haka da sauri ta juyo ta kalle shi, shima kallon ta yake direct cikin ido, bata taba zatan cewa aykin alkhairin da tai xe jawo mata zagi ba da tun farko bama ta soma ba, anyi mata abunda ya tattaka wannan ammah sam bata damu ba amma shi kam abun da yai mata ya sosa mata rai har bata san sanda taji idanun ta na yunkurin kawo ruwa ba a karo na biyuu& .

Ta shafe kusan 30mins a nan tsaye bakin company din bata ga adaidaita ko daya ba se manyan motoci dake wucewa kamar ruwa gashi yamma tayi, nan gun ta durkushe ta rike kanta dake mata wani irin ciwo, can dai ta mike, duk da dai akwai dan tafiya tsakinin babban titin da inda take ammah ganin if ta tsaya anan zata shekara bata samu abun hawa bane ba ya sanya ta mikewa ta fara trekking, har ta kusan isa titi se ga wata hamshakiyar mota da ta dan jima kadan da wucewa ta dawo baya tai parking daidai inda take, sam bata lura da cewa ita motar ta tsaya wa ba don haka ta ciga ba da tafiyar ta kan ta a kasa, ganin hakanne ya sanya me motar yin gaba da ita kadan gami da yin parking, se da ya ga ta iso inda motar tasa take sannan ya fito daga ciki. Kyakkyawan gaske ne na ajin karshe kana ganin sa kaga dan kwalisa me class, dumm taji xuciyar ta ta buga ganin mutum ya tsaya yana kallon ta, da sauri ta wuce sa tana ta faman adduah a ran ta don ta tsorata da ganin mutum a gaban ta haka nan, ganin yana binta ne ya sanya ta kara saurin ta, shima kuma hakan yasa ya kara don kada ta bace masa, can dai ya lura da cewa ta tsorata don haka ya ce  Assalam alaiki, yakuri baiwar Allah ki tsaya ba cutar dake zanyi ba sarai taji me ya ce ammah tai banza da shi ta cigaba da tafiyar ta duk da dai ta dan ji relief da yai mata magana ba wai cigaba da binta yai ba without saying anything ba, haka bawan Allahn nan ya ringa binta har suka kusan isa titi yana mata magiyar ta tsaya ta saurare shi ammah sam ta ki kulasa, se da taga dai da gasken ba daina binta xeyi ba unless ta bashi attention din ta sannan ta dan rage saurin da take hakan yasa ya samu ya cin mata, ajiyar xuciya ya shiga yi kafin yace  Im so sorry ina ta binki nasan na bata miki rai ya karasa maganar da kyar yana me kai inhaler din sa baki wanda hakan ya tabbatar mata da cewa he s asthmatic, ita dai bata ce masa komai ba har ya gama inhaling inhaler din sannan ya kara da cewa  kin sani exercise din da ban shirya ba, anyways it worth it. well& sorry to say young lady but I won t stop following you unless kin ban attention din ki still batai responding masa ba ta ci gaba da tafiya duk da dai ba sauri take ba wannan karan don tun da ta ga ya fito da inhaler se kuma jikin ta yai sanyi don tasan kalar wahalar da masu asthma ke sha don wata classmate din ta na dashi. a haka suka cigaba da tafiya har suka iso main road, nan ma dai Shiru ba nappep din ko anguwar ta manya ce shisa ake wuyar samun nappep din, Ki yi hakuri nasan is not proper for me tna tsayar dake on the road, but wallahi, something in my heart moved when I saw you. I don t even know your name, but I already know I want to spend the rest of my life making you smile, I want to know you& to understand you& and, if Allah wills, I will spend my life cherishing you, so pls my lady give me a chance, please ki taimaka ko number din ki ne ki bani so that ma yi magan ta waya ya fada kamar ze yi kuka, ajiyar xuciya yasmin tai, she could feel the sincerity in his voice, tabbas da ya san ita wacce ko kuma ya natsu ya kalle ta da tun farko be wahalar da kansa ba ya biyo ta har nan, don ita da shi ma ba hadi sam don kallo daya za kai masa ka gane cewa he was born with a silver spoon in his mouth, katse mata tunani yai da fadin  please!!! Ya wani ja kalmar please din kamar yaro karami wanda hakan ya sanya wani murmushi escaping through her lips ba tare da ta sani ba, wayar sa ya ciro ya mika mata making a puppy eyes yace  dan Allah ki sa mun kuma karki ban wrong number samun kanta tai da amsar wayar ta saka masa number din nata, kiran layin yai se gashi keypad din ta ta fara ringing,  kiyi picking call din mana? Ya fada yana tsare ta

6 / 14