INUWAR KADDARA BOOK COMPELET BY MAIMOON

Author :  Maimoon Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 14

6K to 9K   out of 40K words

san dai ba abunda zaki nema na hanaki sedai in bani da shi koh?, dan haka waya ko kwana kike so tayi a gunki bazan taba ce maki a a ba Murmushi yasmin tai gamida sunkuyar da kanta kasa kamar tana gaban ta, tabbas saddiqa nada kirki matuka don ba don ita ba da tuni ciwon zuciya ya kashe ta.  Toh na gode in sha Allah inna dawo nasan kin fara suyar awara se na biyo na amsa na gode daga haka kuma sukai sallama. Tana aje wayar taji cikin ta na kuka hakan yasa ta dubi kayan ciye ciyen da mami ta bata, kamar ko ta sani ta zabo mata wanda zata iya ci. Wani biscuits me dan girma ta dauka da wani juice, ta fara ci a hankali, se da taci taji ya isheta sannan ta sanya ragowar cikin aljihun ta. Gama cin nata keda wuya taji wani bacci na yunkurin yin awan gaba da ita ayko ta kwanta nan Kasan carpet din ba jimawa ko bacci me dadi yai awan gaba da ita.

 Jasmin!!! A hankali ta bude idanun ta da sukai mata nauyi, ta sauke su kan mami, da sauri ta tashi zaune tana faman rufe dogon gashin ta.  Ashe kwanciya kikai?? mami ta tambaya tana zama gefen gado, gabadaya ta ji ta takure se Kace wacce ta Aykata katon sabo murya na rawa tace  ban sani bane bacci ya dauke ni Murmushi mami tai don ta kula da halin da ta shiga,  toh tashi kiyi sallah, zan ayki habu se ya maida ki gida koh? Toh kawai tace sannan ta mike ta nufi inda take da tabbacin cewa toilet ne. Koda ta fito bata ga kowa a dakin ba, tunani ta shiga yi akan inane gabas, tsoron kada ta sallaci inda ba daidai ba ne ya sanyata fita daga dakin. Zaune take a parlor ta mimmike kafa akan kujera se faman pressing phone take, har Yasmin ta karaso parlors bata sani ba don hankalin ta yayi gaba na kan abunda yake yi , tsayuwar kusan 1min tai tana jiran nazli din tai noticing dinta ammah batai ba don haka ta tattaro duk wani courage din ta tace  dan Allah ina ne gabas? Se a time din ta dago ta kalle ta tace  where is where? Ajiyar zuciya Yasmine tai kafin tace  where s the qibla please? Dan jimmm nazli tai kafin tace  Ohhh there tana fadin haka ta cigaba da danna wayar ta, ko second daya bata kara ba ta bace daga gun, ta kula itama nazli tana da saukin hali duk da dai tsoronta ya shige ta tun sanda suka shigo ta bude musu kofa, tana idar da sallah ta fice daga dakin daidai mami na saukowa daga upstairs,  kin idar?  ehh mami ta fada tana wa sa da gefen hijab dinta,  iya number din parents din ki nake da banda naki, drop your number here mami ta fada tana me mika mata tsaddadiyar wayar tata, a hanakli ta saka hannu ta amsa, within seconds ta sanya mata number din nata mami tace  good gobe by 7 habu will come and pick you up coz akwai guests dazanyi and I need your hand a hankali tace  Allah ya kaimu kudi mami ta bata tace  ga wannan kisa credit marairaice wa tai zatai magana mamakin ta hade rai tace  have you forgotten about the promise you made?? Or lemme know if kinyi breaking promise din naki ne kanta a kasa tace  nooo mami, na gode Allah ya saka da alkhairi daga haka tasa hannu ta amshi kudin taima mamin seda safe. Seda suka bar layin sannan tace da habu  dan Allah in tambayeka mana?  jiki na rawa habu yace  laaa ay ba damuwa ina jinki tsabar zumudi Saura kadan yai balle da wani matashi dake kan scooter din sa, ayko yaron ya kumduma masa ashar, Sam habu be bi ta kansa ba don gabadaya ya tattare natsuwar sa yana jiran yaji me yasmine din zata ce masa, complementary card din ta zaro a hankali ta mika masa tace  dan Allah kasan wannan address din? amsa yai ya parking can gefan titi sannan ya shiga kallon card din, mika mata yai kafin yace  kwarai kuwa nasan gun ai ko wani matashi kika tambaya a kasar nan harda kewaye yasan wannan sunan, dominion auto ba? gidan motoci kenan ay ko a week dinnan ma se da na kai su hajiya kamar tana da halaka me karfi ita da me gun duk da dai ba wanda yasan fuskar me gun ko a social media sudai nasu posting pictures din motoci sedai customers din sa wanda suka taki sa a suka xo yana gun ko kuma ya gadaman haduwa da su amman kamar ance lawyer ne sunan sa umar ko omair? Ohoo dai amman dai ya san aykin sa gaskiya don duk case din da ya solver se yai wining haka naji ana fade, suna ma da branches fa har a kasar waje. Ita duk ba wannan bayanin ta tambayesa ba ammah se faman zuba yake kamar wani parrot, kasa yai da murya kafin yace  motar zaki saya ne kema? banza tai masa don ya fara bata haushi, ganin dai ba basa amsar zatai ba hakan ya sanya shi fadin  in xuwa zakiyi aise in kaiki don duk hanya ce shiru tadanyi tana nazarin maganar tasa, da taso kawai ta tura sako ta email din company din, ammah kuma hanaklin ta ya kasa kwanciya da xuwa da wallet din gida kada tsautsayi ya sa ammah ta gani ta shiga uku ta lalace don haka ta yanke shawarar kai wallet din harcan company din ko ma wa ta gani taba wa ajiya tunda akwai suna and lots of information za a gane koma na waye, don haka ta dago kai a hanakli sannan tace  toh na gode& 
(Anya habu be shiga uku ba da shegen surutun nan nasa ba? Ita kuma hajiya yasmine bakwa ganin don taga fuskar wannan bawan Allahn yasan ya ta daukar wallet din nasa instead ta bawa security guard?? Da gaske ne nazli nafa kirki kode yasmin makauniya ce bamu sani ba? =?? )

Thank for the love and dua=ؤ?
A cigaba da mun sharing xuwa groups, friends and family pls=?+?& & .


INUWAR KADDARA*



By moon


Chapter 3: The Wallet That Led Her to Him


*****

Dominion Auto wasn t just a company It was power.
Gini ne mai tsawo, an yi shi da gilashi mai kyalli, yana haskakawa kamar yana nuna wa duniya cewa shi ne ke da iko. Sunan DOMINION AUTO an rubuta shi da manyan haruffa masu azurfa a saman ginin wanda ba za ka iya wucewa ba tare da ka kalla ba, hakanan habu ya danna hanccin motar tasa after ya karbi entery card agun security guard, Koda suka isa parking lot nan suka fara arangama da Motoci masu tsada wanda sukai sahu sahu jere cikin tsari, kowacce mota tana kyalli kamar ba ta taSa ganin ?ura ba. daidai inda ake parking ya tsaya sannan yace  to mun karaso a hanakali tace  na gode Allah ya saka da alkhairi  in biyo ki ciki ne kokuma injira ki anan? ya fada yana me kallonta ta mirror, Sam bata dago kai ta dube sa ba sema yunkurin fita daga motar da ta shiga yi  a a nan ma yayi na gode da sauri habu yace  aa ke dai ki shiga ki fito ina jiranki anan coz hajiya ta dankan amanarki don haka sena karasa aykina sannan boyeyyar ajiyar xuciya ta sauke kafin tace  to bara naje na dawo daga haka ta shiga walking slowly towards the entrance door hannun ta rike da wallet din nasa gam, her fingers were slightly shaking kamar ance za a kwace daga hannun ta. Cikin ranta ta ayyyace cewa wannan gun it didn t feel like somewhere someone like her should enter, amma duk da hakan ta kara step daya xuwa gaban glass door din wanda ya sanya glass door din budewa automatically.
nan fa wani cool air yai brushing against her skin, wanda ya sanya ta zare idanun ta a tsorace sannan ta furta  Subhanallah ganin kofar zata rufe ne ya sanya ta saurin shige wa ayko ya rufe da ita. Shigarta keda wuya wani sanyi me hade da kamshi ya kara dukan ta wanda bata san sa adda tai folding hands dinta around her body ba, everything looks expensive ga wani Shiru da cikin gun ya dauka like people were afraid to make mistakes. Employees din are moving quickly, neatly dressed, and focused. Murmushi ko digo babu akan fuskar su saboda gabdayan su abu daya suka sani wanda shine  the owner doesn t tolerate nonsense.

Dakewa tai ta nufi reception area, inda wata well-dressed lady ke a kewaye da wani table da looked like it cost more than her entire life. The receptionist looked up, her eyes scanning her from head to toe, don yanayin dressing dinta is simple. Too simple for a place like this, Ammah duk da haka tai forcing polite smile Sannan tace

 Good afternoon and welcome to Dominion Auto Please, have a seat while I notify the manager of your arrival. Would you like a glass of water or perhaps some coffee while you wait? Da sauri ta girgiza kai sannan cikin rawar murya tace  no thank you Im not buying anything, rather looking for someone called OMAIR SURAJ murmushin kan fuskar receptionist din be dauke ba sedai ya canza ya zama controlled and more distant. Do you have an appointment? ta tambayi yasmin din calmly, girgiza kai tayi kafin tace
 No& but it s very important.  I m sorry, you can t see him without an appointment. Ta fada tana danna keyboard din computer dake gabanta, dan Allah, it s very important plss ma am ajiyar xuciya receptionist din tai kafin tace  look m sorry but the person you are looking for is the boss here and he is currently unavailable. Kamar zatai kuka tace  I have his item with me I just want to give it to him and go. Sam recepnist din bata bi ta kan zancan cewa wai akwai abun sa a gun ta ba, don sam in ba don kyaun da take da shi ba batai kama da wacce boss din su xeyi interacting ba har ta samu item din sa, mutumin da ko yayan governors or ministers suka xo sayan motanci basu isa su gansa ba indai ba suda appointment da shi. Don haka ko me wannan yarinyar ma zata ce mata bazata saurare ta ba balle har taja mata a kare ta a ayki Ana zaman kalau. on a serious note tace  He s in a closed executive meeting with external partners. No interruptions are allowed. Tai Shiru se kuma tace  even staff are not permitted to see him right now. dogon numfashi ta sauke cikin ranta ta ayyana cewa  wai yanxu dan adam ake hana gani haka kamar ba mutum ba wannan wani kalar jaraba ce can kuma kawai ta daura wallet din da take rike da shi tun daxu kan table din wanda ya sanya receptionist din ware idanun ta don tabbas ta ganshi da shi jiya da daddare da ce bar company din, muryar yasmine din ce ta katse ta da fadin  Can I just leave it for him? Shiru tai tana mamakin me wallet din sa ke yi a gunta can kuma se tace  You can, but all personal items must go through internal documentation and security checks which may take time before it gets to him Jin abinda ta fada ne kuma gashi yamma ta fara yi saboda lokaci ne na sanyi don haka tace  It s okay& I ll come back tomorrow  okay drop your number here tsabar mamaki ma ya sanya ta kasa cewa komai ta rubuta number ta bar gun tana mamakin shiko wannan wani kalan mutum ne haka da akejin tsoron sa har haka, tuna cewa habu na jiran ta ne ya sanya saurin ficew daga gun. Ko a hanya tunani kawai take ita mamakin ma da take shine Sam ita receptionist din batai tunanin ko zata gudu da item din da tace mata ba? Or duk cikin tsoron rasa aykin ne? ta jefa wa kanta tambayar. Koda habu yai dropping dinta godiya tai masa da adduar allah ya tsare hanya, kamar bakinsa ze yage ya amsa mata da  ameeeen adon gari. Bata kara bi ta kansa ba tai wucewar ta tabar sa.

********

Tundaga nesa ta hango gun suyar saddiqa makil da mutane alamun ta fara suyar kenan, so tai ta sallalba ta wuce saboda yawan mutanan wanda mostly maza ne ammah se saddiqar ta hango ta don haka ta karasa gunta tana dan sakar mata murmushi, mikewa saddiqa tai bayan ta sakarwa kanwar ta cokalin suyar awarar ta nufi inda Yasmin din take don tasan bata son shiga cikin mutane maaza ko mata. Sannu da dawowa yasmin har kin gama? Ta tambaya tana sakar mata murmushi, cikin sanyayyiyar muryar ta tace  ehh na gama  toh shikenan mu karasa cikin gidan saddiqa ta fada tana ruko hannun ta, da sauri tace  a a saddiqa kina aykin ki kuma? Ki bari kawai kije ki karasa kinga kar abar ma umma kayanta haka nan dan harara saddiqa ta jefa mata kafin tace  baki ga na bar ummita agun ba? Muje nidai dan Allah akwai maganar ma da nake so na miki daman bata kara yi mata musu ba ta bi saddiqar da ta rike mata hannu kamar wata er yarinya. Se da ta fara gaida mahaifiyar saddiqa wacce ta amsa mata da fara a sannan ta shiga dakin su saddiqar. A bakin katifar dakin suka zauna kaffin saddiqar ta mika mata wayar tata da screen din nata yai daka daka tsabar dakuwar da tai a kasa tace  gashi nan hannu tasa ta amsa kafin tace  bara nasaka sim dina naga sun ban kyautar 200mb da sauri saddiqa tace  a a ina da data dazu masoyi ya saka min bata ce mata komai ba se Murmushi da tai kawai ta shiga operating wayar. Email dinta tai login a cikin wayar kafin ta shiga tura sako kamar haka,
 Dear Mr.
I hope this message finds you well.
I happened to come across your wallet. It contain several important items, so I wanted to reach out to inform you as soon as possible. Please let me know the best way to return them to you. You can reach me through this email. Seda ta karanta sau biyu sannna ta tura, a ranta tana tunanin ko taba wa saddiqa ajiyar su zuwa sanda zeyi responding to her email ko kuma sanda za a kira ta daga can company din, mikewa saddiqa wayar tayi tace  na gode ba abunda saddiqar tace mata se hararar ta datai, sosai takejin haushin yadda yasmine din take treating dinta kamar ba kawarta ba ga dan bazan sanyin hali, tun tana kokarin canzata harta barwa Allah komai don a koina haka take behaving, saukin kanta yayi mata yawa. Ganin kamar da magana a bakin kawar tata ne ya sanya ta cewa  meya faru ne yasmin? Ajiyar xuciya tayi kafin ta kwashe labarin fita da sukai hartayi gamo da wallet din, daga karshe ta kare da cewa  ina gudun naje gida da wannan wallet din tsautsayi yasa ammah ta gani in shiga uku ta fada kamar zata fashe da kuka don harta hango abunda ze faru da ita, dafata saddiqa tai kafin tace  look ki dena ma wannan tunanin ba abunda ze faru, i will keep the wallet with me duk sanda suka neme ki se kixo ki amsa don sam ban goyi bayan ki tafi dashi gida ba coz any mistake game over mika mata wallet din tayi tace  gashi ki aje a gun naki bara naxo na karasa gida ta fada tana mike wa, dan bata rai saddiqa tai kafin tace  ayy dole kice zaki tafi na miki maganin problem dinki, yaushe rabonda mu zauna muyi hira and kinfa ji nace maki akwai maganar da zamuyi amma shine zaki ce zaki tafi? Ita wacce kike tsoro fa bata san kin dawo ba don haka ki zauna muyi hira ki huta don anjima inkin koma bazaki samu damar yin hakan ba. Murmushi tai kawai ta zauna saboda Jin me saddiqar zata fada mata. duk maganar da saddiqa take hanaklin ta ma baya gun don harga Allah tana matukar tsoron ammah don ba abun mamaki bane don ta taba lafiyar jikin ta ba,  yasmin! Yasmin? Wai kina ma jin me nake fadama kuwa? na am ehh. Me ki kace ehh ina jinki ta fada a hargitse, girgiza kai saddiqa tai kafin tace  ni nama yanke shawarar zan basa number din naki don idan take ne na kula so kike ki mutu a gaban ammah bakiyi aure ba da sauri yasmin tace  a a saddiqa nidai karki bawa kowa number na dan Allah  yasmin waike me yake damunki ne ehh? kinfi kowa sanin me kike fuskanta right amman kuma banga kina kokarin nema wa kanki ma fita ba, haka ma sanda inna tabarau tace zata dauke ki koma can mariri fur kika ki wai saboda Abby da siblings dinki wanda kinsan dai bazaki nunama ammah son  yayan ta ba ko? Kuma shi ma

3 / 14