INUWAR KADDARA BOOK COMPELET BY MAIMOON

Author :  Maimoon Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 14

9K to 12K   out of 40K words

abbyn mijinta ne tana son sa keme kin sani koh? Don son da take masa ne ma yasa ta tsane ki da late mom dinki so duk abun da zatai dole ta kula da lafiyar sa da duk abunda ya shafe sa, ammah kika ce waike a a, shi kansa abbyn zeso ki koma gun inna tabarau ammah kika ki har cikin ran inna bata ji dadin watsa mata kasa da kikayi a ido ba don nan taxo ta sami ummah tana mata mitar abunda kikayi, kinki binta kinki kuma yarda kiyi auran dukda dai aure lokaci ne ammah kema you are not trying at all saboda kin ki bawa kowa dama saddiqa tai maganar a dan fusace, daidai nan kanwar ta ta shigo da kwanun soyayyiyar awaran da umman su tace ta kawo ma su Yasmin din, hannu tasa ta amsa ta aje a gaban yasmin din that was looking at different direction, idanunta sun cicciko da kwallar da saura kiris ya xubo mata, matsar da plate din daga kusa da ita tai kafin ta matsa kusa da ita ta rungumo ta, a hankali take jin saukar hawayen kawar tata a bayan ta, patting bayan ta ta shiga yi kafin tace  kiyi hakuri ni ban fadi duk haka bane don nasa ki kuka ba, ammah kema kinsan cewa bazaki dauwwama a hakan ba ko? Inaga nafi kowa jin haushin ganin ki cikin wannan halin shisa duk nake kokarin samar miki mafita, I know you are trying your best kuma kina addua, in sha Allah komai xexo karshe very soon, and maganar munnir bazan sake ba balle ma na basa number dinki ta fadi hakan tana dago ta daga kafadar ta, tana share mata hawaye. haka ta ringa kwantar mata da hankali har suka samu suka ci awaran, bayan sun gama tai sallah daga nan kuma ta tafi gida bayan saddiqa ta raka ta hanya.

Bakin ta dauke da sallahma ta shiga gidan ta hadu da hafsa data shirya cikin uniform din Islamiyyah wanda hakan ya tabbatar mata da cewa makarantar zata, tana ganin ta ta rungume ta, with full of excitement tace  yaya kin dawo? Ya aykin? Se da ta raba jikin ta dana hafsa sannan tace  ehhh er albarka na dawo, yi maza ki wuce makaranta naga kin makara kar malam tasi u ya zaneki kamar tai kuka tace  toh yaya ammah dai inna dawo zaki ban labari koh? Gyada mata kai kawai tayi tana murmushi daga haka sukai sallahma tabi kanwar tata da adduar Allah ya tsare hanya, daga nan ita kuma ta karasa cikin gidan. Anan bakin kofar dakin su ta tadda ammah zaune tana sosar kunne da tsinken ashana, kan laps din ta kuma su twins ne ke kwance suna baccin su hankali kwance, sallama tai amma ammah bata amsa mata ba se dago kai da tai ayko suka hada idanu, da sauri yasmin ta sauke nata kasa tana Jin xuciyar ta na dukan uku uku, da kyar ta tattaro duk natsuwar ta kafin cikin rawar murya tace  sannu da gida wani gajeran tsaki ammah tai kafin tace  ke ni karki ishe ni kin wani xo kina rabewa kamar wata kadangariya, dallah xo ki wuce kije can tuka tukan kwanar masallaci ki deban ruwa ta fada tana gyara wa hasana kwanciyar ta.
Haka nan yasmin ta shiga debar ruwan ba ji ba gani, duk wani maxubin ruwa na gidan seda ta cika shi tass da ruwa ita kadai ba me temaka mata don da ace kanin ta umar na nan ko kuma yaran layi da zasu temaka mata su dauko mata har kofar gida ita kuma se ta karasa dashi cikin gidan. Bucket dinda take zuba ruwan dashi ne kawai ya rage mata, gabadaya ji take kamar ana caccaka mata wuka a gadon bayan ta da kuma kafadun ta, haka nan ta kara daukar kafa ta nufi tuka tukan dake bayan layinsu, da kyar take iya Jan kafafun ta tsabar ciwon da suke mata, a wannan karan tun da taje debo ruwan ta lura da wani matashi dake ta faman bin ta da kallo kamar xe cinye ta, yi tai kamar bata san yana yi ba, chan dai da yaga kallon bexe taimaka masa da komai ba se ya fara bin ta a baya yana fadin  Assalam alaiki seda ta dan firgi ta da Jin muryar sa a bayan ta don bata dauka ya biyo ta ba, ganin da gaske fa bin ta yake kuma ba shida niyar dena bin nata ne ya sanya ta kara saurin ta shiko be dena bin nata ba sema kara nasa saurin da yai don kada ta bace masa, ayy garin sauri bata kula ba tai tintibe da dutse se ji kake  shaar ruwan ya malale a kasa, da sauri saurayin yace  subhanallah, sannu baiwar Allah, sannu ina fatan dai baki dai ji ciwo ba ko? Sannu nasan ni naja kika fadi sannu ya fada a daburce yana me daga bocket din, ay bata san sanda ta furta kalmar  na shiga uku ba tana me daura hannayen ta a bisa kan ta bayan tayi tozali da fashasshen botikin ammah wanda take bragging akan cewa tunna auran ta ne, wasu hawaye ne suka shiga bin cheeks din ta ba kakkauta wa, da sauri ta amshe bucket din daga hannun sa ta mike da sauri tabar gun ko ta kan jikin ta da ya baci da ruwa da kasa batai ba tai saurin barin gurin tana share hawanyen dake fita ta cikin idanun ta.


Wane ne Omair Suraj?
Me yasa komai a kansa yake da tsauri haka=???

Anya baza mu hada kudi mu biya ammah bucket din auren ta ba =???

Wait!!! Wai ni kadaice nake son wannan kawar yasmin din saddiqa =?)?d'?
Da alamu itace zata ringa sata akan hanyar daidai lol =??& .


INUWAR KADDARA

BY moon
Chapter 4: The price of a broken bucket&


Tafi minti 10 nan tsaye bakin kofar gidan tana ta faman xubda kwalla,  uban me kike yi anan? Tsabar firgita da jin muryar ammah se da tai taga taga zata fadi, karaf idon ammah ya sauka kan fashasshen bucket din ta, wani ashar ta mulmulo tana bin yasmin din da kallo, in ta kalli bucket din se ta kalli Yasmin din, murya na rawa yasmin tace  ammah wlh- ban-ban sani ba- wlh kus- ay bata bari ta karasa ba ta figo ta cikin gidan, kasancewar yasmin din bata da wani kiban kirki hakan yasa gabadaya ta afka cikin gidan, reshan bishiyar dirimin dake tsakar gidan ta karyo ta shiga lafta mata a ko wani sashi na jikinta, tun tana kukan me sauti tana rokan ta akan da ta yi hakuri har muryar ta ta disashe, su twins da suka tashi daga bacci se kuka suke kamar ransu ze fita cikin gwarancin su suke fadin  ammah yaya a a ko ta kansu bata bi ba se da ita kan ta taji ta gaji da dukan nata sannan ta cillar da reshen da ya fatattake a kasa, in banda sheshekar kukan ta ba abin da kake ji,  wannan ma kadan nai miki wlh, banza kawai, ni zaki dora wa hawan jini? To wallahi kan ki doran se na kashe ki a gidan nan, zaki tashi nan gun ko sena xo na kara miki? ta fada tana me kokarin karyo wani reshen, ganin hakanne ya sanya ta mike wa da sauri ta shige dakin su ta zauna nan kasa tana cigaba da kukan xuci. Gabadaya ko ina na jikin ta ciwo yake mata ga wani irin mugun ciwo da kanta ke mata, sosai jikin ta yai zafi kamar garwashi, ji take kamar cikin fridge aka cillata tsabar sanyin da take ji, hijab din ta tai amfani dashi gun rufe jikin ta ammah kamar bata saka komai ba don ji tai kamar ma sanyin kara mata akai don haka ta sanya hannu ta janyo wani tsohon bargonta ta yafa a jikin ta, duk da bargon ba shida wani kaurin kirki ammah ta dan ji dama dama da ta lulluba da shi, tana cikin wannan halinne taji muryar su hafsa da umar a tsakar gida, da sauri ta mike zaune gamida cillar da bargon can gefe guda, sam bata son yaran su tashi suna ganin bakin mahaifiyar su don haka bata taba nuna masu cewa mahaifiyar su is doing bad or something similar to that ba, umar ne ya fara shigowa kamar an jefo shi, yana ganin ta ya nufe ta da sauri yana fadin  yaya sannu da gida, Ashe kin dawo tun daxu da kyarr ta iya furta  yauwaaa umar ya makaranta? Ta tambaya tana faking smile din ta gamida kai hannun ta kan gashin kansa ta cire masa wani zare, dan rike hannunta yai da niyar yaga me ta cire, da sauri yace  kai yaya, kin ji jikin ki kuwa kamar ruwan zafi bakida lfy ne? Ya tambaya looking so disturbed daidai nan itama hafsa ta shigo dakin tare da su twins da suke ta kuka akan se ta basu akori kishiyar da ta taho dashi daga makaranta, duk da dakin da dan duhu ba shi ya hana hafsa ganin shatin bulala kwance a gefen fuskar yasmin din ba, tsayawa tai cak tana kallon er uwar tata, ganin duk ya damu ne ya sanya ta fadin  ummm dan zazzabi nakeyi ammah yanxu ma na warke kamar zeyi kuka yace sannu yaya bara In dauko miki maganin ciwon kai a dakin abby ya fada yana me kokarin mikewa, da sauri yasmin tace  a a ka bari in an shiga sallah magrib ka dauko yanxu dai ka je ka cire uniform din ka  toh yaya yana fadin haka ya mike ya fara yin abun da ta saka shi yi, se a time din ta maida kallon ta kan hafsa, hada ido sukai da sauri ta ce  kukan me sukeyi ne? Ki shigo dasu ciki mana hafsa kin tsaya bakin kofa kuma magriba tayi uffan hafsa bata ce mata ba se taso kan su twins da tai gaba suka karaso cikin dakin. Labari umar ya tsaya basu na dan wani Islamiyyah su da yaiwa malamar su rashin kunyaa aka zane shi, gabadaya hankalin yasmin baya kan labarin don ji take kamar ana sa guduma ana farfasa kashin ta tsabar ciwon da take ji a jikin ta, a hankali take saka hannu tana goge hawayen dake gangaro mata ba tare da ta bari sunyi noticing ba, a haka har aka kira sallar magriba umar ya fice domin yin alwala, hafsa ce kawai ta dawo don umar ya tafi masallaci yin sallah, zama tai nan kusa da yasmin da duk ta fara fita hanyacin ta, dafa ta tai ayko nan take ta firgita don a tsora ce take sosai, ruwa da paracetamol din da ta dauko ta aje kafin tace  sannu yaya nice, tashi misha maganin kafin ammah ta fito daga daki jin hakan ne ya tabbatar mata da cewa sneaking tai ta dauko ruwa da magani ba tare da ammahn ta gani ba, a hankali ta amshi ruwan da maganin ta watsa a bakin ta tana yatsine fuska, ita dai hafsa se binta take da kallo kawai don sosai take matukar tausayi da kuma kaunar sistern nata. Da kyar ta samu tai sallah saboda wani jiri da take gani, Sam taki yarda ta kwanta duk dan kada ta kara jama kanta wani bala in, gashi tun daxu take son taje gun abbyn ya shima kuma tsoro ya hanata yin hakan. kamar a mafarki tajiyo muryar ammah daga can tsakar gida tana fadin  uban wa kike jira ya daura duramen tuwan ehh firgit ta tashi bayan ta gazgata cewa ba mafarkin take ba gaskiyane, da kyar ta samu ta daura dumamen tuwan don kanta kamar anan buga mata guduma haka take jin sa, ko da ta gama ta xuba wa kowa sannan ta kai dakin abby dake bacci, aje robar tai can gefe sannan ta fice daga dakin ta koma nasu dakin ta kwanta, Sam batai gigin dibar abincin ba don dama duk sanda ta sake ta danyi laifi to tabbas ba ita ba cin abinci a gidan nan. Duk yadda siblings din nata suka so su shiga daki su bata bincin a dabarance se da sukai ammah maman su ta hanasu. Tabbas yanxu ba iya zazzabi ke damunta ba harda yunwa da ta addaba ta, a hanakali ta kai hannunta cikin aljihunta ta laluba biscuit din da ta taho dashi dazu, hannunta har wani shaking yake tsabar yunwa, da sauri ta fara afawa a bakin ta kamar wani yace xe kwance mata, wasu hawaye ne suka fara bin gefen idanun ta, kuka take so tayi me sauti amma tsoron abunda xe biyo baya take, don haka ta saka tafin hannun ta ta rufe bakinta tana kuka marar sauti. A daddafe ta samu ta tasha maganin da taji kamar kara mata zazzabin yai, daren ranar bata samu bacci ba don daga ta kwanta se ta firgita ta bude idanun ta da sauri, se gurin 3:50 ta kwanta, 5:10 kuma kiraye kirayen sallar asuba ya tashe ta. Koda ta tashi tadanji dama dama sedai jikinta har yanxu yana ciwo kamar a time din ake dukan nata. Bata yarda ta koma baccin aa uban ba don bata manta da kashedin da ammah tai mata jiya ba gashi kuma mami tace da wuri za a xo daukar ta don haka ta mikewa a hankali ta tattaro Kayan shimfidar ta sannan ta jona batirin wayarta jikin direct charger, ta janyo hijab dinta ta fice daga dakin. Ruwan zafi ta fara dorawa sannan tai wanke wanke, seda gari ya danyi haske sannan ta shiga share tsakar gidan, tana cikin sharar ammah ta fito daga dakin ta tana mika, da sauri yasmin ta zube kasa gamida sunkuyar da kanta tace  ina kwana  aje sharar nan ki hada kunu ki kai dakin tsohonki tana fadin haka ta shige dakin su don taso su hafsa dake bacci don time din shida har ta dan gota. Koda ta shiga dakin baban nata kwance ta ganshi kamar kullum ya kurawa sama idanu, gaishesa tai kafin ta aje masa kunun a gefensa,  zaunar dani ya fada yana me yun kurin mikewa zaune, da taimakon ta ya samu ya zauna, ajiyar numfashi yai kafin yace  yasmin! A hanakali ta amsa masa tana me kallon gefe guda don bata son yaga hawayen dake makale a gefen idanun ta, cikin rarraunar murya yace  Ina me takaici da bakin cikin ganin ki a haka, tabbas kaddara ce ammah harda sakaci na, tun ina raye kenan na kasa baki kulawa yadda ya dace what if yau aka ce na fadi kasa matacce me ze faru? Sam banida maruba da babu, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ya fada yana me rintse idanun sa, share hawayen da ya gangaro mata tai nan take taji wani zafi don gun ciwo yake mata sakamakon marin da ta sha a gun, Murmushi tai kawai sannan tace  kasha karya huce bara naje na gama ayki na tana fadin haka ta mike da sauri ta bar dakin tana Jin xuciyarta na mata ciwo, a haka ta samu ta karasa aykin ta na yau da kullum Banda yiwa kannen ta wanka don yau ana sanyi sosai kuma suna mura. karfe 8:50 habu yace ta fito ya kusa karaso wa, kamar jira take nan da nan ta mike ta saka blue black din hijab dinta daya haska fatar ta, har ta xo fita daga dakin se kuma ta koma don kallon fuskar ta a mudubi, se data tsorata da ganin yadda fatarta yai jawur ga gefen fuskarta da jini ya dan kwanta, da sauri ta dauke idanta kan mudubin gamida rufe gefen fuskarta da hijab dinta, daga nan kuma ta fice daga dakin bayan taiwa kannenta sallama, a bakin kofar dakin abbanta ta tarar da ammah ta baje takardun kudin adashi tana baza lissafi, jiki ba kwari ta nufi dan nesa da ita ta tsuguna kafin tace  na tafi a zafafe ammah ta dago tace  Ammah kedai anyi sha sha, to uban me zan miki ehhh?? Goyaki zanyi ko me? gashi saboda sakarci kin batar dani a abunda nake, zaki tashi ko se na daka ki da safen nan? Ta fada tana me yunkurin mikewa, ay da gudu ta mike ta fice daga gidan, tafiya take tana haki don seda ta je karshen layinsu sannan ta daina gudu don tasan tsaf zata iya biyo ta harnan taci ubanta don Sam ita bata rena abun duka. Tun daga nesa ta fara hango wata kamar saddiqa a kofar gidan su, seda ta matso kusa da ita sosai sannan ta tabbatar da cewa itan ce, saddiqar ce da kanta ta karaso gun nata kafin tace da ita  tun dazu ina nan ina jiran wucewar ki, ammah Shiru, ga ajiyarki hannu yasmin ta saka ta amsa tana yi mata godiya kafin tace da ita  har yanxu ba ai replying email din ba koh?  Ehh fah ina ma ta duba wa ammah Shiru ko in baki wayar ne in yaso if sunyi seki wuce ki kai masu? Saddiqa ta fada tana me mika mata wayar, da sauri yasmin ta girgiza kanta kafin tace  a a ba ayi haka ba in an yi replying kawai kya kirani sena wuce na kai Sam saddiqa bata so hakan ba se dai tace da ita  to shikenan duk yadda kike so ta karashe maganar tana dan tsira mata idanu, ganin hakanne ya sanya yasmin din saurin cewa  toh zan tafi se anjima da sauri saddiqa ta riko hannun ta tace  me zan gani haka? Kinga yadda face dinki ya canza launi kuwa? Allah ya isan ki Wallahi, me kika mata

4 / 14