INUWAR KADDARA BOOK COMPELET BY MAIMOON

Author :  Maimoon Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 14

30K to 33K   out of 40K words

ta na dukan uku uku. Guraren karfe 1:15 yasmin na zaune kan daddumar da innah ta aro masu gun ahalin wannan tsohon tana laxumi bayan ta idar da sallah se ga doctor sambo nan ya xo duba abby shi da wasu nurses guda biyu, ko daya gama yai ma abby ya jiki sannan ya juya dan barin gun, inna ce tai saurin dakarar da shi da fadin  dakta yaushe wannan dan albarkan ze xo ne? Wallahi ka ganmu nan duk shi muke jira ya xo mu kara masa godiya ammah kaji sa shiru ta fada tana yake hakoran ta da suka ga duniya, Murmushi dr sambo yai kafin yace  wai doctor hakeem? Inna tai saurin noddding head din ta ya yin da yasmin ta kara baza kunne tana jiran ta ji me dr sambo xe ce,  ayy iya laraba da alhamis kawai yake shigowa nan asibitin don a asibitin mahaifin sa yake ayki a ragowar kwanakin ammah dai zaku iya ganin sa ya xo nan din if Allah ya nufa yana gama fadin hakan ya bar gun suma nurses din suka rufa masa baya. Haka kawai ta tsinci kanta da bacin ran da bata san dalilin sa ba, guraren bayan la asar suna shirin komawa gida kwatam suka jiyo sallamar sa, dago kai yasmin tai da sauri ayko suka hada ido ya sakar mata murmushi iri tai kasa da kanta tana Jin heart din ta na beating very fast gefe guda kuma tana Jin farin cikin da bata aan dalilin sa ba, se bayan da suka gama gaisa wa da su innah sannan tace da shi  ina wuni ba tare da ta kalle sa ba, amsawa yai cikin sakin fuska kafin ya maida duban sa kan abby dake kwance yace  baba munyi magana da doctor sambo yace gobe za a sallame ka se kima yau shiruu yana me adduar Allah ya sa ya yarda da abinda ya xo masa da shi din dan ya kula yasmin gun mahaifin ta ta gado natsuwa da kuma tarbiya gabadayan su idanun su na kan hakeem banda yasmin dake wa sa da fingers din ta ammah kunanta na jiran jin zancen sa, se da ya tattaro natsuwa sosai kafin yace  a asibitin da nake ayki akwai foundation din da suke kula da masu lalurar stroke, in ba damuwa baba zanso ka amince ay transferring din ka xuwa asibitin don kula lafiyar tsitt kake ji, kowa na mamakin abin da hakeem din ya fada, with shock yasmin ta dago ta kalle sa, he looks so serious, ta kula ba wai don son da yake mata kadai ya sanya yake wa familyn ta hidima ba kawai dai yana yi ne don Allah, da kyar abby ya iya fadin  bawan Allah baka sanni ba ban sanka ba duk da dai ance na Allah basa kare wa ammah wannan dawainiya tayi tayi yawa, i think stroke is my destiny zan cigaba da adduah da kuma godema Allah har sanda zan koma masa kai kuma Allah yai maka albarka abby ya fada da muryar sa da bata wani fita sosai, yasmin batai mamakin Jin abinda mahaifin ta ya fada ba don ta san halin sa baya son daurawa kowa nauyin sa,  haba malam kai kanka baka Jin dadin yanayin da kake ciki zaka ce a a? Kadai duba ka gani wannan bawan Allah ya xo zai taimaka ammah kuma kace a a ay be yi dadi ba abun ammah ta fada cikin tausasa muryar da yasmin bata taba ji tayi amfani da shi ba, nan su innah ma suka saka baki da kyar abyy ya yarda da bukatar hakeem all in the name of be son ya wahalar da shi. Se da ya tabbatar basu bukatar komai sannan ya mike ya bar gun yana ma abby Allah ya kara sauki. hakeem be kira ta ba se bayan sun koma gida sannan, ko da tai picking call din rasa abun fadi tai dan bata ma son ta Ina zata fara masa godiya ba, tsaf ta gane cewa ba wani foundation ya dai hakan ne don ya taima ki abbyn,  hello your majesty? Muryarshi me dadin sauraro ya daki kunan ta, a hanakli tace  mun gode sosai Allah ya biya ka da gidan aljannah se da hakeem ya numfasa kafin yace  jasmine ki daina mun godiya, I did dis all because of Allah kinji? Allah ya bama abby lfy a hankali ta furta  ameen, toh kaima Kace ameen da adduar da nai maka Murmushi ya saki me sauti kafin yace  ameen ya rabbi jasmin daga haka yai mata sallama dan yana da patient din da zai yi attending. Washe gari asabar akai discharging abby, ranar Monday kuma ya koma hospital din su hakeem don duba lafiyar sa kamar yadda hakeem din ya buka kuma har yau be san tana yin aykatau ba don daya tambaye ta mesa ba a taho da ita hospital din ba se tace masa ambar mata jiran gida ne daga haka kuma be kara tamabayar ta ba har abby yai sati guda yana xuwa asibitin tare da kawu lawal. A bangaren gidan mami kuwa yasmin sosai ta maida hankali ta kan aykin ta, duk wani abun da xe sa tai crossing part da omair se da ta dakile shi don tun wancan ranar har yau bata kara ganin sa ba se dai taga giftswar sa.

NOTE: (Ischemic Stroke shine stroke din daya samu Abby caused by a blood clot blocking blood flow to the brain, wanda bai fiya effecting maganar mutum ba shisa Abby ba wani sosai yake shan wahalar magana ba though yana struggling kadan kadan)& .

***********

Soosai sukai sabo me karfi da Hakeem sabon da bata taba zaton cewa zatayi da wani bil adama ba, don duk rashin san maganr ta indai da hakeem ne takan saki jiki sosai saboda he s very kind and well mannered uwa uba kuma ya iya magana. Indai ba ayki take ba toh tabbas tana makale da shi a waya, a halin yanxu komai nashi ta sani shine dai har yanxu be gama fuskantar abunda take ciki coz yasmin tayi phd a iya nuna komai ba komai bane ba don har yanxu be san tana aykatau ba. A bangaren ammah ko bata samun damuwa da ita sosai saboda inna na nan don koma za tai se dai tai a bayan idon innar. Wata ranar alhamis bayan kawu lawal sun dawo daga asibiti shi da abby da a yanxu ya fara samun sauki sosai don yakan iya motsa jikin nasa duk da yana Shan wiya kafun yai hakan wanda likitan dake kula da shi ya sanar dasu cewa baban nasarace daya fara motsakar arm da leg din sa duk da ko yana Shan wuyan yin hakan sabanin da da sam baya iya yin komai kuma baya ji ko an taba part din nasa ammah yanxu Alhmdllh har maganar sa ma ta fi na da fita, all thanks to Allah and Hakeem. Watarana kawu lawal ya sa aka kira ammah, inna da kuma ita Yasmin din dakin abby, bayan sun zauna inna tace  kai lawal lafiya muna cikin zama zakai mana kiran gaggawa haka? Kodai jikin ibron ne ya kara tashi ta karasa maganar tana kallon abby da idanun sa ke a rufe. gyaran murya kawu lawal yai kafin yace  Lfy kalau inna don abun alheri ne ya same mu gabadayan mu Gabadaya suka xuba masa ido banda Yasmin da kanta dake kasa, innah tace  tohh wannan wani abu ne haka iyeeh? Kawu lawal ya bata amsa da fadin  wannan yaro de likita ya same ni yace yana neman izinin fara neman yasaamin in har ba ai mata miji ba, ni ko nan take na ce masa ba ai mata ba kuma nace na bashi dama ko yanxu yake son a daura aure za a iya daurawa don yaron ya burge ni daya mutumtani ya xo ya same ni da wannan maganar ya kuma girmamani ya kuma nuna cewa ni uba ne a gun yasamain, haka shima uban yasaamin din yace shi bashida damuwa matukar yasaamin din tace tana so toh ya bada go ahet ba su inna ba ita kanta Yasmin din tayi mugun mamaki da ya sanya ta dago kai tana kallon uncle din nata coz hakeem beyi mentioning xe aywatar da hakan nan kusa ba though he kept mentioning that he s very serious about her and he want to marry her amma batai zaton da wuri haka ba don dudu basu fi 2 weeks sa haduwa ba. Inna ce ta rangada buda tana me rungumo yasmin din jikin ta gamida fadin  kai Alhmdllh Allah mun gode maka, daman ance me hakuri shi kan dafa dutse ya kwankwadi roman sa, kai madallah Daman Wallahi ina tai wa yasaamin kwadayin yaron nan dan yaron akwai hankali da mutunta na gaba da shi, toh Allah ya tabbatar da alkhairi don wannan hadi ya ma hadu don ita kanta jikar tawa bata ce a a ba don yaron masha Allah son kowa kin wanda ya rasa, ita ma baza ma ta fara cewa a a ba ko yasaamin dita? Ta kare zancan tana kara manno yasmin jikin ta wacce sam hankalin ta be tare da ita coz tama rasa me za tai kuka zatai ko dariya? Da kyar ammah ta hadiye wani abu me mugun daci da ya tsaya mata a makogaro tsabar bakin ciki da takai ci, ko ba a fada mata ba ta san hakeem dan masu hannu da shuni ne don ko fatar jikin sa ka kalla zaka tabbatar da hakan, ta ina ma za ai haka ta faru? Ina ai baze yu ba er kishiya ta auri wannan tsalelen mutumin? kuma da rai na da lafiya na? A a baxe yu ba Wallahi ammah ta ayyana duk wannan abun a ranta tana me hura dan hancin. Kawu lawal ya maida duban sa kan yasmin da duk jikin ta ya gama yin la asar kafin yace  ke! Kinji duk abinda muka fada ko? Ina fatan kema zaki saki jiki ki nuna masa kauna don yaron da gaske yake ba yaudara yaxo yi ba don yace ma nan kusa manyan sa zasu xo shiru yasmin tai don bata san me zata ce ma wan mahaifin nata ba ga idon ammah dake ta mata yawo a jikin ta don kallon ta take kamar zata cinye ta jira kawai take ta ji me zata ce, mikewa tai ba tare da ta ce komai ba ta fice daga dakin, tana jiyo sanda inna ke sakin guda tana fadin  kai wannan abu ya mun dadi dan bakin ciki yau se dai ya mutu kusan 10mins tana rike da wayarta karar ringing tone din wayar ne ya dawo da ita daga tunanin da take, as expected shine ke kiranta, har kiran ya katse batai picking ba and she doesn t know why tai hakan. Gabadaya ta kasa bacci she s feeling a little bit nervous coz se take ganin kamar zaren ba kalar yadin bane ba but still theirs something she s feeling deep down about him something very strange something she have never felt before. Tun da ya kira sau uku yaga batai picking ba ya kyale ta kawai don be son ya takura mata sam.


Washe gari ta shirya da sassafe kamar kullum habu yai dropping din ta a gidan mami, ita tai aykin gidan kaff coz bahar ba tada lfy, tun da ta xo ta kula da yanayin mami kamar ba dadi don tayi looking kamar ita ma bata da lfyn. Tun bayan dawowar omair Nigeria familyn dadyn su omair suka tada bori sosai gami da sako ita mamin a gaba kan cewa ita ta xuga dan nata ya ce ya fasa auren Suhaila, yau wannan ya kira yai mata kalar tasa dibar albarkar gobe wannan ma ya kira yai nasa don sun so ma su xo gidan mamin amma mahaifin suhailan ya tsawatar musu don ya ce shi baxe saka omair ya auri er sa don dole ba tunda yace be so shikenan a hakura Allah ya hada kowa da rabon sa don shi sosai yake respecting feelings din mutane more especially omair da bama ka gane yana son abu ko baya so ba. A bangaren daddyn nasu sosai ya bude ma mami wuta akan cewa ita ta kitsa komai saboda wani manufa nata daban and yace mata komai omair ke yi ita ke sangarta shi, sosai abun ya bata mata rai don maganar su hajja da sauran en family be dake ta ba amman na dadyn nasu ya taba ta coz ta dauka shi ne mutum na karshe da xe yarda da wannan zancan amma se gashi yana cikin masu sukar ta. Guraren 12 lokacin yasmin na blending fresh fruits da bahar ta fada mata tai blending ta kuma yi storing a fridge taji kamar motsin mutum, da sauri ta juya ayko da saurin tai kasa da ido tai don bata son ma tana kallon cikin idon sa me bal in kwarjini, take cikin din ya dauki kamshin turarensa me mugun kamshi, cikin natsuwa ya fara takawa cikin kitchen din hannun sa dauke da mug din da ya sha coffeen da mami ta sanya nazli hada masa, fuskar nan tasa a hade ko kallon inda take beyiba yai dumping cup din cikin sink har cup din na making sound din da ya sa ta dan tsorata kadan, daga haka ya fita daga kitchen din ba tare da ya kara kallon inda take ba. Yana fita ta koma gun cup din ta shiga dauraye wa tana me turo dan karamin pinkish lips din ta don yadda ya tsorata ta ba karamin bata mata rai yai ba. Fitar sa da kusan 3mins se ga mami ta shigo ita da nazli, shirin wani abinci suka shiga yi wanda da ka gani zaka san ba na nan bane ba, ba wanda ke magana cikin su coz har face din su looks so serious, mami ta saka yasmin din ta yanka mata fruits ayko ba shiri ta shiga yin hakan, dining din sama suka kai komai da komai da sukai, mami tace mata kar ta tafi ta tsaya ita da nazli su daura abinci don anjima kadan zatai baki, haka ko akai ita da nazli suka shiga kitchen din suna girkin ba me cewa kowa komai don nazlin ma playing wani Turkish drama tai a ipad din ta while cooking even though ma duk yasmin ce ke yin aykin. Guraren 3 aka xuge gate din gidan, da sauri nazli ta bar kitchen din ba tare da ta bi ta kan ipad din nata ba, kofar parlor ta bude ta tsaya tana kallon mahaifin nata that was on a phone call, yana karasowa bakin kofar ta nufesa tana murmushi da ya kara bayyana kyawun ta,  Ho_ geldin daddy (barka da xuwa daddy) shima ya mayar mata da murmshin gamida da mata side hug sannan yace  Sa ol k1z1m (na gode daughter) daga haka ta matsa masa ya shiga sannan ta amshi dan karamin trolly bag din sa a hannun habu sannan ta kullo kofar parlon. Se kallon ko ina na gidan yake, A haka har suka karasa upstairs inda mami ke a zaune tana jiran karasowar su, mikewa mami tai ta nufi in da mijin nata yake tai ma masa sannu da xuwa ya amsa mata cikin natsuwa, kallon ko ina yake kafin yace mata  where s he?  He s in his room, but would you mind taking shower, eating and resting before you dive into the matter? Coz I could see that you are tired shiru dady yai for some seconds kafin yace  alright then daga haka mami ta amshi trolley din hannun nazli sanan ta ce da ita ta je ta sanar ma brother din ta cewa dad din sa ya dawo. Ko da nazli ta shiga part din na sa ba ta samesa a parlor ba, don haka ta karasa bakin room din sa ta shiga knocking a hankali gamida kiran sunan sa, ta shafe kusan 2mins a tsaye a gun before ta bar gun don ta kula be da niyar budewa, ko da ta koma bata ga kowa parlon ba don haka ta wuce can kitchen in da ta baro yasmin na girki. Har daddy yai sallah yai wanka kuma yaci abinci omair be fito ba shi kuma daddy be kara tamabayar mami ina yake ba, satar jiki mami tai ta nufi part din omair din, ko da ta taba kofar se taji shi a rufe alamun ya saka key ta ciki, nannauyar ajiyar xuciya mami ta sake kafin tace  open the door tana fadin haka ta koma kan daya daga cushion din parlon ta zauna, ayko bayan 40secs se gashi ya bude kofar, kallon sa ta shiga yi sama da kasa, sanye yake da dark brown jallabiya, ajiyar xuciya tai kafin tace  ba zaka fito ka gaida dad din ka ba? Bace komai ba se nufar kofar fita da yai ita ma ta mike ta bi bayan sa, daidai ze murda handle din kofar aka budo kofar, daddyn sa ne ya bayya na fuskar nan tasa a hade wanda sosai kaman sa da omair din ya bayyana, matsawa yai baya sannan a shake yace  welcome bac.. ayy daddy be bari ya karasa ba ya dauke shi da wani marin da nan take fararar fatar sa ta koma jajir, ko hannu be sa a face din nasa ba coz beyi mamakin hakan ba, da sauri mami ta nufi daddy tana fadin  dan Allah ka yakuri, calm down please ka bar da sauri ya daga mata hannu yana huci hakan ya sanya ta yin shiru tana me girgiza ma omair din kai alamun he should not act bad. Da kakkausar

11 / 14