Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : True Hausa Novels
BOOK TWO 2
MATAN AREWA
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________
Page 3⃣3⃣
Magana nake son yi amma sam bakina ya ƙi bani haɗin kai wajen furzo da abinda ke cikina, so nake na farka daga nauyayyan baccin da nake yi da yake haddasa mini wannan mummunan mafarkin.
Shigowar maman Hanan tare da dafa kafaɗana da tayi, hakan ya tabbatar mini da cewar a farke nake kuma a zahiri abubuwan suke gudana ba cikin bacci ba.
"Lafiya Na'ima meya faru?"..
Kukan da ya ɓalle mini ya hana ni damar furta mata komai, illar takardar hannuna da na miƙa mata ta buɗe cike da rawar jiki. Kafin ta kai idanunta ga yaya Yusuf da har yanzu yake tsaye ya bamu baya.
"Yusuf saki kuma? a wani dalilin meye yarinyar nan ta aikata maka?. Duk haƙuri da biyayya irin na Na'ima. Idan ba a cikin hayyacinka kake ba ka gaugauta dawowa domin wallahi zaka yi da-na-sani".
Shuru ya:yi mata ba tare da ya ce ko kanzil ba kafin ya juyo dafe da goshinsa da jijiyoyin kansa suka shimfiɗa raɗau-raɗau bisa goshin. Idanunsa sun ƙanƙance suna zirayar da hawayen da yake sauƙar har saman haɓarsa. Ya fice ba tare da ko kallo mu ba balle ya ce damu wani abu.
Dafe ƙirjina nayi wasu hawayen da nake jin sauƙar su a fatan fuskana tamkar ruwan dalma suna sauƙa, ba kuka nake akan sakin da yaya Yusuf ya yi mini ba. Zubda hawaye nake yi akan ban san me zan ce da iyayena idan suka tambaye ni abunda ya faru ba. Domin ni dai a iya sani na ban aikata masa laifin da na cancanci wannan ɗanyen hukuncin ba, ban aikata masa abunda har zai sanya almakashi ya datse alaƙar dake tsakaninmu ba. Muryar maman Hanan da suka dirarwa kunnuwana suka tilasta mini wartsakewa.
"Kiyi haƙuri Na'ima kiyi addu'a Allah yasa hakan ya zamto alkhairi ga rayuwarki, ya sauya miki da alkhairi".
Da ƙyar na fizgo numfashina cikin sarƙafewar harshe nayi ƙarfin halin faɗin"Anti ni ba sakin bane ya sanya ni kuka, tunda na san ko ba rabuwa ai akwai mutuwa kuma idan ta gifta dole a ɗauki dangana. Amma menene nayi wa yaya Yusuf da zai zartar da wannan hukunci gare ni?, ban taɓa tinanin rana makamancin wannan ba a rayuwar auren mu. Ashe duk soyayya idan zama ya ƙare bata hana datse igiyoyin alaƙa komai jimawar su?, na zama bazawara zan raini cikin dake cikina cikin gidanmu".
Kamar wacce aka tsirawa matsilli na haɗiye kukan da nake yi ina share hawayena, na riƙo hannun maman Hanan da take taya ni kukan na sanya mata sakamakon asibitin haɗi da faɗin"Gashi dan Allah ki bashi don ni ba zan ƙara mintuna biyar cikin gidan nan ba".Na ƙare faɗi ina ƙoƙarin miƙewa taƙi sakar mini hannu.
"Na'ima babu inda za ki yanzu magriba fa ake ƙira ki bari sai da safe, dan Allah yanzu kika je a wannan lokacin za ki ɗaga musu hankali ne".
"Nima hankalin nawan a ɗage yake".
Na faɗa ina fizgewa na fara haɗa kayana, ta kuma riƙe akwatin"Dan Allah Na'ima kiyi haƙuri sai gobe na roƙe ki kinji, kafin nan sai ki sama hujja tunkarar iyayenki idan ya sanar dake laifin da kika yi masa".
"Ba zan tsaya ba ba zan kuma zauna ba. Na zauna nayi masa meye? bayan da idonki kika ga takardan sakin da ya yi mini gidan mu zan tafi".
Na faɗa cikin ƙaraji tare da sulalewa ƙasa ina kuma sakin wani kukan, duk yanda naso daurewa abin ya ci tura. Daga haka kunnuwana suka daina tantance mini zantukan da maman Hanan take yi sai dai ganin bakinta yana motsawa da hakan ya tabbatar mini da magana ta cigaba da yi. Miƙewa nayi na cigaba da haɗa kayana. Kayan sawana kaf na haɗe cikin manyan akwatunan lefena biyu, na saka hijabina na fara fitar dasu tsakar gidan maman Hanan ta kuma riƙe ni "Dan Allah kiyi haƙuri Na'ima ki bari sai gobe kije dan girman Allah na roƙe ki kinji?".
"Raina ba zai daina soya ba, matuƙar ba barin ciki gidan nayi ba zamana ya ƙare cikinsa dole nayi nisa dashi".
Sallamar maman Anwar shi ya dakatar da maman Hanan daga furzo zancen dake bakinta, ko gaisawa basu yi ta shiga tambayar lafiya maman Hanan ce ta iya labarta mata abinda ya faru a taƙaice. Kalmar innalillahi take ta faman nanatawa kafin ta dafo kafaɗata haɗin da cewar"kiyi haƙuri Na'ima gaskiyan maman Hanan ki bari zuwa safiya sai kije wataƙil kafin nan a samu ya faɗi abinda kika yi masa".
"Ba zan iya ƙara koda mintuna biyar a gidan nan ba, dan Allah ku fahimci raɗaɗin da naji a raina".
Na faɗa cikin zubda ƙwalla maman Anwar ta ce to muje gidanta na kwana kafin gobe tunda mai gidanta ya yi tafiya. Ba don naso ba muka tafi gidan natan, alwala kawai nayo nayi salla na kwanta ina jin wani zazzafan zazzaɓi yana neman rufe ni. Ina jin tattaunawar su maman Hanan da ƙyar na iya yin sallan isha'i shima a zaune na kwanta cikin ɗakin maman Anwar.
Tunanika daban-daban suna ziyartar kwakwalwata, a zuci na furta kalma"ya rabbi ya dubi lamarina".
Ko yaya na rufe idona nishaɗantattun lokutan baya da muka ɓata tare da yaya Yusuf da babu komai a cikin su face so, ƙauna, tattali da tarairayan juna da kuwa tsantsan kulawa nake gani. A hankali na shafa ƙasan marata wasu tsiraran hawayen suna biyo gefe da gefen kuncina. Ashe haka ko wacce macen da ƙaddarar rabuwar aure ya faɗa mata take ji?, kuma har masu rangwamen hankali a cikin al'umma suke ganin laifinta?. Haƙiƙa babu wacce zata zaɓarwa kanta shiga cikin irin wannan yanayin face ƙaddara ta zana hakan a gare ta. Ban iya cin abincin da maman Anwar ta kawo mini ba ban iya ko kallon sa ba balle na kai shi bakina. Tabbas ba don bacci ya cika cikakken ɓarawo ba da zai iya ɗauka ta ba, a halin da nake a ciki ba.
Figigi na buɗe idanuna da suka yi mini nauyin gaske, sakamakon maganganun da masarrafan jina ya naɗo mini. Duhun ɗakin bai hana ni hangen mutum biyu turmi da taɓarya haihuwar uwayensu ba, saurin rarumar wayata nayi na kunna tocilanta na manta da yanayin da suke ciki na haske su.
Babu shiri na saki wayar ƙasa har sai da tayi wani ɗan ƙara, ina runtse idanuna tare da kamo duk wata addu'ar da tazo mini. Sam na gaza gaskata abinda na gani domin kuma maman Hanan da maman Anwar idanuna suka gano mini da kai tsaye zan ƙira hakan da mungun gani.
"Wayyo ɗaɗi wayyo ɗaɗi".
Furcin da naji kenan da kunnuwana suka kasa tantance mini muryar wacece daga cikin su, lamau na komar da kaina kan matashin da nake kwance tare da toshe bakina da ɗan kwalina domin gab nake da sakin ƙara. Saboda ba kaɗan ba na ruɗe wani firgici fiye da wanda nake ciki ya kama ni. Gabaɗaya jikina ya ɗauki mazari tamkar ana jona wutar lantarki tun da uwata ta haife ni ban taɓa cin karo da tashin hankali irin wannan ba.
Sumbatun da suka cigaba dayi ya tilasta mini ƙanƙame jikina waje guda, wai daman haka suke fita hayyacin su yayin da suke aikata wannan ta'asan ko meye?, na jefawa kaina tambayar don ko hasken da na haske su dashi bai yi nasarar dawo dasu duniyar zahiri ba.
Can suka koma sauƙe ajiyar numfashi kamar waɗanda suka yi gudun ceton rai.
Tunda ya fice daga gidan ya nufi gidan Anty Binta da ƙyar ya kai kansa cikin gidan kafin ya zube akan gwiwoyinsa, hawayen suna ambaliya a dandamalin fuskarsa. Amir ne ya shiga ɗaki a guje ya sanarwa Anty Binta ga kawu ya shigo yana kuka, a hanzarce ta fito tana faɗin"Kai Yusuf lafiyarka kuwa meya faru?".
"Anti shikenan tayi min nisa shikenan ba zamu ƙara kasancewa a tare ba, ba zamu ƙara zama ƙarƙashin inuwar aure ba. Anti da hannuna na rubuta mata takardan saki". Cikin kuka yake furtawa yana nuna mata dahannayensa, tsugunawa tayi gabansa kafin ta ce"Waye kenan?".
"Na'ima na saki matata".
Taɓe baki tayi tare da zagba masa harara"To Na'imar uwarka ce? da don kun rabu zaka zauna kana wannan kukan, dalla ka tashi kasan inda dare ya yi maka. Mata kuwa zaka samu ko ɗari kake so wanda ma suka fi Na'ima komai".
A raunane ya kallo ta"Tabbas zan samu wata mace, amma ba kamar Na'ima ba".
"Zaka samu Yusuf Allah ya yi maka albarka domin ka faranta min rai".
Shuru kawai ya yi mata domin shi kaɗai ya san yaƙin da ake yi a ƙirjinsa, miƙewa ya yi ya fice baya jin zai iya komawar gidan. Domin bashi da ƙarfin gwiwar haɗa ido dashi a masallaci ya kwana.
Ban iya ko motsawa ba har aka yi ƙiran assalatu a daddafe nayi sallan a zaune. Ban cire hijabina ba na fara jawo akwatina da zummar barin gidan, duk tausa ta da maman Anwar take yi ko kallon ta ban yi ba, taje ta ƙira maman Hanan take na rufe idanuna saboda bayyanar da tayi a gabana. Haka nan naji bana ƙaunar ganin fuskarta balle cigaba da sauraran abina take furta mini da nake jin su tamkar kaɗawar guguwa. Hannu na ɗaga mata a zafafe na ce"ki dakata mini maman Hanan babu abinda za ki ce dani, bayan abinda idanuna suka yi mini tozali dashi daren jiya kin bani mamaki. Idan mai shiryuwa ce Allah ya shirya ku gabaɗaya".
Na ƙarishe zancen ina jefa musu harara ita da maman Anwar da jikkunansu gabaɗaya ya yi sanya ba kamar maman Hanan da har ƙwalla suka wadaci idaniyarta. Akwatina na ja nayi waje, na sama abinda hau na nufi gidan iyayena cike da matsanancin faɗuwar gaba.
Har ƙofar gidan ya kai ni domin na roƙi hakan a wajensa kasancewar bani da ko anini a jikina. Ina sauƙa yaya Majid yana fitowa daga cikin gidan, nayi saurin isa gare shi na ce"Yaya dan Allah ɗari biyu nake so zan sallami mai adaidaita". Duk mamakin da nake hangowa kan fuskarsa bai hana shi zaro mini kuɗin da na buƙata ba. Ina ba wa mai adaidaitan ya tafi bayan ya gama dire mini akwatuna. Har lokacin yaya Majid yana tsaye babu abinda yake yi face bina da ido ta gefen shi na raɓa na wuce cikin gidan a hanzarce saboda kukan dake shirin ɓalle mini.
Sashinmu na nufa na tarar da ƙananan ƙannenmu masu zuwa makarantar primary suna kari ko makaranta basu tafi ba. Umman su Anty Kubra ce kaɗai a tsakar gidan haka nan ita ta fara ganina.
"Ke Na'ima lafiya? da wannan farar safiyar?".
Faɗin hakan da tayi ya yi dai-dai da shigowar yaya Majid ɗauke da akwatina. Maimakon na bata amsa sai ma wani kukan da ya kufce mini, kafin na zube kan ƙafafuna saboda rawar dasu ke suna alamta mini gajiyarwar su ga jimirin ɗaukar nauyin gangar jikina, tausayin kaina da halin Ummata zata shiga suƙa narkar da raunanniyar zuciyata.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 3⃣4⃣
Tunin raguwar matan gidan suka bayyana suna rige-rigen watso mini tambayoyin dake cikin bakinsu akan lafiya menene?. Ban tanka musu ba har Anty Zakiyya da Ummata suka fito tun kafin su ƙariso yaya Majid ya fizgo hannuna tamkar zai fincike mini ita daga jikina, bai dire ni ko'ina ba sai tsakiyar ɗakin Umma ya wantsilo ni. Ya nuno ni da yar manuniyar ƴatsarsa"wai ba magana ake miki ba? kin yiwa mutane banzan. Meya faru meya fito da ke daga gidanki da wannan farar safiyar?".
Shuru nayi masa ina sheshsheƙar kukan da na gaza samun ikon akan kaina na tsayar dashi, a kiɗime Anty Zakiyya ta ranƙwafa a gabana haɗi da cewar"Na'ima nutsu kiyi mana bayanin abinda yake faruwa, wani ne ba lafiya ko kuma mutuwa aka yi?". Jijjiga mata kaina nayi alamar a'a Umma ta karɓe da faɗin"to menene ya faru?, ina shi Yusuf ɗin?".
"Umma ya sake ni Yusuf ya sake ni".
Na faɗa wani kukan yana turniƙe ni, tare da bankaɗa musu zungureriyar fatar takardan dake ɗauke da saki ukun da yaya Yusuf ya yi mini. Yaya Majid ne ya ɗauka tare da warewa ya fara karantawa a bayyana, tun kafin ya gama Umma ta dafe kai tana tsayar da idanunta a kaina da nayi saurin yin ƙasa da nawa. Don haka nan naji ba zan iya jurar kallon tsakiyar ƙwayar idonta mai bayyanar da tsantsan tausayi gare ni ba
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!, saki kuma har uku me kika aikata masa haka mafi muni?".
Yaya Majid ya watso mini tambayar cikin tsananin ɓacin raina, tare da nufo ni gadan-gadan tamkar zai rufe ni da duka. Runtse idanuna nayi jikina yana cigaba da ɗaukar mazari Anty Zakiyya ce ta shiga tsakani ta ce dashi"Dan Allah yaya Majid ka nutsu a bi abun nan a hankali, kar a aikata abinda daga baya za'a zo ana cizon ƴatsa". Dafe kansa yayi tare da cije leɓɓe.
Umma taja numfashi ta fesar kana ta ce"Kaje ka sanar dasu Abbanku, a san abinda za'a yi". Ficewa yaya Majid ya yi domin aiwatar da zancen na Umma. Yana fita na kuma tsananta kukan da nake yi duk tambayar da Anty Zakiyya da Umma suke jeranta mini wani na bin wani ban tanka musu illa kukan da nake yi, na kifa kaina akan cinyar Umma tana bugguga bayana a hankali cikin sigar lallashi da tausayawa.
Babu jimawa yaya Majid ya dawo ya ce muje sashin hajiya Babba su Abba ma duk suna can. Da ƙyar na miƙe saboda juwan dake ƙoƙarin jefar dani, sai da Anty Zakiyya ta riƙe ni muka fito, taf filin tsakar gidan cike da matan gidan da ƴaƴansu ƙwan su da ƙwarƙwatan su. Koda da ban ɗago idanuna ba tabbas jikina ya bani duk idanunsu na bisa kaina.
Muryar Daada naji muna daf da ficewa daga sashin namun tana faɗin"Umman Na'ima lafiya kuwa?, tun safe Na'ima tazo gidan nan duk nan babu wanda hankalinsa yake kwance. Musamman ganin halin da ta shigo cikinsa. Kuma yanzu kuna ƙoƙarin fita ba tare da kun sanar da mu komai ba".
Sauƙe ƙatuwar numfashi Umma tayi kafin ta ce" ba komai Umman Abasiya bari muje Abbansu na ƙira".
Daga haka muka fice izuwa sashin Hajiya Babba. Abba, Baba da Baba ƙarami muke iske zaune suka amsa sallamar da Anty Zakiyya tayi suka kafe ni da ido har muka zauna a sanyaye duk na gaishe su.
Suna amsa a taƙaice haka nan ma Hajiya Babba, takardan sakin yana hannun Baba ƙarami yana karkaɗa ta a hankali ya dube ni ya ce"Na'ima mun wayi da gari da wannan baƙar takardan da Abdul-majid ya kawo mana ita, mai ɗauke da saki uku da mijinki ya yi miki. Menene ya faru tsakanin ku har ya yanke dukkan alaƙar dake tsakanin ku?".
Rawa jikina ya fara sanin da nayi ni kaina bani da amsar tambayar Baba ƙaramin. Kuma nima zan so na san laifin da na aikata masa da na cancanci wannan hukuncin, Maganar da Hajiya Babba ta fara yi shi ya katse ni daga karatun wasiƙar jakin da nake yi.
"Takwara sanar damu meye faru? kama ki ya yi da cin amanarsa ko kuwa menene?".
Kaina kawai na jijjiga mata kafin nayi jarumta raba tsakanin haƙwarana da suka manne da juna na ce"Hajiya babu ko ɗaya nima kaina ban san mena aikata masa da na cancanci haka daga gare sa ba, a lokacin da ban yi tsammani ba. Abu ɗaya na sani shine ya canja mini ya canja daga malam Yusuf ɗin da na aura ya koma wani daban. Nayi haƙuri da hakan kamar yanda kuka nusar dani muhimammacim haƙuri da nasarar dake bibiye da wanda ya yi riƙo dashi, jiya ya fita kamar yanda ya saba sai dawowa ya yi tun kafin lokacin dawowar sa bai yi ba ya bani wannan takardar. Duk makiyar da nayi masa akan ya sanar dani laifin da nayi masa bai saurare ni ba, matar wansa da muke gida ɗaya da ita ta ce nayi haƙuri na bari sai yau nazo gida tunda lokacin magrib ne".
Shuru ya biyo bayan zancen nawan na ƙarshe, tsawon daƙiƙai goma babu wanda ya ce ƙalla sai can Abban ya yi gyaran murya kafin ya shiga faɗin"innalillahi wa inna ilaihir raji'un!, tabbas kana naka ne Allah yana nashi kuma a ko yaushe lissafinsa shine akan dai-dai. Mu muna nan cike da murnar kammala karatunki ashe abinda Allah ya tanadar miki kenan auren ma lokacinsa ya yi . Da ace saki ɗaya ko biyu ne da an sasanta komai kin koma ɗakinki domin ita ƴa mace kimarta da darajarta bata cika a idon mutane har ma gaban ubangijinta kamar in tana ɗakin mijinta. Amma saki uku kam babu zancen komawa zama ya ƙare don haka kiyi haƙuri ki ƙara haƙuri kuma ki ƙara wani akan wanda kika yi a da. In sha Allah sai kiga Allah ya sauya miki da babban rabo, Allah ya yi miki zaɓi mafi zamtowa alkhairi ga rayuwarki Allah ya yi miki albarka".
Can ƙasan maƙoshina na amsa da kalmar amin, haka nan ma su Umma duk suka amsa kafin Baba ya karɓe zance da faɗin"Haka ne yaya amma dole mu nema shi. Domin muji me tayi masa wannan ai wulaƙanci ne ai tana gata ba daga sama ta faɗo ko rana tsaka aka jijjiga bishiya ta faɗo ba, dole ya sanar damu laifin da nayi masa. Duk haƙurin yarinyar nan a zama dashi amma ya rasa abinda zai saka mata dashi sai saki, bayan canjawar da ya yi da kowa ya sani ko girman da yake bamu a da idan aka kwatanta da yanzu ya yi faɗuwar tasa".
Tabbas furcin Baba ɗauke suke da tsantsan ɓacin ransa game da lamarin, jijjiga kai hajiya Babba tayi tare da riƙo dukka hannayena ta sanya cikin nata kana ta ce"kiyi haƙuri Na'ima ki sanya wa ranki dangana. Zanen ƙaddararki ce hakan wanda babu wanda zai iya goge shi kiyi haƙuri".
Kaina kawai na ɗaga mata, haka suka yi ta aikin lallashina kafin su Abba suka fice yaya Majid ma ya bi baya su.
A nan sashin Hajiya Babba ta ce na zauna, hakan kuwa aka yi na kwanta domin wani sanyin zazzaɓi ne yake ratsa ƙasussuwan jikina yana bi har ta cikin ɓargona yana yawo cikin